Showing 21001 words to 24000 words out of 34298 words

Chapter 8 - Asp Zarah 1 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

201



"Gaskiya Baaba zanyi missing ɗin dramar ku da Sahibaty."

"Mene ne kuma meizu.?" Baaba ta faɗa cikin gyatsina.

Wannan karon har Zarah da Saleem saida suka dara sosai.

"Rabo da su Baaba kwanan nan zan kaiki London a koya miki turanci kema." cewar Saleem.

"A'a ɗan nan meye haɗina da turanci kuma, ku dai da suka asirce ku sai kuyi ta fama."

"Kunga idan kuka biyewa Baaba to tabbas yau zaku rasa flight, ku hanzarta na sauke ku a airport ɗin nima aiyuka gareni sosai a office." cewar Zarah tana miƙewa.
Suma miƙewa sukayi inda Jidda ta shiga ta fito musu da trolleys ɗinsu.

"Mu zamu wuce Baaba sai munzo biki." Inji Saleem.
"Ɗan albarka mungode Allah yabar zumunci, ai bikin ma a can Gombe za'ayi muma duk zamu tattara mu biyo bayanku acan za'ayi komai."

"Toh Allah ya kawo ku lafiya."

"Ameen yaron kirki, a ƙara hakuri dai da juna."

"Idan ma da ni kikeyi ba kulaki zanyi ba kinga tafiyata." cewar Jidda.

Har gurin mota ta rakasu tana musu addu'ar sauka lafiya har saida taga sun fice a gidan kana ta juya ta koma falo.

Basu daɗe da isa airport ɗin ba jirginsu ya tashi bayan sunyi sallama cike da kewar juna da zasuyi, zuciyarta gabaɗaya babu daɗi ta nufi office ɗinta. Bata ko yi minti biyu da zama a kujerarta ba Bala ya shigo bayan ya nemi izini, ganin yanayin da take ciki yasa ya ajiye takardun daya shigo dasu ya fice, takardun da ya ajiye ta jawo tare da fara nazartarsu, bayanai ne kan wani da suke zargin yana safarar miyagun kwayoyi wanda zai shigo garin Bauchi nan da kwana biyu, inda ta wannan hanyar suke fatan tabbar da zarginsu tare da kamashi muddin zarginsu ya tabbata.
Tsaki taja mai sauti bayan tayj tunanin hanyar da ita kaɗai ce mafita a garesu batare da sunsha wahala ba, da kanta take so tayi wannan aikin gudun kada a samu matsala musamman yadda yawancin jami'ai yanzu zuciyarsu ta gurɓace da son kuɗi, saidai kuma batason aikin dazai dinga kaita hotel ko kaɗan amma babu yadda ta iya dole wannan karon tayi wannan aikin da kanta.
Gabaɗaya wuninta na yau a office tayi shi ne cikin tsara yadda aikin zai kasance cikin sauƙi batare da sunsha wahala ba, sai ƙarfe shida tabar office ɗin bayan ta zaɓi team ɗin da zasuyi aikin tare.
Bata tsaya doguwar hira da Baaba ba yau saboda a gajiye take, hakan yasa bayan sunci abincin dare ta wuce ɗakinta ta kwanta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

"Momi zamu wuce." cewar Abdallah da suka fito a sashin M.J cikin shirinsu na tafiya garin Bauchi ganin amarya Zarah, sunyi kyau cikin dakakkiyar farar shadda da suka saka iri ɗaya sai zuba ƙamshi sukeyi musamman M.J da ya fito a asalin ango mai shirin amarcewa da sabuwar amarya.

"Yauwa ƴaƴan kirki ga wannan ku kaiwa ƴar tawa, ku gaishemin da Mamana kuma." cewar Momi dake zaune tana miƙawa Abdallah wata ƙaramar jaka.

"Me amaryar mu ta samu ne haka Momi." ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe jakar.
Hannunshi ta buge kana tace.
"Ban yarda a buɗe ba, ku bata shi yadda na baku."

"Toh Momi mun wuce."

"Allah ya kiyaye hanya ku gaishesu."

M.J ke jan motar yayinda Abdallah ke gefenshi yana zuba surutu, tun yana kulashi har ya gaji ya daina wanda hakan yasa shima Abdallah ya maida hankalinashi kan wayarsa saboda sanin halin miskilanci irin na M. J.
❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄
Cikin shirinta na ƴan sanda ta sauko ƙasa hannunta riƙe da agogo tana ƙoƙarin ɗaurawa, yayinda take ɗauke da wata jakar baya madaidaiciya mai matuƙar kyau da sheƙi.

"Zan wuce office Baaba." ta faɗa bayan ta zauna a hannun kujera tana ƙarasa ɗaura agogon.

"Yanzu Zara'u mijin da zaki aura zaizo ganinki amma bazaki haƙura da zuwa aikin nan ba yau."

"Aiki mai mahimmanci zan gabatar Baaba sannan bazai wani ɗaukeni dogon lokaci ba idan ya iso ki kirani sai na dawo, sannan Raliya ta shirya musu abinda ya dace."

"Shikenan Allah ya bada sa'a ya kuma kare."

"Ameen Baabata nagode sosai." ta faɗa tana ficewa a falon.

Kai tsaye office ta nufa, bata wani ɓata lokaci sosai ba suka wuce hotel ɗin da zasuyi aikin acan bayan ta canja kaya zuwa doguwar rigar abaya sannan tayi rolling da gyalen rigar.
Mintuna kaɗan suka isa, can nesa da gate ɗin sukayi parking, mintuna kaɗan sai ga wata tsadaddiyar mota ta shiga hotel ɗin.

"Jeka Bala ka tabbatar kayi kyadda ya dace." Zarah ta faɗa.

"Toh ranki ya daɗe." Ya faɗa yana mai fita a motar, tabbas idan bakasan shi ba baza kayi tunanin jami'in tsaro bane saboda kalar shigar da yayi ta ƴan iska, kai tsaye farfajiyar hotel ɗin ya shiga tare da nufar inda motar tayi parking.
Glass ɗin motar ya ƙwanƙwansa, sauke gilashin baya akayi inda wani hamshaƙin mutum ke zaune.
"Lafiya kuwa ɗan saurayi." cewar Alhajin.

Waige-waige Bala tayi kamar mara gaskiya kafin ya fara magana irinta ƴan shaye-shaye yace
"Alhaji naga kamar kazo hutawa ne shiyasa nace bari nayi maka tayin zafafa ko zasu tayaka hutawa."

"Shigo daga ciki." ya faɗa bayan ya buɗewa Bala ƙofar.

"Banason idanun mutane shiyasa nace ka shigo daga ciki, yimin bayani sosai."

"Ya Alhaj akwaisu dayawa fa amma yanzu ɗayace ta rage, sunanta end of discussion saboda zazzafa ce sosai." cewar Bala tamkar me maye.

"Kada kasani asarar kuɗi fa ka kawomin ƙazama kamar ka." ya faɗa yana gyatsina saboda kayan jikin Bala sun matuƙar yagalgale.

"Ina fada maka ya Alhaj, zafafa nake dasu bari na nuna maka hotonta." ya ciro wayarsa a aljihun wandon jikinshi, hoton da Zarah ta ɗauka ɗazu ya nuna mishi wanda take sanye da doguwar riga.
Laɓɓansa ya lasa bayan yaga hoton kasancewar sa manemin mata yasa babu ɓata lokaci ya fito da rafar kuɗi na dubu-dubu ya ajiye guda biyu a cinyar Bala tare da faɗin.
"Kirata yanzu tazo."
Sowa Bala yayi tare da danna kiran wayar Zarah yana faɗin.

"End of discussion harka ta tashi maza kizo yau kakarmu ta yanke saka."

Katse wayar yayi yace.
"Yanzu zaka ganta yanzu ya Alhaj."
Buɗe kofar motar akayi inda direban Alhajin ya shigo tare da faɗin.

"Na gama komai yallaɓai ga key ɗin ɗakin nan room 234 a sama."

"Ohk" kawai yace tare da karɓan key ɗin.

A daidai wannan lokacin kuma M. J da Abdallah suka shigo garin Bauchi sannan kai tsaye suka nufi hotel ɗin domin kama masauki, Abdallah ne ya fita a motar domin zuwa kama musu ɗaki, bai ɗauki lokaci ba ya dawo imda aka basu room 233 buɗe ƙofar yayi tare da faɗin.
"Mr. President sai ka fito mu shiga."
Fitowa yayi suka nufi cikin hotel ɗin, a wannan lokacin ma Zarah da Alhaji Mati sun fito a motarsa suma da nufin zuwa ɗakin da aka kama mishi.
Abdallah da M. J ne a gaba yayinda suku ma suke baya a lokacin da suke haura matattakalar dazata sada su da inda jerin ɗakunan suke.
Tamkar ance ya waiga..........

_Insha Allah daga next page bazan ƙara free page ba, nagode sosai da ƙaunar da kuka nunawa littafina. ASP ZARAH VIP GROUP, ASP ZARAH FANS 1 DA ASP ZARAH FANS TWO INAYINKU SOSAI DA SOSAI NAGODE MATUƘA._

_BY_
_JASMINE._🌸🌸
*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP, tuntuɓi 07048961623._

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*

__Kallo ɗaya yayimata ya gane ta saboda yawan ganinta da yake yi a cikin mafarkinshi tun bayan haɗuwarsu da ita a Abuja, take yaji wutar tsanarta ta ƙara ruruwa a zuciyarshi, tsaki yaja mara sauti bayan ganin irin kallon da Alhaji Mati yake yiwa Zarah na tsantsar maitar buƙata, tamkar zuciyarsa zata fito waje haka yake ji lokacin dayaga sun shige ɗakin bayan an buɗe mata ƙofar. Kwafa yayi shima yabi bayan Abdallah suka shige nasu ɗakin.

"Duk sanda nayi magana sai ka dinga ƙaryatani bayan sai na tabbar nake faɗa, gashi yau dai ka tabbatarwa idanunka." cewar M.J

Kallonshi Abdallah yayi cikin rashin fahimta yace.
"Kai da waye kake magana haka."
"Ina tare da wani bayan kai ne anan.?" cike da jin haushin tambayar ya amsamai.
"Sorry ranka ya daɗe bangane akan me kake magana ba."
"Kwanakin baya ba tare da kai mukayi maganar wata ƴar sanda a Abuja."
"Oh wannan yarinyar da har yau nake fatan sake ganinta , gaskiya duk da bansanta sosai ba ta burgeni matuƙa."
"Mtswww" M.J yaja tsaki tare da kuma faɗin
"Sai kayi kuma ai, itace wacce muka hauro tare suka shiga next room ɗin nan."
Miƙewa Abdallah yayi daga kwancen da yake tare da cewa.
"M. J banason wasa fa wai da gaske kake police ɗin nan ce muka hauro tare dasu."
"Dama ina wasa da irin wannan maganar ne."
"Allah ya kyauta" shine kawai abinda Abdallah ya faɗa tare da miƙewa ya shige toilet, bai jima ba ya fito bayan yayi wanka. Shima M.J toilet ɗin ya shiga yayi wanka ya fito, basu wani jima ba suka fita domin isa inda zasuje.

A ɓangaren Zarah kuwa bayan shigarsu ɗakin, hannunta Alhaji Mati ya riƙo da nufin janyota jikinsa ya rungumeta saidai kafin yayi hakan cikin dabara ta zame hannayenta tare da zama a gefen gadon tana faɗin.
"Alhaji bazaka watsa ruwa ba tukun, kayi dogowar tafiya kayi wanka zaka fi jindaɗin aiwatar da komai cikin nutsuwa."

"Tabbas wannan shawarace mai kyau, bari nayi wankan na fito, ko zaki taimakamin ne." ya ƙarasa faɗa yana mai kashe mata ido.

"A'a shiga kafito dai, yanzu nayi wankan kafin na fito."

Bai ce komai ba ya cire babbar rigarsa tare da shigewa banɗakin, ganin shigarsa yasa tayi saurin nufar inda akwatin kayansa yake, bata wani sha wuyar buɗewa ba saboda ta rigada tasan komai, kamar yadda suke zargi, kaya ne sosai a saman jakar saidai acan ƙasa rafar kuɗi ne sosai sai hodar ibilis.
"Zaku iya shigowa Bala zarginmu ya tabbata ku shigo cikin shiri." ta faɗa a hankali.
A buɗe ƙofar take dan haka jami'an suka shigo tare da yiwa ɗakin ƙawanya cikin shirin ko ta kwana.
Zigir! haihuwar mahaifiya , haka ya fito daga banɗakin yana faɗin.
"Gaskiya baby ina...." maganarshi ce ta katse take tashin hankali yayiwa fuskarshi tambari, juyawa yayi da nufin komawa cikin banɗakin saidai hakan bai yiwu ba sakamakon damƙarshi da wani jami'i yayi, zagaye shi sukayi sa'an nan wani a cikinsu ya taimakamai da kayansa, shidai ya kasa cewa komai illa rawar ɗari da yakeyi, ankwa aka ɗaura mishi hannu tare da tisa ƙeyarsa aka wuce dashi batare da an bashi damar magana ba duk da irin kallon da yakewa Zarah na zargi tare dason yi mata maganan.
Bincike suka cigaba da gudanarwa tarw da sauran jami'ai biyu dake tare da ita, sun jima kafin suka tattara zuwa ofishin nasu.

Sai da Abdallah ya tirsasa M.J kafin ya yadda suka tsaya a wani mall suka yiwa Zarah siyayyar abubuwan da sukasan mace zata buƙata musamman mai shirin yin aure.
Cike da murna Baaba ta tarbesu bayan isarsu gidan, nan suka gaisa tare da hirar yaushe gamu wanda yawanci tsokanace kawai take yimusu, sun daɗe suna hira kafin daga bisani Abdallah yayi ƙarfin halin tambayar Zarah ganin har zuwa wannan lokacin batazo ba sai Raliya dake ta hidima dasu.

"Zara'u dai sai shiriyar ubangiji, saida nace karta fita aikin nan yau saboda zuwanku amma tayi biris dani wai akan idan kunzo akirata aiki zatayi mai mahimmanci a can ofishin nasu." cewar Baaba cikin kwafa.

"Allah sarki dama tana aiki ne.?" Abdallah ya kuma tambaya.

"Ehh tana aiki kuma itama shugaba ce a wajen, ko bataje ba bazata samu matsala ba amma dan naci saida ta tafi, bari na kirata ta dawo yanzu ungo dubamin numbarta anan zakaga ansaka Zara'u." takarasa faɗa tana miƙa mishi ƙaramar wayarta.
Shidai M. J yanajinsu amma bai tanka ba, saidai ranshi yayi mugun ɓaci da lamarin wannan yarinyar da akeson ya aura, wato an faɗa mata zaizo shine ta saka ƙafa ta fita.

Kiran wayar ake tayi amma bata ɗagawa, hakan yasa M.J ya umurci su kuma falon Abba su zauna, nan suka bar Baaba tana ta mitar Zarah taƙi ɗaga mata waya da gangan saboda bata da gaskiya.

🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶🥶

A hankali ta kulle ƙofar tare da murɗa key ɗin jiki kana ta isa kan gadonta ta zauna tare da fiddo da wata ƙaramar waya da ke ta kawo wuta alamun ana kiranta, karawa tayi a kunne tare da faɗin
"Barka da safiya ranka ya daɗe."

"Baki da hankali ne Raliya, shin ban tsara miki yadda nakeson ki gabatar da komai ba, wato saboda kinga bakya kusa dani kike tunanin zakiyi abinda kikaga dama ko? Toh wallahi duk wani motsinki kinsan a tafin hannuna yake, saboda bakisan mahimmancin abinda ya kaiki ba har zakiyi saken da za'a cire camera daga inda kika aji. Mtssww! Baki san darajar wannan abun da muke nema koh, wallahi ki kiyayeni Raliya kiyi abinda nagaya miki cikin tsari, yanzu tayaya zamu samu masaniyar inda abun yake bayan ancire cameras ɗin, kiyi gaggawar nemowa kanki mafita tun kafin raina ya kai ga ɓaci, Nonesense!." Batare da jiran abinda zatace ba ya kashe wayar.

Kuka mai ciwo ne ya kwace mata, kifa kanta tayi akan pillow tare da fara rera kukan cike da takaicin maganganun mutumin da take matuƙar so da ƙauna a gareta, a gefe guda kuma takaicin cire cameras ɗin ne ya dameta wanda ta tabbar wannan aikin Zarah, ta rasa gane alƙiblarta, tamkar mai aljanun da suke faɗa mata sirrin mutum haka take, a ɗan zaman da sukayi ne ta fahimci haka. Tabbas a da taso ta rangwanta mata kodan albarkacin Baaba, amma a yanzu batajin ko iyayenta dake kabari ne zasu dawo rayuwa suce ta haƙura da satar Diamond ɗin nan ba zataji maganarsu, dole ta sake shiri domin tasan ta wannan hanyar ne kaɗai zata iya cimma burinta na rayuwa da Alpha a matsayin masoyi.
Miƙewa tayi tare da share hawayen da ya ɓata mata fuska ta nufi ƙofar fita daga ɗakin saboda jin kiranta da Baaba keyi.

"Gani Baaba". Ta faɗa bayan ta iso falon.

"Yauwa Raliya kiramin direba na aikashi ya tahomin da Zara'u tunda naga batada da niyar dawowa."

"A'a Baaba kinsan yanayin aikinsu fa, ki barta zata dawo yanzu idan yaje ma ba lallai su barshi ya ganta ba."

"Shikenan amma tabbas zata gamu da fushina idan ta dawo, yanzu da ba ƴan gida bane ai kunyata mu zatayi kenan."

"Ayi haƙuri Baaba, kina buƙatar wani abu ne." Raliyan ta faɗa tana mai sunkuyar dakai ƙasa.

"A'a bakomai jeki kema ki huta kinyi aiki sosai."

"Nagode" ta faɗa tare da nufar ɗakinta.


✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️
*SINGAPORE*

Daddy ne zaune da wani kyakkyawan matashin saurayi a wanj keɓaɓɓen lambu mai cike da shukoki kaloli daban-daban, kallo ɗaya zaka yiwa saurayin kaga tsantsar kama da sukeyi da Zarah da kuma Rahama saidai ƙarin hasken fata da Zarah tafiso duka, hannun Daddyn na akan kafaɗar saurayin da idanuwanshi sukayi jazir saboda kukan daya sha, hankacif ya saka tare da ƙara goge mishi idanunshi yana faɗin.
"Kayi haƙuri Son muma har yanzu haka mukeji a zuƙatan mu bayyanawa ne kawai bama yi, amma kayi hakuri ka biyoni mu koma gida." cewar Daddy

"Daddy bazan iya zama a Nigeria ba alhalin babu waɗanda zan iya gani na samu farin ciki."

"Kada kace haka As-Siddiq zaman ka anan bashine zai iya dawo da waɗanda suka rasu ba, idan kace baka da kowa toh mufa ko baka ɗaukemu a matsayin iyaye bane dama, ƴan uwanka mata fa, bawai ina nufin bazan iya riƙesu bane tamkar ƴaƴan da na haifa amma suna buƙatarka a kusa dasu a matsayinka na wanda zasu dinga gani tamkar ɗan'uwana da ya rasu, kaine kaɗai zaka iya rarrashinsu musamman Zarah da ita bata kukan fili saina zuciya wanda yafi ƙuna, kayi haƙuri ka shirya mukoma gida tare dan Allah ina neman wannan alfarmar."

"Daddy kai ubane a wajena baka da buƙatar neman alfarma a wajena, umarni kawai zaka bani na aiwatar, insha Allahu zuwa ƙarshen shekara zan tattaro na dawo gida."

"Me zaka tsayayi anan har ƙarshen shekara? Bayan haka ma bikin ƴan uwanka za'ayi nan da wata ɗaya da sati biyu ka shirya kawai mu tafi tare."

Idanunshi da suka fara washewa ya waro wanda hakan yayi mishi kyau matuƙa, kafin yace.
"Wasu ƴan uwan nawa kuma Daddy."

"Ehh ƴan uwanka Zarah da Jawwad, insha Allah nan da wani lokaci za'a ɗaura aurensu."

"Amma ita Zarah ce ta amince da auren Bro Jawwad ɗin? Ko dama suna soyayya ne ban taɓa sani.? Amma yarinyar nan batada hankali duk ana maganar nan shine bata taɓa faɗamin ba ɗazu ma fa munyi waya da ita amma take cemin babu komai, yanzu ina ita ina miskilancin M.J mut..." lura da yayi da wanda suke maganar ne ya sashi yin shiru batare da ya gama maganar ba tare da sunkuyar da kanshi ƙasa cike da kunyar maganganun daya yiwa Daddyn.

"Kada kaji kunyata Son, ko nine a matsayinka tambayar da zanyi kenan yanzu tamkar uba kake a garesu kanada damar yin bincike a duk wani lamari daya shafesu."

"Kayi haƙuri Daddy, zan shirya mu wuce tare."

"Toh nagode Son, Allah yayi albarka".

"Ameen" yace kana ya tsiyayi ruwan dake ajiye akan teburin wajen yasha, nan suka zauna suna hira kafin daga bisani suka miƙe tare da barin wajen.

👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️👩‍✈️

Saida ta kammala duk wasu mahimman abubuwa da duka dace game da case ɗin kafin ta nufi gida cikin hanzari saboda jiran da ake mata .

Da sallama ta shiga falon, ganin Baaba a zaune ta sha kunu ne yasata faɗin
"Dan Allah ayimin afuwa Baabata aikine mai matuƙar mahimmanci ya tsayar dani."

"Zaki wuce kije ki samesu ko yaya."

"Haba ko wanka bazaki bari nayi ba, da kayan aikin zanje ne wai"

"Wallahi idan baki wuce ba zan saɓa miki, yo menene ai gwara suka ganki da kayan aikin su san ba ƙarya na musu ba, ki wuce kafin raina ya ɓaci"
Babu yadda ta iya haka ta nufi ƙofar falon Abban saboda batason tayi abin da zai ɓata ran Baaba tunda yanzu ita kaɗai ta rage musu.

Abbdallah na kishingiɗe a doguwar kujera yayinda M.J ke zaune yana danna waya, sallamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login