Showing 3001 words to 6000 words out of 32136 words
Allah ya nuna min lokacin da za ki fara yiwa mutane allura”.
Dariya ta yi ta ce, “Iya Baba fa ba zai barni in yi irin karatun nan da kike so ba, shi kullum maganarshi ta aure ce Iya. Ni kam duk abin da zai rabani da ke da gidan nan Iya bana son shi ko da karatun ne, kuma kin san ba a yin babban karatu a nan kauye sai an dangana da birni, wa muke da shi a birni? Iya ki daina sama ranki abin da ba za ki samu ba”.
Jikin Iya ya yi sanyi amma ba ta karaya ba. Ta ce, “Gaskiyarki Rahane, nan Takai gaba daya ban da Ado direba ma wa yake zuwa birni? Shima da me ya tsira ban da shaye-shaye? Sai dai jikina da mafarkina suna bani ke wata ce Rahane, don haka kada ki karaya, ki sa a ranki kema kina da burin karatun da nake sonki da shi. Babu ta yadda Ubangiji baya shirya al’amarinsa”.
Rahane ta gyada kai ta mike ta nufi tsakar gida ta daura alwala ta gabatar da sallar azuhur, sannan ta shiga madafi ta dauko robar abincinta a karkashin turmi. Tubani ne da mai da yaji Iya ta yi musu mai silbi, sai wucewa yake silif-silif! A makogwaronta.
Ta kammala ta share kejin zabbinta da na kajinta, ta share tsakar gidansu tas, ta debi ruwa ta yi wanka ta sanya kayan makarantar allo ta yamma da take zuwa, ta dau allonta ta yiwa Iya sallama ta tafi makaranta.
Wannan shine tsarin rayuwar Rahane a kullum.
Yamma lis! Malam Rashidu ya dawo gida ya jingine kekensa a jikin danga, ya dauko kullin buhun da ya dawo da shi daga kasuwa ya shigo gida.
Dai-dai lokacin da ita ma Rahane ta dawo daga makarantar allo, ta yiwa babanta sannu da zuwa ta cika mishi buta da ruwan alwala ta kawo mishi.
Ya ce, “Sannu Rahane, Allah ya nuna min aurenki da miji na gari”.
Murmushi kawai ta yi. Ya yi alwala ya shige masallaci.
Rahane na cin tuwon ta bayan isha’i wani yaro ya shigo ya ce, “Wai ana sallama da Rahane”.
Kafin ya rufe bakinshi Iya ta yi wuf ta sunkuto tabarya ta yi kan yaron dai-dai sanda Malam Rashidu ya sawo kai, ya yi maza ya rike tabaryar tuni yaron ya yi ta kansa.
Ya ce, “Haba Iya, idan kika fasa musu kan Da me za ki ce dasu?”
Ta ce, “Gafara nan tun ban sauketa a kanka ba, gobe idaan sun kara aiko shi ya yarda ya zo”.
Ya ce, “Yi hakuri Iya, ba wani bane Ado ne, kuma da izinina ya zo su gana da Rahane”.
A firgice Rahane ta dago ta dubi mahaifinta, kamar ba ta ji dai-dai ba. Iya ta saki tabaryar ta ce, “Wane Ado kake nufi?”
Ya ce, “Ka ji Iya, Adon guda nawa ne ban da wannan makocinmu, mamallakin gidannan da muke ciki?”
Iya ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Kanka daya Baban Rahane?”
Ya kama hannun Iya ya zaunar da ita ya ce, “Ki kwantar da hankalinki Iya, na riga na bawa Ado Rahane, ki bar kama jita-jitar jama’a a kan Ado domin mutumin kirki ne”.
Iya ta saki baki tana mishi kallon mamaki, ta ce, “Adon da yake shan wiwi, taba da sholisho, ‘ya’ya shida kowanne uwarsa daban. Adon dake sakin aure da zarar matar ta samu ciki? Wanda yake rayuwa kudu cikin arna shi ka dauki kamilar diya kamar Rahane ka ba shi?”
Malam Rashidu ya yi murmushi ya ce, “Su matan kin san me suke yi masa yake sakinsu? Amma Rahane fa? Bana jin ta, don ba ta da matsala. Ki yiwa mutumin da ake yada jita-jita a kansa kyakkyawan zato, don a karshe hakkinsa kawai ake dauka.
Duk wadannan abubuwan da ake fadi game da Ado a garin nan na yi bincike a kansu.
Na farko dai Ado yana shan taba amma ba abin maye ba. Na biyu ba zai tafi da Rahane kudu ba, a nan zai barta tare da matarsa ta yanzu. Na uku su matan da yake saki din laifinsu ne ba nashi ba kamar matarshi ta farko Hassu sata ta yi mishi, ita kuma.....”
Kawai Iya sai ta tashi ta barshi a wurin ta shige dakinta. Rahane ta yunkura za ta bita ya balla mata harara sannan ya nuna mata hanyar kofar gida.
Ta toshe bakinta ta soma kuka ta nufi kofar gida.
Ado na tsaye jikin kararen da suka zagaye gidan, zai yi shekaru talatin da bakwai. Baki ne wuluk wanda idanunshi suka koma ruwan kasa suna nuna alamun shaye-shaye. Bakinsa wawakeke cike taf da jajayen hakora, bai da tsayi, don ko ita ta fishi tsayi.
Ta karasa gabanshi tana kuka kawai ko uffan ba ta ce mishi ba. Ya gyara tsayuwa bakin nan a bude ya ce, “Haba Rahane? Mene ne abin kuka? Maimakon ki godewa Allah ni Ado mai shanu da mota na zo gareki na nemi aurenki ta hannun mahaifinki?
Ni masoyinki ne, ba kowacce mace nake iya cewa ina so ba, sai mai sa’a kamarki. In baki yi murna da hakan ba, to ba za ki yi kuka ba”.
Rahane ta ga cewa kuka ba zai mata ba, gara ta roke shi ya yiwa Allah ya rabu da ita ko kadan ba ta son shi. Ba tun yau ba, haka nan ko ganinshi ba ta son yi saboda kamanninsa.
Ta ce, “Don Allah don Annabi ka yi hakuri ka nemi wata, ni makaranta nake so na yi...” Ta ci gaba da kuka.
Ya ce, “In don wannan ne Rahane daina kuka, zan barki ki ci gaba da makaranta amma bayan anyi auren mu”.
Ta zaro ido ta ce, “Ni ba zan yi aure ba, yoyon fitsari yake sawa”.
Ya bushe da dariya ya ce, “Duk karyar nasara ce Rahane, iyayenmu da kakanninmu basu kai ki ba duk aka yi musu aure, me ya same su?”
Cikin kuka ta ce, “Nifa bana sonka, ko dole ne?”
Ya yi fuska sosai, sai kuma ya ce, “Ayya! Kin makaro, zamanki lafiya da matsiyacin ubanki kawai shine ki yarda ki aure ni, wanda daga ana bashi ‘yar dari biyar ya yarda ya bani aurenki. In ke baki sona, ni ina sonki, dama ba son na zo nema ba tunda baki da kunya, har ki dubi tsabar idanuna ki ce bakya sona, ba ki yi tunanin cewa ina da kamar ki a gida ba.
Aure kuwa nan da sati biyu tunda kin bullo min ta nan. Makarantar ma na fasa barin ki kiyi, shashashar wofi!”
Ya karkace ya zaro kudi a aljihunsa ya haska da cocilan ya ce, “Ungo nan, ki raba ke da kakarki”.
Ya kuma turo mata wata katuwar leda, “Amshi nan ki sabunta tufafinki kafin a kawo lefe shashashar yarinya da ba ta san abin arziki ba”.
Juyawa ta yi tana kuka sosai ta nufi cikin gidansu bata karbi kudi da ledar da yake tura mata ba.
Ya bi bayanta ya kira wata yarinya dake sai da gyada a nan gefensu, ya ba ta kayan da kudin ya ce ta kai mata. Shi kuma ya saki wani matsiyacin fito ‘fiii-fiii....’ ya yi gaba yana cewa,
“Kwanan nan zan farke santaleliyata, Rahane!”.
Rahane na shigowa gida tana kuka ta yi ido hudu da Babanta a tsakar gida yana dakon shigowarta.
Kofar dakinsa ya nuna mata, wato ta shiga. Shi kuma ya tashi ya bita. Ya zauna a kan tabarmar shi ta kaba dake shimfide a dakin ya dubi Rahane wadda ke ta kokarin hadiye kukanta karfi da yaji.
Ya ce, “Rahane!” Ta cira kai ta dube shi idanunta jawur.
Ya ce, “Ni Babanki ne, ni na haifeki, kin san kuma ba zan cuceki ba. Ko baki son auren Ado ki yi hakuri ki tusawa zuciyarki son.
Na samu kaina da talauci mai yawa, kada ki manta gidan nan ma da muke ciki na Ado ne, amma yau tsayin shekara goma sha daya tun haihuwarki Ado bai kara karbar kudin haya na ba.
Idan na ce zan gaya miki irin taimakon da Ado yake mini ba za ki taba yarda ba. Ya sha siye kayana don in samu abin da zan baku ku ci, ba don yana da bukatar su ba.
Duk halin banzan da ake kira mishi ni na yi bincike kansu ban gani ba, zancen nan da nake miki yanzu haka ya samo min aikin kula da dawakin Hakimin Takai, na daina wahalar shan rana a kasuwa, babu wani cinikin arziki. Idan kika ki auren Ado me kike so in ce masa, ko in masa na biyashi alherin da yake yi min?
Don haka ki kwantar da hankalinki, ki kwantarwa Iya. Idan har kina kaunata Rahane ki nunawa Iya kina son auren nan kin ji Rahane? Don Allah ki fitar dani kunyar Ado”.
Rahane ta daga kai. Ta yarda kawai da kudi Ado ya saye Babanta. Abin da ba ta taba tsammani ba, kwadayi daga Babanta!
Ya ce, “Shi kenan Rahane jeki. Allah ya yi miki albarka”.
Ta mike hawaye na mata ambaliya ta fita ta samu Iya na sallah mai tsayi, sai ta hau ‘yar yaloluwar katifarsu ta kwanta.
Barci ya kasa dauke Rahane, duk iya satarsa kuwa. Duk da kasancewarta karamar yarinya ‘yar shekaru goma sha daya tana da zurfin tunani da hangen nesa.
Tana son Babanta fiye da yadda shi yake sonta, ta san Babanta ba shi da kwadayi, don haka ta yi matukar mamakin yadda ya yi hakan, kamar ma tsoron Adon yake ji.
Ta tuno wai ya samo masa aikin kula da Dawakan Hakimi, kuma baya karbar kudin hayarsa. Wannan ne dalilin da yasa zai bashi ita. Abune da take da yakinin cewa, Iya ba za ta taba yarda ba, wato ayi mata aure yanzu, don haka ta dan samu salama a cikin ranta.
Har barci ya dauke ta, kayan da Ado ya biyota dasu suna nan a gefe ko daga su Iya ba ta yi ba.
Da asubahin ranar Iya ta tashe ta don ta yi sallah. Ita kuma tana hada kayan su cikin Ghana must go. Kaf ta hada kayansu bata rage komai ba.
Rahane na sallah tana jin Iya da Babanta na fafatawa. Iya na cewa, “Gidan Ado ko? To daga yau bamu kara kwana cikinsa ni da Rahane, in dai a kansa ne za ka ba shi auren yarinya mai daraja irin Rahane. Sai ka san yadda za ka yi da shi da kudinsa da kake ci.
Ba aikin gidan Hakimi ba, Allah yasa aikin Hajji ya samo maka. Sai ka ganmu, sannan ka yi mata auren”.
Iya gigicewa Malam Rashidu ya gigice, don ya san halin Iya kwarai in ta furta abu, to wallahi ba mai iya hanata.
Shi ba wani abu bane don sun tafi, bai san ya zai yi da Ado ba wanda ko mahaliccinshi baya tsoro, yadda yake tsoron Ado a kwanakin nan.
Ya yi magiyar ya yi lallashin amma Iya ta yi banza da shi. Da ya gaji ya mike jiki babu kwari ya fita, ya kasa zuwa ko’ina yana zaune a dakinsa ya saka wannan ya kwance. Bai ma san sanda Iya tasa Rahane a gaba ba suka fice. Rahane dauke da dakon kayansu zuwa tashar motar Rake suka hau bayanta suka bar Takai baki dayanta.
****
[12/24/2019, 17:56] Takori: Tunda suka hau titi Rahane kuka take tana tunanin Babanta da abin da ka je-ya-zo. Shi kenan yanzu ta rabu da Babanta? Shima ta raba shi da mahaifiyarsa dake matukar son shi? Ina za su? Yaushe zasu dawo? Ko dai ta hakura ta ce da Iya su koma ta auri Adon?
Ita kanta Iya kuka take ranta cike da tunanika masu yawa. Ko dai su koma ne? Ta fishi iko da diyarsa ne? Ko ta fishi sonta? Ta daure mata gindi kenan ta ki yin biyayya ga mahaifinta. Ita ba aure ne ba ta son a yiwa Rahane ba, mijin ne bai yi mata ba, da shekarun Rahanen.
Mummunan hatsarin ya faru ne a kwanar shiga garin Tsangaya. Inda wata motar haya peageout irin masu mugun gudun nan ta karawa Akori-kurar raken da su Rahane ke ciki ta kife.
Wasu suka zubo kan titin, wasu suka fada cikin ramuka motar ta danne su. Tsirarun motocin dake gabansu da bayansu suka tsaya don kawao agaji. Ga shi babu jami’an tsaro a kan titin baki daya.
****
Cikin wadanda aka kwasa zuwa asibitin koyarwa na Kano, cikin masu hatsarin da suka tsira da numfashinsu har da Rahane. Cikin gawarwakin da aka kai mutuware kuma har da Iya Bilki.
A hankali Rahane ke bude idanunta tana kallon likitan da ke tsira mata allura cikin jijiyoyin hannunta.
Abubuwan suka soma dawowa Rahane tar-tar a idanunta. Da sauri ta juya gefenta inda Iya Bilki ke zaune, babu kowa. Kai dakin ma da take ciki ba ta taba ganin irinshi ba. Haka mutanen da take gani suna gilmawa ba ta saba ganin irinsu ba.
Wadannan fes-fes suke cikin fararen kaya masu tsabta, ba irin kalar jama’ar da ta saba gani bane.
Dr. Mansur, ya manyanta sosai, shine babban likita yau a emergency, yana daga zaune yake bai wa dalibansa dake tsaitsaye lacca na taimakon da za su yiwa Rahane, wadda goshinta ya fashe ko’ina kaca-kaca da jini a jikinta, ba za ka iya tantance iyakacin raunin da ta ji ba.
Dinke nan, like nan haka suka yi ta yi, yayin da kuka ya gagari Rahane saboda azabar da take ji a cikin gangar jikinta tayi azaba. Ta suma ya fi sau uku suna kakaba mata oxygen tare da bata taimakon duk da ya dace.
Washegari da ta farka karfe takwas na safe da dan sauki jikin nata. Don haka ta fara kuka a hankali. Dai-dai da shigowar Dr. Mansur da tawagar kananan likitoci dake binsa a baya.
Cikinsu har da photocopy na Dr. Mansur wato matashin likitan da ke (housemanship) mai amsa sunan I.M Takai, wato IBRAHIM MANSUR TAKAI.
Da gani babu tambaya ka ga uba da dansa. Duk da yanayin halayyarsu a fuska ya nuna ba daya bane, domin shi Dr. Mansur mutum ne mai sakin fuska sosai, sabanin Ibraheem da yake mutum mara walwala sam-sam. Duk abin da Dr. Mansur ke yiwa Rahane suna jotting ne.
Dr. Mansur ya matsa dai-dai kan Rahane ya dora hannunshi a kanta ya ce, “Daina kuka kin ji? Insha Allah za ki samu lafiya”.
Ta cira idanunta da suka kada suka yi jawur a hankali ta dube shi, bakinta na motsi amma ta kasa magana.
Ya dubi Ibraheem ya ce, “Dagata ta zauna”. Ya cirata ta zauna ya tusa mata filo a bayanta ta zauna sosai.
Dr. Mansur ya ce, “Me sunanki?” Bin shi ta yi da ido kawai ba ta yi magana ba. Ya ce, “Ku rabu da ita ta warware a hankali”.
Nurse din da suke tare ta mika mata kofin tea. Dr. Mansur ya ce, “Bata shayin ta sha Ibrahimu”.
Ya yi kamar bai ji ba, ya yi baya kadan ya dan tura Eric Ipatobe abokin karatunsa dake gabansa yayi baya. Shima Dr. Mansur sai ya yi kamar bai ga abin da ya yi din ba. Cikin girgiza kai ya karbi kofin ya matsa sosai ya soma bata da kansa. Yana fadi cikin ransa, dani kake zancen, wallahi sai na kwashe maka maki (marks).
Mamaki ya kama su dukkansu, Doctor Mansur da kansa! Da sauri Nurse din ta karba tana bata. Ya dan ja baya ya sarke hannun shi a kirjinsa bai kara kallon Ibrahim ba. Ya ci gaba da feso musu lacca kamar Obama ya diro Nijeriya.
Kwana uku Dr. Mansur na kula da Rahane, ta ji sauki sosai amma ta ki magana. Don haka ya soma tunanin akwai wani abu. “There must be something wrong beneath!” Ya fadawa su Ibraheem.
Ya girgiza kai ya juya gare su, “Tana bukatar ganin likitan kunne da makogaro yayi examining dinsu, wanda wannan ba shine darasin da muke a kanshi ba tukunna, muna neman lafiyar gangar jikinta ne gaba daya”.
Cikin sati biyu Dr. Mansur ya ba da hankalin shi da kwarewar shi gaba daya a kan Rahane da shi da Dr. Imam, kwararren likitan kunnen da