Showing 15001 words to 18000 words out of 44162 words

Chapter 6 - Amani Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

19 Nov 2024

235

ka cece ni zai kashe ni Daddy ya ce bani Mukhtar din tace Daddy Allah ya sawwake ya taba min waya ya shafa mata bakin hali irin nasa abin nata sai ya koma baiwa Alhaji dariya, ya ce alright, bari in kira shi ya katse kiran nasu ya soma kiran Mukhtar.
Yana ganin kiran Alhaji amma kuma yana tuki don haka saida kiran ya katse. Ya gangara gefen titi ya kashe motar sannan cikin nutsuwa ya bi bayan kiran Alhajin.
A yadda ya tausasa murya ya kuma russunar da kai duk da Alhajin baya ganin sa sai kayi tsammanin da mahaifin sa ya ke magana, ya ce Alhaji muna hanyar dawowa kana son wani abu ne? Alhaji cike da damuwa ya ce No Mukhy, karar ka aka kawo min kala-kala, ka bi ta a hankali ka ji? Ka san wani lokacin haka take abu na yayan fari. Mukhtar ya saci kallon ta sai kumburi take kamar zata fashe ya ce Alhaji ai babu damuwa ina iyawa da ita, musamman da wani lokacin tana abu zayyal majnunah (kamar mahaukaciya), abinda bazan lamunta daga gare ta ba shine rashin kunyar da take maka, ka gaya mata ta dinga maka magana with respect irin yadda yaya suke yi wa iyaye, saboda kai ne gaba da ita ba ita ba. Idan ta cigaba da yi maka magana irin haka bazan kara daukan ta a mota ba.
Alhaji ya ji dadi, ya ce Mukhtar kada ka damu da shirmen Tafisu ka ji? Ka san wanda baida mahaifiya a kusa sai ana masa uzuri Mukhtar yace ni ba zan yi ma ta uzuri da wannan ba, babu uzuri a cikin biyayyar iyaye, in dai a kan daga sautin ta sama da naka ne zan iya bubbuge bakin ta Alhaji Alhaji yayi murmushi yace to shariar taku ta fi karfin waya, ku dawo gida sai mu yi ta a zaune. Kuna ina yanzu?
Yace muna hanya ko rabin isowa gida bamu yi ba. Ni gaskiya Alhaji a gate zan sauke ta, ni kadai zan je na dauko Hajiya, daga can ina da inda za ni Alhaji ya ji wani iri ya ce Mukhtar ban san ka da rashin kirki ba kada ka fara akan kanwar ka ya ce Alhaji sai ta daina yi maka fada zan yi kanwa da ita, in ba haka ba kowa ya yi rayuwar sa cikin gidan nan ba ruwan Yaya da kanwar, bani da zuciyar da zata iya daukan ana raina min kai.
Daga haka ya kashe wayar sa Alhaji na fadin ka dai shigo da ita kada ka sauke ta a gate don Allah ba don halin ta ba.
Duk abinda suke fada a kunnen Amani, mamaki da haushi ya hana ta ko kwakkwaran motsi, anya wannan mutumin bai taki komai ba? Yaya kana zaman yaron gida kake ma uban gidan ka Gadara irin haka shi kuma yana biye maka sai kace uban da ya haife ka? Amani ta saci kallon sa sai suka hada ido, ya kashe ta da harara, yana kokarin cire farin gilashin idon sa don ya sha round din da zai kai su unguwar su. Wani irin kyau ya yi a idanun ta mutum tamkar shi yayi kan sa, kai kace wani balaraben Madinah ne idan yana magana, tsafta da wanka sun kama jikin sa radam.
Sai ta tuno alfarmar da take so yayi mata duk da ya bakanta mata rai yadda bata zato amma wannan ce dama ta karshe da zata iya rokon sa don ba haduwa suke yi ba, sai dai ta hange shi a harabar gidan daga balcony din ta yana shiga mota zai fita ko ya shigo gidan. Ko ya zo daukan Alhaji su fita.
Ta rasa ta ina zata fara don kwata kwata babu fuska daga Mukhy, yama kara daure fuska tamau da suka hada ido don kada ta kawo masa wargi, ya lura da kallon kurillar da ta ke masa wanda ya wuce shariah. Shikuma baya son ko kalma guda ta hada shi da Amani don kada raini ya shiga takanin su irin wanda takewa kowa da ke karkashin ta.
Ya Allah ya zata yi da wannan mutum mara sakin fuska? Sai kawai tayi kundumbala tace, Man, ina son fidda kudi ne daga corporate account dina? Mukhtar bai san cewa magana take da shi ba, ya dauka ma a wayar ta take magana da wani daban don haka ko juyowa bai yi ba.
Amani ta daga murya da dan amo tace na tabbata kai ba kurma bane, but you are acting kamar baka ji!
Sai yanzu ya san da shi ta ke, ya kuwa kara daure fuska yaci gaba da tukin sa. Amani sai ta fara hawaye don abun yayi mata ciwo mai yawa, baa saba yi mata irin haka ba, kowa na gidan girmama ta yake yi yana nan-nan da ita yana rawar jiki idan ta bada umarni, balle wanda ke matsayin yaron Baban ta ya yi mata irin wann funfurus din.
Kuka ta soma yi sosai har da sheshsheka da fyace hanci, tace tunda dai na san kana ji na, halin ka ne shariya da wulakaci, to bari in fadi sako na, ya rage naka ka yi min alfarmar ko kada ka yi.
Ina so zan cire kudi 5 million zan yi amfani da su bana son Daddy na ya tuhume ni, idan ka ga alert dinnan alfarma ce kada ka fada masa tunda dai kudi nawa ne, ba na wani ba.
Mukhtar ya rage gudun motar ya dan juyo kadan ya saci kallon ta, sai kuka take tana fyatar hanci kamar wadda aka yi ma wani mugun duka, kada ya je ta daura masa sharri, don ya ji an ce masa mata makirai ne. Ya kashe motar gaba daya a gefen titi ya ce.
Da ni kike?

Amani ta ce aa da sitiyarin motar ka nake. Karo na farko da Mukhtar ya yi wani miskilin murmushi, ya ce to kai sitiyarin mota ana maka magana!.
Amani ta kara rushewa da kuka tace Allah yasa ayi maka irin wulakancin da kake yi min. Allah ya hada ka da daidai kai, Allah ya sakawa mahaifina amana ta da ya baka kake ci don ka san ka asirce shi.
Mukhtar ya bugi sitiyarin sa ya ce ban da muguwar addua ga wanda baki sani ba Maam, you will never know what a man like me is going through, I hate hayaniya, ki gaya min wace alfarma ce kike so? Bana son koke-koken banza me na yi miki? Wane kudi kike magana a kai? Kuma me zaki yi da su? Ban fahimce ki ba anymore.
Amani ta dan ji dadi, at least hargagin ta ya sa ya kula ta, ta share hawayen ta da gefen mayafin ta, ta ce ba damuwar ka bane abun da zanyi da kudi na, kawai bana so Daddy ya ji ne, da ba zaka san ma na cire ba
to kin san ba damuwa ta bane kuma bai shafe ni ba don me zaki sako ni ciki? An gaya miki ina shiga abunda baa sa ni bane? Ai kawai ki yi abinda kika ga dama nima in yi aiki na na daukar zance in kai gaba, tunda shi aka sa ni, ba sai kin saka ni cikin shaanin ki ba, mind your own business and leave me alone.
Ya ja motar suka cigaba da tafiya Amani na gayawa kanta ta gara ta canza taku, tunda har kuka yana karya zuciyar sa ya saurare ta, ko baya so, ya bata amsa ko yaki Allah to zata rage izza tunda ta lura izzar ta ke tunzura shi ya ki sauraron ta.
Tabbas yau ta gamu da wani sabon mutum a cikin rayuwar ta, wanda bata taba ganin mai hali irin nasa ba.
Bawan Allah ko wa kake da suna? Na yi rantsuwa ba ta hanyar banza zan kashe kudin nan ba, kawai bana so Daddy na ya san da fitar su.
Ta sassauta murya ta ce kayi min wannan alfarmar, ba don ni ba ba don hali na ba.
Mukhtar ya yi mata kallon kin ishe ni haka kafin yace zan yi miki only in kin gaya min gaskiyar ko me zaki yi da kudin nan, bana backing munafurci da rashin gaskiya komai kankantar su, in kina da gaskiya ba zaki nemi a boyewa mahaifin ki wani abu da zaki aikata ba.
Amani ta share ido da bayan hannun ta ta marairaice, sai ta dan bashi tausayi, ta ce wallahi ina da gaskiya ta, trust me, kuma ta hanya mai kyau zan yi amfani da su yanda ba zai gane ba, don bai san irin ciwon da na ke ji in naga kowa a jikin uwar sa ba.
Ta cigaba da cewa Malam COO (Chief Operating Officer) ni din ban taba ganin uwa ta ba sai a hoto, ban rasa komai ba amma ina so in je gare ta, ba don kuma na raina kulawar Daddy na a kaina ba, sai don kowannen su matsayin sa daban a gare ni.
Zuciyar Mukhtar ta dan yi laushi, laushin da shi kan sa bai zaci tana da shi ba, yafi zaton zuciyar sa tafi dutse tauri amma ashe akwai sauran tausayi a cikin ta, akalla ya gamsu, tunda ba shaye-shaye zata yi da kudin ba don tafi masa kama da masu banka kwaya, yace I will think over it. But remember always zaman Alhaji nake ba zaman wata Amani ba!.
Maganar shi ta karshe bata yi mata dadi ba. Ta yi kuta ta ce kai a rayuwar ka baka da humanity ne? baka da concern? Baka da sabo da mutane kuma baka daukar kowa da muhimmanci sai Daddy?
Ya murmusa kadan, har beauty point din fuskar sa ya lotsa ciki sosai yace ban san ta ba humanity din, concern kuwa ko maanar ta ban sani ba, mai yuwuwa sanda ake rabon su ni ina Diffa. Kin san ni dan Diffa ne, Diffa region, ta kasar Nijar.
Amani ta kulu iya kuluwa, ta yaya ba zai dauki abinda ta gaya masa da muhimmanci ba bayan sirrin ta ne da bai kamata ma ta gaya masa ba? Zai bi ta da bakar magana bayan ta bude masa sirrin ta? Maganar mahaifiyar ta fa take masa, wadda bata taba gani ba, yana mata maganar wani garin su.
Daidai lokacin da suka iso tangamemen gate din gidan su Amani. Dama bata son zuwa dauko Hajiya Rabi. Ba tun yau ba ta fahimci matar zal wajahaini ce (mai fuska biyu) a gaban Daddy kawai take nuna kaunar ta, a bayan idon sa kuwa kashi ya fi ta daraja a gidan nan. Shi yasa itama ta kama kan ta, sam bata shiga shaanin Haj. Rabi ko hanyar sassanta bata bi, ta kuma yi wa kanta alkawarin bazata bari Daddy ya sake ta ko ya san halin ta a kan ta ba, don ta gaji da aure-auren sa da ake faman kirga masa akan ta.
Mace ta karshe da Alhaji ya saka wai ita Zaibi, ta fadi maganar data tsaya mata a rai har gobe ta kasa mantawa, kuma daga kanta ne ta kudiri aniyar hana Daddy kara sakin kowacce mata duk mugun halin ta. Gara ta bar su da halin su ta nemo tata mahaifiyar.
Cewa matar ta yi ga gidan nan ta bar mata, karshen soyayya Alhaji ya auri Amani ya maye gurbin ta da ita.
Don haka tun kafin ya gama daidaita parking ta soma kokarin bude kofar don ta fice kada ma ya ce suje dauko Hajiya Rabi tare, sai ta ji ta gadagau wato ya rufe ta automatically.
Kallon tambayar dalili Amani tayi masa. Idanun ta fal hawaye. Mukhy ya daure fuska sannan ya shafa sumar kan sa ya ce da ita as a brother, zan hore ki da abu daya, duk rintsi kada ki kasance mai munafuntar mahaifin ki, domin mahaifin ki extraordinary Uba ne, musamman a kan ki, ban taba ganin uban da ke son yar sa irin son da mahaifin ki ke yi miki ba. Don haka bai cancanci ki boye masa komai da ya shafe ki ba.
Mai zai hana ki same shi officially ki gaya masa damuwar ki, akan son ganin Maman naki? Im sure yadda Alhaji ke son ki da girmama lamarin ki ba zai ki kai ki ga mahaifiyar ki ba.
Wane irin bincike ne saboda Allah har miliyan biyar? A kasa ake hako kudin? In gaya miki gaskiya an doki hancin ki, don an ga baki da wayau, kuma you are desperate, a kan bukatar ki, ni ki bar ni zan lallaba Alhaji ya kai ki gun Maman naki on koboless (babu ko sisin ki) ba kuma don ke ba sai saboda Alhaji ne ya haife ki. Wani kwayan mutum guda daya da nake matukar kauna da girmamawa.
Alhaji da kan sa ya fi dacewa ya gaya miki inda take, ba sai kin bi ta karkashin kasa kin sha wahala ba
Amani ta yi ajiyar zuciya tana jin wani irin relief na zagayeta a zuciyar ta, yau Mukhy kamar ba shi ba, yana magana ne ta hanyar bata dukkan attention din sa da concern as a brother, duk da ba kallon ta yake ba wayar sa ya ke dannawa a duka maganar da yake yi, amma kuma ya dauki zancen yanzu da muhimmanci, ba don komai ba sai don ya tuno tasa UMMAMIn. Yadda yake son Ummami da yadda yake son zama kusa da ita bai samu ba, ba don komai ba sai dalilin norms, culture and traditions irin na gidan su. Ya yarda rashin kulawar ta a tare da shi ne duk yayi mujazar matsalolin sa a rayuwa da a yau suka saka shi garanranba a duniya. Amani na bukatar tallafin uwa da gaske. Musamman a kan dabiun ta da tarbiyyar ta, kai har addinin ta ma yana bukatar gyara, in yayi duba da irin dressing din da take fita da shi da rashin kunya ga na gaba da irin tabarar data ke yi wa mahaifin ta.
Amani ta ce I wish Daddy din zai saurare ni a kan damuwa ta irin yadda ka saurare ni yanzu, to ba zai saurare ni ba, ban san abinda ya raba su ba amma ko zancen ta baya so na yi masa, ya dauki gaba mai tsanani da mahaifiya ta yana fadin muddin na zabi zuwa gare ta to shikuma zai sallama mata ni ne.
Ta share hawayen ta tace and I love my Daddy more than everybody, saboda da shi kadai na taso, da kaunar sa gare ni na budi ido. Ban san kowa sama da shi ba ko yan uwan mu na Faskari sama-sama na san wasu daga cikin su, bani da wa bani da kanwa.
Cikin tausayi Mukhtar yace me yasa ba zaki neme su ba? Dangi da kike gani suna da matukar muhimmanci a rayuwar mutum, musamman ke da kike mace, daya tal a wurin iyayen ki, babu dan uwa babu yar uwa, it is your duty ki nemi dukkan su ki gyara gurbin rashin zumuncin dake tsakanin ku don hakika kina bukatar su, amma karkashin yardar mahaifin ki, dont ever try to hide anything from him no matter how bitter, ba abunda lallashi da ban baki ga iyaye bazai sa su yi maka ba.
Jikin Amani yayi sanyi kadan, don ta sani bata lallashin Baban ta sam kullum sai rigima da rikici in tana son ya yi mata abu dole ya yi, a kan zuwa gun maman ta ne kawai da korar Mukhy daga gareshi kawai ya taba turje mata, tace cikin murya mai ban tausayi,
ka ce zaka nemo min Mama na? Mukhtar ya ji wani iri a jikin sa da yadda tayi maganar murya na shaking, ya bude mata kofar yace cikin basarwa idan na lallashi Alhaji ya yarda ki je din, ni da kai na zan nemo ta, zan kuma kai ki duk inda take.
Amani ta fita tana dan murmushi, a ran ta tana fadin ashe dai yana da dan kirki ko yaya ne, ga taushin murya, ga jan class, fuskar ce dai bata taba canzawa daga yanayin ta na rashin annuri da bacin rai. Tamkar wanda kullum ake yi wa mummunar bushara ko ake yankan naman jikin sa.
Bai tsaya ta gama bacewa ba ya ja motar sa ya nufi airport don cika daya umarnin na Alhaji. Wato dauko matar sa.
Ya dauko Hajiya Rabi suka kamo hanyar gida, a hanya tana ta mitar an bar ta a shanye a filin jirgi, baa zo daukar ta da wuri ba, mota ba tasa ba amma ya tafi yawon banza da ita yana kwambo a cikin gari gurin yammata, idan yana ikon sa da jin kan sa ya dinga tsayawa iya kan Alhajin da ya kawo shi ya kuma daure masa gindi yana baza iko a gidan mutane, kada ya kuskura ya shiga gonar ta. Ita warki ce daidai kugun kowa yanzun nan zata yi maganin mutum, ko Amani bata isa ta shanyata ba balle shi wani banza a banza.
Mukhtar ya sunkuyar da kai yana jin ciwo a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login