Showing 9001 words to 12000 words out of 34298 words
mutum ne shi mai matuƙar taka tsantsan kasancewar shi wanda jami'ai ke nema ido rufe shiyasa baya taɓa bada damar a ga wani sashi na jikinshi koda kuwa farce ne. Idan kuwa kayi nasarar ganin wani abu nashi to daga wannan lokaci zaka zama makusancin shi bayan an shiga dakai wani ɗaki mai taken _Kusanci da Alpha_, wata ɗaya cur ake kwashewa ga duk wanda ya samu nasarar shiga wannan ɗakin saidai mutum yakan fito ne a galabaice. Idan mai tsawon kwana ne zaiyi dogowar jinya, idan yazo da ƙarar kwana kuma saidai a wuce da mutum kabari. Babu wanda yasan abinda akeyiwa mutum a cikin wannan ɗakin domin hatta Raliya da aka shigar da ita tace bazata iya tuna komai da ya faru ba.
Ko bayan mutum ya samu kusanci dashi bazai ƙara samun damar ganin wani sashi na jikinshi ba saidai zai kasance yana kasa saɓa umarnin Alpha ɗin koda kuwa umartarka yayi da kashe kanka.
*Abuja*
Cikin kwanciyar hankali da tsari ake gudanar da taron na ƙarawa juna sani a harkar aiki inda Zarah tayi zarra kwarai wajen baiyana dabaru da koma salon aiki da kowani jami'i ya kamata yayi amfani dasu, a cikin kwana huɗun da tayi a gari Abuja an samo nasarar zaƙolo manyan masu laifi da aka daɗe ana nema, hakan yasa aka shirya karramata a ranar ƙarshe da za'a kammala taron a matsayinta na jajirtacciyar ƴar Sanda da hukuma ke son irinta.
Kasancewarta mace kuma kyakkyawa yasa manyan masu muƙami a rundunar Ƴan Sanda ke ƙoƙarin janta a jiki amma taƙi bada damar hakan, domin hatta ɗakin da aka kama mata a hotel ɗin da aka sauki baƙi irinta wanda sukazo daga wani gari taƙi karɓa. Gidan wata abokiyar karatunta na sakandire dake zaune da mijinta a cikin garin Abujan nan ta sauka.
*Bauchi*
A yau ne akayi addu'ar kwana bakwai na rayukan da aka rasa a farfajiyar gidan marigayi Alhaji Abdul_Jalal, inda akayi saukar alqur'ani mai girma tare da yiwa mamatan addu'o'i.
Ƙarfe biyu jirginsu Ammi ya ɗaga zuwa Cairo ita da maigidanta da kuma Rahma da suka wuce da ita domin cigaba da duba lafiyar saboda har zuwa wannan lokacin bata magana tun bayan farfaɗowarta.
Daddy da Momi ma bayan sallar la'asar suka ɗauki hanyar tafiya Bauchi. Sai gidan ya ragw daga Baaba sai Muhammad Jawwad da wata tsohuwa da Daddy ya samu domin tayasu zama sannan jami'an tsaron da Mustapha ys ɗauki nauyin ajiye musu guda biyar.
Shima Muhammad Jawwad a washegarin ranar zai wuce Abuja ya ziyarci wani abokinshi dake aiki acan, sa'an nan daga can ya wuce ƙasar England domin haɗo takardunshi tare da takardar shaidar aiki da yakeyi acan saboda samun sauƙin cigaba da aikinshi a Nigeria.
Washegarin kuwa shima ya wuce garin Abuja, kasancewar su Daddy basuyi mishi batun Zarah ba shiyasa baisan tana garin ba.
Ƙarfe 12:30nr ya isa garin Abujan inda abokin nashi yazo ta taryeshi a airport ɗin, daga nan kai tsaye gidanshi suka nufa.
Bayan yaci abinci ya huta ne ya buƙaci su fita domin zaga gari.
Ta fito da nufin tafiya gurin da suke ƙaddamar da taron kiran wata abokiyar aikinta Toyin wacce suka haɗu wajen taron ya shigo wayarta inda ta buƙaci ta biyo ta hotel ɗin da take domin su wuce tare.
Agogon hannunta ta kalla taga akwai sauran mintuna 45 kafin a fara taron hakan yasa ta yanke shawarar tsayawa a wani resturant da tagani domin siyan burger da ta tashi da marmarin ci a yau.
Suna ƙoƙarin fitowa daga *Koise Delicies* ita kuma tana ƙoƙarin shiga waya kare a kunnenta, karo sukayi da Abdallah wanda ke gaba yayinda Muhammad Jawwad ke bayan shi.
"Sannu dan Allah." shine abinda ta furta sannan ta cigaba da tafiya tana mai magana a waya inda takw cewa.
"Jirani a reception na hotel ɗin bansan ɗakin ba."
Dogon tsaki Muhammad Jawwad ya saki bayan sun shiga mota kafin yace.
"Suna fakewa da aikin ƴan sanda suna abinda suka ga dama, yanzu menene abin burgewa ga mace a aikin ƴan sanda kuma musulma.?"
Dariya Abdallah yayi sannan yace.
"Nikam naga abin burgewa sosai, ka dubi yadda tayi shiga cikin kamala ba kamar wasu matan dake irin aikinta ba, sannan maganar hotel da kaji tanayi ƙila wani aikim zai kaita can kasan su aikinsu babu inda bayakai mutum."
Baki kawai ya taɓe batare da ya kuma magana ba....
*ASP ZARAH*👩✈️
_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸
*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al'umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩✈️
👩
Free Page
Alhamdulillahi taro yayi kyau an watse lafiya bayan kyaututtuka da aka rarrabawa jami'ai tare da karrama wasu daga ciki inda Zarah ta kasance cikin waɗanda aka karrama.
Saida ta ƙara kwana biyu cikin garin Abuja sakamakon jirginsu Jiddah dazai sauka ta garin bayan ya taso daga ƙasar Malasia.
*_Jiddah ƙawace ga Zarah tun zamanin ƙuruciya, tare sukayi makarantar firamari da sakandire inda bayan sun kammala Jidda ta wuce jami'a yayinda itakuma Zarah ta wuce makarantar bada horo na ƴan sanda. Duk wasu sirrika na Zarah Jidda tasansu kamar yadda yake a ɓangaren Zarah itama._
_A shekarar data gabata ne Jiddah tayi aure inda mijin data aura ya kasance Barrister wanda yake aiki a ƙasar Malasia wato Bar. Saleem, dakyar aka rarrashi Jiddah tabi Saleem ƙasar a waccan lokacin bayan tayi iƙirarin ita bazata iya tafiya wata ƙasa batare da Zarah ba, shima dai Saleem ɗin bawai yana ƙaunar aiki a wata ƙasa bane illa dai kawai yanason ƙarasa yarjejeniyar aiki da sukayi da ƙasar. Tun bayan tafiyarsu kuma basuzo gida ba sai wannan karon da suka tattaro gabaɗaya suka dawo ƙasarsu ta gado._"
Sallama tayi da ƙawarta ta tare da yimata godiya sannan ta wuce filin jirgi inda tanan zasubi wani jirgin zuwa Bauchi.
Tana tsaye jirgin ya sauko daga sararin samaniya, bayan wadu mintuna kuma matafiya suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, sam bata kula ba sai ji tayi an rungumeta gam tamkar za'a tsaga ta.
"Nayi kewarki sosai sahibaty.''
Jiddah wacce ita ke da alhakin rungumar ta faɗa cike da farin ciki, kana ta saketa tare da ƙamewa ta sara mata kana tace.
"Na gaida ASP da kanta."
Murmushi kawai tayi tare da maida hankalinta ga Saleem dake cewa.
"Zan shigar dake ƙara fa Zarah, ganinki kawai yasa ta mance dani ma gabaɗaya."
Dariya sukayi duka sannan suka nufi gurin da aka tana da domin zaman ma tafiya.
Mintuna kaɗan jirgin dazai sadasu da garin Bauchi ya keta hazo.
*England*
Tsaki yaja a karo na ba adadi cike da takaici, tashinsa kenan daga bacci sannan kamar koda yaushe yau ma mafarkinta ya ƙarayi wanda ya haddasa wajabcin wanka ya hau kanshi. Ya rasa dalilin dayasa tun ranar daya ganta kullum dare sai yayi mafarkin yana wani abu da ita wanda hakan ke silar dole idan ya tashi sai yayi wankan tsarki.
Wannan shine dalilin dayasa yake jin wata muguwar tsanarta a cikin ranshi.
Miƙewa yayi tare da shiga banɗaki, bai jima sosai ba ya fito cikin shirinsa na farar riga da baƙin wando.
Wayoyinshi ya ɗauka da niyar ficewa a ɗakin, saidai missed calls din Ammi daya gani a cikin wayar ne yasa shi dakatawa tare da zama a gefen gadonshi yana ƙoƙarin kiranta.
Bugu biyu ta ɗauka tana mai sallama, amsawa yayi tare da gaisheta.
"Har yanzu banga wani alert ba fa Jawwad." Ammi ta faɗa.
Cikin son gane mai take nufi yace.
"Ammi wani irin alert kuma na mene ne."
"Zan saɓa maka fa, ka maidani sa'ar wasan kace. Ko ba dakai mukayi magana zaka turo kuɗi a fara haɗa lefen ba.?" Ta ƙarasa magana cikin hassala.
Dafe kai yayi saboda tunawa da abinda take nufi, gaba ɗaya ya manta da batun aurenshi da Daddy yace zai haɗa da ƴar marigayi wacce bai ma santa a fuska. Shi a tunanin shi girman kai ne ya hanata zuwa ta gaidashi ko tabari su haɗu lokacin da yaje Nigeria, shiyasa yaji baya ƙaunar yin auren duk da matsalar da yake fama da ita na ƙarfin sha'awa.
"Ayi haƙuri Ammi zan turo insha Allah." Ya faɗa cike da biyayya.
"Toh ina jira kada ka sake na ƙara kiranka akan wannan batun idan ba haka ba kuma ranka ɓaci zaiyi." Ta faɗa gami da kashe wayar.
Dafe kai yayi cikin damuwa, shifa yana da ra'ayin irin matar da yakeson aura, amma gashi yanzu Daddy ya ruguza mai duk wasu tsarin shi.
Miƙewa yayi jiki babu laka ya fita domin yana a farkon sabuwar wata da za'a yakeson komawa gida gaba ɗaya, shi da ƙasar turawa kuma sai ziyara ko hutu ko kuma wani abu mai mahimmanci.
.......................
A bakin gate su Zarah suka tarar da wasu mutane biyu da alama dai miji da mata ne sannan marasa ƙarfi.
Ganin motar ne yasa su miƙewa daga durƙusun da suke a gefen gidan.
Tsayar da motar Saleem yayi kamar yadda Zarah ta buƙata, buɗe ƙofar baya ta fito ta nufi inda suke tsaye.
Da sassafar matar ta ƙaraso tare da durƙusawa akan gwiwoyinta tace.
"Ranki ya daɗe ki taimake mu, kwana uku kenan muna zuwa gidan nan amma anƙi bamu damar shiga. Hatta ofishinku ma an hanamu ganinki dan Allah ranki ya daɗe ki sauraremu."
Ɗagota Zarah tayi kana tace.
"Kada ki bani kunya ta hanyar durƙusawa a gabana domin neman wata alfarma, hakan zai sa nayi tunanin ko baki ɗaukeni a matsayin ƴa ba. Ku tashi mu shiga daga ciki muyi magana a nutse."
Ta ƙaramar ƙofa suka shige bayan su Saleem sun shige da motar tuni.
Falon saukar baƙi ta kaisu kana taje kicin da kanta ta kawo musu ruwa da lemo.
"Bismillah ga ruwa ku sha sai muyi maganar abinda ke tafe daku."
Fadin Zarah bayan ta aje tiren dake dauke da gorar ruwa da lemu a kan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon.
"Ranki ya daɗe ba zamu iya shan komai ba ahalin da muke ciki." Faɗin mijin
"Meke faruwa ne.?" Zarah ta faɗa tana mai zama a kujerar dake fuskantarsu.
"Ranki ya daɗe ƴar mu akayi wa fyaɗe, sannan mun tabbatar da wanda ya aikata laifin. Yaron wani ɗan majalisa ne dake maƙobtaka damu amma bayan mun sami mahaifin yaron da batun ya ƙaryata lamarin tare da faɗin zaiyi shari'a damu duk sanda muka nemi ɓata masa suna ko ɗan shi. Yanzu haka yarinyar na gadon asibiti ana neman kuɗin aiki sannan bamu da halin biya." Ya faɗa yana mai fashewa da kuka inda matar ke taya shi.
Sosai zuciyarta ta tsinke da lamarin musamman da taga manyan mutanen da suka haifeta a shekaru suna zubar da hawaye.
"Amma meyasa baku kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa ba.?" Zarah ta tambaya a raunane.
"Tun faruwa lamarin muka kai ƙara ofishin ƴan sanda dake kusa damu, saidai bayan sun gana da mahaifin yaron suka fatattake mu tare da faɗin sharri mukeson ƙullawa ɗan sa. Wannan dalilin yasa muka garzaya ofishinki bayan wani maƙocin ya bamu shawarar yin hakan, tun kwanaki uku da suka wuce muke zirya a ofishin an hana mu shiga shine mai gadin wajen ya bamu adireshin ki." Matar ke wannan bayanin.
Kai kawai ta jinjina tare faɗin.
"Ina zuwa." kana ta miƙe ta fita.
Bata daɗe ba ta shigo tare da Saleem da Jidda, zama sukayi tare da gaisa.
"Wannan shine Bar. Saleem tare da matarsa Dr. Jidda, za muje asibitin tare domin ganin halin da yarinyar take ciki kafin shigar da ƙara a kotu." faɗin Zarah bayan tayi nuni da kujerar da Saleem ke zaune shida Jidda.
Godiya su kayi sosai kana suka miƙe gaba ɗaya suka nufi waje.
Motar Zarah suka shiga duka inda Saleem ke tuƙin.
Mintuna kaɗan suka iso asibitin, kasancewar Zarah ƴar sanda shiyasa basu wani sha wuya ba wajen isa ɗakin da yarinyar take.
Ita kaɗai ke kwance a gadon jikinta rufe da zani yayinda acan kusurwar dakin wata ke zaune kan dadduma da alama dai itace mai jinyar.
Bayan sun mata ya jiki ne suka zazzauna inda Saleem ya ciro ƙaramar sound recorder tare da jan kujera ya ƙarasa bakin gadon yace.
"Baiwar Allah da farko dai ina ƙara jajanta miki akan wannan lamari da ya afku dake sannan inason sanin ko ke wacece.?"
"Da farko dai ni suna na Fahima ina zaune ne tare da iyayena a anguwar bakin kura dake nan jihar Bauchi. Sannan mahaifina mai ƙaramin ƙarfi ne." magana take a hankali alamum dai tana jin jiki.
"Meya jawo afkuwar wannan lamarin a gareki."
"Ina aikine a gidan wani ɗn majalisa dake nan anguwar mu wato Alhaji Nura Mai Riga. Tun lokacin da nafara aiki a gidan ɗan sa Kabeer ke yawan shigemin tare da nuna alamun yanaso muyi sabo sosai saidai ban bada damar hakan ba. To a ranar larabar data gabata ne bayan na kai masa abincinsa na rana kamar yadda na saba kowani lokaci bayan na gama girki ina kai masa nashi bangarensa. Bayan na ajiye abincin ne ya miƙomin kofin dake hannunshi wanda ke ɗauke da lemu ya umarceni da na shanye, naso nayi jayayya saidai yace idan ban sha ba bazai barni na tafi ba shiyasa na karɓa na shanye tare da miƙewa da nufin tafiya sai ya kuma cewa na share mai falon shi yayi ƙura. Tunda nafara sharar nakejin bacci na fizgata kafin nagama kuma bansan inda kaina yake ba sai farkawa nayj na ganni akan gadonshi ya ketamin haddi..." Ta ƙarasa faɗa tana mai fashewa da wani marayan kuka wanda ke nuni da ciwon abin da takeji.
Kashe recorder ɗin Saleem yayi kana ya miƙe ya fita yana musu alama da ido.
Zarah da Jidda ma miƙewa sukayi kana Zarah tace.
"Insha Allahu za'a bi miki haƙƙinki sannan kafin mu tafi za'a sa hannu a shigar dake aikin da za'a miki na matsalar yoyon fitsari da kika samu."
Godiya suka ƙara yi musu sosai.
Sanna su Jiddan suka bar ɗakin.
Saida suka biya kuɗin aikin da za'ayi wa Fahima sannan suka bar cikin asibitin.
A hanyarsh da zuwa gida ne Jidda dake gaban motar ta waiwayo ta kalli Zarah data jingina kanta a jikin kujerar bayan motar tace.
"Zarah kina ganin ba muyi ganganci ba wajen shiga cikin wannan case ɗin daya shafi Alhaji Nura Mai Riga.?"
"Banason halinki na saurin karaya Jidda, kada ki manta Allah yana tare da msi mai gaskiya." Ta faɗa tana mai ɗagowa daga jinginawar da tayi jikin kujerar.
"Waye ne Alhaji Nura Mai Riga.?" Saleem ya tambaya hankalinshi na kan hanya.
*ASP ZARAH*👩✈️
_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸
*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.
*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩✈️
👩✈️
👩✈️
👩✈️
👩✈️
... Jidda ce ta gyara zama tare da fara magana.
"Wani sanannen ɗan siyasa a ciki da wajen Bauchi, anyi mishi shaidar rashin arziki da wulaƙanci gami da cin zarafin na ƙasa dashi, baya ragama kowa kasancewar yana da muƙami ga dukiya kuma daya tara, shiyasa yake taka kowa ya zauna lafiya daga shi har ɗan nashi. Ana faɗin cewa zai iyayin komai akan yaronshi ko da kuwa kisa ne. Shiyasa nake tsoron kar wani abu ya haɗa su da Zarah saboda baza'a haifar da ɗa mai ido ba."
Kai Saleem ya girgiza kana yace.
"Gaki a haka kamar Jaruma amma zuciyarki fal take da tsoro, ni a gani na wannan ba wani abu bane da za'a tsorata har ayi shakkun yin shari'a dashi. Insha Allah zamu zauna anan har sai munga an kwatar ma yarinyar nan hakkinta. Kuma ni zan zame mata lauya."
"A zahiri bakai bane zaka zame mata lauyan amma a baɗini kai ne." Zarah ta faɗa idonta a lumshe