Showing 39001 words to 42000 words out of 44162 words
ba, sai kawai ta shigo kan ta tsaye don ta ga ko lafiya.
Amani ta zuba wa Rakiya idanun ta da suka yi jazir da bacin rai, tana kallon ta tamkar ita ce Balogun.
Rakiya ta karyar da kai gefe ta ce, Afuwan uwardaki na, Alhaji Mukhtar aka ce na rako wurin ki. Alhaji da kan sa ya ce in rako shi.
Kafin Rakiya ra rufe baki, Amani ta samu zarafin ci mata mutunci, ko kunduma mata ashar, Mukhtar din ya shigo dakin kan sa tsaye. Daga jikin kofa ya tsaya hannuwan sa harde da kirjin sa yana kallon Amani da yadda a cikin dare guda duk ta zabure ta fice a hayyacin ta.
Rakiya ta juya ta fita har da rufo kofar dakin, tana fadin a fito lafiya Alhaji.
Mukhtar kallon ta kawai yake daga sama har kasa, wani irin kallo da bai taba yi mata ba. Duk da cewa kayan barci ne a jikin ta gashin kan ta babu rufi, gashin duk ya tarwatse duk ya yi buyaya da shi kamar sabon kamun hauka, shi a idon sa gani ya yi kamar an kara mata kyau da kwarjini, duk da idanun ta sun jeme sun yi zuru-zuru din. Kallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Mukhy da Amani, kallon da su duka suka kasa fassara yanayin sa yayin da Mukhtar ya ji wani abu mai kama da tausayi ya darsu a ran sa game da ita, ganin yadda duk ta sauya kamanni da appearance a kwana daya.
Amma ya riga ya san Amani zuma ce sai da wuta ake iya sarrafa ta. Kamar ba zai yi magana ba don ya san kiris ta ke jira ta saki tantrum, amma sai ya tuna damuwar da mahaifin ta ke ciki a kan ta.
Ya tuna rokon da ya yi masa a kan ya lallaso ta ta zo ta karya kumallo tare da shi sannan su wuce Faskari.
Alhaji yana da hope na cewa, shi kadai zai iya hakuri da tilon yar sa, mai tarin nakasu a halayya da dabia, shi ya sa ya damka masa ragamar rayuwar ta ta hanyar da ta fi kowacce muhimmanci ga dan adam, wato aure. Kuma a istikharar da ya yi daren jiya shi kam bai ji yana kin alamarin nan ba, ya dai san zai sha wahala iyakar sha a hannun Amani, tunda Allah bai halicci zuciyar ta da kaunar sa ba.
Mukhtar ya nisa, ya kira sunan Amani, ba cikin yanayin da yake mata magana da shi a baya ba, na nuna halin ko in kula da alamarin ta. Wannan karon akwai kulawa da dan lallashi acikin sautin sa.
Ya ce, Ki sani cewa komai ya yi zafi ga bawa bai fi karfin Ubangiji ba. Iyaye suna gaba da komai a rayuwar dan Adam. Mahaifin ki ba yaron ki ba ne, ba kuma dan ki ba ne da za ki dinga yi masa duk abin da ki ka ga dama ba.
Ya kira ki kin ki amsa kiran sa, kin bar shi a damuwa, anya Amani kina son gamawa da duniya lafiya?
A hakan kuma ki ke so Allah ya ji tausayin ki ya hada ki da mahaifiyar taki? Alhalin shi din da ya maye miki gurbin ta ba ki tsaya kin kyautata masa yadda yake kyautata miki ba?
Me ki ka dauki kan ki Amani da ki ka zabi yin fito-na-fito da mahaifin ki? Ni da bai haifa ba na zabi in masa biyayya a kan umarnin sa, don na san ba zai ba ni matar da za ta cutar da ni ba. Sannan yana cikin hali na rashin lafiya yanzu, wanda kyautatawa da tausasawa kadai yake bukata daga gare mu.
Yau in aka ce babu Alhaji sai kin fi kowa zama abun tausayi, ba ki ga tsuntsu ba ki ga tarko, baki rabauta daga biyayyar uba ba, sannan uwar ma ba za ki san inda za ki gan ta ba.
Na zaunar da ke na ce ki bi shi a hankali, ki bar komai a hannu na, amma ki ka yi kan gaban kan ki saboda ke ba ki da mafadi kuma ba ki yarda kina da na gaba da ke ba.
Zan iya rantsuwa da Allah kan cewa yan damfara ki ka tura wa kudi, bayan na gaya miki kada ki tura, gaggawar ta mece ce tunda na ce ni da kaina na yi alkawarin kai ki ga mahaifiyar ki amma karkashin umarni da amincewar mahaifin ki?
Yanzu ina adireshin da ki ka sayo miliyan biyar sai ki ba ni in gani.
Kuka ya kubucewa Amani, ba kukan shagwaba ta ke yi ba yau, kuka ne na kubucewar azanci da tausayin kai. In ta ce maganganun Mukhtar ba su yi tasiri a zuciyar ta ba ta san ta yi karya. Da gaske Daddy ya wuce komai a gare ta, kuma bai cancanci reactions din da ta ke yi mishi ba, amma zabin da ya yi mata ne ba za ta taba karba ba, domin ya kaskantata, ya sayar da ajin ta ya zubar mata da ego din ta, muddin Mukhtar zai bai wa auren ta.
Daga nan har kotun koli za ta je don neman hakkin ta a kan hakan, bazata taba yarda tayi auren kaskanci ba, auren yaron Alhaji mara asali, mai halayen da ta ki jini, wato musamman girman kai, da kin yarda a taka shi, ita kuma ta saba taka kowa da ke kasan ta, tunda ta yi kokarin riskar mahaifiyar ta don ta samu mafaka a gun ta abun ya ci tura.
Tana ta kuka tana fyace hanci da share ido da gyalen ta, Mukhtar ya ce, Taso ki biyo ni, mahaifin ki na son ganin ki, in kuma kin ki tashi ko a ka ne zan dauke ki in kai masa ke, na rantse.
A yadda ta ga idanun sa sun rikide cikin bacin rai ta san sarai zai iya aikata abin da ya furta, sai kawai ta mike, ta na so ta ce ya ba ta wuri ta canza kaya, amma ya kasa ya tsare a kofar dakin yana muzurai na ko ta wuce ko ya ciccibe ta.
To ka je zan canza kaya. Ta fada a turbune, fuskar kamar wani kauye wai shi Durbunde saboda turbunewa. Mukhtar sai ya ga akwai bukatar ta canza kayan, bai kamata ta tafi har Faskari da kayan barci ba, sai ya juya yana fadin, Na ba ki five minutes, in ban gan ki a falon Alhaji ba da jakar fita unguwa da trolley din matafiya da kayan ki da zasu yi miki a kalla kwana bakwai a ciki zan dawo.
Don tafiyar tamu ba mu san har yaushe za ta kai mu ba, tunda neman sulhu da gyara zumunci ne zai kai mu.
Ya fice a dakin ya bar mata daddaddan turaren sa na sirnanawa a kofofin hancin ta.
Tana kuka tana komai ta canza kayan jikin ta, ta sanya doguwar riga sannan ta yi maza ta yayibo mayafi ta jefa kaya kala uku da man shafawa da deo spray a trolley da yan sauran abubuwan bukatar ta. A gurguje ta rufo dakin ta fito kada ya kara dawo mata daki, don ko turaren sa ba ta son ji, balle ganin cunkusasshiyar fuskar sa mara annuri da rashin walwala.
Sai da ya taimaka wa Alhaji ya gama kintsawa ya debar masa duk abin da zai iya bukata har nan da kwanaki bakwai kama daga magungunan sa da kayan sanyawa ya kai komai mota. Ya dawo kenan ya tadda ita a falon na Alhaji, da jakar tafiya a gaban ta. Alhaji na ta faman lallashin ta kamar shi ne yar ita uban, yana gaya mata duk abin da ta ga ya yi mata soyayya ce, idan kuma har ta zabi ta bijirewa umarnin sa ta hanyar tozarta shi a idon Mukhtar, to kuwa zai yi hakuri da duk son da yake mata ya sallama ta, zai kwace komai da ya mallaka mata ya kai ta wajen mahaifiyar tata su karata.
Mukhtar ya yi kamar bai ji me Alhaji ke fada ba a karshe, ya ce, Alhaji komai ya kammala, mota an mata full tank an kuma wanke ta sai tafiya ya rage.
Allah ya yi maka albarka Mukhtar, dauki kayan ta ka sa mata a mota, jakar hannun ma karba mata.
Yar murmusawa ya yi, a ran sa yana fadin, Alhaji ke kara lalata yarinyar nan, ya karba mata jakar hannunta wato ga mijin Hajiyar Faskari ko? Ko Alhaji ba ya karba wa briefcase in za su fita balle wannan fitsararriyar.
Tana jira ya daukar mata har jakar hannu kamar yadda Alhaji ya yi masa umarni, sai kawai ta ga ya dauki trolley dinta da hannu daya ya bar falon. Ita ta kai zuciya nesa ta dauki jakar ta rataya sannan ta turo Alhaji a kan keken sa.
Ita da Mukhtar din suka yi kici-kicin saka Alhaji a mota, ya nade keken nasa ya saka a boot din motar. Gidan baya ta shiga ta zauna gefen Alhaji don tana ganin ta fi karfin ta jera kafada da Mukhtar a gaban mota, alhalin yana matsayin yaron Alhaji ko kuwa ta ce direban ta. Zuciyar ta ba za ta taba ba shi wani matsayi bayan wadannan ba.
Alhaji zai yi korafin muhallin da ta zaba don zama sai gani ya yi Mukhtar ya tada motar, ko a jikin sa, shima baya so ya hada kafada da ita, ko ba komai ta kula da Alhaji a bayan motar wanda suka yi masa kujera ta musamman suka sanya mishi belt sosai.
Kamar ya san a karkashin zuciyar ta ta so ya yi magana ta gaya masa mara dadi, ta gaya masa har abada shi yaron gidan su ne, kada wani zancen aure da Alhaji ya furta ya rude shi. Sai aka yi saa bai tanka mata ba, ya ja mota cikin tukin sa na nutsuwa, na kwarewa da kamala suka yi reverse, wanda ba haka ta so ba.
Mukhtar ya sa a ran sa ba zai dinga biye mata ba yanzu kamar da, saboda jiya da ya yi wa Alhaji b.p ya ga ya hau sosai. In ta rasa wanda za ta yi wa rashin kunyar dole za ta yi shiru ta bar su su ji da abin da suka fuskanta yanzu, wato gyara tsakanin Alhaji da yan uwan sa.
Malam Tajuddeen ya bude musu kofa tare da daga musu hannu yana fadin, a sauka lafiya. Mukhtar ya dan daga masa hannu shima, sannan suka fita gate din gidan. Sannu a hankali ya hau bisa kwalta, sannan ya soma shimfida gudu da su kamar zai tashi sama dasu, abin da ya san Amani ba ta so, wato gudu da mota musamman a babban titi irin wannan, baa cikin gari ba.
**** ***** ****
Suna tafe kan titin da zai shiga garin Faskari Mukhtar ya kunna karatun Alqurani mai tsarki ya kure a radiyon motar cikin Suratul Baqarah, duk yadda ta ke so ta yi masa korafin gudun da mota da yake yi da su albarkar wannan karatun da ya kure sai ta kasa, ta samu kan ta da nutsuwa tana sauraron ayoyin na karshe na suratul Baqarah da taji sun mata dadi, kasancewar ita bata saba sauraren karatu ba sai music.
Mukhtar na tafe yana tambayar kan sa shin ko Amani ta taba yin islamiyya? Balle a je ga batun sauke Alqurani? Ya nisa, umh. A lokaci guda Alhaji na tuhumar kan sa da ka sa a ran sa da sakaci mai yawa da ya yi a kan tarbiyya da kuma upbringing din Amani in general. Ya tuna ko hizfi biyar ba ta da shi a kan ta, don tun tana karama da ya dauki wani bayerabe yake zuwa gida yana koya mata karatun Alqurani, da ta yi wayo ta kai munzali sai ta nuna ba ta raayin koyarwar malamin. Dole Alhaji ya sallame shi. Daga wancan lokacin kuma Amani ba ta kara shaawar tahfiz ba, dan wanda ta samu a gun bayeraben nan da shi ta ke karatun sallah har yau.
Alhaji ya nisa yana fadi cikin ran sa,
na yi kuskure mai yawa a rayuwa ta. Allah ka bani ikon gyarawa kafin ka dauki rai na. Allah ya sa Mukhtar ya rike min Amani da dukkan nakasun ta, ba tare da ya goranta mata tarbiyya, ilmin addini da goyon gatan da na yi mata ba.
Yau ga shi ga dukkan alamu Amani na so na kasa lankwasa ta. Wa ya janyo komai?
Alhaji ya kara kudirewa a ran sa sai dai Amani ta mutu, amma sai ya cika kudirin sa, in yaso ya wanke gawar ta ya fara kaiwa gidan Mukhtar kafin ya danganata da kushewar ta, amma ba ta da miji insha Allahu sai Mukhtar din sa. Idan ta bijire masa wannan karon zai ba ta mamaki. (Alhaji ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi).
Daidai lokacin da Mukhtar ya karya kan motar suka hau burjin da zai shigar da su garin Faskari, Alhaji na ta kallon garin iyayen sa da kakannin sa with nostalgia, yana kokarin tuna ko yaushe ne last shigowar sa Faskari? In zai iya tunawa daidai tun lokacin da yake nema kujerar sanatan Katsina ta Tsakiya yana neman kuriar karamar hukumar tasa. Da ya zo ya dan yarfa musu. Ya tuna lokaci na karshe da Yaya Idrisu ya kira shi a waya yana gaya masa Kamilu dan sa ya kammala karatu an turo shi hidimar kasa cikin jihar Katsina ko zai ba shi muhalli ya zauna a gidan sa yayi hidimar kasan?
Yadda ya balbale shi da fada kamar kanin sa yana fadin ba ya son a zo a cika masa gida shi bai iya jaye-jayen yayan dangi ba. Ya tuna cewa uwar Kamilun ita ta shayar masa da Amani, ba don ita ba da bata rayu ba, ko sai da madarar gwangwani.
Yau ga shi ya dawo Faskari babu kafafu sai dai a tura shi a keken guragu, rabin jiki ba ya aiki, kuma kai tsaye gidan Yayan nasa ya dosa, wato gidan su na gado, wannan abun kunya da kayan nadama har ina?
Ita dai Amani da ke gefen sa tana danne-danne a waya, sai gani ta yi Daddyn ta yana hawaye, ya kuma bar su suna ta zuba akan kundukukin sa ba ya ko sharewa wasu na korar wasu. Idan ya kara tuna cewa uwar Kamilu ita ta shayar masa da Amani, amma shi ya kasa daukar ko Kamilun ne ya yi yan watanni tare da shi na hidimar kasa duk irin arzikin da Allah ya yi masa da girman gidajen sa a Katsina. Yailahi! Da wace fuska zai doshe su yanzu? Da wane azancin harshe zai nemi gafarar su? Ba tare da sun yi tunanin sai da lafiya ta kare masa ba ne ya neme su? Don in bai manta ba daga waccan wayar da suka yi da Baba Idrisu har gobe Baba Idrisu bai kara neman sa ba, ya rike talaucin sa da mutuncin sa, ya rike yayan sa a kauye ko birnin Katsina ya haramta musu shigowa don ma kada su nemi kanin uban nan nasu da bai san muhimmancin zumunci da girman zumuncin Allah ba.
Alhaji shi ke nuna wa Mukhtar hanya har kofar gidan iyayen sa, soron gidan duk ya zube, kana iya hango tsakar gidan da duk abin da ke ciki duk da an kare da zangarniyar dabino da azara.
A nan ya umarci Mukhy ya yi fakin motar, daga can hanyar masallaci Alhaji ya hango Yayan sa Malam Idrisu na tahowa, Mukhtar ya fito ya bude but ya fiddo kujerar Alhaji ya warware ta ya dauko Alhajin daga mota ya sanya shi cikin kujerar. Amani ta fito tana ta cin magani da yatsine-yatsine, har da zumbure-zumburen baki, ita ta tura Alhajin zuwa kofar gidan su, yayin da Mukhtar ya tsaya kici-kicin fiddo kayan su.
Daga nesa Malam Idrisu ya hango su babu bata lokaci kuma ya gane Amani tare da wani farin balaraben mutum da bai sani ba. Amma dattijon da ke cikin kujerar wheelchair ko kusa bai kawo cewa kaninsa Usman ba ne.
Amani ta jira rike da hannun kujerar har ya iso, sai a lokacin ya gane dan uwansa.
Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Malam Idi, yana fadin, Me ya same shi? Me ya faru da shi haka?
Zuciyar yan uwantaka! Tuni ya karbe shi daga hannun Amani, da kan sa ya tura shi zuwa cikin gida.
Kai Isya je ka kasuwa ka kira Kamilu ya zo ya bude wa baki dakin sa su aje kayan su.
Yaron da aka kira Isya ya zura da gudu yana waiwayen Mukhtar don ya dauka bature ne ko wani balarabe, fatar sa ta wanku da boko, ya karya hula damanga a saman kansa wadda ta dace da launin shaddah getzner lemon green da ke jikinsa, kai ba za ka ce haihuwar Africa ba ne shi ya fi kalar larabawa.