Showing 21001 words to 24000 words out of 32136 words
ce mai Da wawa...... to hakan ce ta faru da Mamin.
Ta kai ta kawo har barci Rahane da Aziza a gado daya suke yi. Abida ba ta fasa halinta ba, sai dai in Daddy na gida ko Jawahir ta bude mata wuta. Uffan Rahane ba ta ce mata, ita har ta saba ma da rashin mutuncin Abida.
Ina wuta Abida ta saka Rahane! Ranar da ta ganta shirye cikin uniform irin nasu direba zai kai su makaranta.
Rahane aji hudu aka sanyata da aka yi mata gwaji, Abida da Jawahir na aji biyar. Dacta da kansa ya kaita, ya yi mata komai na zama cikakkiyar dalibar DARUL-ARQAM, sai dai Allah ya biya shi.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a zo ba. Rahane ta samu kanta a sabuwar makarantar addinin Musulunci ta DARUL-ARQAM dake cikin tsohuwar Jami’ar Bayero.
Babu laifi tana fahimtar karatun, sai dai abin ya zo mata da tsauri kwarai, a hakan dai ake kukkullawa don Malam Umar yana taimaka mata sosai, musamman da yake ya lura tana da sha’awar karatun, fahimta ce sai a hankali, musamman idan aka yi la’akari da inda ta faro karatun nata.
A haka suka samu hutun karshen zango suka yi jarabawa. Kamar koyaushe ‘ya’yan Dacta Takai sun dauko na dai-daya a ajujuwansu har Azizah, Rahane ce ta dauko na ashirin cikin su arba’in.
Abida ta yi ta sheka mata dariya a mota. Sai dai kamar yadda ta zata Daddy zai yi fushi da Rahane, ba ta ga hakan ba, yaba mata ya yi, ya kuma kara mata karfin gwiwa.
Sanda Malam Umar ma ya basu hutu Dacta ya shirya musu tafiya Takai don ziyarar dangi, kuma Rayhanah ta ga mahaifinta za su yi kwana biyu, wato Asabar da Lahadi.
Ibraheem ke jan motar wanda ta ji kannen shi na kiran shi YA HIMU wato an yanke farkon sunan an kira shi da karshe.
Rayhanah ta rasa irin kiyayyar da wanan dan tahaliki ke gwada mata. Bai taba yi mata magana ba, haka bai taba daga ido ya kalle ta ba. Duk da ta lura rashin son magana halinsa ne, amma ai yana amsa gaisuwar kannensa.
Wani lokacin har yana daukar Azizah su fita harabar gidan, amma ita bai daga ido ya kalle ta. Duk da dai bai fiya zaman gidan ba yana hattama karatunsa,.
A cikin motar ana ta hira, Rayhanah da Ibraheem ne kadai basa magana.
Daddy ya ce a ransa, “Duk halinsu daya!”.
Ana sallar Azahar suka shiga Takai, kai tsaye gidan Hakimi suka zarce. Uwargidan Hakimi Haj. Karima mace ce mai kirkin gaske, kuma ita ce uwar dakin Dr. Asma’u. Tana da yara tara duk mata, duk ta aurar dasu sai autar ta Nabilah wadda ke masifar son Ibraheem, duk sanda suka zo Takai ita ce ke kula da al’amarinsa.
Sai dai shi din har yanzu babu wanda ya san inda ya sa gaba a kanta, tunda har yana kula ta, suna shiri sosai. In sun je gidansu can Kano ko su sun zo Takai, kuma suna waya sau-tari, duk da shi ba kowanne lokaci yake harkar wayar nan mara kan-gado ba, a kwana ana yinta, a wuni ana yinta, babu sallah babu salati, babu amfanawa kai komai, amma ko salatin Annabi ba kowannenmu ke yi kullum ba ko da cikin carbi ne.
Amma waya ita ce rayuwar al’umma a yanzu. Idan ya kashe waya sai week end yake bude ta, week end din ma idan baya komai, kowa dake tare da shi ya san hakan.
Sai Hajiya Indo, ita ce uwar ‘yan mazan gidan, mai bi mata Sadiya, ta rasu wajen haihuwa, sai ta dauki ‘yar ta rike, tunda dama ita duk ‘ya’yanta maza ne sunanta Hibba, sa’ar Nabila ce, ita kuma ita ce ake wa Khalipha kamu, da ita da Nabilan duk suna karatu a Canadian Univeristy of Dubai, yanzu ma sun zo hutu ne. Sai amaryar Hakimi da ya aura bayan mutuwar Sadiya Inna Luba, tana da yara biyar maza da mata.
Hajiya Karima ta dubi Rahane dake zaune gefen Mami ita da Azizah, da yake su Jawahir duk sun fice cikin sa’anninsu.
Ta ce, “Ina kika samo ‘ya mai nutsuwa haka? Ko mai rainon Azizah ce?”
Ta ce, “A’a, ‘yar amana ce Dacta ya bani”.
Hajiya Karima ta sake juyawa tana kallon Rahane ta ce, “To ko ita ce na ji Nabilah na labarin Dacta ya tafi da ita daga nan Takai? Babanta kuma na nan tare damu?”
Ta ce, “Ita ce”. Tana lallatsa wayarta.
Hajiya Karima ta ce, “Allah sarki! Ai kuwa na ji Mai Martaba yana yabon Babanta, ya ce dattijon kwarai ne yana kula da Barga yadda ya kamata. Dawakansa sun kara lafiya da girma, sannan kullum fes suke, wajensu fes kuma ba ya karbar ko taro in ba ihsanin kansa ya yi masa ba”.
(Not interested ga hirar) Dacta ta ce, “Allah sarki, ita ma Rayhanah ba ruwanta”.
Wata baiwar Haj. Karima ta shigo, ta umarceta da ta raka Rahane wajen mahaifinta. Ta kama hannunta suka fita. Azizah ta like mata sai ta bita.
Mami ta ce, “Dauke ta ku je”. Ta kuwa sungumi Azizah a bayanta suka tafi.
Mahaifinta ta fara yin tozali da shi durkushe gaban wani kosasshen doki yana rage masa kofato. A gefe Ibrahim ne ke shafa gashin wata godiya sabuwar haihuwa. Ga yadda ya mai da hankalinsa a kan dawakan za ka fahimci yana son su.
Da gudu ta karasa ta zube gaban Babanta tana dariya. Ibraheem ya kallo su ta gefen ido, sai suka ba shi tausayi, su wadannan wato basu da kowa sai junansu, amma wai shine yake jin haushi don mahaifinsa ya taimake su.
Ya manta cewa duk wanda ya taimaki dan’uwansa Musulmi shima Allah zai taimake shi, shi yasa mahaifinsa kullum cikin nasara yake, saboda taimakon da yake yiwa al’umma. Balle maraya da Allah da kansa ya ce a taimake su.
Yana kallon su kowannesu bakin shi ya ki rufo. Ta ce, “Baba kai ne ka yi kyau haka?” Shima ya ce, “Rahane ke ce?” Sai suka sa dariya.
Ta ce, “Allah Baba in a hanya na ganka ba zan ganeka ba”.
Ya ce, “Ni din kuma fa? Kin canza gaba daya Rahane”.
“Sai mu gode Allah Baba, suma mu gode musu. Mu ci gaba da zama dasu cikin amana, Allah ya ji kan Iya”.
Sai tasa habar zaninta ta share idonta. Shima kokarin mai da kwallar idanunsa yake, ya ce, “Amin ya Allah, Rahane ki yafe ni a kan tirsasawar da na yi kan cewa sai kin auri Ado shine silar da Iya ta rasa ranta don ta tserar dake daga wulakantacciyar rayuwa. Wallahi nima kaina a lokacin ban san dalilin da yasa nake tsoron Ado ba, sai yanzu na gane ba haka ya barni ba, to Allah ya fishi”.
Ta ce, “Kada ka ce kai ne silar rasuwar Iya Baba lokacinta ne ya yi, ko tana dakinta ajalinta ya zo, dole za ta tafi. Baba Dacta ya ce duk sanda muka tuna ta addu’a za mu yi mata, suratul Mulk, Yasin da Ikhlas, shine soyayya ta gaskiya da zamu yi mata”.
Ya ce, “Ikon Allah, Rahane har ilimi kin kara da hankali”.
Ta ce, “Ai Baba makaranta muke zuwa safe da yamma, da dare ma su Baba Dacta na koya mana”.
Ya ce, “Alherin Allah ya tabbata a garesu”.
Himu ya bar wurin don basu ganshi ba, kuma baya so su ganshin. A soro na biyu suka ci karo da Nabila ta hado abincinsa cikin kwandon kayan abinci.
Ta ce, “Ya Himu ina ka shiga ne? Ga shi ina ta kiranka ya ki shiga”.
A takaice ya ce, “Ina barga”.
Suka juya cikin gidan tare.
Yana zaune ya mike dogayen kafafunsa a kan tattausan kilishin (sitting room) din da suke zaune, Nabila na faman zuba mishi jellop din cous-cous wadda ta ji kayan lambu, a gefe cikin dan tangaran farfesun hanta ne, ta diba a cokali ta kai bakinsa.
Ya yi murmushi ya karbi cokalin daga hannunta yana ci suna ‘yar hira. Sai dai duk rabi Nabilan ce ke yin hirar tana ba shi labarin rayuwar makarantarsu.
Sama-sama yake sauraronta, He is curious about something different (wani abu daban yake son sani) kan Rayhanah da Babanta.
Kadan ya ci ya cika ruwa a tambulan ya sha. Ya mike yana laluben mukullansa a aljihunsa ya ce,
“Am coming Nabeelah (ina zuwa)”.
Ibraheem Mansur, (HEEMU ko I.M) kamar yadda kannensa da abokansa ke kiransa. Bai da shiga sharo ba shanu balle abin da bai shafe shi ba.
Amma a yau, haka nan ya samu kansa da son sanin asali da tushen su Rayhanah, da rayuwarsu ta baya. Abinki da karamin gari, kowa ya san kowa.
Don haka bai sha wuyar samun tarihin su Rayhanah ba. An gaya mishi uwarta ta rasu tun lokacin haihuwarta, kakarta da suka yi hatsari tare ita ta raine ta.
Har makarantar su Rahane ya je ya binciko takardunta. Malamansu sun shaideta wajen kokari da son karatu. Sai ya ji hankalinsa ya kwanta da rayuwarta tare dasu.
Sai dai ko a fuska bai nunawa Baba Dacta komi ba. Malam Rashidu ya samu kyakkyawar shaida daga bakin makwabtansa. Amma a da sam hankalinsa bai kwanta da zaman yarinyar tare dasu ba, saboda halin rayuwa da butulci irin na dan Adam.
Sai kuma yake tambayar kansa, shin me yasa ya damu kansa kan yarinyar? Damuwa irin wadda bai taba yi a kan kowa ba??? Ya tattara zancen ya watsar ya shiga sabgoginsa.
Da yammacin ranar yana barga tare da kaninsa Sha’aban dan Hakimi, kowannensu ingarman doki ya zaba Sarkin Dawaki ya aza musu sirdi suka dane suka nufi ‘yar shakatawa bayan gari.
Suna tafe hira suke yi kan sabbin gine-ginen zamani da Hakimi ke yi a cikin garin da ginin gidan saukar baki mai dauke da bukkokin zamani, inda Turawa ke sauka idan sun kawo ziyara. Haka nan Hakimi na sauke bakin alfarma idan sun zo.
Ibraheem ya yi sha’awar wadannan gine-ginen sosai. Yake ce da Sha’aban duk lokacin da ya tashi ginin gida zai sanya ‘Hut’ wato bukka ta gargajiya mai suffar zamani.
Sanda suka dawo magariba ta gabato, suka sauka daga dawakan suka soma alwala a famfon wajen. Kamar an ce da Ibrahim ‘juya’, ya hango Rahane na yankewa Babanta akaifa da nail cut. Sai dai bai jin me suke cewa a tsakaninsu.
To haka washe gari da misalin karfe goma na safe ya shigo bargar domin an kawo sababbin (Polo Horses) daga Ireland duka na Baba Dacta ne, yake ba da hayarsu ga masu sana’ar tseren Dawaki ake masa kiwon su anan bargar hakimi. Sun bambanta sosai da sauran dawakan ko daga koshinsu da shekin da suke yi da kuzari.
Ya dan juya ido sai ya hango Rahane da jibgin kayan wankin Babanta da ta tattaro tana ta dirzarsu kamar Allah ya aikota. Shi kuma Baban yana gefe yana yiwa dawakin askin jelarsu da katon almakashi. Yana cewa,
“Wato Rahane ba kya jin magana ko? Na ce ki bar wankin nan ya fi karfinki in na gama zan yi abina”.
Ta ce, “Albarka nake nema Baba, ka barni in samu, in ban yi maka ba wa zan yiwa? Idan mun tafi ban san yaushe zamu kara dawowa ba”.
Ibraheem ya jinjina kai suka kara ba shi tausayi.
Washegari suka yi sallama da kowa za su tafi, Rahane har kuka ta yi saboda ba ta son barin Babanta. Amma ba ta bari Baba Dacta ya gani ba, sauri ta yi ta dauke hawayen da yatsunta.
Da gudu ta koma ta sake rungume Babanta, sannan ta shiga mota tana share hawaye da sauri.
Har Ibraheem ya kunna mota ya hango Mal. Rashidu tafe da sassarfarsa rike da katuwar leda, don haka ya dakata.
Baba Dacta ya sauke gilashi sai ya mika masa, “Yalo ne da kashu (cashew) babu yawa a yiwa yara tsaraba”.
Hannu biyu Baba Dacta yasa ya karba, ya ce, “Yara sun gode Baban Rayhanah. Allah ya kara nisan kwana”.
Ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro naira dari biyu ya mikawa Aziza, “Ungo yarinya ka sha ruwa a hanya kin ji?”
Mami ce ta karba fuskarta fal fara’a ta ce, “Aziza ta gode Baba”.
Ya daga musu hannu suka ja motar suka tafi. Abida ta juyar da kai gefen taga tana tsaki mara sauti. Kamar ta rufe Mamin da duka da ta karba.
Su kuwa iyayen sun ji dadi har ransu. ALHERI komi kankantarsa dadi gare shi, amma ga wanda ya san mutuncin dan Adam.
Kafin la’asar sun iso Kano. A harabar gidan bakuwar mota ce kankanuwa mai santsi (one door, Camero) fake a harabar adana motoci.
Ai kuwa daga Jawahir, Abida har Azizah fita suka yi a guje har Azizah na faduwa, ta kuwa fashe da kuka, don har bakinta ya fashe.
Da sauri Rahane ta fito ta dauke ta tana goge mata jinin dake fita daga bakinta. Mami na ta fada za su kashe mata ‘ya sai ka ce yau suka fara ganin Khalifan. Amma ko jin ta basu yi ba balle su tsaya. Sai da suka dangane ga dan’uwansu suka rungume shi.
Khalipha na zaune ne a kan kujerar zaman mutum biyu, gwangwanin Maltina ne a hannunsa yana sha, amma saboda rungumar bazata da kannen suka yi masa gwangwanin ya fadi ya zube a cinyarsa.
Farin kaftan nashaddah (hilton) ne sol a jikinsa dinkin Mohammed, amma haka suka wanke shi da Maltinar. Hakan bai sa ya yi fushi ba, surar Azizah ya yi daga hannun Rayhanah ya yi sama da ita ya cilla ya cafe.
Ya ce, “I’m missing you.....”
Ya hadasu ita da su Abidar ya rungume gaba daya yana durkushe dai-dai tsahon su. Ba tare da ya ankara da bakuwar fuskar dake gefe ba.
Ita Rahane daki ta wuce don ta ga hankalinsa na kan kannenshi ko ta gaishe shi ma ba jinta zai yi ba, ta ce bari ta bari sai ya nutsu sai ta gaishe shin.
Khalipha bai samu kansa daga hayaniyar su Azizah ba sai da aka kira sallar magariba. Ya mike dauke da Azizah ya kawota dakin Mami, lokacin ita Mamin tana shirin yin sallah ta wuce asibiti, don yau ma aikin kwana za ta yi.
A gadonta ya dire Azizah ya ce, “Mami Dactan nan (Himu) ya bar miki mukullin daki ne?”
Ta ce, “Ka duba yana jikin kofar”.
Ya rungumeta ta baya ya daura kai bisa kafadunta ya ce, “You didn’t miss me Mami.....”
Ta ce, “Sai in yi ta rawa ina tsalle ka dawo sannan ka yarda na yi kewarka”. Dariya ya yi ya juya ya fita.
Wanka ya yi, sannan ya daura alwala, ya zuba wata shadda kaftan ruwan kasa. Khalipha Mansur baya sanya kananan kaya sam, sai shaddah, yadi ko jallabiyar Saudi ( in a gida ne). Shi yasa Mami ke kiranshi (Dattijo) a yawancin lokuta.
Daga kallo na farko da ka yiwa Khalipha za ka gane mutum ne mai faram-faram da haba-haba da jama’a (sociable) sabanin Ibrahim (anti-social in nature).
To haka a kamanni da sura, Khalipha Mami ne sak, fari sol da shi, ga tsayi ga zati. Kwayar idanunshi ba baka ba ce (brown) ce mai sheki. Da ka ganshi ka ga Mami. Kamar ta yi kaki ta tofar.
Khalipha na da kirkin da Ibrahim bai da shi, ko daga mu’amalar kauna bayyananniya dake tsakaninsa da kannensa, wadda basa samu daga Himu ko kadan. Don haka suma basu dauke shi da wasa ba, suna bala’in kaunarsa.
Ya damu dasu suma sun damu da shi sosai ba kadan ba. Daga sanda ya zo gidan Mami da Daddy sun huta da koyar da yara aikin makaranta. Ya hada digiri dinshi mai daraja ta daya daga Jami’ar (BAZE) a kan hulda da kasashen ketare, sai jiran posting din Bautar Kasa.
Yadda kamanni da halayya suka sha ban-ban tsakanin Himu da Khalipha, haka dabi’u da akidu. Khalipha dattijon ne da gaske, yaro mai halin manya. Don haka shi kansa Daddyn ma sau tari kan kira shi da (Dattijo).
Bayan sallar isha’i duk suna bisa tebir kamar yadda yake a al’adarsu. Rahane ta fito jaye da hannun Azizah, tana ta rigima duk hancinta ya toshe da mura. Rahane sai aikin share mata hanci take da hawaye duka, da guntun tishu dake hannunta.
Ya dan juya ya dube su jin Mami na fadan a daina kunna A.C da daddare tunda ba lokacin zafi ne ba. Ya dan