Showing 12001 words to 15000 words out of 32136 words
fara gogewa da wannan (ta nuna mata tissue). Sai ki sa sabulu ki wanke da kanki. Kin gane?”
Ta ce, “Eh”.
“To maza tube ki yi sai ki yi wankan. Ko in cuda miki baya?’
Ta ce, “A’a, zan iya kada ki fama ni. Amma ba zan iya shiga wannan koramar ba ki zuba min a bokiti”.
Duk dauriyar Jawahir sai da ta ji dariya. Ta ce, “Ba korama ba ce, amma tunda baki so bari in bude ruwan ya fita, sai ki kunna famfon ciki. Amma wannan famfon na zafi ne”.
Ta bude rariyar ruwan ya tafi. Ta kunna mata famfon ta dauko bokitin wanki ta cika mata sannan ta fita.
Abida na durkushe bisa dan gadonta rike da ciki tana ta dariya, don duk tana jinsu. Jawahid ta kai mata duka ta falla aguje ta yi falo tana bawa Mami labari.
Daga daki Daddy ya jiyota shima ya yi dariya, amma ya ciro wayar charger dinsa ya fito ya yi kanta, ta yi tsalle ta boye a bayan Mami tana “Na tuba Daddy.......Daddy Allah ya huci zuciyarka”.
Ya ce, “To kar in kara jin kina mata dariya in ta yi wani abun da baki sani ba, nuna mata za ku yi a hankali ba ki dinga yi mata dariya kina ba da labari ba”.
Ta ce, “To Daddy”.
[12/24/2019, 17:56] Takori: Haka ta yi jika-jikanta a tsaye cikin kwamin da bokiti, ta daga kafa za ta fito santsin kwamin ya kwasheta ya buga da kasa. Ta sake yunkurin fitowa ta sake shan kasa. Rahane ta ce, “Wannan bala’i da me ya yi kama?” Ta koma ta cure jikinta a cikin kwamin ta yi zamanta.
Jawahir ta ji shiru wajen awanni biyu tana zaune gefen gadonta tana jiranta. Da ta tabbatar ba za ta fito ba sai ta mike tana kwankwasa mata ban dakin.
Daga ciki Rahane ta ce,
“Ki zo ki fiddani na kasa fitowa”.
Jawahir ta murda kofar ta shiga ta kama hannayenta ta fito da ita, ta zari tawul ta daura mata suka fito.
Jawahir da kanta take shafa mata vaseline a hankali kada ta fama ta. Ta ciro wasu Pakistan ruwan kwaiduwar kwai cikin kayanta ta mika mata ta sa.
Sai ta ga Rahane ta kasa sakewa a cikinsu, domin dai a wurin Rahane dogon wando sutturar maza ne.
Ta ce, “Don Allah ki bani zani na atampa wadannan santsi garesu”.
Jawahir ta yi dan jim, sai kuma ta bude wardrove ta dauko sabuwar danyar vlisco (Holland) dinta ta bata, ta daura mata zanin, ita kuma ta sa rigar. Ta taimaka mata ta daura dan kwalin, sai ta yi kyan gani.
Lokacin ne Mami da Dacta suka shigo. Dacta rike da gorar ruwan Myer da ledar magunguna fara mai tambarin AKTH. Yana tafa hannu ya ce,
“Yar Dacta! Kin yi kyan gani kamar ba ke ba”.
Ita dai murmushi ta yi, ta zame daga tsayuwa gaban Jawahir ta durkusa a gabansu. Da sauri Mami ta dagota ta zaunar da ita a bakin gadon Jawahir tana cewa, “Ki daina yin wannan durkuson mu mun yafe, ko da fatar baki ki gaishe mu kin ji?”
Ta sunkuyar da kai kawai. Mami ta karbi gorar ruwan a hannun Baba Dacta ta murda tana juyewa a tambulan mai garai-garai, shi kuma yana ballo mata magungunan da ya kamata ta sha a lokacin.
Daya bayan daya yake sa mata kwayar maganin a baki Mami na binsu da ruwa, aikinta kawai hadiyewa..
Dai-dai lokacin da aka kira sallar magariba. A ka’idar gidan duka tare suke yin sallah in har suna gida. Baba Dacta ne ke jan su.
To yau ma hakan, karo na farko da Rahane ta taba yin sallar jam’i a rayuwarta. Sai ta ga banbance-banbance da yawa da irin sallah da alwalar da suke yi a kauye.
Ashe su kawai dungurawa suke yi su mike, babu irin wannan karatun sallar mai dadi da Baba Dacta yake yi, basa bin ka’idoji da sharuddan da aka wajabta a kan sallar.
Sannan bayan an sallame isha’i, sai an dora da shafa’i da wutiri. Sannan ayi hadaka wajen cin abinci a kan tebir. Wanda ba ta san wa ya dafa ya jera su a kan tebir din ba, ita dai kawai ta gansu, ta san kuma ba Mami ta yi ba don suna tare da ita.
Daga nan kuma ta ga su Jawahir sun dauko wasu jakunkuna cike taf da litattafai har Aziza ta dauko nata, suka zube gaban iyayensu.
Nan da nan suka canza harshe daga iyayen har ‘ya’yan suna ta koya musu ayyukan makaranta. Jawahir ce ke tare da Daddy, ya yin da Abida da Aziza ke tare da Mami. Turanci suke yi zallah ba irin wanda ake musu a TAKAI SPECIAL PRIMARY ba.
Sha’awa ta kama Rahane, sai ta ja gefe ta tattara hankalinta a kansu, jefi-jefi Baba Dacta kan kalleta yana kuma sane da yadda ta kafa musu ido babu ko kiftawa.
Karfe tara saura minti biyar duk suka rufe litattafan suka maida su jakunkunansu, suka diba suka yi dakinsu.
Shi kuma Baba Dacta ya mike cikin tuma-tuman kujerun falon irin leather seats din da ko allura ba ta iya huda su, ya murdo labaran kasa na N.T.A yana sauraro.
Kalar kujerun Orange and Black. To haka tattausan kilishin da aka dora akan farin marbles shima ruwan goro ne da ratsin baki, labulayen kuma light orange.
Mami daki ta nufa ta yi wanka ta fito cikin shiri, lab coat dinta fara kal da farin gilashi da hand bag rike a hannayenta. Yau aikin kwana gareta a dakin yara na Isyaka Rabi’u (Paediatric-Unit).
Ta russuna ta sumbaci goshin Baba Dacta, ta shafa kan Aziza dake barci a kan cinyarsa, ta dubi Rahane dake satar kallon su suna bata sha’awa ta ce, “Ni na tafi aiki Rayhana, dauki Aziza kuje ku kwanta, da wuri ake barci saboda zuwa makaranta”.
Ta mike ta ce, “A dawo lafiya”. Ta dauki Aziza a cinyar Daddy ta yi dakin su Jawahir.
Likitocin biyu suka bita da kallo cike da tausayi. Mamin ta fita, Dacta ya ci gaba da sauraron labaran tara cike da tunanin hanyoyin da zai bi ya inganta rayuwar Rayhana, wadda Allah ya sanya mishi kaunarta kamar, koma fiye da yadda yake kaunar su Jawahir.
Tana shiga dakin karamin gado ta dora Aziza wanda ta fahimci shine nata. Abida da Jawahir sunyi wanka sun wanke baki sun sauya kaya zuwa marasa nauyi wanda a ganinta kayan maza ne (wando).
Abida ta balla mata harara ta ce, “Ga (diaper) nan ki sa mata”. (Tana nufin Azizah).
Ta yi sukuti tana kallon ta don ba ta san wani diaper ba. Haushi ya kashe Abida, ta tashi da kanta ta sa mata.
Rahane na tsaye saboda haushin da ta bata ba ta san sanda ta hankade ta ba, saura kadan ta bugu da karfen gadon Azizah.
Jawahir ta ce, “Abida mene ne haka? Wannan ai rashin mutunci ne”. Ita ma ta danna mata tata harar.
Ta fiddo ido ta ce, “Sai dai in a gadonki za ta kwanta wallahi ba dai nawa ba, ta yanka min jiki da faso”.
Ta dau filo ta jefa a kan marbles ta ce, “Ki kwanta a nan, wa ya sani ma ko kwarkwata ce fal kanta tunda ta zo ba ta bude shi ba.....”
Sauran maganar ta makale a makoshinta da ta daga ido ta yi ido hudu da Daddy a tsaye jikin kofa yana kallonta kawai. Ta yi tsuru-tsuru ta yi shiru.
Ya dubi Rahane dake sunkuye da kai ya ce, “Rayhanah!”
Ta dago a hankali ta dube shi,
“Hau gadon Abida ki kwanta”.
Da kyar ta iya bude baki a hankali ta ce, “Baba Dacta ba zan iya kwana a kai ba fadowa zan yi, nan din ya isa”.
Ya ce, “Hau ki kwanta na ce, ba za ki fado ba”.
Ba za ta iya yin jayayya da shi ba, sai ta hau gadon a hankali ta takure a karshensa, duk da ba wani girma ne da shi ba, gadon silver ne karami.
Ya dubi Abida da matsanancin fushi ya ce, “Ke kuma dauki filonki ki kwanta a kasan ki ji in da dadi.
Abida ki kiyaye ni, ki kiyayi taba min Rayhanah. Ban ce lallai sai kin so ta ba, don ba zamanki take ba, kuma ba a kanki take zaune ba. Kin yi na biyu kada ki sake in ji na uku, karonmu dake ba zai yi miki dadi ba”.
Ya ja lallausan bargonta ya rufawa Rayhanah. Ya juya ya fita bayan ya mika mata akwatin hearing aid dinta yana gaya mata yadda za ta adana shi in za ta kwanta ko wanka ko alwala, kada ruwa ya taba shi. Ya kuma nuna mata yadda za ta cire batir din da mayar da shi.
Jawahir ta kasa shiru ta ce, “Daddy wannan ai hearing aid ne, me take yi da shi?”
Ya dan dubeta ya ce, “Me masu amfani da shi ke yi da shi?”
Ta ce, “Karin karfin ji”.
Ya ce, “To ita ma Rayhanah haka”.
A takaice ya gaya mata hatsarin su Rayhanah, mutuwar kakarta, auren da Babanta zai mata da yadda aka yi ya taho da ita.
Jawahir ba ta san lokacin da ta taso ta dawo gadon da Rayhanah ke zaune ba ta rike hannun tad a babu ciwo tana share hawaye.
Ta ce, “Daddy ni zan dinga tayata kula da shi ma”.
Ya ce, “Allah ya kyautata miki kema Jawahir”.
Ta ce, “Zamu kwanta gado daya, ita Abida ta hau nata”.
Ya ce, “Wallahi yau a kan tayal za ta kwana, koma gadonki ki kwanta, ita ma gobe za a kawo mata nata”.
Ta sauka ta koma. Ya kashe musu wuta ya fito ya jawo kofar yana gaya musu suyi addu’ar kwanciya.
Washe gari Abida da ciwon baya ta tashi sakamakon kwanan dandaryar tayal, wannan ya kara fushinta da shigowar Rayhanah cikin rayuwarsu, ta tsaneta, iya kiyayyar da ba za ta iya fassarawa ba.
Tunda har a kanta ne yau Daddy ya yi mata haka. Daddyn da ko tsawa mai karfi baya yi musu, sai dai ya yi musu nasiha.
A haka suka bi jam’in sallar asubahi tare da Daddyn tana ta kumburi, sannan suka soma shirin wanka don tafiya makaranta.
Jawahir ce ta yiwa Azizah ta shiryata cikin kayan makarantarta na play group din DARUL-ARQAM, direba ya kwashe su suka tafi, suka bar Rayhanah ita kadai a dakin ta takure can gefe a kusurwar gado,.
Sai yanzu ne kewar Iya Bilki ta dawo mata sabuwa, ta shiga kuka a hankali amma mara amo, domin ta toshe bakinta da dan kwalin kanta.
Karfe takwas da rabi dai-dai na safe motar Mami ta shigo farfajiyar gidan, I.M ke tukin, shima a asibiti ya kwana.
Jefi-jefi suna hirarrakin da suka shafe su shi da mahaifiyarsa, ya yi parking din motar a muhallinta yana cewa,
“Nifa gaskiya Mami zaman yarinyar nan da Daddy ya kwaso bai min ba, kuma ba matsayin ‘yar aiki ba, duk taimakon da ya kamata ya bata na likita da patient dinsa ai ya ba ta, hatta hearing aid din fa shi ya saya da kudi ba kadan ba.
To na mene ne kuma na tahowa da ita? Shi bai san yanzu zamani ya canza ba (sunan litafin Takori mai zuwa) Kowa ta kansa yake, ka jawo mutum inuwa shi kuma da ya ji sanyinta ya turaka rana”.
Mami ta ce, “To ni dai babu ruwana mun riga mun rufe wannan babin da shi. Da ai na kowa ne HIMU (sunan da take kiranshi kenan wato Ibrahimu)”.
Ya kyabe baki bai sake cewa komai ba, ya dauko jakar Mami da lab-coat da sauran takardunta suka shige ta kofar kicin.
Firji ta fara budewa ta dauko robar ruwan FARO mai rangwamen sanyi ta sha tambulan biyu.
Al’adarta kenan a kullum da safe kafin ta sanya komi a cikinta yana da fa’ida sosai, ga lafiyar jiki da ta zuciya.
Ibrahim dakinsu ya wuce don ya yi wanka, jinsa yake kamar a kwatami saboda rashin wankan. Mutum ne mai masifaffar tsaftar gaske, sannan mai baudadden hali.
Abin nufi, da wuya ka gane inda Ibrahim Mansur Takai ya sa gaba, ba za ka iya gane farat daya yana da kirki ko ba shi da shi ba, mahaifinsa kadai ya san kansa, shi kuma kadai ya iya tafiyar da shi da baudadden halin nasa.
Ibrahim na da kyau, wanda kallo daya za ka yi mishi ka ga hakan. Wankan tarwada, mai tsayi da rashin kauri. Yana da siririn saje a gefen fuskarsa mai laushi da sheki, da ka ganshi ka ga Mansur Takai, ta karan hancin, da manyan idanunsu.
Sannan mai tattsauran ra’ayin akidun Malam Nasara. Sai dai kuma mutum ne mai riko da sallah, tabon sujjadar dake tsakiyar goshinsa kadai ya isa shaidar hakan.
Ba za ka iya dorar da wani abu a kan halayyar shi ta zahiri da badani ba, wannan sai mahaifinsa, duk yadda kuke da shi kuwa.
Nutsuwa irin ta Ibrahim daban take, za ka iya ganin hakan a kan ko me yake yi, kamar cin abinci, sallah, tafiya da duk wani motsi da zai yi ko a karatun likitancinsa.
Dacta Mansur na son Ibrahim son da baya yiwa Yayansa Khalipha, saboda komi nashi Ibraheem ya dauko. Magana in ba mai muhimmanci ba ce Ibrahim baya yinta, ko hira ake cikin abokan karatu Ibrahim baya tofa nashi in ba mai ma’ana ba.
Kasancewa ranar Lahadi ce, Dacta bai zuwa office don haka basu fito ba shi da Mami sai karfe goma na safe, cikin sassaukar shiga ta zaman gida. Mami doguwar riga ce kirar Kuwait ruwan toka a jikinta, ta kame jelunan kitsonta da ribom. Shi kuma Dacta shirt ce mara nauyi fara da shudin jeans a jikinsa.
Ibrahim suka tarar bisa tebir yana kalaci, shima ya yi wanka ya yi fes da shi cikin Hilfiger Jeans ruwan bula, gashin kansa da ya yiwa saisaye yana kwance bakikkirin da shi sai sheki yake. Ga turaren shi mai sanyin kamshi na tashi a hankali a falon.
A kujerar dake fuskantar shi Dacta da Mami suka zauna. Dacta ya dubi Mami ya ce, “Rayhanah ta karya ne?”
Ta ce, “Anya? Bari in dubo ta”. Ta mike.
Da ta shiga dakin gani ta yi kamar ba kowa, can ta jiyo shesshekar kukanta can a kusurwar gadon Jawahir.
Ta shiga ta tsugunna a gabanta ta kama hannunta ta ce, “Kuka Rayhanah? Me aka yi miki?”
Ta jata jikinta a hankali tana lallashinta. Dacta ma aje cokali ya yi ya nufo dakin don ya ga Mamin ta jima.
Shima durkuso ya yi a gabanta ya ce, “Mene ne Rayha? Me ya same ki?”
Cikin kuka ta ce, “Iya za ni”.
Ya ce, “Daina kuka Rayhanah, addu’a za ki dinga yiwa Iya a duk lokacin da kika tunata. Wanda ya riga ya mutu baya dawowa, sannan baya son kuka, addu’a yake bida.
Rayhanah kowa da kika gani yana yawo a doron kasa, wata rana za a wayi gari babu shi. Har mu din kuwa. Ba Iya kadai ba, duk jiran wa’adinmu muke. Duk sanda kika yi sallah ki karanta suratul Ikhlas kafa uku ki ce Allah ya kai mata ya fi ki dinga yi mata kuka. Addu’a take so kin ji”.
Ta daga kai. Ya ce, “Good! To taso muje ki ci abinci”.
Ya kamo hannunta har dining. Ai kuwa Ibraheem ya aje cokalinsa ya mike, don ba zai iya cin abinci tana wajen ba. She is ugly at all (mummuna ce), ga ciwuka ga dafaffiyar fatar kauye. Wannan abun haushi na Daddy da me ya yi kama?
Mami dake hadawa Rayhanah tea ta cira ido ta dube shi ta ce, “Ya ka tashi? Ka koshi ne?”
Tuni Daddy ya karance shi. Ya dauke fuska don baya son ganin ma inda yarinyar take kada ya yi amai, ya wuce yana cewa “Eh, Mami”.
Ta turawa Rahane kofin shayin, ta zuba plantain da dankali ta tura mata “Ci maza ki sha magani”.
Ta karba, amma sai ta dauko filet din da kofin ta zauna a kan marbles ta fara cin abinta.
Duk suka yi mata dariya, kuma basu ce da ita ta tashi ba. A wurin Rahane su suna kan kujera ita ma ta