Showing 33001 words to 36000 words out of 44162 words

Chapter 12 - Amani Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

19 Nov 2024

237

saboda takamar yana da fada a wurin ka.
Tana gama fadin haka ta juya ta bar wurin da gudu-gudu, sauri-sauri babu inda ba ya kyarma a jikinta saboda dimauta.
Mukhtar kuwa komawa ya yi tamkar mutum-mutumi a wurin, ko kwakkwaran motsi bai iya ya yi ba. Haka ya kasa dago kansa da ya sunkuyar saboda kunya. Ga mamakin sa sai ya samu kansa da jin kunyar Alhaji mai tsanani. A can wani sako na zuciyar sa kuma ya samu kan sa da jin dadin wannan tayi da yayi masa. Shi ma ya san ba ya kyautatawa Amani yadda duk maaikatan Alhaji ke mata, haka ba ya bata respect din da maaikata suke bata, kullum jin kan sa yake sama da ita, ba ya yarda da subordination, shi mutum ne da ba ya yarda da raini ko kaskanci, wannan kuma a cikin jinin sa ne na iyaye da kakanni.
Maganar aure da Alhaji ya yi yanzun kuwa tsakanin sa da Amani sai ta kashe duk wani kuzarin sa, ta jefa shi a wani yanayi da bai taba shiga ba na zurfin tunani da mutuwar jiki.
Maganganun Amani wadanda suka zamo raddi ga mahaifin ta, kuma zagi a gare shi ko kadan ba su dame shi ba. Fassarar da ta dade tana yi masa a zuciyar ta ne yau Allah ya matsi bakin ta ta fada a gaban sa.
Da kyar ya iya mikewa tsaye lokacin da Alhaji ya ce ya tura shi a kujerar sa ya maida shi falo ya huta.
Har suka yi sallama da Alhaji, bayan ya bashi magungunan sa na yau ya sha, Mukhtar sanyin jikin sa da bugun zuciyar sa basu koma daidai ba. Da kyar ya iya takawa zuwa gidan sa wanda bai da nisa da gidan Alhaji. Ko motar sa a gidan ya bar ta don ya san ba zai iya tuki ba.
**** **** ****
MUKHTAR
Mukhtar ya yi kwance a tsakiyar lallausar gadon sa yana sake tariyo maganganun ubangidan sa Alhaji Usman Faskari, kauna ce zallah ya nuna masa wadda babu algus, kuma wani bare bai taba yi masa irin ta ba, kuma bai taba samun kwatankwacin ta ko daga iyayen sa da suka haife shi ba.
Ya soma laluba lungu da sako na zuciyar sa don son gano stand din da ya ajiye Amani, a zahirin gaskiya wannan yarinyar ba tun yau ta ke fizgar zuciyar sa ba, ta dade tana saka shi a faduwar gaban da bai san dalilin sa ba, sai ya bar wa ran sa a cewa kyawun halittar ta da kwarjinin ta ne yake razana shi, yake sanya shi faduwar gaban, kamar yadda duk wani lafiyayen namiji bazai iya kauda kai a kan ta ba ba tare da ya ji zuciyar sa ta motsa ba. Ya sha zama a cikin dare yana tuno wasu abubuwa da suka shafe ta a duk lokacin da wata alaka ta hada su suka fita a mota tare ya kai ta wani wuri, bisa umarnin Alhaji. A irin wadannan lokutan kwana yake da tunanin ta a ran sa. Fitsarar ta, rashin kunyar ta, hararar ta da tijarar ta duk basu bace masa. Ba don murmushi yayi kaura daga rayuwar sa ba da yace wadannan halaye nata duk da baya son su, to fa hakika suna saka shi murmushi a yawancin lokuta. Amani Faskari, tana da babban alamari a tare da shi wanda ya dade da kasa ganewa.
A yau da Alhaji da kan sa ya yi masa tayin auren ta ya shiga rudu, ya shiga dimuwa da tunani mai yawa, wanda hakan ya saka shi tono duk wasu tsofaffin feelings din da ya san yana ji a kan Amani; and he realized for himself cewa ya dade yana son Amani, in dai pleasant feelings din da yake ji a can kasan ran sa a kan ta shine SO, to ya dade yana ninkaya a cikin sa ba tare da ya ankara ba, har sai yau da tayin Alhaji da kan sa ya ankarar da shi, amma kuma halayen ta sun sa ba ta burge shi, kuma ba ya son ko daya cikin dabiun ta. Ya na son ta a kasan ransa a can wani lungu da bai taba dauka da muhimmanci ba. In ba haka ba me ya sa ko kadan ba ya son zancen auren ta da Alhaji Sadi? Me yasa ranar da Alhaji ya gaya masa ya bada auren ta ga Alhaji Sadi ya kasa barci a tsayin daren bakidayan sa?
Me ya sa yake kishin ganin ta babu lullubi (mayafi?) ta fito waje ma'aikata maza na kallon ta, don duk lokacin da ya gan ta babu lullubi a gaban maza sai ya ji zuciyar sa kamar ta tarwatse. Duka wadannan alamu ne na So, don ba a kishi sai da So, sai dai son bai zo a muhallin da ya dace ya zo ba, wato Amani ubangida ce a gare shi, sannan ba ta da tarbiyya da cikar addinin da mutum irin sa za ya so ta, har yayi fatan ta zama uwar yaran sa. Ko ya aura ya kai gaban iyayen sa su karba cikin sauki.
Ya taso a gidan da ba'a san komai ba sai mutumta Dan Adam, tsatstsaurar tarbiyyah ga 'ya'ya maza da mata, gidan rikon addini da dattaku, gidan da dan gida ba shi ne Da ba, gidan da DAN RIKO daidai yake da dan gida har wani lokaci ya fi shi sakewa.
Amani Faskari ta dade da satar wani kaso mai girma a zuciyar sa, wanda zai iya cewa daga Allah ne kawai, ban da haka in kyau ne ya baro mata ma su amsa sunan mata da suka dame ta suka shanye a kyau, dukiya, ilimi da gatan da take takama da shi. Amma babu wadda ta taba saka shi a irin situation din da yake samun kan sa a duk lokacin da ya ga Amani. Something like miracle, (abin kamar karama) tana da wannan boyayyen tasirin a kan sa.
Mukhtar ya shiga ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun, wannan wace irin masifa ce ke neman hawa kan sa? Ya yarda da auren Amani ya yi ya ya da ita da rashin kunya da rashin tarbiyyar ta? Wadda ba ya tunanin ko karatun sallah ta iya daidai. Above all aure a gare shi a yanzu na nufin komawar sa gida, wanda bai taba shiryawa nan kusa ba. In Alhaji ya dage a kan bakan sa na aura masa fitsararriyar yar sa wa zai karba masa auren? Tunda ya san babu kowa nasa a kasar Najeriya? Kodayake Alhaji ya dauka iyayen sa sun rasu ne, shi ya sa ba ya takura masa a kan zuwa gida, duk lokacin da ya ce ya je ya gaida dangin sa zai ce zai je ne ba ya so ya tafi ya bar masa ayyuka da yawa ya sha wahala, har Alhajin ya gaji ya daina masa maganar zuwa ganin dangin sa don ya dauka ma iyayen sa sun rasu.
Yanzu kuwa da Alhaji ya bullo masa da zancen aure sai ya ji wani sako na zuciyar sa yana missing gida, yana kewar Diffa. Sama da komai yana kewar UMMAMIn sa.
***** ***** ****
AMANI
Zamu iya cewa yau Amani dan karamin kwancewar kai ne ya same ta a dalilin furucin Alhaji gareta. Wasu notuka a cikin kan ta ta ji sun kwakkwance tsabar rudanin da mahaifin ta ya jefa ta. Ta nufi cikin gida tana tafiya tana hada hanya, saura kadan su yi karo da Hajiya Rabi da ke kokarin hawa benen Alhaji. Ai kuwa ta bangaje Hajiya sai da ta kusa kai wa kasa don ba ta zaci bangazar ba, duk da ta ga Amanin ta taho a fusace kamar kububuwa, ta ce a ranta, mai yiwuwa ita da baabzinen Alhaji ne, don ta san shi kadai ya tsaya wa Amani a makogaro ta kasa fyato shi. Don ya fi karfin ta a gun Baban ta.
Hajiya Rabi ta dafa bango kafin ta kai kasa, ta ce, Ni ki ka bangaje? Kwaya ki ka sha da ba za ki dinga lura ba kina tafiya kai a sama kamar zakanya? Ai ba ni na kar zomon ba, ko ratayar sa ba a ba ni ba, jairar yarinya tatacciya, mara kunya, goyon namiji.
Amani ta sa kafa zata hau bene kenan, jin abin da Hajiya Rabi ta fada ya kara tunzura ta, da ma ya ya lafiyar Kura? Alhaji ya gama kaskantata da cewa zai bada sadakar auren ta ga yaron sa da ta fi tsana a duniya, wannan annamimiyar kuma ta ce mata goyon namiji? Bari ta nuna mata goyon namiji.
Ta wawuri Hajiya Rabi ta maka da kasa, da ma Hajiyar ba ta da jiki sam, Hajiya ta zuba ihu amma ba wanda ya jiyo ta sai Rakiya mai aikin Amani. Ita ta zo ta rike Amani da ke huci kamar maciji ya sare ta.
Rakiya ta shiga lallashin ta tana fadin, Uwar daki na mai abun alheri, Hajiya babar ki ce, a dinga hakuri, uwar ki ce kamar kowacce uwa tunda Alhaji na auren ta. Ki yi hakuri ki wuce sama, bana so ki karasa gawar da ba taki ba. Ko ba kya ganin babu tsoka a jikin ta? Me za ki dauka in kin dake ta?
Amani ta soma hawaye, wanda ba ta san yaushe suka zubo ba, zafi biyu ne ya tarar mata, ta ce, Rakiya bar ni in zubar mata da hakora don ta fi tabbatarwa ni jaira ce, tatacciya, mara kunya, goyon namiji.
Rakiya ta yi maza ta ce, Wane mutum? Wane ita ta yi miki wannan zagin duk inda alkhairi yake ga talaka kin iya shi, zagin data yi miki ba zai rage ki da komai ba tunda ba ya fitowa a goshi. Kowa ya san albarkacin ki ta ke ci da ta yi wannan dadewar a gidan nan.
Da haka Rakiya ta samu ta lallashi Amani ta raka ta har dakin ta ta dawo sannan ta tada Hajiya da ke kuka tana fadin, yau sai Alhaji ya sake ta kafin mahaukaciyar yar sa ta karya ta a banza.
Tana tashi wurin Alhaji ta nufa, lokacin Mukhtar bai dade da shigar da shi dakin barcin sa ba, shi kuma yayi masa sallama ya tafi gidan sa. Alhaji yana kakkabe filon sa zai kwanta, Hajiya Rabi ta fado dakin tamkar an jefo ta.
Biro da takarda ta dauko ta kawo masa har kan cinyar sa ta ce, Sakar ni, na ce sakar ni, kafin in sa filo in danne ka wallahi. Ka haifi jaraba, ba tarbiyya ba ganin girman na gaba, in sha Allahu ita ce ajalin ka!
Alhaji Usman ya ce, Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Kawai sai ya karbi takardar ya rattaba wa Hajiya Rabi saki. Ya ce, Duk abin da ke sassan ki ki kwashe ki tafi da shi na ba ki, amma tunda ki ka muzanta Amani da mugun kalami irin haka na gama auren ki, da ma ita ta ke roko na in zauna da ke.
Bakin halin ki babu wanda ban sani ba da yawon ta zubar da cin amana ta. A sauka lafiya Umma-ta-gaida-Assha.
Amani da ta shiga daki duk da lallashin da Rakiya ta yi mata amma zuciyar ta ta kasa yin sanyi, sai tafasa ta ke yi abubuwa goma da ashirin, sai kawai ta hada kai da gwiwa a tsakiyar gadon ta tana rera kuka tamkar marainiya. Ko da yake ita da marainiyar da uwar ta ta mutu ta bari tun haihuwa ai ba su da maraba, don ko hoton mahaifiyar ta Alhaji bai taba nuna mata ba.
A yau tana kewar mahaifiya ko yar uwa mace, ko dan uwan da za ta kai wa kukan ta, ko wani babba a dangi da za ta kai wa karar Daddy a kan kasksanci da tozarcin da yake shirin yi mata (a wurin ta).
Aure da Mukhy shi ne mafi kaskancin abin da Daddy zai yi mata da ba za ta taba iya yafewa ba. Kuma ko sama da kasa za ta hadu, ba za ta yarda ba, za ta gudu kawai wajen mahaifiyar ta su neme ta su rasa, za ta cire kudade anyhow ta biya mai yi mata bincike kawai ya turo mata adireshi ta koma wajen mahaifiyar ta. Ta yarda yanzu Alhaji ya fi son Mukhy tsintacce a kan ta.
To za ta bar musu gidan, gabanin bashi auren nata. In yaso Alhaji ya maido Mukhtar dakin ta na gidan sa ya zauna madadin ta karshen kaunar da zai nuna masa kenan bayan ta bashi sadakar auren ta.
Hamida ta fado mata a rai, ta share hawayen ta dauki waya tana dialling lambar Balewa. Duk da ta san maganar Hamida kullum daya ce, ta dinga yi wa Daddy biyayya, yau ta san Hamida ko za ta tsokane ta to kuwa za ta taya ta bakin cikin masifar da ta ke neman tunkaro ta.
Abokin kuka aka ce shi ake gaya wa mutuwa, duk da Hamida ba koyaushe ta ke taya ta kuka ba, wani lokacin ma laifi ta ke ba ta, ba ta iya boye mata komai da ya shafe ta saboda tsananin haduwar jinin su.
Ba jimawa Hamida ta daga waya da sallama, sai Amani ta daddage ta bude murya da karfi ta fashe da kuka mai sauti, don da can mara sauti ta ke yi.
Kafin Hamida ta ce komai, sai da ta fara toshe kunnuwan ta da yan yatsun ta, kada a fasa mata dodon kunne, sannan a hankali ta ce, MUKHY ne ko!
Ita ta san Amani ba ta da wata matsala a yanzu da ta wuce Mukhtar. Har ta saba yanzu in Amani ta kira ta, to ta san Mukhtar ya kunso mata. Ita kuma ko kadan ba ta ganin laifin sa, ina laifin mai son Baban ka? Mai taimaka masa?
Amani ta gyada kai kamar Hamida na kallon ta, ta ce, Shi ne Hamida, karewa ma yau komai ya kare, tunda Daddy ya ba shi sadakar aure na.
Wata muguwar dariya ta kutsowa Hamida, ita da ma wannan so da Alhaji ke wa Mukhtar ta san karshen tika-tika tik! Ko dai Mukhtar da kan sa ya ce yana son kyakkyawar diyar ubangidan nasa, ko Alhaji ya hada da kan sa, don cikar kaunar da yake yi wa Mukhtar da kara janyo shi jikin sa har abada.
Hamida ta yi dariya iya dariya, amma bayan ta kashe wayar ta. Sannan ta sake kiran Amani ta ce,
Afuwan Habibty, network ne, na ji abin da ya faru, amma abu bai yi dadi ba, shi ko Alhaji mai yasa zai yi haka? Bayan ya san ba kwa jituwa? To amma ke yanzu a tunani da hankalin ki me ki ka yanke?
Za ki yi wa mahaifin ki mai son ki, mai kaunar ki, mai tattalin farin cikin ki, mai hidimta miki iya rayuwar sa biyayya ne ko kuwa kasa za ki bada masa a ido? Maganar Alh. Sadi fa? Ina ta kwana?
Amani ta yi maza ta ce, kada ki daure ni da jijiyoyin jiki na. Ai hakkin sa ne ya so ni ya kula da ni, amma banda auren dole. Da ne Daddy yake so na Hamida, yake kauna ta, yake tattalin farin ciki na da gudun bacin rai na amma banda yanzu.
Idan har zaki lura da kyau zaki gane Mukhtar kadai yake so yanzu, tunda har yana fadin bai iya hada jinin jikokin sa da na kowa sai nashi.
Ta sake rushewa da kuka, ta ce, Hamdy, ina cikin tashin hankalin da Allah kadai zai iya fidda ni. Tunda har Daddy ya yi wannan tunanin. Kin sani na ki jinin mutumin nan da duk abin da ya shafe shi, tun yanzu sai abin da ya ce ma Daddy, ina ga ya zama son inlaw din sa ko ya haifa masa jikokin da baya da su? Ai shikenan kuma Daddy cewa zai yi ba ni ya haifa ba shi ya haifa.
Hamida na ta guntse dariya, ta ce, Fisabilillahi Habeebty me ye abun tashin hankali a wannan abun arziki? Cewa nake da tsoho zai aura miki saan sa? Da ki ka yi hakuri kika fawwalawa Allah kika kuma bashi zabi, nima kuma nayi ta taya ki da addua ba gashi Allah ya amsa ya dube mu ba? Shi da kan sa Daddyn ya fasa ba tareda rayuka sun baci ba, ya zabo yaro santalele ya baki, son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login