Showing 18001 words to 21000 words out of 44162 words
ran sa, yau wata wadda bata ko kai matsayin mai gugar takalmin sa ba ke zagin sa haka, wai kwambo! Duk ba komi ya janyo masa ba sai zabar barin gida da independent life, an ce kuma a kowanne neman halal akwai challenges, ya cigaba da tuki bai ce mata komai ba.
Ba tun yau ba ba sa ga maciji da Hajiya Rabi, ta fannin ta ba don komai bane sai don son da ta lura Alhaji na masa. Daga Amani sai shi a wadanda bata so ta bude ido ta gani a gidan nan, amma fa bata taba nuna hakan a gaban Alhaji ba. Kullum nuna masa take tana kula da Amani irin kulawar da uwa take yi wa dan ta, tana kuma son wannan yaro nasa mai hankali da amana da kullum yake yabo a gaban kowa.
Shi kuwa Mukhtar ya san wacece Haj. Rabi sanin da ko Alhaji bai yi mata ba, shiyasa kawai ya ji baya son matar, wato ya san tana dan taba yawon barbada a waje don ba sau daya ba ba sau biyu ba ya taba ganin ta a hotels daban daban tare da wani mutum. Kuma har kofar gidan mutumin ya sha kawo ta. Duk da ba zai ce ga hakikanin abinda suke yi tare ba jikin sa yana bashi tarayyar banza ce don Alhaji yana da ciwon suga mai hana lafiyar auratayya.
Yana ajiye ta ya juya ya koma Company, akwai muhimmin aikin da zai yi wa Alhaji amma tun shigar sa office din sa sai ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Mukhtar Diffa, ya hau safah da marwah, hannanyen sa biyu zube cikin aljihun farar shaddar da ke jikin sa. Ya rasa abinda ke tsaye a wuyan sa ya ki wucewa. Ya rasa meye ya tsaya masa a rai. Sai da yayi tsam da ran sa ya fafimci ba komai bane kukan Amani yake tunawa da shagwabar ta, da fyatar hanci cikin yanayin sakalcin ta.
Sai ya ji wasu sassa na jikin sa suna respoding. Zuciyar sa na vibrating. Ya tuna matsananciyar damuwar da ke kwance kan kyakkyawar fuskar ta a kan son ganin mahaifiyar ta, sai ta kwadaita masa son ganin tasa Ummamin shima, kwarai ya gane da gaske take son ganin Maman nata, wasu abubuwan data yi a yau sun tsaya masa a rai, sun kasa bacewa, musamman kukan shagwabar nan nata is arousing something in him komai dakewar sa don bai taba ganin wanda kuka ya yiwa kyau irin Amani ba.
Tsaki yayi cikin jin matsanancin mamakin kan sa, ya dauki kiran Alhaji da ya shigo masa a daidai lokacin. Ya ce Mukhy kana ina ne? Ina office Alhaji ya fada a kasalance. Alhaji ya ce to in ka kammala ka zo zamu yi wata muhimmiyar shawara. Kai bari kawai in gaya maka. Haka kawai ina zaune wani tunani ya zo min, ina son tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina.
Mukhtar ya yi azamar rufe baki sannan ya bude, yana mai jinjina hadamar duniya irin ta uban gidan sa, me Alhaji yake nema kuma a siyasa da rayuwar sa bakidaya? A tunanin sa duk abinda dan adam ke nema a duniya Alhaji Usman ya gama samun sa, kamata yayi ya maida hankali ga kula da tarin dukiyar sa da neman lahira da aurar da wannan gansamemiyar sakaltacciyar diyar tasa, ba neman wani mukamin siyasa ba a yanzu, wand aba lallai yayi nasara ba, a fili ya ce Alhaji bari in zo kawai, wannan ba maganar waya bace.
Yana tafe a hanya yana tunanin ta hanyar da zai bi ya lallashi Alhaji kada ya tsaya takarar nan, ba don komai ba sai don ya san mawuyaci ne alummar Katsina su zabe shi yanzu, don duk wani mukami da ya rike a baya bisa magudi ake bashi ba don alummah na so ba, sai don kasancewar yana da iyaye a babbar jamiyyah masu karfi a gindin murhun, jamaa basa son Alhaji Faskari ne saboda kankamon sa, da rashin jan talakawa a jiki sai ka ce ba dan siyasa ba. Wasu yan jaridar ma kan ce, HON. USMAN FASKARI; dan siyasar da ya rasa dukkan attributes da qualities na yan siyasa amma yana da saa a siyasa.
Mukhy na tunanin karshen ta ya salwantar da dukiyar kamfanin sa a banza, wajen kamfen, kuma ya zo bai ci ba. Mukamin Sanata daban na gwamna daban. Mukamin gwamnatin jiha tabbas sai da soyayyar talakawa.
A sanin sa ko Zakkah Alhaji baya iya badawa, har sai bayan zuwan sa gare shi, shi Mukhtar din, da ya tsaya tsayin daka da lallashi da nasiha a kan Alhajin, bisa dole ya sa shi ya dinga fidda zakka don tsaftace dukiyar sa.
Sau tari, Mukhy kamar shine Ogan Alhaji subordinate, da wuya ya fadi abu Alhaji ya tsallake, don yayi amanna ba zai cuce shi ba, in Mukhy yayi magana akan abu, Alhaji baya iya tsallakewa saboda son da yake masa da yardarm da ya yi masa.
Sanda ya iso gida Alhaji na tare da baki. Ya yi sallama ya shiga falon, Alhaji ya bashi iznin zama, Mukhtar ya gaida hamshakin mutumin dake tare da Alhaji, cikin ladabi y ace da Alhajin yace zan jira a karamin falo kafin ku gama Allhaji no Mukhtar, zo zauna, gara a yi shawarar nan tare da kai, you are part of me, samu wuri ka zauna.
Mukhtar ya zauna bisa kilishi can gefen kafar Alhaji. Alhaji da bakon sa suna kan kujera, Alhaji yace Mukhy, wannan da kake gani shine aminina Alhaji Sadisu Talle, shugaban sabuwar jamiyyar data take tamu yanzu a farin jini wato PRC (Public Relation Congress) da ake wa lakabi da SAWUN GIWA. (ya take na Rakumi). Mun yi shawara da shi zan bar AC in koma PRC don AC bazasu yarda su bani takara ba. Sun riga sun tsayar cewa wannan karon yaro matashi mai jini a jika zasu baiwa takara.
Suna cikin wannan maganar kafin Mukhtar ya furta komai Amani ta sauko daga upstairs da zummar wucewa kitchen (madafi), yunwa take ji, ga mai aikin ta Rakiya ta je kasuwa, sai idanun Alhaji Sadi suka sauka akan kyakkyawa Amani.
Babu wanda ta gaisar a cikin su ta wuce zuwa kofar da zata kaita kicin, shi kan sa Alhajin yau sai da yaji kunyar wannan rashin tarbiyya ta Amani. Sabida matsayin Alhaji Sadi a wurin sa a ce yar sa ta wuce bata gaida shi ba, shi dama Mukhy baya layin ta. Data damo abinda zata sha wato quaker oat da madarar ruwa ta peak tazo zata wuce ta koma sama batare da tace musu uffan ba. Alhaji Usman ya yi jan wuya yace.
Shin Tafisu baki ga Alhaji Sadi Talle bane zaki wuce baki gaida shi ba? Ta zumburi baki, kafin ta ce da Alhaji Sadi din ina yini? Ba tare da ta juyo ko ta durkusa ba, ko jira ya amsa bata yi ba tayi wucewar ta sama.
Alhaji Sadi ya shiga yage baki duk sai ya dabarbarce ya rasa nutsuwar sa, sai mutsu-mutsu da baki yake yi ya kuma rasa abin cewa tun saukowar Amani falon ta tafi da imanin sa, yana tambayar kan sa ina Alhaji Usman ya samo wannan kyakkyawar diya haka? Babu kama ko ta farce shi da ita, ko adopting din ta yayi? Ya rasa yadda zai yi ya tambaya sabida Mukhy da ke zaune ya tsare shi da fusatattun idanun sa don ya gane canzawar sa da rudewar sa tun saukowar Amani. Shi Mukhtar takaici da haushin yadda dattijon ya kwalalo ido da baki yana bin Amani da wani mayataccen kallo har da hadiyar miyau yasa ya mike. Alhaji yace ya zaka tafi Mukhy bamu gama shawara ba? Yace Alhaji ban yi sallah ba ina zuwa. Nan kuwa ko zancen takarar Alhaji baya son ji, balle ya bar jamiyyar sa ta amana wato AC da ya dade a cikin ta ana damawa da shi. Kai shi bai ma yarda Alhaji Sadisu zai sa a bashi takara a PRC ba duk da matsayin sa na shugaban jamiyya, don ya san bashi da farin jini yafi yarda da cewa kudin sa zai ci ya wofintar da shi. Duk da cewa ba yau suke tare ba duk da banbancin jamiyya dake tsakanin su. Abota ce tsakanin su tun ta kuruciya.
Ai Alhaji Sadi kamar jira yake Mukhtar ya bar wurin ya muskuta cikin kujerar sa bakin sa nata motsi yace shin Hon. Usman wannan kyakkyawar diya taka ce ko yar riko ce? Hon yayi dariya yace Amani ce fa, Amani Faskari, ita kenan yar daya jallin jal dana mallaka duniya da lahira.
Sai a lokacin Alhaji Sadi ya hau tuna komai na Alhaji Usman yana bearing wannan sunan ne wato Amani Faskari, bai taba sanin sunan yar sa ne Amani din ba, don bai taba jin irin wannan sunan ba.
Alhaji Sadisu ya shafa gemun sa da sajen sa yana murmushi yace ai kawai Hon. Ka ce ta zo gidan sauki tuwo na mai na, abu nawa maganin a kwabe ni. Ka bani auren ta ni kuma na maka alkawarin kujerar gwamnatin Katsina sau biyu, ko ana ha maza ha mata sai ka yi.
Hon. Usman a matsayin sa na uban da bai taba jin wani ya tare shi yace yana son Amani ba, saboda kowa cewa yake tafi karfin sa saboda izzar ta da irin rainon da yayi mata, sai ya ji dadin maganar kwarai, ya ga cewa tabbas Alhaji Sadi zai iya da Amani ba tare da yace tafi karfin sa ba shi, tunda in dukiya da mukamin siyasa ne da take takama yana da su ne shima Sadi a cikin su yake dumu-dumu har ya dara shi komai yanzu, in ka dauke yawan shekarun sa da suka zarta nasa, da furfurar data soma samun muhalli tsilli-tsilli a saman kansa, sai ya ga cewa zai iya bashi auren Amani muddin zai taimaka masa ya zama gwamnan jihar su.
Babban burin sa na yanzu kenan wato zama gwamnan jihar Katsina.
Alhaji Sadi bai bar gidan ba sai da suka kulla yarjejeniya a rubuce da shi da Alhaji Usman cewa zai tsaya masa a matsayin sa na shugaban jamiyyar PRC a bashi takarar kujerar gwamna shi kuma kafin nan ya aura masa yar sa Amani.
Ya so a yi maganar nan a gaban Mukhy, amma Mukhtar din tunda ya zame da sunan zai je yayi sallah ya ki dawowa.
Haka kawai ya kasa jure mayataccen kallon da Alhaji Sadi ke bin Amani da shi, kuma in zaa kashe shi bazai ce ga dalili ba. Shi kawai yana ganin ba girman Alhajin bane.
Basu kara haduwa da Alhaji ba sai washegari. Lokacin da Alhaji ya gaya masa yarjejeniyar da suka yi da Alh. Sadi washegari suna hanyar zuwa ofishin Alhajin, Mukhtar suman zaune yayi.
Ya yarda neman Mulki yana fidda wasu dattijan a hankalin su.
Ina Amani yar shekaru 20 ina tsoho dan shekaru 65 banda kwadayin Mulki da neman sa ido rufe irin na Honourable Usman? Kai bama wannan ba wani dunkulallen abu ne ya zo ya tokare shi a makogaron sa ya kasa cewa Alhajin sa komai, sai kawai ya maida hankali ga tukin da yake yi zuciyar sa na wani irin bugawa fat-fat.
Alhaji Usman yace baka ce komai ba Mukhy, ko shawarar tawa bata yi bane? Na san ka da tsinkaye, amma nima ina da amfanin da zan samu a cikin auren, ai wato komai mutum zai yi a rayuwa yanzu ya fara hangawa ya auna ya gano ribar da zai samu a cikin sa.
Kaga in ya auri Amani zai taimakamin na zama gwamna, zai tsaya min kan duk mai son taka ni a jamiyya, abinda na tsara shine sai in nada ka mataimaki na amma ko shi ban gayawa hakan ba, ka nemo mata kayi aure kai ma mu tara dukiya iyakar tarawa, mu Mulki Katsina tare, mu ci duniyar mu da tsinke, amma na yi rantsuwa ba mijin da zai ci min dukiyar Amani, don ita na tara mawa, komai nata zai koma karkashin kulawar ka da amanar ka ko da ta auri Alhaji Sadi.
Hatta kayan daki ka ga ba sai mun yi mata ba gidan Alhaji Sadi duniya ne; babu abinda babu cikin sa. Kudin komai dana tanada don auren ta sai a kara jari dasu a boutique din ta ka ga dadin auren mai akwai kenan.
Gashi babu mace yanzu tare da shi tun rasuwar uwar yaran sa bai kara aure ba, yaran bakwai duk sun manyanta, biyar daga ciki sun yi aure. Don haka Amani bazata yi masa rainon yara ba. Ya ka gani?
Mukhtar Diffa dai ya zama mutum-mutumi a zaune. Tuki kawai yake ya rasa amsar da zai baiwa Alhaji. Bai san cewa ya bar hanyar da zata kai su company ba ya dauki wata daban da bai san inda zata kai su ba, har sai da Alhajin ya ankarar da shi, sannan ya koma da baya ya dauki hanya daidai.
Da Alhajin ya takura sai ya ji ta bakin sa sai ya ce ni me zan ce Alhaji? Banda Allah yayi zabi mafi alkhairi?. Tunda kun riga kun rubuta yarjejeniyar a rubuce ai bani da say. Kome zan ce is too late.
Sai dai naso ace Amani din da yardar ta aka zartar da komai. Saboda ina tsoron maka halin yaran zamani, kada ta baka kunya Alhaji. Yaran yau baa sha musu alwashi irin wannan.
Shima sai a lokacin yayi wannan tunanin na cewa ba lallai Amani ta yarda ta auri Alhaji Sadi ba in aka yi laakari da yawan shekarun sa.
A sanin da yayi wa Amani bata taba nuna tana shaawar a yi mata aure ba, tafi shaawar cigaba da rayuwar ta cikin hutu a gidan su, cigaba da tabara da wadaka da dukiyar mahaifin ta, ta hanyar yin kwalliya ta kece raini da sanya sitturu masu karshen tsada da hawa duk kalar motar data ke so wato yawan canza mota new mdel duk shekara, burin ta kenan.
Rana daya azo a ce an bada auren ta ga tsoho abokin baban ta don cimma wani kuduri na siyasa, abin zai zo mata banbarakwai, shima ya san ya daukowa kan sa Dala babu gammo. Dama Amanin ga ta nan ga kamar ta wajen hankali da tarbiyya.
Har suka iso ofishin Alhajin babu wanda ya kara magana a cikin su, Alhaji na cikin taraddadin yadda zai fuskanci Amani da maganar. Mukhtar da ke tuki na kokawa da numfashin sa dake faman kai kawo a tsakanin kirji da zuciyar sa.
Kwana biyu a tsakani Alhaji na ta nan nan da Amani, ya rasa ta inda zai bullo mata da zancen Alhaji Sadi, ya tuna lokacin canza motar ta yayi bari ya nemo motar da take mafarki in yaso yace mata Alhaji Sadi ne ya kawo mata a matsayin goron na gani ina so, ga Alhaji Sadin ya takura yana so ya bashi izni ya fara zuwa zance. Ya san in bay a yi da gake ba zai sha kunya idan Alhaji Sadi ya tare ta da zancen kafin shi. Don haka yau dai yayi kundumbala ya kira Mukhtar falon sa.
Suka zauna shi da Alhajin cikin dakin sirrin Alhaji, Alhaji Usman yace Mukhtar na yi abinda ya zo ya dame ni, har yanzu na kasa gaya mata zancen nan, jiya ta zo min da admission na son tafiya karatu a jamiar Queen Mary, ta ce tana so in yi mata iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta inda zan bullo mata.
Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce Alhaji Amani yar ka ce, me yasa kake shayin ta? Hakan bai dace ba ko kadan Alhaji yace rikicin ta nake tsoro, baka san ta bane, wanizubin kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta take komawa, bana sanin ta ina zan shawo kan ta. Mukhtar na so ya ce ita siyasar dole ce da zaa saida farin cikin ya domin ta? A fili kuma yace Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da ita ka gaya mata hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta fahimta tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi biyayya, zan taya ka tausar ta.
Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo takardar sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce Tafisu na ji kina korafin injin motar ki yana kara, nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya. Amani ta karbe mukulli da murna tace My Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini kai Baba na yace ai yau kyautar ba daga ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko? Wannan abokin nawa da yazo satin da ya wuce?
Amani ta ce ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo,