Showing 42001 words to 44162 words out of 44162 words

Chapter 15 - Amani Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

19 Nov 2024

239

Uwa, ku ne tafe? Sunan da yake kiran Amani, kasancewar sunan mahaifiyarsu ta ci, wato Inna Amina mai rasuwa.
Amani ta zumburo baki, kafin ma ta furta wa Yayan uban nata gaisuwa ta alada sai da ta saki korafi irin na rashin kunyar da ta saba yi wa Alhaji.
Za ka fara ko, daga zuwa na? Kira na da UWA? Shi ya ce min wani TAFISU kai ka ce min wani UWA, bayan ga suna na mai dadi na yanka.
Dariya Malam Idrisu ya yi don shi a duniya yana son Amani, duk da halin ta kuwa, ya sa matar sa uwargida Talatu ta yi musu shimfidar tabarma karkashin katuwar dalbejiya da ke tsakar gidan.
Mukhtar ya gaishe shi cike da girmamawa, ya gaida Baba Talatu, Baba Idi na son tambayar Amani inda suka samo kyakkyawan mutum haka, shi kuma ba balarabe ba, don ga hausa ras a bakin shi, amma ya fi damuwa ya ji yadda aka yi dan uwan sa ya koma rayuwa a wheelchair.
Faduwa ya yi a bandaki, ka san yana da hawan jini, shine ya samu stroke. An fidda shi asibiti har kaar Faransa Allah bai sa ya mike ba. Amma yanzu a hakan da sauki sosai, tunda yanzu yana magana ras, yana kuma iya motsa duka hannayen sa.
Baba Idrisu da Baba Talatu suna ta sallallami da jajantawa, tuni suka manta da halin Alhaji. Baba Idi ya ce sai a koma na Hausa, ya san inda ake maganin irin wannan lalurar ta hanyar gargajiya a garin Kaita.
Wannan lalurar da suka samu Alhaji a ciki sai ta maida komai ba komai ba na laifukan Alhaji a gun su, don dan uwan ya damu sosai, tunda shi da ma ba wai yana kwadayin abun hannun shi ba ne, aah zumunci na Allah yake yi da shi, kuma kulawar sa garesu kadai yake bukata.
Kafin dan lokaci Kamilu da yayyen sa biyu Jibril da Usama sun iso gidan, Jibril da matar sa da yayan sa hudu haka shi ma Usman da yaya biyu. Suna ta lale-marhabin da Baffan nasu, tare da jajanta lalurar da ta same shi.
Alhaji sai ya fashe musu da kuka yana neman gafarar Baba Idrisu, yana kuma tambayar Sahura.
Talatu ta ce, Gobe insha Allahu za ta aika mata ta zo daga Funtua.
Nan aka shiga mayar da zance tsakanin Alhaji da Yayan sa Malam Idrisu, ko ya rike dan uwan nasa a baya, ganin halin da yake ciki da nadamar da ya zo da ita duk sai ya ji rikon na narkewa a ran sa. Duk da haka ya fito fili ya gaya wa dan uwan sa yadda yayi wasarere da zumunci bai kyauta ba, ba ya neman kobon sa amma dole ya kyautata zumuncin Allah muddin yana son gamawa da duniya lafiya.
Alhaji har su Kamilu sai da ya bi daya bayan daya ya nemi gafarar su, ya tambayi kowannen su abinda yake ciki, suka gaya masa, cewa wasu cikin su kasuwa suke zuwa wasu gona wasu sun yi karatun NCE wasu har degree, sai Alhaji ce wadanda suka yi karatu a cikin su zai tafi da su a duba ayyukan da suka dace da su a kamfanin Amani, wadanda ba su yi karatun ba ma duk ba zai rasa irin aikin da ya dace da su ba.
Baba Idrisu ya ce, Ai kam ba ka kwashewa duka ka barmu mu kadai, sai kananan yara. Ka dai dauki masu takardun bokon ka bar min sauran su ci gaba da kasuwa da gona.
Alhaji ya ce, Mukhy, sai a binciki irin sanaar da suke yi din a nan a bunkasa ta, a ba su training a kai, sannan a ba su jari mai tsoka.
Consider it done Alhaji.
Abu dai ya yi dadi tsakanin Alhaji da dan uwan sa da yayan dan uwan sa.
Sai washegari Sahura ta iso don amsa kiran da Baba Idi yayi mata tun jiya, Alhaji sai ya ga duk ta tsofe ta mokade saboda wahala, don mijinta ya rasu ya bar ta da yaya takwas. An yi sulhu cikin tausayin juna sun yafe wa dan uwan su, suka ce ba su taba kullatar shi ba ko don Amani da bata yada su ba ita, kullum addua suke masa koda kuwa sunan sa kadai suka ji an fada a kafafen yada labarai.
Baba Idi ya ce, Ah toh ni ai ban damu ba, na sani ko ba-dade ko ba-jima za ka neme mu, tunda ba ka da wadanda suka fi mu.
Kusan kwanan zaune suka yi ranar da Sahura ta zo ana ta maida zance da labarin juna. Alhaji ya ce, tunda Sahura ba ta da karamin yaro duk ta aurar da su, na karshen ma yana makarantar Alkalam a Katsina, to zai tafi da ita gidan sa ta zauna tare da Amani kafin wucewar ta gidan mijinta.
Sahura, Baba Talatu da Baba Idi har suna hada baki wajen tambayar Alhaji cikin mamaki, Uwa ta samu miji ne?
Don su kam basu ga mijin da zai iya daukar Amani ba.
Alhaji ya gyara zama da filon da aka sa masa a bayan sa, ya soma warware musu tun ranar farko na haduwar sa da Mukhtar a kasar Faransa, da irin gudunmawar da ya bayar ga habakar dukiyar sa, amanar sa, halayensa, rikon addinin sa da irin gudun duniyar sa. Ya kare da ba su labarin zuwan Alhaji Sadi neman auren Amani, da sanadin samun lalurar sa da jinyar sa da Mukhtar ya yi a Paris, tare da Amani, halayen Amani da Mukhtar yake tolerating, har da ganewa da ya yi cewa Mukhtar zai iya da halaye da dabiun Amani marasa kyau har ya samu ta gyaru ko ba ta so, a dalilin ganewa da ya yi Mukhtar kadai ta ke shakka, kuma shi ke iya lankwasa ta ta bi raayin sa ko ba ta so.
Wannan ne dalilin da ya sa ya yanke shawarar hada su aure duk da Amani ba ta so, domin auren su ne kadai zai dorar da kyakkyawar dangantakar shi da Mukhtar din.
Yana so wannan ya zama wasiyya da ya bari ko da ta Allah za ta kasance a kan sa gabanin ya daura musu aure da hannun sa.
Yan uwan nasa sun fahimta, sun kuma gamsu da hujjojin sa. Rashin kunyar Amani wa ta bari? Tun tana karama yi ta ke har ya zame mata dabia a girman ta. Mukhtar din kamar yadda Alhaji ya ce yana da dakakkiyar zuciya kuma ya san halin ta, sannan bai yi musu ba da Alhaji ya ce ya ba shi aurenta. Suna da kyakkyawan hope na cewa zai rike Amani ko don kaunar da ke tsakanin sa da mahaifin ta.
Amma sai Baba Idi ya ce, Ka binciki asalin sa? Ka gana da iyayen sa? Ka san daga inda ya fito, kuma ina dangin sa?
Alhaji yayi danjim! Kafin ya ce, Ai ni ko daga sama Mukhtar ya fado, wato bai da iyaye, ko tsintacce ne a kan bola na bashi auren Amani, shaidu ya rage su shaida.
Ni zan masa waliyyi, kai ka yi wa yar ka Amani walicci, goben nan nake so in mun sauko sallahr jumaa lafiya a daura musu aure.
Jiki na na bani ko ma daga wane tsatso Mukhtar ya fito tsarkakken tsatso ne. Tsatso kuma mai albarka. Zaka taya ni fahimtar hakan idan ka zauna dashi na kwana uku.
Baba Idrisu ya ce, Duk da haka, bayan daurin auren dole ya dauki matar sa ya kai ta ga iyayen sa su sanya musu albarka, in basa raye to bazasu rasa dangi ba.
Alhaji ya ce, Na fahimta, amma a halin yanzu na fahimci Mukhtar yana da damuwar da ta fito da shi daga gida wadda ta saka ko a yi masa zancen ya je gida ba ya so.
Bana so na takura masa (for now), da cewa lallai sai ya koma gida zan aura masa Amani, zan ba shi lokaci har zuwa sanda shi da kan sa zai bukaci hakan a karan-kansa, ba abin da lokaci ba ya iya canzawa a rayuwar dan Adam, amma zan roke shi kamar yadda ka ce kan su je garin iyayen sa bayan auren ya gabatar musu da iyalin sa, don su san da auren sa, ba sai sun tara yaya ba sannan su je musu, wajibi ne mu san mun damka Amani a hannun dangin sa da kan mu, saboda gaba a ke hange da yayan da za a haifa.
Baba Idrisu ya gamsu da wannan shawarar ta Alhaji.
Sun tsayar cewa gobe Jumaah bayan saukowa masallaci za su daura auren Amani da Mukhtar. Alhaji zai ma Mukhtar walicci Baba Idi zai wa Amani. Baba Idrisu ya dage Alhaji ya bar Mukhtar ya biya sadakin sa da kan sa. Don da cewa ya yi sadakin ma shi zai biya masa.
Daga Amani har Mukhtar ba su san wainar da iyayen suke soyawa ba, don sun basu wuri ne don su gana da junan su. Shi Mukhtar yana dakin Kamilu inda aka sauke shi, Alhaji dakin da Jibril ya tashi ya bari aka share masa. Amani tana dakin budurwar gidan da ba a yi wa aure ba mai suna Laure. Ta yi korafin cizon sauro, sai da Laure ta je ta sayo maganin sauro ta kunna mata. Nan ma ta ce ba ta son warin sa, a nemo na fesawa. Laure ta fara gajiya da iskancin Amani, ta ce sai ki koma dakin Baba Talatu, ni ba zan kara fita a daren nan ba.
Amani ta ce, Aah, gara in yi maneji da nakin ya fi tsafta kada in je berayen ta da ke tsere a gaban mutane su gwagwiye min kafa.
Washegari Baba Idi ya sa Baba Talatu ta yi karin kumallo mai kyau duk gidan, kunun tsamiya aka yi da lafiyayyen kosai, aka kuma hada da shayi da biredi, saboda Amani da ta ce ba za ta sha kunu ba. Baba Idi ya ce, Ki yi ta yi. Nan din dai shi ne asalin ki, sarkin iyayi da kidifiri, kuma saboda ke tuwon gero za mu yi anjima miyar kuka da daddawa.
Alhaji ya yi dariya ya ce, Tafisu ce, don Allah a dafa mata mai maiko.
Baba Idrisu ya ce, farin balaraben mijin ta ya ba mu na cefane ne? Tunda ya zo fuska ba walwala, sai tamke fuska yake yana muzurai kamar yaci babu, a yi mutum kamar mai fuskar shanu?
Amani ta tashi ta bar wurin, saboda bakin cikin Baba Idi ya alakanta aure tsakanin ta da Mukhtar. A ran ta ta ce, Ah toh! Ashe ba ni kadai na ki jinin yadda yake da rashin walwala ba, mai nuna zuciyar sa ba humanity ba compassion a cikin ta ko kadan. Balle a kai ga zancen soyayya iri ta mata da miji.
Amani ta kyabe baki, a fili ta ce Allah ya tsari gatari da saran shuka ba dai ni Amanin ba. ta ce a ran ta muna komawa Katsina za su neme ni su rasa. Wallahi ba zan zauna a aura min wanda zuciyata ba ta taba kauna ba, kuma har abada ba za ta taba so ba. Na bi jar fata da gudu da bakin gashi na tattake ba takalmi a kafata.
Ana saukowa masallaci a babban masallacin jumaa na garin Faskari Baba Idrisu ya gaya wa Liman a dakatar da mutane, zai daura auren yar sa Amina diyar kanin sa. Tun wayewar gari ya karbi sadakin Amani daga hannun Mukhtar Diffa, wanda ke ji da ganin komai na faruwa kamar almara. Ya kasa gasgata cewa shi Mukhtar ne zai yi aure yau. Ya biya sadaki mafi albarka, wato mafi kankanta daga aljihun sa, wanda ya kasance gumin sa ne. Bai gasgata duka abubuwan da ke faruwa ba, wadanda yake gani kamar a mafarki, sai da ya ji an shafa fatiha, mutanen garin Faskari da suka halarci sallar jumaa a yau duka suka shaida daurin auren Mukhtar da Amani.

*** *** ***

Mu karasa a littafi na 2.
Sumayyah Abdulkadir
07030137870 (whtsp only)


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login