Showing 30001 words to 32136 words out of 32136 words

Chapter 11 - Rayuwar Rayhana Book 1 Hausa Novel Complete

Takori   

28 Dec 2024

197

ce, “Mami SOYAYYAH!”
Sai ta yi murmushi ta ce, “Alhakin Hibba ne, wace mai tsautsayin ce again?”
Ya ce, “Mami ban sameta ba, an kasa ni”.
Ta kara yin murmushin ta ce, “Ba ita kadai ce diya mace a duniya ba, Allah yasa hakan ya zama mafi alkhairi. Wani zubin in Allah ya tsara abu, sai ka ga na gaban ya fiye maka amfani. Ni tuni ai na yi maka mata Khalipha, jira nake ka zamo settled tukunna kafin in gabatar maka da zancen”.
Cikin Halifa ya karta ya bala’in kadawa. Da sauri ya ce, “Um-um Mami, bar zuciya da abin da take so. Har yau din dai da nake gaya miki ban fidda rai da samunta ba. Wani sanadi zai iya zuwa idan har matata ce Allah ya bani in aureta. Tunda an ce matar mutum kabarinsa”.
“Ya ya sunanta? A ina take Dattijo? Su waye iyayenta?”
Ya ce, “Mami tunda a yanzun bani da damar aurenta sanin wadannan amsoshin ba zai amfaneki da komai ba”.
Cikin rashin damuwa da lamarin ta mike tana fadin, “Toh! Allah ya maganta maka, ni na dauka wani muhimmin al’amari ne, zancen Radhiyyah kuwa na baka sati har biyu ka yi tunani a kai”.
A cunkushe da zancen ya ce, “Radhiyyah kuma? Gaskiya Mami bana son ki sa ranki ga abin da ba zai yiwu ba. Matakin iliminta ya wuce wanda nake so a macen da zan aura kafin in aure ta. Nafison duk wani ilmi da mace zata yi bayan sakandire tayi shi a gida na. Kuma da kadan na girmeta, in zan iya tunawa shekara uku na bata.
Haba Mami, ai an dena irin wannan hadin auren yanzu a kauye ma ba a birni ba, gaskiya ta min tsufa.
A perception dinki ban zaci akwai irin wannan tunanin ba, na abubuwan da aka yi a can wani karni can da ya shude. Na soyayyar ma yaya aka kare da shi balle na hadi?
Ki barni kawai in na samu wadda za ta maye min gurbinta da kaina zan gaya miki. Amma don Allah Mami kada ki kara daga maganar nan, kada zumuncin da ke tsakaninku da Mamanta ya lalace a kan abin da ba zai yiwu ba”.
Cikin mamaki Mami ta ce, “Ni kake cewa haka Dattijo?”
Da sauri ya gyara kuskurensa da cewa, “Ba nufina baki da iko a kai bane Mami, kawai ina gaya miki abin da zuciyata ke gaya min a kan maganar. Ki yi hakuri idan kalamaina sun bata miki rai, I’m sorry Mamee! Ki yi hakuri don Allah”.
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta fita. Allah kadai ya san abin da take sakawa da warwarewa a zuciyar nan tata. Mami na son ‘ya’yanta matuka, tana kishinsu irin kishin nan mara amfani, wanda ya kimsa mata tunanin cewa da akidar cewa ba za ta bari su auri wadanda suke mutuwar so ba, sai wadanda ke son su, don kar su rabata da su.
Irin ‘yan’uwansu su Hibbah, Nabila da Radhiyyah diyar aminiyarta Dacta Halima wadda ta ki auren minister saboda mahaukaciyar soyayyar da take yiwa Khalipha.
Mami na da wannan kudurin cikin ranta tuni, wanda kuma take da yakinin ko za ta yi yawo tsirara ne sai ta cika shi. Saboda masifar son da take wa ‘ya’yanta.

****


ASabar, biyar ga watan Yuli, rana ce ta ziyarar ‘yan makarantar kwana. Khalipha na tsaka da aiki a Office kiran Mami ya shigo wayarsa. Ya dakatar da komai ya daga ya fara gaisheta.
A gurguje ta amsa tare da cewa, “An zabe ni zuwa karbar (Award of the best paediatrician of Africa) a kasar Djbouti zamu tafi har Daddy gobe insha Allahu, so ba zamu samu zuwa ma yara visiting Katsina ba, shine na ce ko za ka samu sararin lekasu can Katsina tunda ba ranar aiki ba ce?”
Khalipha ji ya yi kamar yana yawo a kan gajimare dan dadi. Ga dama ta samu ta ganin Rayhanah wadda yau sati shida kenan bai dora ido a kanta ba, ba da tsimi ko dabararsa ba.
Domin dai Mami ba ta taba cewa yaje musu visiting ba, shi bama ya sanin yaushe ake yi sai dai Mamin ta ba shi labarin cewa yara suna gaishe shi.
Amma sai ya dan danne farin cikinsa ya ce, “O,k, to ba matsala Mami zan yi kokari in gani ko zan samu zuwan in b azan je gida ba, Congratulations Mami! Safe journey........”
Suna murmushi dukkansu suka aje wayar lokaci guda.
Aikin da ke gabansa kasa karasashi ya yi, ya hada komai ya rufe ya aje ya mike ya nufi gida.
Washe gari ranar ta kama Juma’a, bayan ya fito daga sallar Juma’a ya nufi Sahad ya soma shopping. Ba kayan ci kadai ba, har da na amfani. Wani irin Shopping yake yi kamar ba sai ya yi losing energy dinsa da lokacinsa ake ba shi kudin ba.
Sai dai kuma kayan abinci ne ya sayi komai na mutum uku, sauran kayan amfani kuwa sitturu nena sanyawa a gida ko makaranta designers ‘yan gidan versace da channel hade da dogayen riguna kala-kala da tafi amfani dasu.
Kayan shafa na Avon da coesmetics, deo-sprays duka ‘yan gidan Avon. Ya ma manta a makaranta take. Shi kansa bai san adadin kudin da yake kashewa ba, burinsa kawai Rahane ta koma irin yadda yake son ganin matarsa.
Filin makarantar ya cika ya batse da motoci da jama’a. Ba tun yau ba, tsarin Ulul-Abaab ke burge Khalipha ba. Jama’a makil kowa nasa yake nema, sai manya-manyan coolers kawai ake saukewa da katan-katan na kayan abinci da abin sha.
Lokacin da Khalipha ya iso karfe goma sha biyu dai-dai, tunanin Khalipha shine cikin wannan bataliyar al’umma ina zai je ya nemo ‘yan kannen nashi?
Don haka ne kawai ya fito daga mota ya jingina jikin kofar direba ya harde hannayenshi a kirji, don bai san ma wa zai tambaya ya nemo mishi su ba.
Sanye yake da shaddah getzner baka kar da bakar hula kalar shaddar dinkin Mohammed. Khalipha fari ne sol mai wata irin fata jawur da ta fi kama da ta mutanen Hurghada (Middle East). Hasken fatarshi ne kadai yasa ake danganta shi da Mami amma ba kamanni ba, domin ya fita kyau nesa ba kusa ba, musamman kanannadaddiyar sumar kanshi. Haka yake kamar ruwa biyu.
Kamar an ce da Khalipha juya, ya karyar da kai ya juya wani sashe daban. Rayhanah ce zaune a gindin wata bishiyar lemon tsami mai karancin jama’a ta yi tagumi da hannuwanta biyu, ko me take tunani? Allah masani.
Sanye take cikin uniform dinsu na daliban Ulul-Albaab da gajeren farin hijabi iya kafadunta. A idanun Khalipha har tsayi da zati ta kara. Duk wasu alamu na cikar budurci sun bayyana a jikinta. Kirar jiki dirarre wanda bai da alaka da kiba, cin kitse (cholestrol) ko over-eating duka babu su a jikinta. Da ganinta ka ga rainon likitoci wadda ke cin komai moderately kuma cikin tsarin balance diet na Bature.
Ya kai kallonshi ga fuskarta, kalarta choculate (wankan tarwada), fatarta fresh kamar ta yaran goye. Ba ta da dogon karan hanci gashi nan dai dan matsakaici sai manyan idanu dake lumshewa da kansu. Mai gazar-gazar din gashin gira dana ido bakake wul.
Rayhanah na da lebba masu dan kauri da sulbi kuma zagayayyu (kissable). Bayan wannan, Rayhanah ba ta da wani mugun kyan da za a dorar.
Wannan ita ce irin matar da yake so, ya dade yana nema, yana lalube bai samu ba. Ashe tana nan cikin gidansu. Duka wadannan nazarce-nazarce da ya yi, ya yi su ne cikin dan lokaci da bai gaza mintuna biyar ba.
Zuciyarshi na bugu da sauri da sauri ya rintse idanunsa, kafin ya yi tattaki zuwa inda take zaune. A lokacin ta sadda kanta kasa ne don haka ba ta ga tahowarshi ba, har ya tsugunna a gabanta. Sassanyan kamshin Chrome Legend ya tsirga har cikin kanta.
Da sauri ta dago ido ta dube shi, “Yaya Khalipha!” Ta fada cike da al’ajabi da farin cikin da ta gagara boyewa.
Murmushi ya yi, “Yaya Rahane”. Dariya ya bata sosai, don rabon da ta ji wani ya kira ta da wanann sunan, tun ranar da Babanta ya bar duniya.

A rayuwarta kuma ba sunan da take so irin Rahanen. Suna ne na mahaifiyarta da bata taba gani a duniya ba. Suna ne da Babanta ya zabar mata don kar ya manta da Yalwatinsa. Suna ne da ake kiranta da shi a Takai da intonation daban-daban.
Muskutawa ta yi ta soma share masa kura da dan hankicin dake hannunta kan dan kututturen itacen bishiyar da ta ke zaune.
“Sannu da zuwa Yaya Khalipha, yi maneji da nan ka ga duk an kwashe kujerun”.
Murmushi yake sosai, ya kwaikwayi ‘yar muryarta “Yi maneji da nan Yaya Khalipha”.
Kunya ce ta kama ta, ta rufe fuskarta da zara-zaran yatsunta.
“Ka sha hanya”.
Ta fada ba tare da ta daina murmushin da ke like a tattausar fatar bakinta ba.
“To ya za ayi? Ai ko bangon duniya Rahane ke karatu ba zan yi kasa a gwiwa wajen zuwa ziyararta ba, balle Katsina”.
A zuci yake fadi, bai san a fili yake yi ba saboda azabar son da ke kara ruruwa a zuciyarsa.
Sai ta yi dan jim tana nazarin kalamansa don sun dan yi mata tsaurin fahimta.
Ya ankara da katobarar da ya yi, ya yi saurin gyarawa da cewa, “Ina su Abida kike zaune a nan ke daya?”
Ta sadda kai ta ce, “Ni tun safe yau ban ga Abida ba, Jawahir muna zaune nan tare kawarta Teemoh ta zo ta yi kiranta su gaisa da ‘yan gidansu”.
Ta fadi haka ne don ta kare Abida, a zahiri kuma Abidar mari ta zabga mata cikin (domitory) a bainar jama’a, kan wai ta shafa vasiline dinta don nata ya kare. Jawahir kuma ba ta shafa vasilne sai lotion, abin da ya kaita ga shafa na Abida kenan.
Wannan wulakancin da Abida ta yi mata shine dalilinta na kadaicewa, tana tunanin rayuwa, canje-canjenta da juyinta, kamar rawar ‘yammata wai na gaba ya koma baya, da abebaden ban tsoro dake faruwa a cikinta.
Abin nufi, kowa baya tunanin gaba, wato me gobe za ta haifar? Mutuwa na iya zuwar wa bawa kowanne lokaci amma ta kasa gane me mutane masu irin halin Abida ke daukar duniya.
Da suke tozarta dan Adam don baya da shi, shi ba kowa ne ba. Sun manta da darajar da Allah ya yiwa dan Adam, har ya fadi da kansa cikin Alkur’ani mai girma cewa, ‘Ya karrama dan Adam…..’.
Da wannan tunanin da ta yi ne cikin ‘yan mintuna a gaban Khalipha idanuwanta suka kawo ruwa, suka kada suka yi jajir. Tunda ta sunkuyar da kanta ba ta kara dagowa ta dubi Khalipha ba kada ya gane bacin ranta.
Shi kuma Khalipha har zuwa lokacin kallon ta kawai yake cike da matsananciyar kauna cikin kwayar idanunsa, zuciyarshi harbawa take da gudun gaske sakamakon ganewa da ya yi Rahane kuka take.
Bai san sanda ya baje shaddarshi a kas, ya zauna dirshan agabanta ba, kiris ya rage su dunkule waje daya. Gaba daya ya manta a inda suke. Da murya mai sanyi yake fadin.
“Daina tunanin komai cikin rayuwar nan Rayha, tunda ga ni, zan zame miki uwa, uba, kawa, yar uwa, dan uwa, aminiya, masoyi, sannan MIJIN AURE.
Insha Allahu, daga ranar da aka daura mana aure (idan har kin amince) kin gama zubar da hawaye a kan kalubalen rayuwa. Ina sonki Rayhanah, Rayhanah za ki aure ni???”

Mu biyo Rayhanah da Yaya Khalipha a littafi na biyu. Don jin amsar ta. Tare suke. Sumayyah Abdulkadir ce Manan SAFAH da MARWAH. ke yi muku fatan alkhairi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login