Showing 6001 words to 9000 words out of 44162 words
LTD.
Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko dai Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko kuma abzinanci. Cikin ukun dai. Duk da haka a kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran yake yin ta.
Ina Magana da mai wannan layin ne? In sha Allahu kana tare da mai wannan layin Engnr. Othman Fass. Ya kasa furta sauran da accent din sa. Amma Alhajin ya gane yana son cewa Faskari ne.
Sai ya karasa masa da cewa Eh nine Engnr. Usman Faskari.
Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu? Na tsince ta a jirgin kasan da ya taho daga Bordeaux zuwa Paris. Na samu wannan lambar a jikin daya daga cikin identity cards din ka.
Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana hailala, ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception.
Cikin daren baa kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin. Ya dauko wallet din sa ya bashi. Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma kirga kudin sa ya ga suna nan cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba, ya tabbatar ba abinda aka cire.
Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya baa cire ba.
Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa. Sai ya bi bayan sa. Ganin cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna ba bahaushe bane Baabzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar wadanda ke tahowa karatun boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar, kasancewar kasar Faransa ce ta goya kasar Nijar.
Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da character da attitude din sa sun yi matukar impressing din sa.
Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin;
Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka?
Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da koin kula irin nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin annuri ya ce da Alhaji Usman,
suna na Mukhtar.
Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah.
Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba, yana rokon sa Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici.
Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon. Usman yayi a kan ya karbi kudin dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa, amma kyakkyawan matashin baabzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin jirgin da zai koma Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can, kasancewar interview din da ya yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi nasara ba.
To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar ka, samun irin ka a cikin matasa is a blessing. Ka cigaba da wannan halin na taimako da amana zai kai ka har inda baka taba zato ba.
Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba. Ni kuma mutum ne mai son mutane masu amana. Don ta yi karanci a wannan zamanin.
Still fuska ba walwala ya ce na gode.
Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din. Tafiyar sa kadai abin a bi da kallo ne, saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita.
Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari. Don haka washegari ya kira shi da layin da ya kira shi jiya, suka gaisa.
Alhaji Othman ne ko?
Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa. Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je gida? Alhamdulillah ya bashi amsa. In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na wuce gida Nijeriya gobe. Yace babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan zo in same ka kasancewar daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala har nan Baba. Murmushi Alhajin yayi yace na gode Da na sai ka zo, don Allah ina jiran ka.
Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin yasa aka shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta sutturu masu tsada, agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din, da niyyar ya je ya kai masa har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan kudin da ya barma shin.
Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon. Usman ba. Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi maana, ba kowa ke cin arzikin sa ba bayan tilon yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai rowa kwarai. Tsakanin sa da duk wani maaikacin sa albashi kadai, babu ihsani. Amma shi wannan yaron ya nuna masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya, sabanin daukar da yake yiwa kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman gasashshen tsuntsu daga sama, shi yasa yake so ko yaya ya gode masa.
Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa suke cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabiar da yake kai, wato son ci daga haram ko halak kamar sa.
Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan Euros dake dankare cikin wallet din sa.
Ko a satin da wuce ya kori maaikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi masa sama da fadi da wasu yan kalilan kudade. Bayan kuma kudaden ma bata suka yi cikin lissafi amma a hannun su.
Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin da shi, sanye yake da farar shirt an rubuta Fred Perry da bakin wandon CK Jeans. Dogon matashi, kakkarfa, farin baabzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin sa kamar an sa ruler an ja masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na halittar sa ya zauna a inda Allah Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa zati da kamala, ga wata lallausar suma da ta taru a saman goshin sa ta abzinawan usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi tamkar Baindiyen nan mai farin jini (Shahrukh Khan).
Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya sauko kasa su ci abinci tare. Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa baya damun sa.
Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate guda, sai ya kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi cike da kauna, sai ya sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a plate daya.
Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har yaji abinda yake son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris.
Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana kiran yankin nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na biyu a nan kasar, daga jamiar Paris Saclay University. Ya gayawa Alhajin tun baya kammala masters din sa ya nemi ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar shi ba dan kasa ba, don haka zai koma Hong-Kong yanzu ya nema a can. An ce suna bada ayyuka sosai ga yan Afrika, shi neman na kan sa ya fito, ba yanzu zai koma gida ba.
Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin arziki babu ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar.
Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya gaya masa, cewa daga digirin sa har master first class ne. Alhaji Usman became highly impressed da jin hakan, sai kawai Alhajin ya ce, ina ma za ka iya zaman kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda ni din bani da Da namiji, sai mace tilo, ina neman mataimaki a kan harkoki na wanda zan iya ja a jiki na in sakar masa ragamar kamfani na. Na kuma yaba da halayen ka.
Mukhtar ya ce ban taba zuwa kasar Najeriya ba Baba, amma ina jin labarin ta, kuma ina son aikin yi kwakkwara wand azan tsaya a kan sa da kafafu na, musamman wanda ya shafi kasuwancin kamfani, a nan buga-buga kawai nake babu permanent job ga wadanda ba yan kasa ba, ni kuma ba yanzu zan koma gida ba.
Don haka zan bi ka in gwada in gani, idan naji dadin kasar, zan zauna, don bani da abun yi ko na koma Diffa. Kuma babu wanda ke jira na a can.
Cikin mamaki Alhaji Usman ya ce ina iyayen ka?
Nan da nan fuskar Mukhtar din ta wani irin sauya, ta rine ta yi jajir abin ki da farin mutum. Wani yanayi ya shiga na kokawa da numfashin sa da Alhaji Usman ya kasa karanta. Shi da kan sa ya baiwa kan sa amsa da basa raye kawai. Sai ya shiga yi musu addua ba tare da shi Mukhtar din ya ce masa komai a kan su ba.
Amana ce ta hada mu, naji ina kaunar ka kamar dan da na haifa saboda halayen ka da suka burge ni, ina fatan wannan amanar tayi ta yado da yabanya a tarayyar mu.
**** **** ****
Mafarin zuwan Mukhtar Diffa kenan gidan su Amani, tarayyar da ta zamewa Alhaji Usman sanadin alkhairori masu yawa.
Bai sakar ma Mukhtar ayyukan sa na sirri ba sai da ya cigaba da gwada shi iyakar gwadawa ta hanyar yawan aiken shi kai kudade banki, domin da farko kamfani ya kai shi, ya bashi ofis, a matsayin Chief Operating Officer (COO) ya kuma bashi gidan zama a kusa da gidan sa wanda babu nisa da kamfanin Faskari Investment cikin birnin Katsinan Dikko.
Excellent Performance din da Mukhtar Diffa ya soma nunawa daga zuwan sa ya razana kowa, domin yana zuwa ya canza akalar komai zuwa na zamani, ya kawo sababbin innovations masu tafiya da zamani na yadda zaa bunkasa hanyoyin da kamfanin ke amfani da su wajen shigo da kayayyakin da kamfanin ke shigo dasu Najeriya daga Faransa da sauran kasashen Europe irin Mexico. Har ila yau, COO Mukhtar Diffa, ya kawo hanyoyin samun cigaba ga maaikata ta hanyar karawa maaikata sani da dabarun kasuwanci a zamanance, ta hanyar shirya (capacity building programs) iri-iri da yake shiryawa a kai-a kai ga kananan maaikatan Faskari. Ya tsame masu lalaci daga ciki ya kai su kasa, ya maye gurbin su da masu hobbasar cikin su.
Ya kuma takura wa Alhaji a kan kara albashi da welfare din maaikata da yake kankamewa. Kan ka ce meye wannan hakan ya sayo ma Mukhtar farin jini gun kananan maaikata, ya kuma kara musu himma da maida hankali, sannan ya kawo conducive working atmosphere ga dukkan maaikatan Faskari Investment.
Shi ba hausa ce ta ishe shi ba, amma da zuwan sa Katsina ba jimawa sabida cudanya da hausawa da maaikata a company, da kuma shi kan sa Alhajin da ke masa magana kullum da hausa don ya kware, a sannu bakin sa ya fara iyawa sosai, a hankali a hankali kuma accent dinsa na Francaise da abzinanci ya fara barin bakin sa sabida rashin abokin yi.
Mukhtar Diffa, ya soma rikidewa yana koma wa zallan Ba-katsine, in ka cire nannadaddiyar sumar kansa da launin jar fatar sa da ke fallasa shi, matsayin kyakkyawan Baabzinen mutum dan hutu kuma dan zamani, hatta hausar bakin sa kafin shekara guda ta koma ta Katsinawa.
****** ****** ******
Sanda Alhaji Usman ya kawo shi gidan tana makarantar kwana aji daya a Ulul Albaab, ya dade a gidan ma bata san da shi ba, a lokacin Alhaji bai mayar da kamfanin da sunan ta ba, so ko ta zo hutu ba wani haduwa suke ba ko a ce bata san shi ba ko da ta hange shi, don bai cika zuwa gidan ba a Kamfani yake rayuwar sa, daga gida sai ofis, Mukhtar ko aboki bai da shi, sai Malam Tajuddeen mai gadin gidan Alhajin.
Ranar da ya fara ganin ta wata asabar ce, direba ya dauko ta daga makaranta yana cikin motar Alhaji a harabar gidan yana jiran fitowar Alhajin zasu wuce duba wata gona da Alhajin ya saya a garin Bindawa, ji yayi yarinyar wadda fitowar ta Kenan daga mota tana zagin direban ta cikin daga murya wai yayi parking ba a kofar shifa falo ba, yana nufin da kafar ta zata taka har kofar falon ko yaya? Ga zakin murya cau ga zare ido kamar tana yi wa dan ta fada, shi kuma Malam Sirajo yah au rawar jiki yana bata hakuri tare da cewa Mukhy ne yayi parking a kofar falon yana jiran fitowar Alhaji, amma duk da yadda ya kwantar da kai ya bata hakuri data fito sai da ta tsarta masa miyau a fuska ta ce donkey, monkey, idiot!
Mukhtar na shirin fitowa ya dauke yarinyar nan da mari sai ga Alhaji ya fito hanzari yan cewa yi hakuri Mukhy, ina jiran isowar TAFISU ne kada ta dawo bana nan an tafi dauko ta yana daga ido kuma ya gan ta cikin uiform din ta ta doso shi da gudu, Alhaji ya bude hannu yana Oyoyo! Da Tafisu na. Ta rungume Alhaji duk da ta fara kirgen dangi ma a lokacin suka yi ta murnar su kafin Alhaji ya ce mata ta shiga ciki, ya sa an shirya mata komai, gobe sabuwar matar da auro zata tare bazatayi kadaici ba wannan hutun. Direban data tsartawa miyau shi ya dauko jakar ta ya shigar mata da ita bayan yasa hankici ya goge fuskar sa, a ranar kuma ya ajiye aiki a gidan su Amani.
Mukhy da Alhaji suka kama hanyar Bindawa, Mukhtar ke tukin Alhaji na gefen sa yana bashi labarin itace tilon yar sa Amani da yake bashi labarin tana makarantar kwana, ya ce ka gan ta Tafisu akwai rigima ga kyuya, nikadai nake iya mata. Ai komai nata na uwarta ta debo, yadda Jalan haka Tafisu take, kullum ina godewa Allah da bata debo kannina ba
Mukhy dai tuki yake bai ce komai ba, amma a ran sa ya ce ai gara da kamannin naka ta debo, da wannan halin nata na rashin kunya, yar karama da ita da raina na sama da ita. Shi bai taba ganin rashin tarbiyya irin na yau ba. Imagine in shi ta yi wa abinda ta yiwa Malam Sirajo, wallahi sai ya mare ta, kuma daga ranar ko nawa ake biyan shi bai kara aiki a gidan su.
Basu kuma kara haduwa ba har ta koma hutu, don shi ba wani zuwa gidan yake ba sosai, idan ba Alhaji ya neme shi a gida ba, duk harkokin su a kamfani suke yin su.
Ya zama cewa in tazo hutu sau tari ya kan gan ta ko daga nesa ne, a harabar gidan ko a falon Alhaji, itama ta kan hango shi daga can saman balcony na saman benen ta, ko a falon Alhaji in suna ganawa ta sirri, wani lokacin ta kan shigo, in ta gan shi sai ta koma, bata taba gaishe shi ko yi masa magana ba, shi dai ko gaisuwa bata hada su tun da ya gane bata da kwalli a idon ta, sannan Alhaji baya kwabar ta, ta raina duk wani maaikaci na gidan, aka ce hanyar lafiya a bi ta da shekara, sosai ya kama kan sa, ko ya ganta zai bar wuri shima, don ya san zuciyar sa ba irin ta sauran maaikatan Alhaji bace, da suke iya shanye duk wani rainin ta da wulakancin ta saboda Alhaji.
A haka suka rayu tsayin lokaci a gidan Hon. Usman, ko in ce tsayin shekaru, har Amani ta soma zama budurwa sosai, babu wata sanayya ko wani cordial relationship a tsakanin ta da Mukhy.
Tana gama sakandire ba jimawa ta samu gurbi a Jamiar Bauchi, da taimakon