Showing 9001 words to 12000 words out of 32136 words
Rayhanah”.
Ya dau waya ya ce, “Ibraheemu jeka ofishin ‘yan sandan nan ka ce su zo min da wannan mutumin da nasa aka kama yanzu-yanzun nan”.
I.M Takai tsaye ya yi rike da wayar hannunshi “What’s wrong with Daddy ne?” Ya dubi wayar hannunshi sosai cike da takaici, sannan ya dubi Nabilah diyar Hakimi da suke tsaye tare, “Mts! Daddy ya samu matsala Nabilah!”
Ta ce, “Matsalar me?”
Ya sake hura hanci ya ce, “Jirani ina zuwa”. Ya juya ya fita.
Cikin dan lokaci an kawo Ado fada. Malam Rashidu ya dube shi jikinsa yana ta rawa ya ce, “Yauwa don Allah ku sa a sake shi”.
Haushi ya kama Hakimi ya ce, “Kai Malam ka nutsu ka san a inda kake bama son shirmen banza”.
Malam Rashidu ya koma cikin nutsuwarsa. Dacta Mansur ya dubi Ado sosai ya ce, “Da gaske kana son auren diyar Malam Rashidu?”
Ado wanda ya ci kaniyarsa sosai a hannun ‘yan sanda ya ce, “Eh”.
Dacta ya ce, “Shine kuma za ka yi mata fyade a gaban ubanta?”
Ya ce, “Ba nufina kenan ba”.
Dacta ya ce, “To meye nufin ka na tsaraita ta?”
Ya yi shiru. Dacta ya ci gaba da kallonsa a ransa yana mamakin Malam Rashidu, wai wannan mutumin mai kama da ‘yan fashi zai aurawa innocent yarinya kamar Rayhanah.
Ya boye mamakinsa ya ce, “Sulhu nake nema da kai”.
Ado ya dago a fusace, sai kuma suka yi mishi kwarjini ya kasa cewa komai. Dacta ya ci gaba da cewa, “Ka lissafa duk abin da ka kashewa Mal. Rashidu da ‘yarsa zan fanshe su ba ta isa aure ba!”
Ado ya gallawa Mal. Rashidu harara wanda ya takure ya yi lakwam yana kallon Ado a tsorace. Ado ya bude wawulon bakinsa ya ce cikin zafin rai, “Hakorana da aka zubar min fa?”
“Zamu makala maka na roba yanzu”.
Ya ce, “To a rabani da ‘yan sandan nan”.
Hakimi ya ce, “An raba ku”.
Ado ya ce, “Naira dubu dari biyar zaku bani, kuma su tashi su bar min gidana”.
Hakimi ya yi murmushi, ya jawo wata bakar akwati ya bude, ya dauko daurin kudi ‘yan dubu-dunu dauri biyar ya zube su a gaban Ado.
“Gasu, gidanka kuwa ko komawa ba zasu yi ba. Duk tarkacen dake ciki ma sun bar maka. ‘Yan zaman makokin ma in kaso ka koresu ka koresu su zo nan su yi”.
Ado ya gigice don dai kawai ya shaci kudin ne da gayya bai taba zaton ba za suyi musu ba.
Ya kwashi kudi ya nade cikin rigarsa ya mike zai fita, cike da tsoron kada su kwace kafin ya kai kofa. Dariya ta kama Dacta Mansur ya ce, “Hakoran fa Ado?’
Ya ce, “Barsu kawai, zan je kudu a sa min”.
Gaba daya suka sa dariya har Mal. Rashidu dake takure a gefe sai da ya murmusa.
Karshen diramar Ado da Rahane kenan. Tunda ya hada kudin nan ya gudu ya bar Takai, ya bar ‘ya’yansa da matarsa ba a kara jin duriyarsa ba. Aka bawa Mal. Rashidu muhalli a cikin gidajen bayin Hakimi, washegari ya fara aikinsa na kula da Dawakin Hakimi.
Dr. Mansur da dansa I.M suka taho Kano da Rahane, bayan ta yi sallama da babanta.
RAHANE A GIDAN DR. MANSOOR
Gidan Dr. Mansur Balarabe Takai babban gida ne mai tsarin gaske a unguwar Lamido Crescent, wanda ke rufe cikin bakin girgijejen get. Asalinsa Turawa ne suka zauna cikinsa shekaru masu yawa da suka gabata lokacin mulkin soja sanda suka bude kamfanin PZ da za su koma kasarsu suka sayarwa gwamnati.
Lokacin da Dr. Mansur ya yi kwamishinan lafiya a Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya, gwamnati ta bashi gidan ya zauna, da tenure din su ya kare ya yi kokarin da ya sayi gidan da taimakon mahaifinshi mai girma Hakimin Takai na III (Balarabe Sardauna).
Haka ya ci gaba da sabunta gidan, yadda zai yi dai-dai da zamanin da ake ciki har kawo yau.
Gidan farin fenti ne da shi, kana shigowa cikin get din gidan mikakkiyar kwalta ce wadda zata sadaka da rumfar adana motoci a kalla biyar, ba tare da kowacce ta gogi ‘yar’uwarta ba.
Idan ka yo gaba kadan grass carpet ne wanda zai kai ka bakin kofar reception din gidan. A cikin reception din matattakalar bene take wadda za ta sadaka da falon sama da yake kunshe da dakunan barcin jama’ar gidan.
Dakunan barci hudu ne a cikin falon, daya na Dr. Mansoor, daya na Mami, daya na I.M da Yayansa Khalipha, wanda a halin yanzu yake karatu a jami’ar BAZE dake Abuja, yana karantar hulda da kasashen ketare wato (International Relation). Daya dakin na Abida da Jawahir ne, sai autar su Azizah.
Abida shekarunta takwas, Jawahid goma, Mami ta dade bayan haihuwar Abida kafin ta haifi Aziza wadda ke da shekaru uku a halin yanzu.
Saboda tsantsenin tarbiyya irin na Dr. Mansur bai warewa I.M da Khalipha daki a wajen gidansa ba, duk da girmansu tare yake dasu yana ganin kowanne motsinsu. Idan abokai ne ga reception nan bai yarda ko baskwata su zauna ba, masu aikace-aikacen gidan ne a baskwatan.
Motar Dr. Mansur ta sako kai farfajiyar gidansa. Ibraheem ne ke tukin. Dacta na gaban motar rike da jaridar This Day da ya saya a go slow din roundabout na kofar Nassarawa. Rahane na baya a makure jikin kofar motar kamar ka ce kyat! Ta bude murfin motar ta arta a na kare.
Abida da Jawahid ne zaune a rumfar adana motoci tare da malamin Islamiyyarsu dake zuwa duk Alhamis da Juma’a yana koya musu karatun Alkur’ani da Hadisi, tajweed da Tawheeed, ga bakin allo (black board) an kafa musu cikin rumfar adana motocin. Ta bala’in raina malamin, don Abida ‘yar rainin wayau ce, sabanin Jawahir da ko magana ba sosai take yinta ba.
Jin shigowar motar Daddy Abida ta nutsu daga mintsinin Jawahir da take yi, shi kansa Malam Umar ya lura Abida ta shiga taitayinta, don haka ya juyo don ganin abin da ya nutsar da ita.
Daddy ne da Ibraheem ke fitowa daga mota, tare da wata dukun-dukun din yarinya baka wuluk! Kanta a daure cikin wani bakin tsumma da wani sidadden silifa a kafarta, ko’ina a jikinta ciwo ne, wani da plasta wani plastar ta daye.
Abida ta soma zungurin Jawahir don ita ma ta juya ta ga abin da ta gani, amma Jawahir ta yi banza da ita ta ki juyawa ta ba da hankalinta sosai ga Malam Umar.
Malam din ya aje Alkur’anin dake hannunsa ya isa ga Daddy ya tsugunna yana gaisuwa. Daddy ya amsa ta hanyar bashi hannu sukayi musabiha. Tuni Ibraheem ya shige gida. Daddy ya kama hannun Rahane suka doshi reception.
Rahane dai taku take a tsorace, don ita tunda Allah ya halicce ta bata taba ganin waje irin wannan ba, kamar Aljanna da ake kwatantawa.
“Mami! Mami!!”
Daddy ke kira a falon sama.
Ta fito daga laundary inda take shanyar kayan Azizah data wanke cikin injin wanki, sanye take da riga da siket na wani bakin material mai yarfin light green flowers, gashin kanta kame da hair-bound, shima light green ya sauko har kafadunta. Duk wani likita kirki ne da shi, to haka Dr. Asma’u Takai, musamman kasancewarta likitar yara.
Amma a yau kam ga dukkan alamu za suyi fada da Dactan nata, don kirkin nata bai kai nan ba.
Za ka rantse ba ta haifi Da kamar I.M ba, balle kuma Yayansa Khalipha. Ta fi kama da matashiya ‘yar shekaru talatin ba talatin da tara ba.
Ta fito falon tana fadin “Dacta na!” Shima ya ce, “Mamina!!”.
Ya juya ga Rahane, “Rayhanah matsa ki gai da Mamanku”.
Sai a lokacin ta kai idonta ga Rahanen da ta zube a gabanta tana fadin “Barka da yamma Hajiya”. A firgice ta juya ga Ibraheem, sannan Daddyn ta kasa tambayar komai.
Dariya ce ta kama Ibraheem ganin idanun Mami sunyi mitsi-mitsi, ya lallaba ya shige dakinsa kada dariyar da yake yi ta fito.
Daddy ya yi murmushi ya isa ga Rahane yasa hannu ya cira ta daga zubewar da ta yi kamar bawa a gaban Ubangijinsa. Ya zaunar da ita a kujera yana ce da Mami
“Karin ‘ya na kawo miki, sauran bayani sai anjima, yanzu ba ta abinci da ruwa tukunna mun sha tafiya”.
Ta dan saki fuska ta koma kicin ta zubo abinci a plate da robar ruwan Eva mai sanyi da lemun La-casera ta kawo mata kan tebir. Amma da ta kira yarinyar ta ce ta zauna a kujera ta ci, sai ta ga ta sauke plate din kan marbles ta bararraje abinta tana ci kamar Allah ya aikota saboda yunwa.
Ta bi bayan mijinta cike da mamaki. Ta same shi yana cire safar kafarshi a gefen gado, ta zauna a kasan kafafun nashi ta karbe shi. Sai da ya yi wanka ya kwanta yana hutawa, Mami ta matsa jikinsa tana cewa,
“Ina ka samo yarinya bakauya haka?”
Ya ce, “Garinmu Takai”. Ta ce, “Yar waye?”
Ya ce, “Yar AMANA!”
Ya tashi daga kishingidar da ya yi ya kama hannayenta masu taushi ya ce, “Mami batun yau ba ni da ke muke da bambancin ra’ayi a kan al’amura da dama, amma kowa ya kasa rinjayar dan’uwanshi ya bi nashi ra’ayin.
Amma a yau ina neman alfarma Mami, wadda na san mai girma ce a gare ki, ita ce ki rike min Rayhanah kwatankwacin rikon da kike yiwa ‘ya’yan da kika haifa.
Ko da komai bai zamo hundred parcently equal ba, ki kwatanta kara da karamci. Rayhanah da ubanta ba shegiya ba ce. Sai dai marainiya ce ba ta da uwa, ta rasu tun lokacin haihuwarta. Ta girma a hannun kakarta, ita ma yanzu babu.
Na tserar da ita ne daga kaskantacciyar rayuwa da ubanta ke so ta yi, wato early and abusing marriage, sakamakon wasu extraordinary characteristics dana gani a tare da ita.
Ban taba haduwa da pateint din da ya shiga raina irin ta ba. Sannan ta gamu da ‘lalura’ wadda dole a tausaya mata, a bata kwarin gwiwar da zata fuskanci rayuwa a, duk yadda ta zo mata.
Ta samu hearing impairment wanda bazamu ce a sakamakon hadarin da suka yi bane, har yanzu source din, bai bayyana garemu ba, har sai anyi CT Scan and MRI Scan, wadanda bamu da injinan yin su anan Nigeria, in kin lura akwai hearing-aid a kunnenta. Mami ban taba neman alfarma kin kasa yi min ba, a yau wadda nake nema ma ba za ta gagareki ba, tunda kin saba haihuwa kin san ciwon DA. Yadda naki yake a ranki haka na kowa yake a zuciyar nashi iyayen.
Ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmominki gareni, ki rike min RAYHANAH da zuciya daya, ni kuma duk abin da kike so zan miki Mami. Wallahi-wallahi ko da bani da shi zan nemo. Kawai ina so Rayhanah ta yi rayuwa mai kyau kamar ‘ya’yanki. Ta yi ilimi, ba tare da nakasunta ya nakasta rayuwarta ba. Zan samu Mami?”
Ta sauke idonta a hankali kan mijin nata, ta rasa shi wane irin mutum ne, mai maida damuwar wani tasa. Ba ta da muguwar zuciya ko kankani, sai dai ba ta son kowa ya rabi rayuwarta da mijinta da ‘ya’yanta.
Ba ma wannan ne abin tsoron ba, za ta hada ‘ya’yanta ne da yarinyar da ko asalinta ba ta sani ba? Kai rigimar Daddy da yawa take.
Ta ce, “Daddy zan yi maka alfarmar da kake so, amma a bisa sharadi biyu”.
Kallonta ya yi, kallon ke nake sauraro. Ta ce, “Ka yi min alkawarin WATARANA ba zaka ce za ka hada aure tsakanin ‘ya’yana da wannan yarinyar ba. Sharadi na biyu shine, zan raba musu daki da su Abida, don hankalina ba zai kwanta ba idan tana tare dasu”.
Dariya ta bai wa Daddy sosai. Ya ce, “Mamee!”
Ta ce, “Dacta naa!!”
“ki kwantar da hankalinki da Rayhanah, ba zan kawo abin da zai cuci su Abida ba. Am their Dad, remember? Baki fini son su ba!!!.
Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa kisa ranki a inuwa sassanya, Allah zai baiwa Rayhanah miji na ban mamaki wanda zai kaunaceta domin Allah ya rungumeta da lalurar ta, ba ‘ya’yanki ba, masu hali da akida irin taki, ‘ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba! MAZA ma tukunna, baki gansu ba Mami.
In kin so ki aura musu ‘ya’yan Queen Elizabeth, karshenta dai kenan ko? Ki rubuta ki ajiye, babu aure tsakanin ‘ya’yanki da Rayhanah! Tunda ita baki dauketa cikakkiyar mutum ba”.
“Ba haka nake nufi ba Dacta na?”
“To ya ya ne?”
“(A bit.......depressed). Ta ce, “Ni dai in hakan za a yi bani da matsala da yarinyar”.
Dacta ya ce, “Mami, hoo!”
Rahane tuni barci ya kwasheta a kan marbles din dining, inda ta ci abinci. A haka su Abida suka shigo suka sameta, Abida, Jawahir da Azizah suka sunkuya suna kallonta.
Abida ta leka tafin kafarta ta ga faso da kaushi! Ta ce, “Ehoo! Yau faso zai yaga bedsheet din Jawahid, don kuwa ba dai gadona ba”.
Aziza kuwa dukanta take tana cewa, “Tashi-tashi, cinnaka zai cijeki, ki hau gado”.
Jawahir kuwa hannunta ta kama tana cewa, “Tashi muje daki za ki dauki sanyi a nan”.
Ta bude idonta a hankali tana kallon su. Ba ta taba ganin kyawawan mutane irin wadannan yaran ba.
Dacta ne da Mami suka fito tare jin hayaniyarsu, suka gansu zagaye da ita kamar sun ga wata sabuwar halitta. Mami ta ce, “Mene ne haka? Ku kaita daki mana ta yi wanka sai ta kwanta ta yi barcin”.
Abida ta ce, “Ar! Mami kafarta faso! She is smelling bad!! Da soson wa za ta yi wanka?”
Dacta ya dunkule hannu ya danna mata, “Da na Uwaki. Ja’ira mara hankali”.
Ya matsa gabansu ya ce, “Kamata Jawahir kuje daki ki taimaka mata ta yi wanka, kin gani ba ta da lafiya”.
Jawahir ta bi umarnin mahaifinta. Suka shiga daki da Rahane. Ta cika mata ruwan dumi a kwami, ta zuba dettol, ta bare sabon sabulun zest da sabon soso ta bata.
Ta ce, “Ki yi wankan sosai kin ji, amma ki yi a hankali kada ki fama ciwukan ki”.
Ta nuna mata hanger, “Ga towell nan, ki dauki wanda kike so. Wannan kwandon ki zuba kayan da kika cire kayan wanki ne a ciki”.
Rahane ta ce, “Ai ban zo da wasu kayan da zan canza ba in na ajiye wadannan”.
Ta ce, “Zan baki nawa in ji Daddy”. Ta juya ta fita tana cewa, “Ki yi wanka sosai”.
Rahane ta yi tsaye tana kallon katon ramin da aka cika da ruwa aka ce wai ta shiga ciki tsulum! Ta yi wanka. To idan ta nutse fa?
Ta kai hannu a hankali tana shafa gefen kwamin, santsi kamar jikin tarwada. Ga shi fari kal! Shi kansa ruwan kamshi yake. Ta fi minti ashirin ta shafa nan, ta kalli kanta a mudubi, ta kasa ko da cire kayan jikinta. Ga bayan gida tana ji amma ba ta ga masai ba, sai fararen tangaraye a rufe, da ta bude ruwa ne a kwance a cikinsu garai-garai, ta rasa inda za ta sa kanta, domin bayan gidan ya matseta. Ta kuma rasa a inda za ta yi, sai ta goce da kuka.
Daga daki Abida da Jawahir suka jiyo ta, Abida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Yanzu haka faduwa ta yi cikin soka-way”.
Da sauri Jawahir ta iso bakin kofar tana buga mata tana cewa, “Lafiya?”
Ta ce, “Tutu nake ji”.
Ta ce, “Mene ne tutu?’
Ta ce, “Bayan gida”.
Ta murda kofar ta shiga gaba-gadi, nan ta tarar ko kayan jikinta ba ta tube ba balle ta yi wankan, tana tsaye tana share ido. Tausayi ya kama Jawahir, ta bude masai ta zauna a kai.
Ta ce, “Haka za ki yi ki yi bayan gidan. Sai ki murda nan ruwa zai fito ya kora shi. Nan kuma shima zama za ki yi ki danna nan zai yi miki tsarki. Ko ki