Showing 27001 words to 30000 words out of 44162 words

Chapter 10 - Amani Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

19 Nov 2024

233

san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki dauka to ki koma girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa Daddyn ki, ki bashi gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar sa.
I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da bashi da lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa.
Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan ana maganan stroke.
Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah yake son Mukhtar din nan. Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore shi da tuntuni ya kora don gudun bacin ran ki.
To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna lafiya.
My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau, zuciyar ki ta buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara. Ta karasa cikin dariya ta kuma yi maza ta kashe wayar ta. Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi da hawan jinin ta ta ko bugawar zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar. Meye manufar ta?
Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text. Ga abinda ta rubuta mata.
kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch your actions over him, you care too much for him, listen to your heart and understand the actual feelings.
-Yours Hamdy.

Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka, kamar ta yi hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da baa taba yi mata irin sa ba, ta rasa wanda zata ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar? Me zata saurara din banda bugun zuciyar ta dake karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya ta kullum?
Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi fuskar wayar kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai ta samu kan ta tana ma aminiyar ta shaawar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar sa a karkashin mahaifin ta, ta shiga yi ma Amani adduar samun daidaiton raayi da fahimtar juna tsakanin ta da wanda take ganin ya shige gabanta. A ganin Hamida ba wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai wannan Mukhtar din, da tun yanzu yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar zama da Amani da dukkan halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen su na makaranta babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar uwa ne ko sun yi fada ita da kanta Amanin zata zo ta nemo ta su shirya. A ganin Hamida babu mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta. Ta kuma yabawa Mukhtar wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-kala. To amma Alhaji ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa biyayya a kan maganar Alhaji Sadi, yanzu kam ta fi mata shaawar auren Mukhtar yaro dan uwan ta mai halin manya.
Zata dukufa taya Amani adduar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya ta kwarai. Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin ta da nutsuwar ta. Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya.
Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji alwallah zai yi sallah yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada sallah sannan ya shiga ya dauro tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa bace.
Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a gefen gadon Alhaji.
Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in yunwar cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai don kada tace ta gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci.
A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara fidda magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa check up, duk da tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga amfani da wheelchair.
Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su. Yau suka sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj. Rabi taje ta taho dasu daga filin jirgi tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari. Kowa ya zo falo ya jajantawa Alhaji yayi masa sannu da dawowa.
Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin ba, yace kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji asibiti yaje babu lafiya, ya ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da shi.
Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar. Amani tunda ta haura sama ta bar su bata kara saukowa ba.
**** **** ****
Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa Acura, kai da ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka san ba dubiya kadai ya zo ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa gwamnatin sa.
Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da cewa yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura masa, musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da zaka samu Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube ta, amma a zuciyar sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social media, babu lazimi sam babu karatun Alqurani, Amani fa ko addua take son yi sai dai ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta fi ta juriyar tsayuwar dare. A hakan da yake yi ya samu ya rarrage ayyukan kamfani da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude masa ba, ko da yake yanzu ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji ke yi da kan sa a lokacin da yake da lafiya.
Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin. Yana shiga ya ga Alhaji cikin wheelchair a zaune yana kallon talabijin. Alhaji Sadi ya ce Ya salamu sallim, ashe ciwon babba ne haka? Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara? Kai bana jin ma jamiyya zata yarda in tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna tunda ba ni kadai ke da jamiyyar ba.
Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin sannu, sannu yaya jikin naka? Kana iya magana dai ko?
Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai nuna ba, sai yayi murmushi yace ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu, nima na sani, na kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau ne kake mutum gobe zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa a rayuwa ta dana ke neman yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni na dade da janyewa.
Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa diya ta kyakkyawan Future.
Da kyau. In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba zai shafi yarjejeniyar mu ba. Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka, koda tsayar da wannan balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma namijin duniya ne ko daga takun sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka bani auren Amani, yau da shiri na na zo don muyi ganawa ta musamman da ita.
Alhaji yayi murmushi ya ce yadda na fasa takara haka na fasa aurar da ya ta, zan bata yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na aura mata, ko da kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa da Amani yau, ka ji raa yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi kowa farin ciki tunda ba yau muke tare ba na san baka da matsalar da zaa hana ka aure.
Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata. Ina Mukhtar ina tsayawa takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba? Baabzine ne fa!

Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi damar ganin Amani.
Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara korafi Daddy ka san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan? yi hakuri Tafisu, sauko yanzun nan amma kisa mayafi don na san ki da shirme. Kafin ta ce komai ya kashe wayar sa ya barta da mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi? Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima yau ya koya, wato duk inda takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban ta da irin raayoyin sa na akida.
Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado, tana saukowa suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani ta kauce. Haj. Rabi ta ce ji mana? Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba tare da ta juyo ba. Haj. Rabi ta tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin murya.
Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki takaba ko jinya, ni ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika hana shi sallama ta da tuni ya sallame ni. To don uwar ki ke kike aure na da zaki hana a sake ni?
Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani bata taba yi ba sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da kaunarta.
Haj. Rabi ta cigaba da cewa.
idan kin haifu cikin Usman da Jalan yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan kuwa kin ki, in kun ki ji ba kwa ki gani ba. Don wallahi sai na saka masa filo a hanci na karasa shi, ko in saka masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma dole a bani tumunin takaba. Amani bata iya ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji da sauri. Ta fado dakin cikin gigita tamkar an jefo ta.
Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta juya za ta koma. Alhaji ya ce Tafisu bakon ka Annabin ka.
Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban ta a idon Sadi Talle. Ta daga ido tace me kake so a wajena Malam? Alhaji ya soma gurgura kujerar sa mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon.
Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce me kuwa na ke so ban da soyayyar ki Amani? Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa ba?
Amani ta yi kuta, ta ce ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi furfurar banza, ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa ka sa shi a damuwar data kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara shin Katsinar taka ce? Halan bai gaya maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta sayar da yar sa ba? Aikin banza aikin wofi to bana son naka, ko a kafa aka daura min kai zan kunce in zura da gudu Alhaji Sadi ya ce ke mara kunya! Ya ishe ki haka, kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni ina iya auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje. Don haka kada ki sake ki zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan.
Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama. Mukhtar ya bayyana a falon cikin bakaken shirt da wando na NEIMAN MARCUS, sumar nan nannadaddiya ta sha gyara da Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa. Amani na ganin shigowar sa, bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya rufto mata, ga bakin cikin aj Haj. Rabi da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin, ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya kawo mata dauki, kawai sai ta mike ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka mai karfi.
Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a bakin kofar ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa tana kara rike shi, sai ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya saita kan sa. Tsawa ya daka mata ya ce sakar ni nace, bana son sakarci.
Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle. Ka roki Alhaji ya yi min iyaka da su, shi da Haj. Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin nan damar gani na, tunda ya zage shi ya ci mutuncin sa. Alhaji Sadi ya yi tsaki ya tashi ya fice daga gidan. A ran sa yana cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure.
Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta kuka, ta cigaba da cewa ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk wanda ya ga dama amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj. Rabi. Ka rokar min shi ya gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita gidannan ko tana so ko bata so. Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya.
Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin nasa juyawa ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba. Amani ta tsanan ta kukan ta tana cewa ka taimake ni!
Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka kada suka yi jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance, in the first instance ta san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi? Sai don ya zage ta zata zo masa da wasu zantuka da basu shafe shi ba? A fusace ya ce me yasa sai ni? Me yasa sai ni zaki aika na gaya wa Alhaji sakon ki? Baki da baki? Baki fi ni kusa da shi ba? Ko ko ni dan aiken ki ne? Mtsw!
Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta makalkale suna vibrating. Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da Alhaji ya bashi wanda babu nisa zuwa na Alhajin.
Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa akan me ke faruwa da shi haka? Me ke addabar zuciyar sa? Me ke saka zuciyar shi cikin jin zafin Amani, don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi? Shin abinda yayi mata anya ya kyauta tunda yau ta zubar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login