Showing 1 words to 3000 words out of 32136 words

Chapter 1 - Rayuwar Rayhana Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

28 Dec 2024

186

 [12/24/2019, 17:56] Takori: RAYUWAR RAYHANAH! 1
Garin TAKAI, karamar hukuma ce dake cikin birnin Kano, galibin jama’ar Takai Fulani ne da Hausawa farare da bakake, duk inda bahaushe da bafillace suke babbar sana’arsu Noma da Kiwo, manoma da makiyaya sune kashi tamanin cikin dari na jama’ar garin. Kowa ya san jama’ar Takai ya san su da hadin kai da taimakon junan su, rashin son zaman banza, sana’o’in dogaro da kai musamman saye da sayarwa na abinda suka noma da karfin su ko suka kiwata.
Kowa a garin Takai kokarin neman na kansa yake babu wanda ya dogara da wani ba ga mazan kadai ba har matan manya da yara, tsofaffi, ‘yammata, da samari da wuya kasamu wanda baida sana’a, domin neman rufin asirinsa da iyayen sa ko iyalinsa.

Kasuwar Takai tana ci ne ranar Talata. Don haka kamar kowacce Talatar, Malam Rashidu, yana nan bakin kasuwa ya baza hajarsa kwano-kwano cike da dankalin Hausa (Sweet Potatoe). Tun karfe goma na safe har zuwa yanzu karfe biyu na rana babu wanda ya zo inda yake balle yataya dankalinsa. Malam Rashidu yana zaune ne akan shimfidar buhun sa a tsakiyar rana shi da dankalin nasa ko lema babu, ya hada kai da gwiwa kamar zai fashe da kuka, idanuwansa duk sun zurma ciki sabida yunwa da damuwa.
Babban tashin hankalin sa rashin sanin me zai baiwa diyarsa Rahane ta biya kudin makarantar da aka koro ta jiya akan bata biya ba. Rashin abin da zai basu su ci a yau bai daga hankalinsa ba kamar rashin kudin makarantar nan wanda yake janyowa tilon diyarshi a duniya koma-baya a makaranta, ba don rashin kokari ba, a’a, illa yawan fashi adalilin yawan korarta da ake yi na tsayin satittika a kan rashin biyan kudin makarantar nan.
Wasa-wasa har karfe hudu yana nan zaune babu ciniki ko na kwandala. Ya mike ya fara sallar la’asar akan buhunsa da ya shimfida, dai-dai lokacin da wata mota Akori-kura ta yi fakin inda yake.
Ado direban shanu ne dagaTakai zuwa kudu kuma makocin malam Rashidu ne sannan mutumin da yake zaune a gidan sa kyauta shi da iyalin sa ba haya suke biya ba, akan haka ne Malam Rashidu yake matukar girmama Ado, duk da a haife ya haife shi.
Ya fito daga motar ya rufe ya bi Malam Rashidu a sallah, bayan sun idar sun yi addu’a sun shafa ya dubi himilin dankalin dake gaban Malam Rashidu yace
“kamar dankalin naka baya karewa” Malam Rashidu cikin jimami yace “ya za’ayi? Yanayin kasuwar kenan, sai godiyarAllah”
Ya jinjina kai ya ce, “Gaba daya na nawa ne?”
Yace “na naira dari biyar ne”
Ya ce, “Juye min shi a buhu duka”.
Ya kaikace ya zaro kudi a aljihun wandonsa yana irgawa, cikin mamaki mara misaltuwa ya soma juye masa dankalin a buhunhunan biyu, ya daure bakin buhun sosai ya kinkima yasa mai a bayan Akori-Kurarsa.
Adon ya damka masa kudinsa ya mike yana cewa, “To ni na tafi, zan kaiwa iyali, kaima ka koma gida ka huta, in kuma za ka bini ka rage wahalar tafiyar kasa sai ka bini in sauke ka”.
Malam Rashidu ya yi masa godiya hawaye sun cika idonsa, ya ce, “Da keke na zo, kuma zan dan tsaya in tsintarwa su Iya dan cefane”.
Ado ya kunna Akori-Kurarsa mai masifaffiyar karaji yana cewa da Malam Rashidu,
“Wannan godiya haka Malam Rashidu? Ai ba kyauta na baka ba, kayan ka na siya”.
Malam Rashidu ya dafa murfin motar tasa ya ce, “Duk da haka ka taimake ni, Ado Allah ya biyaka ya duba gabanka da bayanka”.
Ado ya ce, “To Amin”. Ya ja motarsa mai hayagaga da buyagin karfe da salansa ya tafi.

Malam Rashidu ya soma nade shimfidarsa ya tattara shirginsa da butar alwalarsa ya dora a gaban kekensa ya sanya su tsakanin hannayensa ya ja kekensa a hankali ya fita daga bakin kasuwa.
Sai da ya yi gaba sosai sannan ya tsaya ya auni gero rabin tiya, dawa rabin tiya, masara tiya daya, ya sayi gwalagwajin kayan miya ya dora a kariyar keken, sauran kudin ya kulle su ya yi gaba.
Ya isa gida ana kiran sallar magariba. Ya aje kekensa a jikin danga, ya soma kokarin sassauke kayan.
Jin motsin shigowarsa Rahane ta yi sauri ta fito bayan danga inda kullum nan yake jingine kekensa, ta karbi kayan a nutse tana yiwa mahaifinta sannu da zuwa. Sanye take da wata kodaddiyar atamfa ‘yar wakas (wax) koriya fatau da ita kamar gudawa duk ta kode.

Rahane ba ta a layin kyawawa ko munana, gata nan dai saisa-saisa, sai dai kuma ga dukkan alamu doguwa ce nan gaba kadan, kuma tana da dirin jiki na budurci mai kyau.
Rahane a nutse take da wata irin nutsuwa mai ban mamaki kai baka ce bakauyiya ce ba, wadda aka Haifa kuma ta tashi akauyen tun iyayeda kakanni, komi a sanyaye take yinsa da nutsuwa da rashin kuzari. Wannan halitta ce ta Ubangiji, amma yara sa’o’inta a kauyensu tsammani suke iyayi ne da yauki ko yanga da kidifiri.
To dai azahiri rashin kuzarin Rahane bai da nasaba da yanga ko iyayi, hasali ma dai bata san su ba, amma dai har da rashin samun abinci mai dauke da sinadarin calcium, protein, vitamin da mineral, sai carbohydrate kadai.

Asalin Malam Rashidu mutumin garin Tsangaya ne, wani kauye a karkashin karamar hukumar Albasu. Almajiranci ya zo Takai, to kuma sai Allah ya yi abincinsa a nan yake, domin yana karatun allo yana dako a kasuwar Takai, har ya harhada ‘yan abin da yake samu yana sarin abubuwa daban-daban na fannin kayan abincin kauye masu saukin farashi yana aunawa yana sayarwa a kasuwa, irin su Gurjiya, Gyada, Yalo, Albasa da ire-irensu.
A nan Allah ya hada shi da Yalwati, bafulatanar Takai ce ya aure ta ya samu ya kama musu hayar gidan kasa mai daki biyu, dan iyayenta sun ce basu yarda ya tafi da ita Tsangaya ba, don haka bayan auren shi da Yalwati (Rahane) ya je Tsangaya ya dauko mahaifiyarshi da ta rage mishi Iya (Bilki), don mahaifinshi ya dade da rasuwa, ya bata daki daya. Shi da Yalwati suna daya.
Gidan ko rijiya babu, ba wuta ba ruwa sai an je tuka-tuka an debo. Babu ko daben siminti, zagaye yake da danga, babu masai sai rami ya haka da kansa ya yi mishi karamar kofa da azara, a nan suke wanka da lalurar su.
Yalwati yarinya ce mai hankali, don haka zaman amana suke da surukarta Iya Bilki. Iya bata da sa-ido, ba ta shiga shirgin da ba nata ba.
Don haka suke jin dadin zama da ita. Sannan ba kwance take ba, da yake da sauran karfinta tana saide-saiden kayan miya, kuka, karkashi, busasshiyar kubewa, daddawa, farin maggi, gishiri, man ja da man kuli, barkono, citta, tafarnuwa da sauransu, tana rufawa danta asiri.
Ita ma Yalwati surfe take ana biyanta, don haka in Malam Rashidu ya samo wani abu wani lokacin sai su ce a zuba a asusu don tarar bukatar bazata, su kukkula su yi abinci daga aljihunsu itada Iya.
Yalwati tana kiwon tumaki da kaji, zabbi, kwakwa da kunkuru, kuma Allah ya sanya mata albarka a ciki, kullum kara yawa suke, in tana da bukatar da ba za ta iya da aljihunta ba sai ta dauki daya ta sayar ta rufa asirinsu ita da mijinta da surukarta.
Ba karamin so Malam Rashidu yake yiwa Yalwati ba, domin abokiyar rufin asiri ce. Ba ta taba daga masa harshe ba tunda ya aure ta, haka kuma take zaune lafiya da mahaifiyarsa. Har Allah ya bata ciki ta haifi ‘ya mace mai kama da ita, sai dai ko fuskarta ba ta gani ba, mai yanke kauna ta yanke.

Mutuwar Yalwati ta wujijjiga Malam Rashidu yanda mutum ba zai taba zato ba. Ya daina wanka, ya daina walwala, ya daina shiga jama’a, ya daina zuwa kasuwa, ko ya ci, ko ya kwana da yunwa, duk daya. Hatta jam’i da makota a kofar gida ya daina zuwa, shi kadai yake sallarsa a dakinsu da Yalwati.
Wannan ya daga hankalin mahaifiyarsa da abokanansa matuka. Bai taba cewa a bashi jaririyar ya gani ba, don a ganinsa ita ce ta yi silar rabuwarshi da matarsa mai sonsa.
Don haka mahaifiyarshi da masu kaunarsa suka dukufa yi mishi addu’a. Iya tasa ake yi mishi rubutun dangana, aka rubuce mishi Alkur’ani ya sha, don haka a hankali ya soma warwarewa ya koma harkokin shi, amma ba kamar da ba.
Iya Bilki, ta ci gaba da rainon jaririya wadda ta mayarwa da sunan mahaifiyarta na asali wato Rahane. Dangin Yalwati sun so karbar Rahane su rike a wurinsu amma Iya ta ki, ta ce da ranta ba za ayi haka ba, sai ko bayan ranta za a raba Rashidu da ‘yar Yalwati.
Da taimakon madarar shanu (fresh) da waken suya, kunu da koko Rahane ta rayu a wajen kakarta. Idan da abin da Iya Bilki ke so a duniya bai wuce Rahane ba.
A hankali Rahane ke rikidewa tana komawa mahaifiyarta Yalwati sak! Ta kamanni, dabi’a da halayya. A haka rayuwarsu ke garawa a hankali.
Rahane na girma hankali na ratsa ta. Ba ta da kwaramniya sam, hatta muryarta sanyi gare ta. Amma fa wasan dandali baya wuce ta, ko ba za ta shiga ba ayi gadar da ita da sa’o’inta ba, za ta zauna gefe ta kunna aci-bal-bal ta tasa farantin dafaffen kwan zabo da take sayarwa a kofar gidansu tana sayarwa, wanda Iya ke dafa mata kullum da yamma. In ta sayar ta zuba a asusunta don zabbin gidan duka nata ne suke yin kwan ta diba. Cikin kasonta na gadon mahaifiyarta.

Sanda Rahane ta isa shiga makaranta lokaci ne da ya zo wa Rahane da karin hankali, ta lura mahaifinta bai damu da ita ba, sai ita kuma ta dage wajen kyautata masa da yi mishi hidima, gyaran dakinsa, wankin kayansa masu datti da zuba mishi ruwan wanka, rowan alwala a buta da sauransu.
Har kekensa take wankewa, sannan kullum ya dawo gida da gudu take taryo shi ta karbo kayan da ya zo dasu ta yi mishi shimfidar sallar magariba.
Tun baya kula har ya gane wata Yalwatin ce Allah ya bashi a matsayin diya. A hankali zuciyarshi ta soma kaunarta, da kanshi ya dauketa ya kaita makarantar firamare, sai dai mai nisa ce sosai da gidansu.
Don haka kullum yake goyata a bayan kekensa ya kaita, in sun tashi ta biyo kawayenta su dawo, don lokacin yana kasuwa.
Makarantar na karbar naira dari biyu da hamsin duk bayan watanni uku daga kowanne dalibi, haka yake kukkullawa ya biya, in bai bayar ba a koro ta, ta kwashe kwanaki a gida kamin ya samu ya biya.
Don lokacin Iya Bilki ta tsufa ainun ba ta sana’ar komai. Tun mutuwar Yalwati yau shekara tara kenan, Malam Rashidu ya ki yin aure, ba don komai ba sai don cewa ya san ba zai samu mai halin Yalwati ba da nagartarta.
Haka nan Iya Bilki ba ta fasa takura masa ba a kan ya yi auren, yana ta ba ta uziri. Don haka ba tare da yin shawara da shi ba ta nema mishi auren Zinaru kanwar Yalwati, uwa daya uba daya, da aurenta ya mutu tana da yara hudu tare da tsohon mijinta.
Shekarar Zinaru biyu tare da Malam Rashidu ta tada bala’in ba za ta zauna ba don talaucin ya isa. Ba haka ta saba a gidan tsohon mijinta ba. Dole ya sawwake mata tun da sauran mutunci, ya kuma roki Iya da ta yiwa Allah ta kyale shi da auren kowacce mace ba zai iya ba, sannan ba kowacce mace ba ce za ta iya zama da shi da talaucinsa irin Yalwati ba! Ta barshi ya raini diyar Yalwati kadai, ya inganta rayuwar ta, yayi mata aure in ta kai munzalin. Wannan ne kadai burin sa a rayuwa.
Bayan wannan ba shi da wani sauran buri, sai na gamawa da duniya lafiya, da cikawa da imani.

Iya ta share hawaye da habar zaninta saboda tuno Yalwati, da tijarar Zinaru, Allah daya gari bamban, kama da wane ba ta wane! Ita dama ta hada auren ne don tunanin Zinaru za ta yi halin Yalwati, ta rungumi diyar ‘yar’uwarta.
To ita Zinaru ma a tsayin shekaru biyu da ta yi a gidan, baiwa ta maida Rahane, suna ji suna gani basu isa suyi magana ba saboda tsoron bala’inta. Don haka rabuwarsu da ita, sai suka ji su sakayau.
Tun daga wannan lokaci Rashidu da mahaifiyarsa basu kara yin zancen ya yi aure ba. Kula da rayuwar Rahane ne a gabansu, da tarbiyyarta, lokacin shekarun Rahane goma sha daya tana firamare aji biyar.
Wata irin shakuwa ce tsakanin Rahane da kakarta, tamkar ta uwa da danta. Iya Bilki na da fada sosai, kuma ba ta daukar wargi. Duk wanda ya taba mata Rahane ko ya ya take da iyayensa ba ta kyalewa.
Idan samari suka aiko kiran Rahane da tabarya take korarsu, in har ka tsaya, ta rusa maka a baya. Wannan yasa duk samarin masu son Rahanen shakkarta, ba mai tare ta da zancen banza irin na sa’o’inta, don sun san karon da iyayensu za suyi da Iya Bilki.
Don haka Rahane ba ta da wani saurayi, amma sa’o’inta da yawa har an ba da su, wasu an sa musu rana. Iya kan ce da Rahane,
“Rabu da shashashai ki yi ta karatu, so nake ki zama malamar asibiti ki taimaki masu haihuwa a kauyen nan, kina dai ganin yadda duk auren wurin ya janyowa su Saude yoyon fitsari, ana ta fada a Radio a daina yiwa kananan yara aure amma basa ji”.
Shi kuwa Malam Rashidu ba shi da buri irin ya ga ya aurar da Rahane dai-dai wannan lokacin ga managarcin miji kamar sauran tsararrakinta, amma tunda ya lura Iya ba ta ko son zancen sai ya tsahirta. Daga baya Ado direba mai gidan dasu Malam Rashidu keciki ya daina karbar kudin hayarsa, sabida wani kuduri nasa na daban.
***
[12/24/2019, 17:56] Takori: Rahane ta shigo da kayan da babanta ya shigo dasu ta aje a tsakar gida, ta yi maza ta kawo mishi ruwan alwala ya karba ya ce, “Sannu Rahane kin ji? Allah ya yi miki albarka”. Ya karbi butar ya yi waje domin ya samu jam’i.
Su ma Rahane da Iya alwalar suka yi, Iya na sallah a daki Rahane na yi a tsakar gida. Bayan sun idar Rahane ta karasa gaban murhu tana cire itacen dake cin wuta tana zakulo garwashin tana kashewa da ruwa, sannan ta soma kwashewa Iya tuwon, tana sakawa kowa a kwanonsa.
Ta jiyo gyaran muryar babanta na kira a tsakar gida, da sauri ta mike tana amsawa ta zo ta durkusa
“Ga ni Baba”.
Ya zaro sauran kudin aljihunsa naira dari biyu da hamsin ya ba ta ya ce ta kai makaranta gobe ta ci gaba da zuwa makaranta.
Farin ciki ya kama Rahane ta ce, “Na gode Baba, Baba Allah ya kara buda maka”.
Ya ce, “Ameen Rahane, Ni dai fatana ki ci gaba da bada himma, kin ji?”
Ta ce, “Insha Allah Baba”.
Washegari Rahane ta koma makaranta, bayan Malam Rashidu ya sauke ta ya juya ya nufi kasuwa. Suna hanyar dawowa ita da Dije ‘yar ajinsu suka ji karar Akori-kurar Ado a bayansu, duk suka matsa gefe.
Ado ya rage gudun motar yana washe katon bakinsa wai shi a wurin shi murmushi yake. Ya ce,
“A’a, ‘yan makaranta an taso ne?” Jajayen idanuwanshi a kan Rahane.
Ko amsa mishi ba ta yi ba ta ci gaba da tafiyarta. Dije ce ta ce da shi, “Eh, mun taso”.
Ya ce, “To ku shigo in karasa daku”.
Dije ta ce, “A’a, ai mun kusa”.
Har yanzu idanunshi a kan Rahane ya ce, “Wai haka Rahane?”
Ko juyawa ba ta yi ba ta yi banza da shi. Bai ji haushi ba ya ci gaba da washe bakinsa ya ce,
“Tunda bakya magana a kan hanya Rahane, to ina nan zuwa da dare kin ji?”
Bai tsammaci amsarta ba daman, ya tada Akori-kurar sa ya yi gaba, ya kasa rufe bakin.

Iya na daki tana kadin auduga, Rahane ta yi sallama ta aje jakar makarantarta, ta fada jikin Iya Bilki tana fadin “Wash! Iya na gaji sosai”.
Iya ta rungumeta tana cewa, “Sannu ‘yar Iya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login