Showing 18001 words to 21000 words out of 32136 words

Chapter 7 - Rayuwar Rayhana Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

28 Dec 2024

193

Har zuwa inda yau ke motsi, Abida bata daina cuzgunawa Rahane ba, musamman da aka mai da su nesa da gida babu Baba Dacta balle Khalipha.
Jawahir kuwa dama ta riga ta rainata kamar ita ce babbar. Haka take fadawa ‘yan ajinsu da ‘yan hostel dinsu Rayha ‘yar matsiyata ce ta zo ta makale musu, Babanta na kauye ya asirce babansu ya lika musu ita.
Sannan a gaban Raihan take fada, don ba tsoron Jawahir take ba. Uffan ko daga ido Rayhanah ba ta yi balle ta yi magana. Son Abida take bilhaqqi, saboda darajar iyayenta da Yaya Khalipha.
Khalipha wani irin mutum ne mai matukar tasiri da alheri cikin rayuwar Rayhanah, ko kadan baya son ya ganta cikin rashin walwala. Duk da dai dama ba mai walwalwar ba ce. Abubuwa iri-iri na gilmawa a zuciyar Khalipha a kan Rayhanah, yarinya ce da ta iya takun rayuwarta matuka, ta kuma iya tafiyar da mutum da halinsa.

Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa ba kyan sura ba. Rahane mai aji ce (classique). Duk da tushenta shine kauye. Ba kyakkyawa ba ce, sannan ba ta da wani abu mai fizgar hankalin namiji banda halayenta. A fuska kam babu kyan, amma a halittar jiki sai an tona cikin dubu kamin a samu goma irin Rayhanah.
Ba ta damuwa da lallai cewa sai ta sanya hearing aid in ba lokacin daukar darasi ba. Sai ta yi kwanciyarta shiru a kan gadonta, ta yi ta tunanin makomar rayuwarta.
Wato yanzu da Rahane ta kara shekaru, sai ta kara sanin ciwon kanta. Baba Dacta da Mami ba jininta bane, ba ta da kowa da za ta bugi kirji ta ce nata ne banda Babanta. Wanda ke ta fama da kansa a halin yanzu, yau ciwo gobe lafiya ba a san hakikanin abin da ke damunsa ba.
Ranar da Baba Dacta da iyalinsa suka gaji da rikonta, ina za ta je? Tsufa ya soma cimma Malam Rashidu. A zahiri babbar matsalar ciwuwwukansa kenan, ta fahimci cewa ita din abin tausayi ce. Karatun nan da Baba Dacta ya tsaya mata take yi shine kadai madogararta sai Ubangijin Talikai.
Duniya ba matabbata ba ce, haka komai na cikinta yana da lokaci. Ta fahimci akwai ranar da dole za ta bar hannun Baba Dacta da Mami tunda ba su suka haife ta ba.
Ranar da hakan ta faru ina za ta? Takai?
Ai ko gida basu da shi a Takai. Babanta babu lafiya ga tsufa, ta kowanne bangare idan ta duba sai ta ga kawai Allah ne gatanta sai yadda ya ga dama zai shirya mata rayuwa.
Wani tunani ne ya fado zuciyar Rayhanah farat daya, zuciyar ta ce AURE! Rayhanah ki yi aure ki samu ki kafa naki iyalin ki yi tabbatacciyar rayuwar iyali. Ki haifi ‘ya’yan da za su rungumi rayuwarki wata rana.
Amma abin tambayar a nan shine, wa za ta AURA? Wane ne zai iya aurenta da LALURAR ta? Wane miji ne zai juri cewa sai matarshi ta saka inji kafin ta ji magana? Wane ne zai ba ta kwarin gwiwa irin wadda Khalipha ke ba ta? Wane ne mai kirki irin Khalipha?
A cewar Abida ita MUNAFUKA ce, son Yaya Khalipha take yi, shi yasa ta damu da shi fiye da kowa a gidan. Idan ita MUNAFUKA ce don tana son mai kyautata mata, ita kuma da take tozartata a bayan idon Khaliphan yaya sunata? They are all the same kenan ko?
Kwata-kwata ma ita ba ta san wane irin so Abida ke nufi ba, don ta kan ce ya fi karfin ki.....ba ajinki bane.....me zai ci dake? Ya yi kama da mai saran kofaton Doki ne? Da sauran maganganu irin wadannan wanda inda sabo, to RAYHANA ta saba jin ire-irensu daga bakin Abida.
Abida ta fi Jawahir power, ta fita baki, ga tsiwa, ga rainin wayau. In ta raina mutum ya shiga uku. ‘Abida Hukuma’. Sunanta kenan in ji Khalipa, domin duka baya karya mata zuciya sai dai ma ya kara tunzurata ga abin da ake dukan nata a kansa. Ya kara kangarar da zuciyarta a kansa.

****
Wani abu da ya kara ta da ma Abida hankali a kan Rayhanah shine, kokarin da ta zo ta fita sakamakon wasa da tsokanar da ta sawa ranta.
Sunyi jarrabawar shiga aji biyar, Rayhanah ta kwace 3rd position na ajin wanda Abida ke kai tun farkon shigarsu Ulul-Albaab, ita kuma ta kwaso na goma.
Sun zo gida hutu ranar Asabar, a yammacin ranar ne Khalipha ya iso, sanye yake da ‘yar ciki da wando har da babbar riga na wata danyar shadda (sheraton) kalarta coffee wato ruwan kasa. Ya dora hula damanga a kan goshinsa, daman dai Khalipha ba dai iya karya karin hula ba, ita ma ruwan kasa ce.
Takalmin fatar damisa ne a kafarshi budadde wanda kudinshi ya haura naira dubu ashirin, Dattijon, daure yake da agogon polo na fata a damtsen hannunsa launin kayan jikinsa. Shigarshi reception rataye da babbar rigarsa a kafudunshi da wata karamar bakar jaka mai dauke da komatsansa masu muhimmanci.
Da sassarfa ya soma taka steps don cimma falon sama, sai suka yi karo garam! Da goshinsu shi da Rayhanah.
Goshin nasa ya kama ya ce, “Kai-kai-kai! Rayhanah goshi za ki fasa min in rasa matar aure?”
Ita ma ta kama nata goshin cikin irin muryar zolayar da ya yi mata maganar da ita ta ce,
“Kai Yaya Khalipha, kai ne fa ka kara mini”.
Ya bita da idanu luuuu! Wani chemistry ya yi aiki cikin ‘yan dakikai. Ba ta taba ganin irin wannan kallon da Yaya Khalipha ke mata yanzu a idon kowa ba, ji ta yi ba za ta iya jurewa kallon ba don haka ta yi saurin dauke idonta ta rabe ta gefensa za ta wuce, sai ji ta yi ya riko hannunta ba tare da ya juyo ba.
Mintuna uku suka dauka a hakan, ta yi saurin zame hannunta da sassarfa ta karasa sauka daga matattakalar zuwa aiken da Mami ta yi mata wajen Mal. Dahiru maigadi.

Tun daga wannan ranar Rayhanah ta samu kanta da matsananciyar kunyar Khalipha, ba ta kara bari ya ganta ba, in ta jiyo muryarsa a falo ba ta fita. Shi kuma dama tuni ya daina shiga dakinsu, tunda suka dan tasa. Balle yanzu da suka zama ‘yammata ko yau aka yi musu aure gobe za su haihu.
Ya damu kwarai da ya ganta, don haka yake yawan zaman falon amma ko keyarta babu. Mami da Dacta sun je wata seminar likitoci a kan cutar Shan Inna a kasar Algeria, daga ita sai Abida ne a gidan, don Jawahir ma da Azizah suna Jos. Har ya kammala week end dinsa ya koma Rayhanah na mishi boyo.

Khalipha Mansur, zaune a ofishinsa yana shigar da wasu sakonni cikin kwamfuta zuwa Nigerian Embassy Accra (Ghana). A kan zuwan Ghanain President (Rawlings of Ghana), wanda zai zo Nigeria cikin satin ya haura Philippines daga Nigeria suka samu matsalar visa za su fito daga kasar Kenya.
Haka nan ya ji aikin ya gundireshi. A dan tsukin nan tunda ya dawo daga gida, ya rasa gane kansa, ya kasa gane me ke damunsa.
Gaba daya ya tattaro hankalinsa da tunaninsa wuri daya. Ya zubawa tafin hannunshi ido, a hankali kuma ya kai shi hancinsa, still kamshin Escada Sentiment yana nan bai gushe ba, domin ko da ya zo wanka bai yarda ya wanke hannun ba, kada ya daina kamshin turaren RAYHANAH.
Khalipha, duk da cewa yana kan gabar kuruciyarsa, kuma a kan matakin da babu macen da ba za ta so shi ba. To fa ba kowacce mace yake kallo da kima ba har ya taba yiwa kansa sha’awar aurenta, mata iri-iri kam ya yi mu’amala dasu tun zamanin yana karatu, anyi abokai cikinsu an kuma yi ‘yammata, sai dai kuma babu wacce mu’amalarsu ta kai labari tsahon shekara daya za ayi hannun riga, don shi bai yarda yana neman yarinya wani ma yana nemanta ba, daga ranar da ya gane hakan duk son da yake mata ya barta kenan har abada.
Hibba kuwa da Hakimi ke son ya aura, har ta gaji da jiransa ta kama dahir, yanzu haka har an sa mata rana. Saboda tamaula da hankalin da yake mata.
Da fari ya ce karatu, ta jira shi ya karasa, ya dawo ya ce Bautar Kasa. Nan ma ta jira shi. Sai kuma ya dawo ya ce sai ya fara aiki, ta jira shi har ya samu. To fa kuma tunda ya fara aikinsa, bai kara bi ta kanta ba, ita kuma ta ga ba rasa manema ta yi ba zai sa ta tsofe a gida alhalin kuma ba shi da niyyar auren ta. Don haka ta yiwa kanta ludufi ta dauki na damo, ta bar Nabilah da koshin wahala......
Yau shekara guda kenan da kammala karatunsu amma tana nan tana jiran Ya Himu, wanda tunda ya cilla kafa a Chicago ba a kara jin duriyarshi ba, ko waya ba sosai yake yi da jama’a ba, idan ya gaisa da Hakimi sai ya ce a gai da kowa.
Sannan ba shi da takamaimiyar lambar waya, wani zubin ma a bakin hanya zai tsaya ya sa (credit card) dinsa a commercial ya kira wanda ya ga dama ya zare abinsa.
Kowa na kokari a kan Nabilah ta yi hakuri da Ibraheem amma sai tasa musu kuka. Hajiya Karima kan ce, “Nabila ki yiwa kanki fada ki zabi daya cikin masu sonki ki aura tun tauraruwarki ba ta dishe ba.
Kuruciyar ‘ya mace ta dan lokaci ce, shekarunki ashirin da bakwai ga kwalin digiri ga na master, kina tunanin idan Ibrahim ya dawo yadda yake ji da kuruciyar nan zai aure ki? Wallahi shi a lokacin ne zai fara samartakarsa, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”.
Nabila sai dai ta hura hanci ta zumburi baki, ko me za a ce in dai a kan Himu ne ta bayan kunnenta yake wucewa.

Khalipha ya yi baya da lallausar kujerarsa, ya bi jikinta ya kwanta ya lumshe ido. Abubuwa da yawa ke sawa ya so mace, amma ba kyan fuska da kyale-kyale ba, dukiya ko zuzzurfan ilimi. Yana son mace wadda ta san kanta (mai tsare gida da rashin kula maza). Kuma yana son ta kasance mai aji ba kyakkyawar da kowanne karabiti zai biyota a dalleliyar mota ya ce yana sonta ba.
Yana son mace mai kunya, wadda ba ta iya hada ido da namiji in ba dole ba. Mai karancin magana, ba wadda za ta zauna cikin mutane ta yi ta zuba kamar ‘ya’yan kanya ba.
Baya son mai alfahari da son nuna iyawa, baya son mai gwalli da kwarkwasa, baya son wadda za ta cika fuska da jan baki, eye shadow da su maskara da hoda. Baya son wadda za ta rambada ‘yan kunnaye da sarkoki bula-bula (Barima da hudar hanci sun isa). Baya son mai hasken kanti, sai baka mai gogaggiyar fata tunda shi fari ne sol, wadda ba mai ne ya gogeta ba, irin yanayin da take ciki ne.
To amma ya hanga ya duba cikin mata bila adadin bai ga mai wadannan extraordinary characteristics din ba sai RAYHANAH, bai taba jin yana so ya yi aure ba sai yau. Ba kuma da kowa ba da ita kadai Rayhanan Baba Dacta. Hannunta kawai ya kama (by mistake) a ranar ya tuna cewa ashe shima NAMIJI ne mai bukatar mahadin rayuwa.
Lokaci daya kuma lalurar Rayhah ta fado mishi a rai LOVE HAS NO BARRIER ( soyayya bata da shinge). Hasali ma Ji ya yi lalurar tace tun farko ta dasa tausayin ta a zuciyarsa, wanda yayi ta rikida har yau daya bayyana ainahin kalarsa; daga tausayi zuwa kauna.
Lalurar ce kuma har ila yau, da tsantsar hakurin ta akanta da komai ma na rayuwa ta sa ya kara sonta da tausaya mata. Ya ji wani bangare na zuciyarsa na gaya masa kai kadai ne za ka aure ta ba tareda lalurar tat a dame ka ba, ka zauna da ita cikin kowanne hali. Tana da lafiya ko bata da lafiya.
Ka tallafi maraicinta, ka tallafi kanka ta hanyar samarwa zuciya abin da take so, in addition ka samawa ‘ya’yanka uwa ta gari, ka kuma mallaki ragamar rayuwarta da ita kanta Rayhanah.
Ya lumshe ido a hankali ya koma ya jingina da kujera.

****

Duk yadda ya so ya je gida a satin hakan bai samu ba, sai da ya gyara matsalar visar Rawlings daga Nigeria zuwa Philippines. Kawai so yake ya yi tozali da Rayha.
Duka kannenshi akwai hotonsu cikin wayarsa, Raihahn ce kawai babu. Ya dokantu, ya jigatu a tsayin satin gaba daya da son ganin Rayhanah.
Ranar Juma’a da daddare Mami na zaune gaban madubinta tana shafa bayan ta fito wanka. A gefen ta Rayhanah ce take jera kayan Mamin da aka kawo daga wanki a sif din Mamin.
Doguwar riga ce ruwan bula a jikinta da farin Hijab mai santsi iya kafadunta, sallamar Khalipha a falo suka ji yana fadin “Mami na!”
Ta ce, “Ina zuwa”.
Ta karasa shafar ta sanya kaya tana ce da Rayhanah “Dan hayaniyar nan ya iso yau kunnuwanmu ba hutu”.
Ai da jin haka Rayhanah ta lallaba ta shige bayin Mamin ta rufe kanta ta yi zamanta a kan kwamin wanka tana kokarin daidaita numfashinta.
Khalipha ya zame mata dodo, ita kanta ba ta san dalili ba, zuciyarta na jigatuwa a duk lokacin da ta tuna shi. Wannan ya fara ne tun ranar da ya rike mata hannu, ta kan samu kanta cikin yawan tunaninsa da mafarkin sa cikin barci. Wani al’amari ne mai girma da zuciyarta ke fama da shi a kansa da ita kanta ba za ta iya fassarawa ba.
Abida tana Takai, Jawahir ce da Azizah a gidan, ita ma Mamin night duty za ta tafi. Don haka a kintsenta ta shigo falon da lab-coat a hannu.
Ta ce, “Muje ka sauke ni ma gaisa a hanya”. Tare suka fita.
Rahane ba ta fito ba sai da ta bari suka fita ta lallaba ta koma dakinsu ta kudundune ta hau barcin dole. Tana addu’a cikin ranta Allah yasa kada Yaya Khalipha ya neme ta.
Da ya dawo ba kowa a falon, Azizah ce ta fito daga dakinsu da gudu Jawahir ta biyo ta da duka.
Ai tana ganin Khalipha ta yi tsalle ta dane shi, “Yaya Khalipha boye ni za ta duke ni”.
Ya kuwa boye tan, ya ce da Jawahir da ta karaso, “Kina tabata zan rama mata”.
Jawahir ta turo baki a shagwabe ta ce, “Don baka san me ta yi mini bane Yaya Khalipha, duk ta cike min text books dina da zane-zanen ‘yan aljanu”. Abin ya bashi dariya.
Ya ce, “Wai haka Zizahna?”
Ta ce, “Yi hakuri Anti Jawahir ba zan kuma ba”.
Ya ce, “To kin ji ta baki hakuri, sai ki yi mata afuwa Allah yana son masu afuwa”.
Ta juya ta shige daki tana kumburi. Ya ce, “Zizah ina Rayha ne?”
Ta ce, “Tana wanka”.
“To maza je ki gano min ko ta fito ki ce ta zo ta karbi ‘She stillborn’ din da ta bani sautu tun last month sai yau na samu”. Ta juya da gudu ta yi dakin.
Lokacin da ta fito wanka kayan sallarta da hijab dinta dogo har kasa ta sanya ta tada ikama, don haka da Azizah ta ga tana sallah sai ta koma ta ce da shi tana sallah. Ta yi wucewarta harkar gabanta.
[12/24/2019, 17:56] Takori: Haka Rahane ke ta hakuri da Abida, kullum da nau’in wulakancin da za ta yi mata, amma ko cira kai ba ta yi balle ta dube ta,
A kwanaki talatin da suka biyo baya, Rahane ta ware sumul! Duk ciwukan jikinta sun kame sai tabo. Ta yi haske, amma ba mai yawa ba.
Rahane ba kyakkyawa ba ce, amma halayenta masu kyau ne. Sai suka sayo mata kyan a idaniyar jama’ar da ta samu kanta a cikinsu.
Mami ta sha gwada Rahane ta fannoni da dama amma ba ta sameta da wani hali mara kyau ba.
Akwai sanda za ta kirga kudi ta aje a gefen gadonta ta kira Rahane ta ce ta dauko mata wani abun, ta dawo ta kirga kudinta dai-dai take samun su. Anyi haka ba sau daya ba.
Kuma babban abin da ke burgeta da Rahanen shine, rashin son maganarta, da rashin son hayaniya, wadatar zuci, sannan duk da kasancewarta bakauya, to ba ta fiye fiddo kauyancin ba. Ga hidima da Azizah kamar kanwarta ta jini. Sun shaku sosai. An

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login