Showing 15001 words to 18000 words out of 34298 words

Chapter 6 - Asp Zarah 1 Hausa Novel Complete

01 Jan 2025

205

ƴa mace.?"

"A'a babu yarona ɗaya ne dai wannan da muke magana akan shi."

"Ohk to kana da Yaya ko Ƙanwa mace."

"Gaskiya babu dake dukkan mu maza ne iyayen mu suka haifa. Amma lafiya kike min irin tambayar nan ranki ya daɗe."

"Ban kai ga ƙarasa tambayata ba idan na gama zan amsa taka tambayar. mahaifiyar yaron nan yakake jinta a ranka a matsayinta na waccw nake tunanin tun auren ƙuruciya shine har yanzu."

"Gaskiya bazan iya misalta miki yadda nake jinta a raina ba, wannan dalilin ne ma yasa har yanzu banyi mata kishiya ba."

"Masha Allah, yanzu Alhaji misali wani ya shiga gidanka yayi wa matar ka fyaɗe sannan da akayi bincike aka gano mai laifin, wani irin mataki zaka ɗauka.?"

"Wallahi da hannu na zan kashe shi, idan ban samu damuwar haka ba kuma zan tsaya da dukiya da ƙarfina har sai naga an yanke mishi mummunan hukunci akan laifin daya aikata min."

Dariya Zarah tayi sosai sannan lokaci ɗaya ta gimtse kana ta jawo jakar kuɗin gabanta ta zuge zip ɗin kamar yadda yake tare da tura jakar gaban Alhaji Mai Riga kana tace.

"Kamar yadda kakejin zaka tsaya da ƙarfi kuma da dukiyarka ni idan akayi qa matarka fyaɗe, toh ni inajin fiye da hakan wajen ganin na tsayawa kowace mace da aka ketawa haddi domin abi mata haƙƙinta. Wannan kuɗin da ka kawo bazai taɓa canzamin ra'ayi domin na saba riƙe fiye da irinsu, cin hanci koh? Toh kasani cewa bakayi kuɗin da zaka iya bawa Zarah cin hanci ba, wannan kuɗin ko albashin ma'aikatana na wata ɗaya bazai iya biya ba. Shin kasan girman laifin da ka aikata na baiwa ƴar sanda cin hanci.? Tabbas zan baka mamaki kuma dole a yankewa yaron ka hukunci daidai laifin daya aikata. Banason na ƙara jin ko da kalma ɗaya ce ta fito daga bakin ka idan kuma ba haka ba, hmm kulle ka ba wani abu mai girma bane a wajena sannan babu wani jami'in dayasa isa ya saka ni buɗeka idan nayi hakan. Dan haka kaɗau tarkacen kuɗinka ka ficemin daga office." taƙarasa faɗi tana mai buga teburin, wanda hakan ya ƙara ɗarsa tsoro a zuciyar Alhaji Mai Riga domin dai dama ƙarfin hali kawai yakeyi yake iya mata magana amma ba ƙaramin kwarjini take masa ba.

Batare da tanka ba kamar yadda tace yaɗau jakar tare da ficewa daga office ɗin yana mai banko ƙofar da ƙarfi.

Murmushi Zarah tayi sannan tace.

"Mai Riga kenan, ba shirin wasa nayi a kanka ba duk wani motsin ka yanzu a tafin hannu na yake.".

Kiran wayar daya shigo ne yasa ta saka hannu ta jawo wayar daga inda take, numbar Daddy da tagani ne yasa bata ɗaga ba har saida ta yanke sannan ta maida kiran.

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaikumus salam daughter barka da safiya."

"Daddy ina kwana."

"Lafiya lau kun tashi lafiya koh.?"

"Lafiya kalau Daddy ya Momi."

"Gata nan lafiya lau, yasu Baaban dai da mutanen turai."

"Duk suna lafiya Daddy."

"Kin fita aiki ne yau.?"

"Ehh ina office."

"A'a toh bari na bari ki koma gida kar na katse miki aiki, dama nayi tunanin kina gida ne shiyasa na kira muyi magana."

"Bakomai Daddy ba aiki nakeyi ba dama, zamu iya magana babu damuwa."

"Toh Masha Allah, nace ko Baaba ta isar miki da saƙo na.?"

"Ehh Daddy ta gayamin kuma na amince."

"A'a Zarah idan kina da wani ki faɗa kar na tauye miki."

"Babu kowa Daddy."

"Toh nagode kwarai Allah yayi albarka."

"Ameen Daddy."

"Sai anjima ki gaishe da su Baaban."

"Zasuji insha Allah."

Nan suka yi sallama ta aje wayar a gefenta tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi.

"Oh ni Fatimaj Zarah, aure da mijin da bansan shi ba."

Sai kuma tayi murmushi ita kaɗai tare da kaɗa kai.

.........

Shi kuwa Alhaji Mai Riga bayan fitarsa daga office ɗin Zarah cike da takaicin rashi haɗin kai da bata bashi ba, kai tsaye gidan alƙalin kotun da aka shigar da ƙarar ya nufa.

Bai wani sha wahala ba aka shigar dashi cikin gidan, bayan sun gaisa da alƙalin ne yake faɗa mishi abinda ke tafe dashi nason kar a yankewa yaronshi hukunci tare da korar ƙarar gabaɗaya.

Toh ƙasar tamu dai ta ɓaci kowa son kuɗi kawai, babu ɓata lokaci alƙalin ya amince gani irin maƙuda kuɗin da aka aje a gabansa.

Sallama sukayi zuciyar Alhaji Mai Riga fal da farin ciki.




*By*
*Jasmine*🌸
*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki._Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623._

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Page 9*

*ALPHA VILLA*👽

Kamar koda yaushe ba'a taɓa ganin daga inda yake magana saidai a jiyo sautin muryar sa.

"Raliya ki kula sosai banaso a samu wata matsala, yanzu idan kuka bar nan za'a kaiki filin jirgi inda daga can zaki wuce Gombe, kiyi amfani da adireshin dana baki ki isa zuwa gidan kamar yadda na tsara miki, ki tafiyar da komai cikin tsari kada ki bari a gano ki. Gobe da safe ne zaki isa zuwa gidan bayan ta fita zuwa gurin aiki. Kin fahimce ni."

"Na fahimta Oga zanyj komai yadda kace." Raliya dake rakuɓe a gefen ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ta faɗa kanta a sunkuye.

"Banason rawar kai Raliya, samo masaniyar inda lu'u lu'un yake shine kawai aikinki, ban baki damar kiyi yunƙurin sacewa ba wannan aikin ba naki bane. Ina ƙara jaddada mi ki."

"Ba za'a samu matsala ba Oga."

"Ki tashi kije ki gama kintsawa ƙarfe biyar za ku wuce."

"Toh na barka lafiya yallaɓai." ta faɗa tana mai miƙewa daga durƙushen da ta ke sa'an nan ta nufi ƙofar da zata fidda ta daga cikin falon.
........................................


Haka Alhaji Mai Riga yayi ta zagawa yana siye bakin waɗanda ke da masaniya akan case ɗin hatta lauyan bogi da Zarah ta ɗauka saida ya bashi maƙudan kuɗi akan ranar da za'a shiga kotu yayi tawaye yace shi lauya ne mai kare wanda ake zargi.

Yau ta kama ranar lahadi inda gobe ranar litinin za'a shiga kotu, dukkan su suna zaune a falo suna hira jefi- jefi wanda akasarin hirar tsakanin Jidda ne da Baaba domin Saleem da Jidda suna gaban na'ura mai kwakwalwa suna gudanar da aiki.

Baaba ce ta kalli gefen da su Zarah suke kana tace.

"Zara'u ince dai mahaifin naku ya faɗa miki matsayar da ya yanke game da bikin ku."

Kallonta Zarah tayi batare da ta tanka ba ta maida hankali kan abinda ta keyi, Jidda ce ta maida hankalinta wurin Baaba tace.

"Wace matsaya kuma Baaba tunda ta rigada ta amince.?"

"Ai uban nasu yace nan da watanni biyu za'ayi bikin, shima Muhammadun ya kusa dawowa gida domin fara hidimar bikin." inji Baaba

"Lallai kice mu ma mu fara shiri kenan Baaba mun kusa zama amare." Jidda ta faɗa cike da zolaya.

"Sosai ma kuwa." Faɗin Baaba.

"Amma Yaya Sadiq zai dawo bikin koh.?"

"Ehh naji Sulaimanu na cewa sun gama karatun zaije da kanshi ya taho dashi, kinsan tunda yaji labarin rasuwar nan shima yake ta noƙe noƙen son cigaba da zama a cikin turawa."

"Gaskiya kam ya dawo bikin ƙanwa babu babban Yaya ai ba zaiyi armashi ba."

"A toh su daɗi su keji ganin kansu a tsakiyar arna suna shawagi."

"Kai Baaba bafa duka bane arna akwai musulmai sosai."

"Duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ai."

"Baaba watarana dai zamu kaiki ƙasar turawan nan kiji yadda akeji idan ana can."

"Allah ya tsareni ni Faɗimatu, bana fatan gani ko a mafarki na. Zara'u wani irin aiki ne kuke yi haka da baza ki bari kizo kiyi karin kumallo ba, ina fa lura dake kwana biyun nan sam bakyason cin abinci, shiyasa kike ta ƙarewa kamar kazar mayu." Ta ƙarashe maganar hankalinta na kan Zarah.

"Baaba ko kece kika tsinci kanki halin da take ciki baza ki samu nutsuwa ba sai kin kai ga ci." Faɗin Jidda

"Yoo wani hali ne take ciki banda na sama kanta damuwa sai an daina cin hanci a ƙasar nan, waɗanda suka fita ma sun gwada sun ƙyale."

"A'a fa Baaba case ɗin fyaɗe ne a hannunta kuma gobe za'a shiga kotu, shiyasa take ƙoƙarin tara duk wasu hujjoji gudun kada aka dasu, gashi dama iyayen yarinyar ba masu hali bane."

Salati Baaba ta shiga dokawa harda ƴar guntuwar kwalla kafin tace.

"Ashe har yanzu ana wannan rashin imanin a ƙasar nan, shikenan dai shi talaka bazai taɓa hutawa ba. Yanzu mene ne ribar yiwa mace fyaɗe, kawai saboda tsantar zalunci da son rugujewa mutum rayuwa. Insha Allahu duk asirin su saiya tuno an hukunta su, shiyasa nake son aikin Zara'u saboda gaskiyar ta. Nayi ma Muhammadu magana ma dole zai barta ta cigaba da aikinta saboda rashin ta zai iya saka al'umma cikin wani hali."

"Baaba ƙasar tamu yanzu ai sai dak kawai mu cigaba da addu'ar samun gyara, amma kullum lamura ƙara taɓarɓarewa suke yi."

"Kullum cikin addu'a muke kuma bazamu taɓa gajiya wa ba."

Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin dake addabar ƙasar ta mu har zuwa lokacin da su Saleem suka gama aikin suka dawo cikin falon aka cigaba da hirar da su.

Washe gari da wuri Zarah ta bar gidan bayan tayi sallama da su Jidda da zasu haɗu acan kotun.

Kotun ta cika maƙil saboda ba shari'a ɗaya ake gudanarwa ba, baya ga haka kuma abokan hamayyar Alhaji Mai Riga su ma sunzo dan ganin yadda zata kasance.
Shari'a biyu aka gudanar kafin azo kan case ɗin Fahima.

Kamar kowace shari'a, lauyoyin sun hallara a inda aka tanadar musu domin zama. Nan aka umarci su gabatar da kansu.

"Suna na Bar. Labaran Ahmad tare da abokin aiki na Bar. Gideon Wangson mu ne masu kare wanda ake tuhuma." Faɗin ɗaya daga cikin lauyoyi biyu dake zaune a inda aka tanadar musu.

"Shin Bar. Labaran bakai bane lauyan masu ƙara." Faɗin Alƙalin.

"Bani bane my lord." Inji Labaran.

Jinjina kai kawai alƙalin yayi kana yace.

"Ina lauyan masu ƙara."

Shiru babu amsa.

Alhaji Mai Riga ne ya kalli inda Zarah take tare da yin wani shu'umin murmushi mai cike da ma'anoni, ita ma murmushin ta maida masa mai alamar bakasan me kake yi ba. Kafin ya gama mamakin murmushin daya gani a fuskar ta ya jiyo sautin magana.

"Suna na Barrister Saleem Sa'ad ni ne lauyan masu ƙara, my lord ayimin haƙurin lattin da nayi hakan ya faru ne a sanadin cunkoson ababen hawa da na samu a hanya." cewar Saleem wanda shigowarsa kenan ya nufi gurin zaman lauyoyin.

"Bar. Saleem a kiyaye na gaba." cewar alƙalin.

Ba iya Alhaji Mai Riga bane ya shiga mamaki da ruɗun jin abinda ya fito daga bakin Saleem, hatta Labaran saida ya ruɗe domin dai ko kafin a fara gabatar da zaman kotun na yau sun tattauna da Zarah a matsayin shi na wanda zai tsayawa Fahima. Lallai ya tabbatar ta samu labarin zaiyi tawaye shiyasa ta tanadi wani lauyan.

Zufa ce ta fara keto masa ta kowani sashi ba jikinshi, ɗagowa yayi jin alƙali ya buƙaci su gabatar da shaidar su ta farko, sai dai me...............✍🏼

*BY*
*Jasmine*🌸🌸
07048961623.


*ASSALAMU ALAIKUM*

*Uwargida da amarya har yanzu fa ƙofa buɗe take, zaki iya samun damar kasancewa da ni HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA a cikin zafafan darussan da nake gabatarwa a ASP ZARAH SPECIAL FANS GROUP, domin samun dabarun zama da miji, ɓoyayyun sirrikan da zakiyi amfani da su wajen mallake mijinki cikin sauƙi, tare da sahihan kayan gyara na musamman sha yanzu magani yanzu. Kada ki bari ƴar uwarki ta labarta miki.*

*Cikin ikon Allah a ƙanƙanin lokaci group ɗin mu na farko ya cika kuma yanzu haka mun buɗe wani sabon group ɗin ga masu buƙatar su shiga a baje wannan kolin dasu. Kada kumanta dai zaku iya samun damar shiga wannan group ta hanyar tuntuɓar wannan number 07048961623. Ina jiran zuwanku, ni ce dai takun da bani da tamka HAJIYA JAMILA SHARE KUKAN MATA*.

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Paid book_.
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba ki/ka biya N300 kacal na normal group, VIP group kuma N500 amma dan Allah idan so samu ne karki biya VIP idan baki da aure saboda darussan da ake gabatarwa a ciki. Za'a turo kuɗi ta wannan asusun 0153109156 Union Bank, sannan a turo shaidar biya ta 07048961623.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Zarah ya gani ta kafe shi da idanunta masu rikitarwa, nan take ya ruɗe har saida yaji Gideon na gabatar da tambayoyi ga Kabeer kafin ya maida hankali.

Mintuna talatin ana fafatawa tsakanin ɓangare biyun inda Saleem ke gabatar da zafafan shaidun daya tada hankalin Alhaji Mai Riga da muƙarrabansa, domin hatta inda yake cewa Zarah tabbas ɗan shi ya aikata laifin da ake zargin shi saida aka gabatar a gaban kotu. Nan fa kotu ta rikice kowa na faɗin albarkacin bakinsa musamman ƴan adawan Alhaji Mai Riga.

Hutun rabin lokaci aka alkali ya bayar, gaba ɗaya jama'a aka fita waje.
Duk yadda Mai Riga yaso ganin alkalin a wannan lokacin abu ya gagara, hankalin shi ne yaji ya tashi amma tunawa dayayi da irin maƙudan kuɗin da ya bawa alkalin sai ya ɗan samj nutsuwa tare da tabbatarwa kanshi samun nasara.

A daidai wannan lokacin kuwa Baaba tana zaune a falo tana kallon wa'azi a sunna TV, ɗaya daga cikin masu tsaron ne ya shigo tare da shaida mata cewa tana da baƙuwa, batare da dogon tunani ba tace ya shigo da ita.
Jim kaɗan ya dawo tare da Raliya wacce ta ɓadda kama sosai tamkar ba ita ba, wasu tsofaffin kayane a jikinta wanda a kowani lokaci zasu iya yagewa sai wata ƙaramar Ghana-Must-Go itama ta tsofa sosai.
Da sallama ta ƙarasa cikin falon sannan ta zauna ƙasa nesa da inda Baaba take.

"Ki hau saman kujerar mana baiwar Allah." Inji Baaba.

"A'a nan ma yayi Hajiya, ina wuni." Faɗin Raliya.

"Lafiya lau sannu da zuwa, sai dai ban shaida fuskar taki ba kodai gurin Zara'u kika zo ne."

"A'a Hajiya dama nazo neman aiki ne."

"Wane irin aiki kuma daga ina kike.?"

"Ni marainiya ce a garin Tilden Fulani nake, iyayena sun mutu ne sanadiyyar gobara da ta cinye gidan mu tun daga lokacin kuma na rasa masu taimakamin. Toh akwai wata Mata a can gurin namu da take shigowa birni tana aiki shine ta bani shawarar na shigo na zaga gidan masu hali na nemi aikin yi saboda nasamu abinda zan dinga rufawa kaina asiri dashi."

"Duniya ta lalace mutane basason taimako, ai shi maraya idan ka taimaka mi shi tamkar ka zuba adashe ne da zaka kwashe ranar lahira. Kada ki damu insha Allahu za'a baki aiki koda na goge-goge ne."

"Nagode Hajiya Allah ya saka da alkhairi."

"Amin babu komai ai hakkin maraya ne mukeson saukewa."Inji Baaba.

Sun ɗan jima suna taɓa hira kafin Baaba ta miƙe ta shige ɗaki bayan tabar Raliya a falo tana kallo, da sanɗa tabi bayan Baaba dan ganin mai zatayi a ɗakin, ganin shigewarta banɗaki ne yasa tayi saurin komawa falo tare da buɗe jakarta ta ciro wani abu kamar bead na kitson yara ta nufi saman bene. Bata sha wuyar gane ɗakin Zarah ba saboda taswirar gidan da ta haddace a kanta, ɗakin a buɗe yake dan haka tana shiga ta nufi gaban durowar kayan Zarah, wannan abun ta ajiye acan saman durowar ta yadda babu wani mahaluƙin dazai iya cewa akwai wani abu a gurin idan ba anfaɗa ba.
Komawa falon tayi cikin sanɗa tamkar ɓeran dayayi sata yana tsoron a kamashi.


A can kotu kuwa bayan mintuna talatin sun cika aka koma aka cigaba da fafatawa tsakanin ɓangarorin guda biyu, domin dai da alama shari'ar ta kwana ɗaya ce.

Shiru ya ratsa cikin kotun bayan shuɗewar wasu mintuna, duk wannan abu dake faruwa Alhaji Mai Riga lokaci zuwa lokaci yake ɗagowa ya kalli ɓangaren da Zarah take yana yi mata murmushin ƙeta domin dai zuwa yanzu ya gama tabbatarwa kanshi cewa shi ɗin mai nasara ne sannan baza a yankewa ɗansa hukunci ba.
Ita kuwa Zarah zancen zuci take a duk lokacin daya kalletan sai tace.

"Shi dai mutum mara basira ko ina yake ana ganewa."

Alƙali ne ya fara magana kamar haka.

"Bayan sauraron shaidu da ɓangare biyu suka gabatar tare da hujjoji wanda suka gamsar da kotu da kuma kundin tsarin shari'a na ƙasa, kotu ta yankewa Kabeer hukuncin zama a gidan kaso na shekaru goma tare da aiki mai tsanani sa'an nan zai biya tarar miliyan biyar domin nemawa Fahima lafiya, Alhaji Nuhu Mai Riga kotu ta kama shi da laifin yunƙurin baiwa ɗan sanda cin hanci, dan haka kotu ta yanke mishi hukuncin zama gidan horo na wata biyar ko kuma tarar miliyan ɗaya." yana gama faɗin haka ya buga gudumarsa wanda ke nuna alamar ya gama aikin shi na wannan rana.

Kotu fa ta rikice inda Alhaji Mai Riga keta zage-zage tamkar mai taɓin hankali ana riƙeshi, nan fa ƴan jam'iyun adawa da ƴan jaridu suka samu inda sukayi ta ɗaukan hotonan shi, wasu harda yi mashi video.
Haka yana ji yana gani aka wuce da ɗanshi ɗaya tilo tamkar rai zuwa gidan kaso, take kuma ya zube a ƙasa tare da sakin kuka mai tsanani.


"Jidda mu wuce gida kawai ki rabu da Saleem ɗinki da ƴan Jaridun nan." cewar Zarah bayan ta janyo hannu Jidda zuwa wani keɓeɓɓen waje a bayan kotun.

"Mene ne haka wai Zarah ki barni mana a haskani a jarida tare da hubby na."

"Mtssww mu wuce Jidda banason dogon zance, jikina na bani wani yanayi da ban gamsu dashi ba." ta faɗa tana tura Jiddan cikin motar ta, wuta ta baiwa motar bayan ta shiga itama, nan suka bar farfajiyar kotun zuwa gida...... ✍🏼


*By*
*Jasmine*🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Second to the last free pages._

_Paid book._
_Domin samun damar cigaba da karantawa batare da ɗaukarwa kai alhaki ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login