Showing 33001 words to 34298 words out of 34298 words
bansan me suka tattauna ba sai dai daga ƙarshe muryar Daddyn naji yana ta godiya tare da samata albarka.
"Daddy ka daina bani kunya ta hanyar gode min, idan kana hakan sai naga kamar baka ɗauke ni a matsayin ƴarka bane."
"Har abada zaki cigaba da kasancewa ƴata, amma kinsani cewa godiya wajibi ne ga wanda aka kyautatawa, Allah ya miki albarka ya baki zaman lafiya a ɗakin aurenki."
"Amin Daddy."
"Babu wani abu da kike buƙata ko."
"Babu komai."
"Tashi ki kuma cikin ƴan uwa da iyayenki."
Cikin rashin kuzari ta miƙe tare da ficewa a falon, wata hanya ƙarama tabi sai gata ta ɓullo a wani babban falo wanda aka wadata da kayan alatu na more rayuwa tamkar ɗakin shugaban ƙasa, Jidda kaɗai ta gani a falon tana duba wasu takardu, zama tayi a gefenta tace.
"Ya naga gidan yayi shiru haka."
"Ehh duk suna backyard wajen gyaran naman nan, saboda Momi tace kar a barwa ƴan aiki aikin zasu lalata shi."
"Ok nima daga falon Daddy nake."
Kallonta Jidda tayi na wasu sakanni kafin tace
"Ina fata komai ya zama steady."
"Ehh babu wata matsala yanzu."
"Wa kun haɗu da angon kuwa.?"
"Uhmm tun ranar daya bar Bauchi ba mu ƙara haɗuwa ba, Abdallah ne ke jigilar zuwa da kuma kira."
"Sai kinyi haƙuri da lamarin angon nan naki idan ba haka ba zai ɓata mana shirin mu."
"Dole zan kula domin nima jikina yana bani cewa na kusa kama Alpha da hannuna."
"Nima inajin hakan, ya batun Raliya kuwa."
"Na saka an ɓoyeta a wani keɓaɓɓan guri sai ranar da burina ya cika zan fito da ita."
"Hakan yayi kyau, ya kukayi da oganki ne da kikaje neman transfer."
"Ohh Mr. C.P ai saida na tabbatar baya ƙasar kafin naje na processing komai, saidai kawai ya dawo yaji labarin nayi aure a wani gari na barsu da garinsu."
Dariya Jidda tayi kafin tace
"Kin manta waye CP kenan zai iya miki makircin nasa."
Dariya dukayi duka tare da miƙewa suka fice a falon.
💫💫💫💫💫💫💫
A yau ne dai aka ɗaura auren Muhammad Jawwad Sulaiman da Fatimah Zarah AbdulJalal sai fatan samun zaman lafiya a tsakanin ma'auratan biyu duk da ba haka aka tsara ba.
Duk da ba'a shirya shagula ba amma mutane sunzo sosai harda waɗanda ma ba'a gayyata ba duk sun nuna bajin ta, da yamma kuma akayi walimar mata a cikin gidan inda malamai sukayi wa'azi sosai wanda duk akan zamantakewar aure ne.
An raba kyaututtuka sosai baƙi duk sun tafi suna farin ciki tare da fatan alkhairi.
Nasiha sosai Momi da Ammi suka yi wa Zarah wanda ko da mahaifiyar ta ce iyakar abinda zata iya faɗa mata kenan, ita kam in banda kuka babu abinda takeyi saboda tuno mahaifanta da tayi, shikuwa Daddy da aka kai mishi Zarah domin yi mata faɗa kasawa yayi illa kawai yace.
"Fatimah yadda kikemin biyayya a matsayina na mahaifinki ina roƙon Allah ya baki masu yi miki fiye da yadda zakimin, nasan ko ba'a faɗa miki ba zakiyi wa mijinki biyayya, Allah ya kareki daga sharrin maƙiya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya dauwamar da farin ciki a zuciya kamar yadda kike ƙoƙarin ganin hakan a kaina, Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki nasara akan duk abinda kika sa a gaba."
Mutanen dake falon ne suka amsa da Amin, daga haka kuma yabar falon ya shige ɗakinsa domin kwallace ke neman sauko mishi.
Ita kam Baaba da aka kai mata Zarah miƙewa kawai tayi ta bar gurin tana kuka kamar ranta zai fita wanda mutane da dama suka fara zargin akwai dalilin da yasa ake ta wannan koke-koken, duk da cewa ansan wannan kukan ya zama kamar na al'ada amma wanda sukeyi ya wuce ƙa'ida. A haka a sakata a mota aka wuce da ita gidanta dake Federal lowcost Gombe, duk wannan budurin da akeyi Jidda bata ciki domin tun yamma Saleem yazo ya ɗauketa a gidan bikin saboda irin kukan da takeyi.
Duk yadda Abdallah yaso amma M.J ya tubure akan babu wani wanda zaiyi mishi rakiyar ango, dole suka rabo dashi ya wuce gidansa shi kaɗai.
Da haka dai biki ya watse sai fatan zaman lafiya ga amarya da ango.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Wayarsa dake ta faman ruri ne ya saka dole ya sake baturiyar suke manne da juna akan gado ya miƙa hannu ya ɗauko wayar, ganin mai kiran ne yasa shi firgita tare da sauka a gadon yana kara wayar a kunne.
"Barka dai yallaɓai."
"Don't dare to yallaɓai me, wato kaje ƙasar waje kana hutawa kabar komai yana lalacewa anan ko, wannan shine amanar da zaka yi min eye? Saboda na wadata ka da kuɗi shiyasa kake duk abinda kaga dama ko.?"
Cikin ina ina yace
"Ba haka bane yallaɓai ayi min afuwa."
Tsawa ya daka mai cikin fusata ya kuma yin magana yace.
"Afuwar me za'a maka, wato kai kaje ƙasar waje kana sha'aninka koh, ace ina tare da commisioner of police gabaɗaya amma a kama Raliya kusan fiye da sati uku amma ankasa yin komai akai."
"Innalillahi! Yallaɓai Alpha kace an kama Raliya."
"Bani da buƙatar maimatawa tunda kaji me nace."
"Amma garin yaya waya kamata."
"Wa kake tunani.?"
Ido C.P ya waro waje kamar wanda yaga wani mummunan abu mai firgitawa yace.
"Zarahh.???"
"Ka amsa tambayarka."
"Ohh shit! Dole zan dawo ƙasar gobe a fito da Raliya."
"A fito da Raliya fa kace! kasan ko a wani ofishin ƴan sanda Raliya takr zan iya zuwa na fiddata, amma ba anan take ba bansan a ina yarinyar nan ta ɓoyeta ba. Kayi gaggawar kiranta ka bata umarnin fito da ita a ko ina ta aje ta."
"Bari na kira ofishin su yanzu, Raliya bazata kuma kwana a hannunta ba"
Umma"Ina jiran sakamako mai kyau."
"Toh yallaɓai yanzu zan kira."
Cikin rawar jiki ya danna lambar mataimakin shi, ringing biyu ya ɗauka yana gaidashi, bai tsaya amsawa ba ya fara magana.
"Ka kira office ɗin ASP Zarah ka bata umarnin sake yarinyar da ta kulle a cell, ka gayamata wannan umarni na ne."
"Yallaɓai ai babu wata yarinya a ofishin nan wacce aka kulle."
"Ba tambayarka nakeyi ba umarni ne nake baka."
"Amma yallaɓai naga Zarah yanzu ba anan take aiki ba, kila bata zda masaniyar abinda ke faruwa ko dai ba ita ɗin bace.?"
"Bata aiki kuma ??? ASP Fatimah Zarah Abduljalal nake nufi fa."
"Ehh yallaɓai ai ta nemi takardar transfer zuwa Bauchi saboda za'ayi aurenta, jiya ma muka dawo daga ɗaurin auren."
"Damn it!! Wane ne ya aiwatar da hakan ba tare da sani na ba."
"Yallaɓai ta je Abuja ne daga can ta gama komai, wasu signing ne kawai da akeson kayi ni nayisu a madadinka."
"Meyasa ba'a tuntuɓeni ba eyee??"
"Ranka ya daɗe kamar naga babu buƙatar hakan."
Tsaki ya ja gami da ya kashe wayar batare daya kuma magana ba, kanshi ya dafe cikin taraddadin yadda zai kira Alpha ya gaya mai wannan labarin, gabanshi ne ya faɗi ganin kiranshi na kuma shigowa, cikin fargabar mai zai faru ya ɗaga kiran.
"Ya ake ciki??" ya tambaya babu walwala.
"Ehmm dama.."
"Straight to the point, banason dogon zance."
"Yallaɓai wai anyi mata transfer zuwa garin Bauchi saboda zatayi aure acan, jiya ne aka ɗaura auren nata a garin Bauchi."
Shiru yayi baiyi magana ba har hakan ya baiwa CP tsoro, sai can yace.
"Duk abinda kakeyi kabari a yau ɗin nan ka dawo ƙasar nan, sannan karka kuskura ka kirani matuƙar ba shaidamin zakayi ka kuma Bauchi da aiki ba." daga haka ya yanke kiran.
Babu yadda commisioner yayi iya dole ya fara haɗa tarkacensa bayan ya sallami baturiyar da suke tare, cikin lokaci ƙanƙanin lokaci ya gama shirin komawa ƙasarsa Nigeria....✍️✍️✍️
*Tammat bi Hamdulillahi!! Littafi na ɗaya ya ƙare anan, zamu shiga littafi na biyu da izinin Allah kafin sallah. Nima zan ɗanje hutu na kwana biyu kafin mu ɗora.*
*Ina yinku sosai Zarah's fans, Mrs. Khaleel from VIP ina yinki sosai ina godiya da ƙaunarki a gareni Allah ya bar xumunci a tsakanin mu. Sai kunjini a kashi na 2*🥰
*By*
*Jasmine*🌸🌸