Showing 30001 words to 33000 words out of 34298 words

Chapter 11 - Asp Zarah 1 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

204

ba."

"Tab! Ina hutawa mana, kawai naga baka da wanda zai maka ne shiyasa nakeyi."

"Ai kuwa nagode na kusa kawo miki Anty ki huta."

"Da gaske Yaya." ta faɗa da ɗoki

"A'a bance ba karki kaini gaba." dariya sukayi duka sannan ya shige banɗakin yana faɗin.
"Idan kin gama ki ɗaukomin fresh milk."

"Toh"
Sai da ta kimtsa ɗakin sosai duk da jiya ta shigo ta gyara amma tana ganin abubuwan da yakamata ta gyara musu waje, fita tayi domin zuwa ɗauko fresh milk ɗin.
Baaba kaɗai ta tarar a zaune tana kallo sai Raliya dake ƴan goge-goge a gefe.
"Yauwa Zara'u yanzu nake shirin aika Raliya ta kiramin ke."

"Me zanyi miki kuma."

"Bani ke nemanki ba, Abdullahi ke nemanki zakuyi sallama domin daga masallaci zasu wuce."

"Ayya bari na haɗo saƙon Momi naje muyi sallama, suna ina ne."

"Suna can falon baƙi."

"Ina zuwa."

Ta faɗa tana haurawa sama da gudu, ɗakinta ta shiga tare da nufar inda ta ajiye jakar tsaraba data tanadar musu da wacce takeso a kaiwa Momi, rufuwar jakunkunan ta gyara sannan ta ɗaukosu ta fito falon, kallon Baaba tayi tace.
"Dan Allah Baaba Raliya ta kaiwa Yayana fresh milk karya fito yaga ban kai mishi ba."

"Ɗaukomin ni na kai mishi."

"Yauwa" ajiye kayan tayi akan kujera sannan ta nufi kitchen ta ɗauko fresh milk ɗin da cup ta miƙa mata, kayan ta ɗauka ta nufi falon baƙin ita kuma Baaba ta miƙe ta nufi ɗakin Sadiq ɗin.

"Ahh Baaba da kanki kuma, ita little ɗin me takeyi da bazata iya kawomin ta koma ba.?" cewar Sadiq dake ƙoƙarin fitowa daga bedroom sanye da farar jallabiya.

"Bakaji daɗi bane da ni na kawo."

"A'a kawai naga kamar ba aikinki bane."

"Sai kuma kayi idan bazaka sha bane na maida, ita wacce kake magana tana gurin mijin da zata aura zasuyi sallama domin zai koma inda ya fito."

"Yi haƙuri Baaba, dama Bro ɗin yau zasu wuce shine basu faɗan ba."

"Gashi ni na faɗa maka ai."

"Ehh to nima inaga yakamata naje muyi sallama ko."

"Yakamata gaskiya."

"Bari naje na dawo sai muyi hirar soyayya."
Dariya tayi kawai shi kuma ya fice a ɗakin.

Ƙoƙarin riƙe handle ɗin yake domin shiga falon saidai maganganun dake tasowa yasa ya jinkirta domin jin cigaban zancen, muryar M.J ya kuma ji yana faɗin.
"Idan kinsan da kuɗin karuwanci kika siyama uwata waɗannan tarkacen ki tattara kayanki ki koma dasu domin rashin arzikina bai kai matakin da zan iya barin uwata tayi amfani da abin haram ba."

"M.J wai meke damunka ne akan yarinyar nan, wai ko mantawa kake itace wacce ake ƙoƙarin ɗaura muku aure nan da satikai uku masu zuwa.?"cewar Abdallah.

"Abdallah kenan ina sane da duk abinda nakeyi, wannan da kake magana akanta bana mata wanj kallo da ya zarce na mazinaciya, karuwa, sannan kuma fasiƙa mai aikata abinda Allah ya haramtashi, bana mata kallon matar da nake shirin aura domin bata cancanci a alaƙanta ta dani ba bare kuma aje batun aure, ina mata kallo ne na wacce ake ƙoƙarin kawomin domin na horata akan abinda da ta daɗe tana aikatawa." sannan ke kuma, ya waiwaya ga Zarah dake zaune zuciyarta na barazanar faso ƙirjinta ta fito saboda baƙin cikin daya turnuƙeta
"Ina ƙara jan kunnenki tare da baki shawara da ki zubar da duk wasu mugun nufinki nason cigaba da bin maza a gidana domin bazan lamunci hakan ba, a cikin gidana dana gina da tsarkakkun kuɗi bana haram ba a dinga aikata saɓon Allah a ciki, mazinaciyar banza mazinaciyar wofi, wa ya sani ma ko a gada kikayi kika tsotso a no..."

Tasss!!! Ta katseshi ta hanyar baiwa fuskarshi wadataccen mari zazzafa domin zuwa yanzu bazata iya jure cin mutuncin nasa daya bar kanta ya koma kan iyayanta da basa duniyar ba ma.
Baki buɗe suke kallonta, a ɓangaren Abdallah tsantsar farin ciki da mamakin abinda Zarah tayi ne ya hanashi magana, shikuwa M.J baƙin ciki da mamakine suka turnuƙeshi lokaci guda.
"Ni kika ɗaga hannu kika mara.?" Ya faɗa yana huci.

"Na mare ka kuma in gab da yi maka abinda yafi mari zafi matuƙar zaka taɓa mutuncin iyayena, banza kaw..."
Bata ƙarasa ba itama ya wanke mata fuskarta da mari kafin ta kuma ankara ya ƙara wanke mata ɗaya ɓarin da mari mai zafi, saidai ko kaɗan Zarah bataji zafin shi a fuska ba saboda zafin zagin iyayenta da yayi yafi komai ƙuna a gareta.

"Kina karuwa har kin isa ki ɗaga wannan hannun naki mai cike da ƙazantar zina ki mare ni, wallahi baki isa ba kuma ƙunci yanzu kika fara shiga cikinsa nonsense."

A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shigo duk da halin da yake cike bai hanashi yin sallama ba, kai tsaye inda take a durƙushe ya nufa batare da yayi magana ba, hannu biyu yasa ya miƙar ta ita tsaye tare da riƙe hannuwanta suka nufi ƙofar fita daga falon, ɗan tsayawa yayi sannan yace
"Dama sallama nazo yi muku, idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya."
Yana gama faɗin haka ya ja hannunta suka fice a falon, daga Abdallah har M.J babu wanda ya tanka, shikam Abdallah baƙin ciki yakeji na abinda abokin nasa ya aikata tare da dana sanin wannan rakiya da yayi, a ɓangaren M.J kuwa babu wani abu da yakeji a ranshi face ɓacin ran da Zarah ta sakamai ta hanyar marinshi.
Miƙewa Abdallah yayi tare da ɗaukar kayan da Zarah ta ajiye mai ya fita batare daya kula M.J ɗin ba, bayanshi ya bi ganin bai kulashi ba suka fita tare, sun rigada sun sanar da direban dazai kaisu airport ya shirya dan haka bayan motar suka shiga yajasu zuwa airport ɗin.
Ko da suka isa basu yima juna magana ba har zuwa lokacin da suka shiga jirgi ya keta hazo dasu.
Kuka take me matuƙar ban tausayi da sosa ran duk wani mai sauraro har suka isa ɗakinta, kan gadon ɗakin ta faɗa tana cigaba dayin kukan, shikuwa Sadiq nufar inda hoton mahaifansu dake gefe yayi ya ɗauka tare da rungume hoton a ƙirjinshi, sai a lokacin kukan daya danne ya hanashi fitowa yayi nasarar bayyana kanshi batare dayayi ƙoƙarin dakatarwa ba shima ya fara kukan yana faɗin

"Meyasa zai rabamu daku, me muka mishi zai rabamu daku ya barmu cikin gararin rayuwa da rashin gata, Abba! Mami kuna ganin yadda rayuwarmu ta tagayyara da bakwa tare damu, Abba meyasa bakace mutuwar ta ɗaukeni ba ta barka ka kula da ƙannena, Abba inajin kamar na gaza riƙe amanar ƴan'uwana da kullum kake daɗa jaddadamin, Mami kina gani koh? Ki tayani roƙon Allah yayi gaggawar ɗaukan raina bazan iya jure ganin ƴan'uwa cikin halin baƙin ciki da ƙunci ba alhalin ina raye. Kaicona dana kasa riƙe amanarka Abbana yau ga ƴar'uwata tana zubda hawayen baƙin ciki dana maraici sannan ina kusa na kasa aikata komai, Ya Allah kayi gaggawar ɗaukan ra...."
Hannu aka saka tare da rufe mishi bakinshi, bashi da ƙarfin dazai iya hana hakan shiyasa ya cigaba da rera kukan shima mai ban tausayi.
Zama Baaba tayi a gefen gadon ta ɗora hannun hagunta a bayan Zarah tana bubbugawa alamun rarrashi hannunta na dama kuma na kan Sadiq tana shafawa a hankali.
Sun ɗauki tsawon mintuna a haka batare da sun daina kukan ba, ganin haka yasa Baaba tace.
"Idan rai ya ɓaci ambaton Allah akeyi ba kuka ba."

"Baaba na gaji bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, na gaji ta dalilinsu fa muka shiga wannan halin amma abinda zasu saka mana dashi kenan, bazan iya jure wannan cin mutuncin da akeyiwa iyayena ba zan maida musu da Diamonds ɗinsu ko zamu huta da wannan takaicin." Zarah ta faɗa cikin fitar hayyaci, da sauri ta miƙe ta nufi gaban dressing mirro ɗinta tana watsi da duk wasu abubuwa dake kai batare da ta kula da irin ɓarnar da takeyi ba. Sai da zuba komai na kan wajan a ƙasa kafin da fara ƙoƙari tura dressing mirro ɗin gefe.

"Me kike ƙoƙarin aikata ne haka Fatimah?" Baaba ta faɗa a fusace.

"Bazan iya ba Baaba zan basu Diamonds ɗinsu kawai na huta." ta ƙarasa fada lokacin da tayi nasarar tura dressing mirror ɗin gefe, tsugunnawa tayi a gaban wani tiles a wajen, hannu takai da nufin taɓawa sai dai kamar a danna mata remote ta dakata saboda jin kamar anayi mata raɗa a kunne.
"Raliya!!! Batula Raliya na waje." haka taji a kunnenta tamkar wani ke magana, da hanzari da nufi ƙofar fita bata ko ganin gabanta saboda tsananin tashin hankali, da mugun ƙarfi ta buɗe ƙofar.

Rasss! Rasss!! Rassss!!! Haka ƙirjin Raliya ya bada sauti wacce ke tsaye a jikin ƙofar riƙe da sound recorder da kuma ƙaramar camera tana ɗauka duk wani abu dake faruwa ta ɗan ramin ƙofar data buɗe kaɗan ganin mutanen ɗakin basa cikin hayyacinsu bare su lura da ita, tsananin tashin hankali da firgici ne ya ziyarceta lokaci guda ta fara ɗika saboda zufar da tayiwa jikinta ƙawanya lokaci ƙanƙani..

Wata irin shaƙa Zarah takai mata........✍️

😱😱😱😱😱😱😱
*YANZU NE FA ZA'A FARA ASALIN LABARIN _ASP ZARAH_👩‍✈️ MATAR MUHAMMAD JAWWAD KAWAR JIDDAH MATAR SALEEM. LOKACIN DA ZAMUGA ƁOYAYYEN SIRRIN DAKE TATTARE DA JIDDAH YAYI FA🤔*

*SHIN ZARAH ZATA MAIDAWA DADDY DIAMONDS ƊINSA KO KUWA ZATA BARSHI A WAJENTA HAR SAI ZUWA LOKACIN DA ZATA KAUDA ALPHA.???*

*ME ZAI FARU TSAKANIN ZARAH DA RALIYA NE A WANNAN FITO NA FITO DA SUKAYI.???*

*WANI MATAKI DADDY ZAIYI NE IDAN YAJI LABARIN ABINDA ƊANSHI YAKE AIKATAWA GA YARINYAR DATA SADAUKAR DA KOMAI NATA DOMIN KARE DUKIYARSA WACCE TA DALILIN HAKANE TA RASA IYAYANTA SANNAN ƳAR'UWARTA TA FICE A HAYYACINTA.???*

*AURAN MUHAMMAD JAWWAD DA FATIMAH ZARAH NA YIWUWA KUWA.???*

*SHIN ALPHA YANA SAMUN NASARAR MALLAKAR WAƊANNAN LU'U LU'U MASU MATUƘAR DARAJA.???*

*YA BATUN RAHAMA A CAIRO. INA MUSTAPHA KUMA???.*

*SHIN TANA SAMUN NASARAR KAMA ALPHA KAMAR YADDA TASHA ALWASHI.???*

*MEZAI FARU NE IDAN M.J YA GANE IRIN SADAUKARWAR DA ZARAH TAYI AKAN DUKIYAR MAHAIFINSHI.???*

*INA BATUN ALMAJIRAR DA ZARAH TA TAƁA HAƊUWA DA ITA NE.???*

_DUK AMSOSHIN TAMBAYOYIN DAMA WASU NA TARE DA JASMINE🌸🌸 A CIKIN LITTAFIN ASP ZARAH👩‍✈️, YANZU AKA FARA_.


*BY*
*JASMINE*🌸🌸


*ASP ZARAH*

Wata irin shaƙa Zarah takai mata saidai cikin zafin nama ta kauce tare da hankaɗa Zarah ta faɗi ƙasa sannan ta nufi hanyar matattakalar da zai sadata ƙasa, ganinta tayi a gabanta tamkar wacce aka jefo kafin ta ankare taji saukar duka ta ko ina a jikinta ta yadda babu ta inda zata iya kare kanta, dukanta takeyi sosai tamkar wacce ta kama ɓarawo a bayan kanta.
"Baki da hankali ne Zara'u me tayi miki kike dukanta? Ki sake ta tun kafin raina ya ɓaci." Baaba kenan ke faɗi bayan ta fito taga abinda ke faruwa, shikuwa Sadiq yana gefe a tsaye bai tanka ba domin yasan hakan nan Zarah baza ta yiwa Raliya wannan dukan ba idan ba wani mumminan laifi ta kamata dashi ba.
Saida taga ta daina motsi kafin ta sassauta duk kuwa da hargowar da Baaba keyi mata akan ta rabu da ita, hannu ta saka ta fincike hijabin dake jikin Raliyan saidai ga mamakinta ba hijabi ɗaya bane a jikinta, saida ta cire hijabai uku kafin tayi tozali da jikinta kai tsaye hannu ta saka ta juyata daga kwancen da take kamar gawa ta duba gefen wuyanta, kamar yadda tayi tsammani kuwa zanen tatto ne a gefen wuyan nata, bishiyar kwakwa ne da sunan Alpha da aka ƙayata ta hanyar zanen, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayarta ta ɗauki hoton gurin kana ta danna kiran waya tana karawa a kunnenta.
"Kuzo da mota biyu gidan mu." shine kawai abinda ta faɗa kafin ta juya ga Baaba wacce ke sharar kwalla tana sambatu.
Hannunta ta riƙo suka koma cikin ɗakin ta zaunar da ita a gefen gadon itama ta zauna tare da karɓar ruwan da Yayanta ke miƙa mata tasha sannan ta maida kofin yaƙara tsiyayawa ta miƙa ma Baaba itama.
"Shikenan kin ja mana zagi a gari Zara'u za'ace mun kasa riƙe waɗanda ke ƙarƙashin mu."

"Baaba tun ranar da kika gayamin kin ɗauki yarinyar nan aiki na nunq miki banso ba, haka ne."

"Eh sai me dan bakiso ba ai ni inaso, shiyasa kike neman ki mata lahani tana marainiya."

"Wai ke waya gaya miki wannan yarinyar marainiya ce Baaba? Spy ce fa aka turo mana a matsayin mai aiki."

"Mene ne haka.?"

"Ƴar leƙen asiri mana, Alpha ne fa ya turota.?

Wani zabura duka su biyun sukayi a tare suka kuma haɗa baki wajen faɗin
"Alpha.???"

"Kwarai kuwa."

"Kin tabbata little.?"

"Sosai na daɗe da tabbatar da haka banaso na kamata a bisa zargi ne shiyasa amma da ta daɗe da zama a kurkuku, zo muje ɗakinta ka gani."

Miƙewa sukayi duka suka nufi ɗakin Raliyan, sosai Baaba tasha mamakin abubuwan da Zarah ta nuna musu a ɗakin wanda babu ko tantama duk wanda yaga wannan yasan akwai abinda ake ƙullawa.
"Tabbas ɗan adam na da wuyar fahimta, ki duba kiga yadda yarinyar nan ta ɓadda kama ta zo min a maraice tana roƙon abata aiki ashe cutar mu tazo tayi, Allah ya toni asirinta. Allah sarki Zara'u shiyasa sam baki yadda ko gurin zama ku haɗa ashe kinsan abinda kika gani, ni kuma duk da haka ban fahimci komai ba."

"Gaba saiki kiyaye kisan waɗanda zaki dinga zaɓa kuyi mu'amala tare..." Ringing ɗin wayarta ne ya hanata kai aya a zancen nata.
"Ehh ku shigo falo" haka kawai ta faɗa ta kashe wayar.
"Jami'ai sun iso muje."

"Ina za'a kaita ne little."

"Za'a cigaba da tsaronta har zuwa lokacin da za'a kama maigidan nasu a yanke musu hukunci."

"Kina ganin hakan bazai janyo wata matsalar ba."

"Babu abinda zai faru Yayana da izinin Allah."

"Toh Allah yasa."

"Amin " suka haɗa baki wajen faɗa ita da Baaba, sannan suka bar ɗakin zuwa falo inda jami'an suke.

"Ku tafi da ita Nura a fara kaita asibiti a duba lafiyarta daganan sai a wuce da ita station a rufe ta, ban yarda ko waye yazo a fito da ita ba, sannan duk wanda yazo belinta indai ba jami'i bane to a haɗa dashi a rufe, kuna jin abinda na faɗa koh."

"Zamu kiyaye ranki ya daɗe."

"Joy da Halima ku ɗauketa ku kaita mota sai ku wuce."
Sara mata sukayi duka sannan sukayi kamar yadda tace suka fita a falon.

"Allah ya kyauta ya daɗa karemu daga kaidin wannan mutumin."

"Amin thumma Amin.'' cewarsu duka.

"Yauwa Baaba sai batun auren Little da M.J gaskiya za'a janye ba za'ayi wannan auren ba."

"Akan wani dalili za'a janye batun auren? Toh indai akan abinda Muhammadu yakeyi ne wannan auran babu fashi sai anyi shi, watarana ko kuɗi aka bashi yayi wannan abun bazai iya ba."

"Amma fa kinajin irin alwashin da yake ɗauka akanta muddin ta amince akayi auran."

"Naji tun ba yau ba nasan duk abubuwan da yake faɗa game da ita wanda nasan ba haka bane amma inaso mu tura mishi aniyarsa ayi auran. Duk abubuwan da suke faruwa fa bai sani ba na tabbata ranar dazai san wani abu a game da abinda takeyi zaiyi nadamar komai daya aikata a gare ta, dan haka aure nan da sati biyu babu fashi."

"Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhari."

"Amin ai addu'ar daya kamata kayi kenan Allah ya zaɓa mata abinda yake shine alkhairi a wannan auren."

"Uhmm! Little me kuka shirya game da events ne."

"Babu abinda zamuyi Yaya."

"Bai kamata ba gaskiya, ko sports daya ai zamuyi."

"Hakane fa Bro kuma kamar kasan mun daɗe bama yin sport wallahi."

"Eh nasan Sis Rahama zataso hakan sosai."
Murmushi kawai tayi mai kama dana ciwo domin duk sanda za'ayi maganar sports sai ta tuna mahaifanta.

"Wani wasa kika zaɓa."

"Dear inajin volley ball zaifi tunda kaga harda mata a ciki."

"Hakane amma gidan Daddy akwai pitch ne."

"Ehh mana ai saboda mu yasa akayi sports garden tun waccen lokacin idan mukaje muna playing dasu brother Adil da Nusaiba..." sai kuma hawaye shar ya biyo bayan maganarta ta.

"Bana sonki da yawan kukan nan fa little, addu'a kawai zamu cigaba dayi musu, ko kinaso ki haifi yara a rasa gane wacece uwar idan kuna kuka dukanku."
Hannayenta ta saka ta rufe fuska tana faɗin.
"Kai Yaya."

"Ehh mana, tashi muje kitchen mu haɗa dinner kafin Daddy ya dawo."

"Ohh kasan na manta da Daddy na gidan nan, ina yaje ne."

"Ya fita yun ɗazu zai haɗu da wani abokin kasuwancinsa."

"Nagode wa Allah da bayanan wannan abu ya faru."

"Muje kitchen ɗin."

"Yaya akwai abinci fa."

"Ni dai muje muyi ko ma mene ne, da kwaɗayi na dawo ƙasar."
Hanyar kitchen ɗin suka nufa suna hira kamar wasu ƙawaye.

''Allah ya shirya ku."

"Amin" Zarah ta faɗa daga kitchen ɗin...✍️


*Ayimin uzuri da wannan pls banjin daɗi ne, ayi haƙuri.*👏👏👏👏



*Jasmine*🌸🌸
*ASP ZARAH*

_Duk abinda aka sama lokaci..._

Kamar yadda yau ta kasance saura kwanaki biyu kacal a ɗaura auran Zarah da angonta M.J, baƙi na nesa da na kusa duk sun hallara, inda Ammi da Momi suka dage wajen gyara Zarah sosai tamkar wacce zata auri shugaban ƙasa. Babu wasu events da akayi sai sports day da sukayi sai kuma walima da za'ayi bayan ɗaura aure.
Suna zaune su uku a wani keɓaɓɓen guri a cikin garden ɗin gidan Daddy, Sadiq ne a tsakiya sai Zarah da Rahama da suke a gefensa kowaccensu ta ɗaura kanta a kafaɗarsa, kallo ɗaya zakayi musu duka ka tabbatar da cewa suna cikin damuwa sosai, idan ko mutum yasa da mutuwar mahaifansu toh tabbas za'ace maraici ne ke damunsu. Sadiq ne yayi gyaran murya yace.
"Sis kinji abinda ke shirin faruwa da little fa kuma Baaba ta hana a dakatar da bikin nan, ni banaso taje tana shiga damuwa ne kinsanta da rauni."

Rahama wacce tun bayan abinda ya faru ta zama miskila ta wucin gadi, shiru tayi na mintoci kafin tace.
"Dakatar da auren bashi ne mafita ba Yaya, mu bari muga idan anyi auren yana cutar da ita sai mu nemi mafita."

"Bakomai amma indai ya cutar da ita sai na bi mata haƙƙinta ko da kuwa igiyar zumuncin dake tsakanin mu zata tsinke."

"Haka ma bazata faru ba."

"Toh Allah yasa, little tashi kije Daddy na nemanki tun ɗazu mantawa nayi ban gaya miki ba."

Cikin sanyin jiki Zarah ta miƙe tana faɗin
"Ku jira ni fa yanzu zan dawo."

"Mu ma yanzu zamu shigo gidan."

"Toh sai kunzo".
Kai tsaye falon Daddy ta nufa inda yake zaune shi kaɗai da alama ita yake jira, gaishe shi tayi sannan ta zauna a gefe,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login