Showing 18001 words to 21000 words out of 34298 words

Chapter 7 - Asp Zarah 1 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

200

ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Ku tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*M*. *W*. *A*.


Gudu takeyi tamkar zata tashi sama, yayinda Jidda ke mata ƙorafin karfa tayi sanadin tafiyarta lahira bata shirya. Ko kulata batayi ba har suka iso bakin gate ɗin gidan, horn tayi aka buɗe mata ta shigar da motar ciki, sai a lokacin ta samu nutsuwa amma duk da haka tanajin wani irin yanayi a tattare da ita.

''Haka kawai kin rabo ni da mijina, toh wallahi garin ma zamu bar miki tunda mun gama yin abinda ya tsaida mu." Inji Jidda.

"Ba iya garin nake so ku bari ba, dan Allah ku bar ƙasar ma baki ɗaya." Zarah ta faɗa cike da tsokana lokacin da take fita a cikin motar.

Da gudu Jidda ta bita suka nufi hanyar babban falo tamkar wasu ƙananan yara.

"Allah ya shirye ku, wannan ai sai kusa nima na ruga da gudu, manya daku kuna wasan guje-guje, ke Hauwa idan ita bata rigada ta gama girma ba ai ke kam kin girma saiki daina biye mata." Faɗin Baaba wacce ke zaune a falo lokacin da suka shigo da gudu.

"Kai Baaba kin manta wai nafi Jidda shekaru ne.?" Inji Zarah.

"Yo idan kin fita shekaru ai yanzu kam ta fiki tunda a ɗakin mijinta take."

"Saboda kawai tayi auren.?"

"Ehh mana ai ko ƴar shekara 14 tayi aure yanzu dole za'a kirata da yayarki."

"Faɗa mata dai Baaba ko zata daina raina ni." Jidda kenan ta faɗi.

"Nima dai auren nan na kusa yinshi na huta." Ta faɗa tana zama a kujerar da Baaba take kai.

"Ahh lallai da bamu yi shawarar aurar dake ba gaba bamu san abinda zaki dinga furtawa a gaban mu ba." Faɗin Baaba tana tafa hannayenta.

Bata kulata ba saima plate ɗin dake gaban Baaban data janyo wanda ke ɗauke da lafiyayyen dambun shinkafa da yaji haɗi.

"Baaba yau kin tuna da gargajiya ne haka, shiyasa kika kasa jira mu dawo muyi girkin." Zarah ta faɗa tana ɗebo dambun a cokali da nufin kaiwa baki.

"Allah sarki bama nina dafa ba, baƙuwa mukayi shine nace ta shiga kicin ta girka mana gudun kada ku dawo a gajiye, kin ganshi nan yanzu aka gama shine na ɗebo naci."

Harta buɗe baki da nufin cin dambun da ta ɗebo, amma jin abinda Baaba ta faɗa yasata dawo da cokalin tare da maidawa kan plate ɗin.

"Wacce baƙuwa kuma.?" Ta tambaya fuska a yamutse.

"Ƴar aiki na samu mana, tunda Iya Delu dai bamusan ranar dawowarta ba."

"Ƴar aiki kuma.?"

"Ehh ko banyi daidai bane uwata.?"

"A'a kawai nayi mamakin inda kika samo ƴar aikin ne bayan ba fita kikeyi ba."

"Nan tazo neman aikin, toh ganin muna buƙata yasa na ɗauketa, kuma naga tana da hankali da nutsuwa shiyasa bayan haka kuma marainiya ce."

"Ana ɗaukan aiki batare da bincike bane Baaba.?"

Harara Baaba ta wurga mata kana tace.

"Nasan ki ai da shigen bin ƙwaƙƙwafi shiyasa ma na nemi wacce ta kawo ta birnin muka zanta, bayan haka kuma ga lambar ta nan na karɓa idan kinason jin ƙarin bayani, mtsww."

"Me yayi zafi Baaba tunda ke zata dinga taimakawa, nikam ai bani da matsala tunda ba gidan nake wuni ba."

"Yo ai nayi tunanin koh kulle ni zakayi tunda nayi abu batare da izinin ki ba."

Ita dai Jidda bata saka baki ba, tana zaune a kujera ta kurɓar fresh milk ɗin da ta ɗauko, saboda surutunta ne ma yasa bata saka baki ba domin dai Baaba batasan a fara magana a bari ta daɗi ba, shiyasa ta barta da Zarah sanin da tayi cewa Zarah bata da magana sosai, tasan zancen bazai yi nisa ba za'a ƙarƙareshi.

"Kin ci dambun ne Baaba.?" Zarah ta tambaya fuska babu walwala.

"Na ɗebo kenan zanci ai kuka shigomin a birkice."

Batace komai ba ta ɗau plate ɗin dambun ta nufi hanyar kicin.

"Ina zaki kaimin abincin kuma.?''

"Yau ba dambu na tsara zamu ci a gidan nan ba, dan haka babu mai ci. Habibaty taso mu dafa wani abu mai sauƙi kafin SaJid ɗin naki da baya jurar yunwa ya dawo." ta faɗa tana mai shigewa corridor ɗin dazai sada ta da kitchen.
Jidda ma tashi tayi da sauri ta bita tun kafin Baaba tayi magana.

"Ki kiyayeni fa Zara'u wallahi zan saɓa miki, ki kawomim abincin nan tun kafin na iso gurin na sameki." Faɗin Baaba dake ƙoƙarin tashi ta nufi kitchen ɗin.

"Kulle ƙofar nan SaJid karta zo ta dame mu."

"Toh ke wai meye dalilinki na hanata cin dambun ne, nima wallahi ya bani sha'awa so nake naci."

"Kawai naji ban yarda da girkin bane, dan haka babu mai ci."

"Kamar ya baki yarda da girkin ba? tsabtar shi ko me.?"

"A'a bansan hanyoyin da aka bi aka sarrafa shi ba ne shiyasa, da ace ina gida ma babu wata ƴar aiki da zamu ɗauka saidai mu jira har zuwa lokacin da Iya delu zata dawo."

"Ƙyanƙyami ne kawai irin naki amma kina ganin dambun nan ai kinsan an tsabtace shi, nikam banga ƴar aiki da ake magana akanta ba ma."

"Ƙila tana ɗakin da Iya Delu ta zauna. Mu haɗa Jallof ɗin cous-cous kawai nima yunwar nakeji sosai."

Cikin ƙanƙanin lokaci suka haɗa lafiyayyen cous-cous da yaji kayan haɗi da nama, sai lemun citta da fruit salat da suka yi. A faranti suka jere komai, inda Jidda ta ɗauka domin zuwa ta jere a dinning, ita kuwa Zarah fruit salad ta ɗeba a plate ta nufi cikin falon.

Baaba na nan zaune inda ta barta, saɓanin ɗazu da take ita kaɗai yanzu tare suke da wata da bata ga fuskarta ba, remote ta ɗauka tare da canja tasha daga Sunnah TV zuwa TVC News kana ta zauna a kujerar dake fuskantar Raliya dake zaune a ƙasa rakuɓe a jikin kujera.

"Ya zaki canja mana tasha muna kallon wa'azi zuwa tashar arna." Faɗin Baaba a hassale.

"Kiyu haƙuri Baaba ta ki daina wannan fushin da ni kinji, labarai kawai zan kalla na tashi."

Sai a wannan lokacin Raliya da tayi nisa a cikin tunani ta lura da shigowar Zarah, kallonta tayi ta ƙasan ido, ai nan dake ta ɗauke kanta daga kanta saboda wani irin kwarjinin Zarah da ta hango.
Cikin dakiya da dauriya tace.

"Ina wuni ranki ya daɗe."

Kafeta da ido Zarah tayi tana son gano wani ɓoyayyen abu a tattare da ita.
Ita kuwa Raliya kai ta sunkuyar cikin ruɗu tare da tunanin ko Zarah ta gane ta ne.

"Banason haka fa Zara'u kin kafe baiwar Allah da ido tamkar mai laifi a bayan kanta."

"Marabar kaɗan ne." cewar Zarah a cikin ranta duk da batada wani tabbaci akan yanayin rashin gaskiya da zuciyarta ke gayamata akan Raliyan.

"Lafiya." ta faɗa a taƙaice tana mai cigaba da cin fruit salad ɗin.

Sunanan a zaune a falon har lokacin da Saleem ya dawo, Baaba ce take tambayar Saleem ɗin yadda shari'ar ta kasance, baki ya buɗe da nufin labarta mana amma saidai kallon da Zarah ta mishi ne yasa shi cewa.

"Baaba munyi nasara." yafaɗa a takaice domin ya gane ma'anar kallon Zarah a gareshi, nufinta karya faɗi yadda shari'ar ta kasance.

"Hubby kai muke jira tun ɗazu, mu ƙarasa dinning yunwa mukeji."

Su uku suka miƙe suka nufi dinning ɗin, Jidda ce tayi serving ɗinsu, nan suka fara cin abincin.

Kamar wacce aka tsikara haka ta miƙe da sauri ta nufi ɗakinta batare da ta amsa tambayar da Jidda ke mata ba......



*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP kuma N500. A tuntuɓeni a 07048961623 domin biya._

*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

*Free Page*

Haka nan taji tamkar ana umartarta ta zuwa ɗakin, da sallama a bakinta ta shiga duk da tasan babu kowa a cikin ɗakin, maida ƙofar tayi ta rufe kana ta jingina jikinta a jikin ƙofar tana mai ƙarewa yanayin ɗakin, yana nan kamar yadda ta barshi. Gaban durowar kayanta ta isa tare da tsayawa tana kallon gurin, tabbas wani ɓangare na umartarta da bincikar gurin saidai ɗaya ɓangare na hanata ƙoƙarin haka. Ƙarar wayar ta ne ya fargar da ita, kallon fuskar wayar tayi taga Ammi ce mai kiran, saida ta zauna a bakin gadon tukun kafin ta ɗaga wayar.

"Ammi na." ta faɗa a hankali..

"Na'am daughter ya kuke."

"Lafiya lau Ammi ya jikin Rahma."

"Alhamdulullahi jiki ya fara samuwa, yanzu tana iya yin magana wasu lokutan amma ba sosai ba."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Kin fara gyaran jiki kuwa Zarah." cewar Ammi

Cikin son gane mai take nufi Zarah tace.

"Wani irin gyara jiki kuma Ammi.?"

"Zan saɓa miki fa, kina nufin baki fara amfani da kayan da Momin ku ta turo miki ba." cewar Ammin.

Dafe kai Zarah tayi, sam ta manta batun kayan da Momi ta aiko mata dasu.
Jin shiru ne yasa Ammi cewa.

"Kina nufin haka zakije gidan mijin kamar almajira."

"Ni fa Ammi.."

"Ke fa me, toh wallahi ki fara amfani da kayan nan tun wuri, nima ina nan tafe zuwa wani watan domin mu fara shirye shirye da wuri."

"Toh Ammi, Allah ya kawo lafiya."

"Amin ki gaidamin da Baaba, su Jidda sun wuce Bauchi ne.?"

"A'a sai zuwa jibi tukun, akwai wani case da muka gudanar da Saleem ne shiyasa basu tafi ba."

"Ya batun binciken nan Zarah." Ammi ta tambaya cike da rauni.

"Ammi batun bincike ai babu shi tunda an riga da ansan mai laifin."

"Allah ya saka mana wannan zaluncin da ya aikata mana." cewar Ammi cikin rawar murya.

Sallama Zarah tayi mata gudun kada itama ta fara hawayen kamar yadda take da tabbacin kuka Ammi keson farawa.

Miƙewa tayi ta shiga toilet domin yin wanka, jim kaɗan ta fito ɗaure da ƙaramin towel. A gaban madubi ta tsaya, goge jikinta tayi kana ta murza lotion a jikinta sama-sama, hoda ta shafa a fuskarta kaɗan tare da goga lipbalm.
Cikin sauri ta saka doguwar rigar atamfa tare da yana ƙaramin mayafi akanta, wayarta ta ɗauka tare da nufar falon.
Baaba da Jidda ne ke zaune a kujera, yayinda Raliya take can gefe a rakuɓe.
Zama tayi a kusa da kujerar da Jidda take kana tace.

"Barka da yamma Baab."

Kauda kai tayi daga kallo ta kamar ba da ita take magana ba.

Murmushi mai sauti Zarah tayi sannan tace.

"Har yanzu baki gama fushin bane Baaba ta."

Jidda ce ta fashe da dariya ganin yadda Baaba take yatsina tamkar taga abin ƙazanta.

"Ina ganin mu bar yin alkubus din nan sai gobe ko.? Ta faɗa tana ƙoƙarin maida dariyar dake taso mata, tana sane tayi maganar saboda tasan Baaba na matuƙar son alkubus.

"Haba ƴaƴan albarka, kuyi mana shi da dare, na daɗe banci ba nima." cewar Baaba fuska a sake.

Dariya sukayi gabaɗaya kana Zarah tace.

"Sa.Jid ki kwaɓa mana a saka shi a rana kafin anjima."

"Mene ne ma'anar wannan sojut ɗin da kike kiranta dashi." Inji Baaba.

Dariya Zarah da Jidda keyi sosai har saida Jidda tabar kan kujerar ta dawo ƙasa, tsagaitawa da dariyar tayi tace.

"Ke dai Baaba kowani suna saikin ɓata shi, Sa.Jid fa aka ce ba Sojut ba."

"Mene ne ma'anar hakan.?"

"Yauwa kinga Sa. farkon sunan Saleem ne sai Jid kuma farkon Jidda, shine aka haɗa kalmomin biyu ake faɗin Sa.Jid."

Taɓe baki Baaba tayi tace.

"Boko dai baiyi muku rana ba."

Miƙewa sukayi su biyun suka nufi hanyar kitchen batare da sun kuma magana ba.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Kiran wayar dake shigowa wayarsa ne akai akai ne yayi sanadin tashin shi daga daddaɗan baccin daya ɗauke shi tun bayan da yayi sallar asubahi, hannu ya miƙa tare da jawo wayar dake akan bedsite drawer, tsaki yayi mai sauti bayan yaga sunan wanda yake kiran nashi tare da kara wayar a kunne.

"Dama nasan babu wanda zai dinga yimin irin wannan kiran idan ba kai ba, sarkin naci mai zan maka kake damuna."

Daga ɗaya ɓangaren Abdallah ne yayi dariya kana yace.

"Haba mana M. J kiran arziki na maka fa bana tsiya ba."

"Naji faɗi dalilin kiran."

"Yaushe zaka dawo Naija ne mu fara shirye shirye, kasan bamu da wani isasshen lokaci fa."

"Shirye shiryen me kenan."

"Banasan wulaƙanci fa M. J, kana nufin auren naka guda ba zamu gwangwaje ba.?"

"Dalilin kiran naka kenan.?"

"Ehh shi ne dalilin kiran najj yaushe zaka shigo."

"Toh sai anjima, bana da lokacin tattauna magana mara amfani yanzu."

"Zancen auren naka ne babu amfani."

"Sai anjima please." ya faɗa yana mai katse kiran.
Tsaki ya kuma yi a karo na ba adadi cike da takaicin wannan auren da za'a yi mishi, duk wasu tsari nashi an rusa mai, babu yadda ya iya dole yayiwa mahaifinsa biyayya amma tabbas yana da shiri sosai akan matar da aka ce za'a haɗa shi ta ita.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Ƙishin ruwa ne ya damu Zarah wacce ke kwance akan tamfatsetsen gadonta, agogo ta kalla ƙarfe 2:15nd, a hankali ta saukk daga kan gadon tare da zura silifas a ƙafarta ta nufi ƙofar fita daga ɗakin zuwa kitchen domin ɗauko ruwan da yau ta manta bata shigo dashi ba yau, saboda yawan shan ruwan da takeyi duk sanda zata farka da dare.
Gora biyu ta ɗauka bayan ta isa kitchen ɗin tare da apple ɗaya kana ta rufe ƙofar kitchen.

Kamar ance ta waiwaya, haske ta hango a babban falon da Abbansu ke saukar baƙi lokacin da yake raye, cike da mamaki ta nufi hanyar falon domin dai ta tabba ta kashe wutan falon kafin su kwanta bacci.

Abinda ta gani ne ya matuƙar bata mamaki tare da tabbatar mata da duk wani zarginta, Raliya ce....... ✍🏼


_Ku yimin uzuri please, ina shirin rubuta jarabawa ne shiyasa bana samun damar yin long pages. Ur prayers also needed._


By
Jasmine
*ASP ZARAH*

_PAID BOOK_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa biya N300 kacal ko kuma N500 na VIP. Tuntuɓi 07048961623 domin biya a saka ki a group._

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
*M*. *W*. *A*

*Free page*

____Raliya ta gani riƙe da wani abu da take da tabbacin camera ne tana ƙoƙarin mannawa a gefen inda wani babban family photo ɗin su yake, take ta samu duk wasu amsoshin da take buƙata akanta domin tun kallon farko da tayi mata ta hango alamun rashin gaskiya a tattare da ita. Rakuɓewa tayi a jikin window bayan ta hangota ta nufi ƙofar fita daga cikin falon, tana tsaye harta wuce ta shiga ɗakin da aka bata a matsayinta na ƴar aiki, shiga tayi cikin falon batare da ta kunna wutan da ta kashe ba ta nufi inda taga ta ajiye abun, kamar yadda tayi tsammani camera ce da zata iya ɗaukan duk wani shige da fice a falon sannan idan ba mutum ya sani ba babu wanda zaiyi tunanin akwai camera a gun. Ɗauka tayi tare da nufar ɗakin Raliyan, ta wani ɗan rami dake jikin ƙofar ta leƙa ga mamakinta sai ganinta tayi zaune akan katifar ɗakin da ƙaramar laptop a gaban wanda tana iya hangar abinda ke wakana a cikin laptop ɗin, ido ta waro gani hoton ɗakin ta ya bayyana a ciki tare da duk wani abu da ta gabatar tun daga dawowarta har zuwa yanzu.
Kunnenta ta kara a jikin ƙofar ganin Raliya ta ɗauki wayarta ta kara a kunne. Batasan me aka faɗa ba daga ɗaya bangaren sai amsar da ta bayar.
"A'a ranka ya daɗe, ina tunanin sun chanja tsarin gidan ne domin gabaɗaya an canja tiles ɗin da muka sani an saka wasu shiyasa bangane wanda zai kaini underground din ba."

"Alpha." Zarah ta furta a hankali. Tabbas yanzu zarginta ya tabbata Alpha ne wanda ya turo Raliya tayi basaja a matsayin ƴar aiki, bayan sun tabbatar da bata gida a lokacin domin tabbas da tana gida baza a ɗauki Raliya aiki ba. Rufe na'urar taga tayi tare da kwanciya akan katifar, wani murmushi ne ya suɓuce mata bayan ta gama haɗa wasu abubuwa a cikin kwaƙwalwarta, hanyar ɗakinta ta nufa cikin sassarfa.
Tsayawa tayi a tsakiyar dakin tana tunanin ta ina zata fara bincikar cameera din, wardrobe, haka taji tamkar anyi mata raɗa a kunne da sauri ta nufi wajen ta tsaya tare da karema wajen kallo sosai har lokacin da idonta ya hasko mata karamar camera acan saman wardrobe din, murmushi tayi tare da jawo stool ta hau sannan ta ciro camera ɗin. Jujjuyashi tayi a hannunta kafin ta ciro wani ƙaramin box ta saka a ciki, ruwan da ta ɗauko ta zauna tasha kana ta koma ta kwanta.

Washegari bayan tayi sallar asubahi da kanta ta shiga kicin ta haɗa musu abin karyawa saboda tafiyar safe su Jidda zasuyi zuwa Bauchi, ƙarfe bakwai na safiya ta gama shirya komai a dinning kana ta nufi ɗakinta domin yin wanka kasancewar itama zata fita aiki.
Cikin shirinta ta fito ta samesu a falo harda Baaba suna zaune, gaishe da Baaba tayi kana suka gaisa da Sa.Jid.

"Ina kwana Anti." Raliya ta faɗa lokacin da take goge TV stand, sai a lokacin Zarah ta lura da ita, cikin wani ƙayataccen murmushi ta amsa wanda ya saka Raliyan shiga kogin tunani na dalilin yin murmushin nata.

Dinning suka nufa duka harda Baaba da bata cika cin abincin acan ba, Jidda ce tayi serving ɗinsu duka sannan suka fara cin abincin.

"Yauwa Zara'u, munyi waya da mahaifinku ɗazu yake gayamin Muhammadu zai iso anjima sannan zuwa jibi zai ƙaraso nan ku zanta akan shirye shiryen da zaku gabatar." cewar Baaba.

"Uhmm." shine abinda kawai ta furta bayan ta saka tissue ta goge bakinta.

"Kinyiwa Ubanki badani kikeyi ba, mutum sai shegen miskilanci na tsiya." ta kuma faɗa.

Idonta ne ya kawo ruwa ta kalli Baaban da nufin yin magana sai ta rigata.

"Sulaimanu nake nufi." ta kuma faɗa tana harararta.

Dariya Jidda tayi kana tace.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login