Showing 15001 words to 18000 words out of 32136 words
hau kujera, ai ya zama rashin kunya.
Da suka kammala Dacta ya bai wa Mami ‘master card’ dinsa na (First Bank) ya ce ko nawa ne ta cira ta sayawa Rahane sittiru da sauran kayan bukata.
Ta ce, “Ni wannan kan ma na fi damuwa da a wanke. Ba zai rasa dandruff da lices ba (amosani da kwarkwata). Dubi yadda take ta sosa shi”.
Haka tasa Rahane a gaba suka tafi saloon din, ita ke jan motar. Ai kuwa kwarkwata ba a magana. Haka ta yi ta biyo kumfar magani na musamman ana fidda ita.
Sai da suka tabbatar babu ko daya sannan suka gyara mata gashin. Ba ta da wata suma mai yawa, sumarta ba ta fi a kama a ribbon ba, mai karfi sosai ta asalin Kanawa.
Daga nan shagon (Well-Care) ta shiga ta yi mata sayayyar kayan sanyawa masu kyau da tsada. Dogayen riguna ne sai siket da riga, atamfa da les kuma ta ba da dinki a (Diallo) inda ake wa su Abida.
Basu shigo gida ba sai bayan azahar. Tuni su Abida sun dawo har sunyi wanka, sai yanzu Rahane ta ga wanda yake kawo abinci ya aza a tebir. Wani kabila ne sanye da Apron fes da shi kamar ma’aikaci. Ta ji Azizah na ce masa Yohan.
Da gudu Jawahir ta rungumota ta zame dan kwalinta ta ce, “Rayha kin yi kyau, yau tunda na je makaranta nake tunaninki. Don Allah Mami a kai Rayha makarantarmu”.
Mami ta ce, “Ku wuce ku ci abinci ko sai Malam Umar ya zo yana jiranku?”
Jawahir ta makale hannun Rahane suka zauna tare, ta ce, “In ce ko kin cire ‘Aid’ din sanda za a yi wankin kan?”
Ta ce, “Eh, na cire”.
Abida sai cin magani take, ta yi tsaki ta debi abin da za ta iya ci ta yi daki, don ba za ta iya cin abinci gaban wannan kazamar yarinyar ba. Azizah cinyar Rahane ta dare tana ta Alifun Ba’un da A,B.C,D tana da son mutane.
Haushi bai kashe Abida ba sai da ta ga an karo musu gado, wato na Rahane ne. Ta zauna tana ta huci, da ta tuna kashedin babanta kuma sai ta fashe da kuka, don ta lura ba yadda za ta yi, kuma da gaske tare Daddy ke nufin suyi rayuwa.
Karfe hudu dai-dai Malam Umar ya zo. Yana koyar dasu kira’a ne da Tajweed, sannan suyi lesson a boko. Idan yana kwararo kira’a sai ka ce Ahmad Sulyman, haka idan yana baiwa kowanne harafin Alkur’ani hukuncinsa, kamar marigayi (Malam Datti Ahmad Galadanci) Allah ya yi masa rahama.
Rahane na zaune gefe tana sauraron wannan malami, ta ce a ranta ashe mu a Allo shirme muke yi. Ya ja aya ya kuma nuna Abida da ya lura hankalinta baya tare da ita tana ta sokawa Rahane tsinke, ya ce, “Abida, wane hukunci ne da wannan ta’areef?’
Ta zabura ta ce, “Eye? Na’am?”
Ya sake maimaitawa. Ta yi tsit! Ya kuwa daddage ya tsula mata dorinar dake hannunsa, bulalar ta shigeta sosai, ta zabura ta sa kuka.
Ya ce, “Ko ki rufe min baki ko in kara shauda miki”.
Ta toshe bakin da karfi tana kuka.
Ya ce, “Tun dazu ina lura dake babu karatun da kike sai tsokana, ko tausayin yarinyar nan ba kya ji. Dubi raunin dake jikinta amma kike son huda mata jiki”.
Da mamaki Jawahir ta dubi Abida, don da hankalinta baya kansu. Ya ci gaba da cewa, “To zan gayawa Dacta, don ke na lura fitinanniya ce”.
Tana kuka ta ce, “Don Allah Malam ka yi hakuri kada ka fadawa Daddy na daina”.
Ya ce, “To kin yi na karshe”.
Da haka karatun ya tashi.
[12/24/2019, 17:56] Takori: A rayuwar Ibraheem, bai taba damuwa da wani abu bayan iyayensa da karatunsa ba kamar RAYHANAH! Kankanuwar yarinyar da ko kirgar dangi bata fara ba, bata kuma da wani abu attractive da zai dau hankalin namiji ta fannin sura.......bai yarda da kansa ba, don haka ya dauki duk wani motsin da zuciyarsa da gangar jikinsa ke yi a kanta da KARYA........!
Jawahir ta Khalipha su suka taimakawa Rayha ta wanke kashin da Abida ta yaba mata, sannan ta yi wanka ta koma ta kudundune a bargonta ba ta ce komai ba. Sai ajiyar rai take.
Khalipha ya dora hannunsa a kan goshinta, zafi rau! Ya ce, “Tun yaushe kika fara ciwon kai Rayha?’
A sanyaye ta ce, “Tun jiya”.
Ya umarci Jawahir ta kawo ruwa da panadol. Ya ba ta da kansa ta koma ta kwanta.
Abida na gefe tana ta kuka domin ta daku a hannun Khalipha ba kadan ba. Sai dai ko kadan hakan bai sa zuciyarta ta russuna ba daga kiyayyar da take yiwa Rayha. Zuciyarta ce ma ta kara tauri da kangarewa, don yarda da ta kara yi Rahane ta zame mata karfen-kafa.
Daddy ya daina shiri da ita saboda ita, yau ga Yaya Khalipha dan’uwanta da ba ta hada soyayyarshi da ta kowa a zuciyarta ya yi mata dukan kawo wuka a kan RAYHANAH!
Khalipha ya dago idonshi jajir da bacin ran da har zuwa lokacin bai ji ya ragu ba, duk da dukan da ya yiwa Abida.
Ya dube ta sosai tana ta kuka ya ce, “I’m warning you Abidah.... don’t repeat it! Don’t repeat it!! Don’t repeat it!!!”
Ta ce, “To Yaya Khalipha”. Ya mike ya fita ya ja musu kofar.
****
A yau duk gidan shiri suke yi domin halartar bikin kammala karatun su Ibrahim, karshen kure adaka ‘ya’yan Dr. Mansur sunyi. Duka sanye suke cikin English wears kowanne da design din sa, sunyi kyau kwarai. Aziza samfurin ‘george’ Abida da Rayha ‘Mclaren’, Jawahid kuma H&M ne duka riguna da wando domin zama da madaukin kanwa yau da gobe tilas ya koyar da Rahane saka wando. Don su a wurin su (casual wear) ne da babu inda bazasu iya shiga dashi ba. Dr. Mansur baya hana su shida kansa in ya fita waje yake sayo musu saidai ya kudure ya kusan dakatar da hakan da zarar sun shiga sakandire.
Kalar kayan kowanne daban, amma duka babu wadda ba yi kyau ba kamar ka lashe. Kai ka ce irin yaran nan ne dake rayuwa a Honolulu.
Rahane ta kara da farin hijabi, wanda ya sauka a kan kafadunta. A zahiri duka su Abida sun fita kyau, sun fita haske. Amma idan ka dubi Rahane a wannan lokacin sai ka kara marmarin maimaitawa, saboda kalar fatar jikinta baka mai duhu amma mai sulbi kamar Somali, da dirin jikinta da ya soma bayyana da wata irin kamala da nutsuwa hadi da kwarijini bayyananne daga indallahi.
Taron, wanda aka gudanar a dakin taron (Musa Abdullahi Auditorium) dake cikin sabuwar Jami’ar Bayero, ya samu halartar kusoshin ilimi na Najeriya da shuwagabanni, malamai da sarakuna. Farfesoshi da Dactoci, har da mataimakin shugaban kasa.
A jawabin mai girma V.C Proffesor Attahiru Jega, ya ce yau shekaru ashirin kenan da jami’ar ta ba da shaidar MBBS mai daraja ta daya, daga nan ba ta kara samu ba sai yau a kan Dr. Ibraheem Mansur Takai. Don haka ‘chevening scholarship’ dake tallafawa hazikan ‘graduates’ na kasashe masu tasowa dake karkashin majalisar Turai ta bashi zabin duk kasar da yake so ya yi specializing a duk fannin da ya zaba. V.Cn ya kare bayanin sa da cewa “Dr. Ibraheem congratulations!”
Ya fada tare da mika masa hannu suka gaisa, sannan ya mika masa kwalinsa, ya karkata masa hularsa. Sannan ya dafa kafadunsa yana girgizawa.
Sai da Nabila ta san yadda ta yi ta kutsa cikin jama’a tana daukar I.M da V.C hoto duk motsin da sukayi, daga karsh Baba Dacta ya rungumo suka jero tare suna sakkowa daga kan steps din zuwa wajen Mami, wadda ke tsaye harde da hannuwa a kirji, fuskarta ta kasa rabo da kayataccen murmushin dake tattausan bakinta. Itama ta rungume shi Nabilan na ta daukar su hoto.
Kwana biyu da taron Baba Dacta ya shiryawa I.M walima a nan reception din gidan. ‘yan’uwa ne na jiki, abokan arziki da abokan aiki na Baba Dacta da Mami, dangin Mami daga Jos, abokan Ibraheem da na Nabila, hatta Hakimin Takai ya zo da iyalansa.
Don haka Dacta ya kama musu daki a Tahir. Don duk girman gidan nan cika ya yi da ‘yan’uwa da abokan arziki.
Addu’o’i aka fara yi, sannan daya daga cikin malaman Ibraheem (Consultant Dr. Bello Sajoh) ya ba da tarihin Ya Himu, hazakarsa da determinations dinsa kan karatunsa.
Sannan ya ja hankalin iyaye kan su karfafi ‘ya’yansu da karatu a fannin kiwon lafiya don taimakon kasarmu da al’ummar mu. Ba wai bamu da masu hazaka bane a Arewa kamar ‘ya’yan Kudu da sauran kasashen da suka ci gaba, a’a, determination wato (kuduri) yaran Kudu dana sauran kasashen da suka cigaba suka fi namu da jajircewa kan goal attainment, sai kuma ZUCIYA.
Ya ce,
“har yanzu Najeriya tana sahun underdeveloped societis, bai yarda da cewa tana shaun developing ba, saboda rashin zuciya da lalaci irin namu, muyi ta diban miliyoyinmu muna kai wa Turawa don suyi mana magani muna kara bunkasa su alhalin ba a fimu da komai ba.
Maimakon masu kudinmu da shuwagabanninmu su yi amfani da miliyoyin wajen gyara asibitocinmu da kawo magunguna masu inganci da kayan aiki ko da a matsayin sadakatul jariya ne. A’a, sai suke kaiwa Turawa suna karawa mai karfi-karfi, kasarmu kuwa da marasa hali ko oho!
Ka je asibitin gwamnati irin su Murtala da asibitocin koyarwar mu ka ga yadda ake wulakanta talaka da masu haihuwa. Lafiya ita ce gaba da komai, karatun kiwon lafiya bai yi tsamarin da al’umma ke duban shi da shi ba, nutsuwa kawai yake bukata da jajircewa.
Masu hazakarmu sun tattare a (Social Science) maimakon (Physical Science) da Arewa ke bukata, ba don rashin kwakwalwa ba sai tsoro da muka sawa zuciyarmu a kan ilimin. Don haka ne ‘yan Kudu suka fi mu ci gaba a fannin, suka fi yawa a kasashen ketare domin neman ilimin Kimiyya.
Dr. Bello ya ci gaba da cewa,
“a yanzu sabuwar gwamnatin da muke ciki ta yi alkawura na daukar nauyin daliban Arewa a fannin kiwon lafiya, amma fa sai da hadin kan iyaye. Dutyn sune su ba wa ‘ya’yansu maza da mata kwarin gwiwa a kan ilimin kimiyya, musamman mata a kan (Gynaecology) wanda yake halastacce a addininmu.
Ya ba da misali da Ya Himu, kwata-kwata shekarunsa ashirin da bakwai amma saboda samun kulawa da iyaye tsayayyu a kan al’amarinshi da kwarin gwiwar da ya sanyawa ransa da zuciya yau ga shi a cikakken likita (General Practioner) da zai iya duba kowacce irin cuta ta yara ko ta manya ya yi (prescribing) ya fadi maganinta, da yadda za ayi a kauce mata da kuma yadda za a shawo kanta in ta yi qamari. Me ya fi wannan amfani ga al’umma? Me ya fi wannan zama abin alfahari a zuciyar iyaye?”
Jama’ar sun ji dadin tunasarwar Dr. Bello, iyaye da yawa sun dauki shawararsa. Ba irin cimar da ba a ci ba.
Ibraheem ya samu kyaututtuka na alfarma. Hakimi mukullin dalleliyar mota ne. Su su Rahane yawo kawai suke cikin mutane ita ba ta ma san taron me ake yi ba sai da Jawahir ta gaya mata.
Yaya Khalipha ya tafi jihar Sokoto inda aka tura shi bautar kasa. Mami na zaune a falo tana waya da Khalipha, Himu ya fito cikin shiri da alama fita zai yi.
Ta yi mishi alamar ya dakata ta karasa magana da Khalipha. Ta gama ta ajiye sannan ta dube shi ta ce, “Ya za ka fita ba ka karya ba?’
Ya yi dan tsaki ya ce, “Ban jin cin abincin yanzu, heart burn ke damuna”.
Ta mike ta isa ga table ta hada mishi shayi mai kauri tana firfitawa ta ce, “Atleast ka sha wannan, rashin cin abincinka ya fara damuna Ibrahim.
Wai me ke damun ka ne? Na lura tunda aka yi maganar auren nan duk ka bi ka rasa kuzari. Nabilan ce ba ka so ko ya ya ne? Idan ka san ba sonta kake ba don me za ka bata mata lokaci har zuwa yanzu kana yi mata yawo da hankali?
Yarinyar nan ta ki kowa sai kai, iyakar soyayya ta gaskiya ta nuna maka, ba ta cancanci rana daya ka juya mata baya ba”.
Ta dauko GESTID tana girgizawa, shi kuma ya soma kurbar tean a tsaye. Sai da ya shanye ta zuba gestid din a cokali ta ba shi da hannun ta cikin bakin sa. Fuskarsa da zuciyarsa cike da jin dadin kauna da kulawar da uwarsu ke musu, kamar wasu kananan yara.
Ita kwata-kwata bata ganin girman su, kullum yadda take treating su Jawahid haka take treating dinsu, wani zubin har sai Dr. Mansur ya ankarar da ita. Ya ce, “Mami nifa ba yanzu zan yi aure ba, don haka ki ajiye zancen Nabila aside. In ta samu miji ku rufawa kanku asiri ku aurar da ita. Ba zan taba auren macen da ta fara cewa tana sona ba!”.
Baki Mami ta saki, ta ce, “Mai sonka kuwa ai shine masoyinka. Bakin da ya furta SO, baya dawowa ya furta kiyayya”.
Murmushi ya yi, ya sumbaci goshinta ya yi gaba.
“Sai na dawo Mami ba nisa zan yi ba”.
Ta ce, “Nima rainin hankalin za ka yi mini Himu?”
Birki ya ja, sannan ya juyo. Cikin damuwa ya ce, “Mami ya ya za ayi na raina miki hankali? Cewa nake ra’ayin da ke zuciyata kika tambaye ni? Na gaya miki gaskiyar abin da zuciyata ta yarda da shi. Bayan wannan ma ba zan yi auren zumunci ba Mami”.
Ta ce, “Hujjah?”
Ya ce, (cikin bude ido kadan) “Hujjoji barkatai”.
“Kamar wanne da wanne?”
Komawa ya yi cikin kujera ya zauna, ita ma Mamin haka, dab da shi ta zauna.
“Idan ma’auratan suka samu kuskuren fahimtar juna, kowanne zai bi bayan bangarensa ne. Sai ki ga su ma’auratan har sun manta sun shirya a tsakanin su amma abin zai yi ta zama a zuciyar iyayen nasu, a dinga kallon juna da shi. Daga nan zumunci zai baci, kin ga garin hada zumunci an lalata shi.
Irin zumuncin da na taso na gani tsakanin Mai martaba Hakimi da Daddy ban taba ganin irin sa ba. Bazan yardain zamo sanadin da zai yi tuntube ba ko kankani. Ina son yadda suka faro shi suna yin sada gaskiya su cigaba da yin sa har karshen rayuwar sub a tareda mun samar da tangarda a cikin sa ba.
Idan na auri Nabila ko laifi tayi min bazan iya hukuntata ba, zan yi ta yi mata uzuri da Baba Hakimi, haka shima ko wacce irin cuta zan yi mata bazai tada kai ba balle ya kalla, nikuma yadda bana son a danne hakkina haka bana danne hakkin kowa. Don haka auren zumunta baya cikin tsarina, don a ganina auren mugunta ne kawai.”.
Murmushi ta yi ta ce, “Hujjarka is invalid. Kai dai kawai ka ce baka ra’ayin Nabila, don in kana sonta har zuciyarka ba za ka tsaya yin la’akari da wadannan kananan abubuwan ba”.
Ya ce, “To Mami maganin kada a ji, kada a yi”.
Ya mike ya fice ta bishi da idanuwa. Sannan ita ma ta mike ta soma shirin tafiya ofis.
****
Kwanaki ke juyawa a hankali su koma satittika, satittika su bada watanni, watanni su bada shekara. Kamar yadda rayuwa take a kullum kenan, komai ma juyawa yake. A haifa, a mutu, a girma, a tsufa.
To hakan ce ta faru da Rayhanah, shekarun girma sun soma juyata daga kwaila zuwa matashiyar budurwa. Mai dauke da wasu ilhamomi da dama.
A yau Rahane shekarunta goma sha hudu, sun kammala karamar sakandire a Darul-Arqam suna jiran fitowar jarrabawarsu (placement) don wucewa babbar makaranta.
Shekaru biyu kenan da wucewar Ibrahim Jami’ar Chicagon Amurka, inda yake fafutukar kwalin zama cikakken (nephrologist) likitan koda. Yayin da Khalipha tuni ya kammala bautar kasa ya fara aiki da Ministry of External Affairs dake Abuja.
A yanzu idan kika ga Rayhanah zai yi wuya ki shaidata farat daya. Ta saje da ‘ya’yan Baba Dacta, fari kawai suka fita, sai fatarta ta ba da wata irin kala ta wankan tarwada mai sheki, jikinta ya fara cikowa ya nuna ilimi da hutu zallah.
Lokacin da jarabawarsu ta fito, kowacce makaranta daban ta ci. Amma Baba Dacta sai ya tattarasu su duka ya kai su ULUL-ALBAAB (Science Secondary) dake Katsina. Azizah ce ta ci gaba da Darul Arqam.