Showing 1 words to 3000 words out of 26864 words

Chapter 1 - Halin Rayuwa Book 1 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

117

HALIN RAYUWA

1


NA

07035586299

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)

1



Hakkin Mallaka [m]
Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne

GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu
ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji.
Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin
Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe
Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da
wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa
ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da
gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace.
Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga
daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje,
Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa
zumuncin da ke tsakaninmu.

Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi
6/7/1434

GODIYA

Godiya mai dumbin yawa gare ki.
Rabi'atu Faruk Jauro (Ministry of Commerce and
Industry Yola, Adamawa State) Da Zainab Sunusi Kofar
Gabas Danbatta, Zainab Abarshi Yawuri
2

HALIN RAYUWA
A duk sanda naci karo da wata kalma da
ta danganci rayuwa gabana kan fadi in
tsinci kaina cikin wani matsayi na tsoro da
razana, wani lokaci ma in ji na samu kaina cikin
halin da zuciyata kan samu kanta cikin yanayi na
kaikawo saboda tunawa da al'amuran da suka
shafi jiyana da yau dina, in suke jin wani
mummunan faduwar gaban idan na tunan ba ni
da tabbatas ko masu niya bisa gobena.
A mafi yawancin lokaci kuma in har nayi irin
wannan tunanin to nakan samu kaina ne da yiwa
gwanin halitta godiya da bai sanya mana wani
tabbataccen al'amari ba in dai cikin wannann
rayuwar tamu ne ta wannan dunyar, duk abinda
ka gani zai wuce.
Farin ciki ko bakin ciki yana da lokaci, komai
yayi farko wata rana zai yi karshe. Wani karin
maganar ma sai ya ce abin da ya baka tsoro a yau
babu mamaki gobe ya baka tausayi, wasu ma da
suka yi wa rayuwa irin fahimtar da suka yi wwa
rayuwa irin fahimtar da suka yi mata sai suka ce
wai ita din tamfar hawainiya ta ke, ta kan iya
canza launinta a kowane lokaci.
Al'amuran da na gani a shekaruna na
kuruciya sun sanya ni son bayar da labarina ga
na kasa dani ba don wani labarin dadin bayarwa

3



ke gare shi ba, a'a sai dai don ya zamo hannunka
mai sanda a gare su. Ya zamo musu wani darasi
da za su rika don su kauce daga aikata kurarai
irin na kuruciya kurarai da kan zamo tanfar na
tsalle daya mai jefa mai shi rijiya.
Wannan labari da nake nufin bayarwa a yau
labari ne da ya danganci halin da rayuwata ta
kasance shekaru talatin baya da suka wuce a
lokacin da na ke da shekaru tara kacal a duniya.
Ni Maryam Abubakar, na taso ne a gidanmu
gaban iyayena uwa da uba cikin gata kulawa da
kuma tarbiya, a wantcan lokacin da nake magana
a kai iyayena uwa da uha suna matukar sona
musamman ma Babana wanda Sunan
Mahaifiyarshi ke gare ni bisa hakanne ma bai
fadin sunan nawa sai yake kirana da kalma ta
Yacuwuna' kalmar da ke nufin ohaifiva ko
uwa cikin harshen barbarci.
Wani dalilin da ya kara tsananin soyayyarshi
gare ni ko in ce muni da Yayata Khadija wacce
take ta girme ni da yawa, don a lokacin da nake
da shekaru. taranne a ka yi bukinta da wani
saurayinta da suka so juna tun suna 'yan yara,
Ibrahim shi ne din bai da kowa sai mu, nai da
dangi ko kuma in ce ya dade rabonshi da yayi
mu'amalla da su ba ya ma maganarsu.
4


Nasha jin Innata a wancan lokacin tana ce
mishi Mallam ko ba don mu ba kai ni wurin 'yan
uwannan namu in gano su saboda yaran nan su
gansu su ban iyayensu da danginsu saboda in mu
ne yau ba mu ne gobe ba, su kuwa dangi
musamman na uba ko don maganin gori a neme
su.
A mafi yawancin lokaci ta kan yi irin
wadannan maganganunne har ta gama ba tare da
ya tanka mata ko ya ce mata uffan ba. Sai dai
wannan bayani da nayi a kan Babana bai hana
shi zamowa daga cikin mutanen kirki ba, mutumn
ne mai tsananin hakuri mai gudun bacin ran
wani, mai girmama makwabci wanda ba ya shiga
harkar da ba tashi ba, ba mai yawan magana ba
ne mafi yawancin lokaci hirarshi takan yi nisa ne
kawai da makwabcinshi Mallam Hodijo wanda
suka zama tanfar yan uwa shi da shi ga shi
kuma sai aka yi dace Babana Babarbare ne
wanda ko zanen da ke fuskarshi ya isa ya
bayyanar da asalinshi.
Haka shima Mallam Hodijo Bafulatani ne da
bai bukatar sain an tsaya bayani a kan shi, don
haka sai abin nasu ya kara zamowa gwanin
sha'awa kullum a cikin zolayar junansu suke
suna raha tare da barkwancin wasan fulani da

5

Barebari, haka kuma alaka take tsakanin Innata
da matar Mallam Hodijo mai suna sumaye.
Wani dalilin da ya karawa Babana sonmu ni
da 'yar uwar tawa shine, kasancewar matarshi
mata mai wabin 'ya'ya cikin haihuwa bakwai da
aka yi ne aka samu mu biyun muka rayu.
Rashin sanin dangin Babana ko rashin
mu'amallar da su bai hana gidanmu zamo wa
gidana Jama'a ba Innata mai 'yan uwa ce ban da
haka kuma mata ce da ta iya mu'amalla da
mutane da ke kuma iyakacin kokarinta wajen
kiyaye hakkin makwabtanta.
Ita din kuma mata ce da yawan mu'amallarta
da 'ya'yan da ba nata ba, ya zamo dalilin da ta
zamo uwar yara da yawa maza kuma da mata
kanana da kuma 'yan samari.
Gwanar kitson ce da kuma lalle bata laima da
kwiya kan hakan sannan bata taba damuwa dayi
don a biya ta ba, don haka kullum ta zaunar da ni
da nufin yi min kitso ko lalle to zata hada ne da
duk yaran da muke wasa da su a wannan lokacin
tayi mana kitso da lallen tare da wannan dalili sai
tayi sabo da iyaye da yawa na yaran da take yi
mana kitson nan ko lallen tare wasu daga uwa
godiya bayan sun aiko mata da abin hasafi ta
mayar su biyo baya.

6

Wasu yaran da ta zamo uwa gare su kuma
musamman yan mazan daga yawan ciyarwarta
ne tana ganin yaro cikin wani zata zaunar da shi
ta zuba mishi abinci in har ya yarda yaci zata
gaya mishi gobe ma kazo daga haka har sai zuwaa
wurin nata ya zame mishi jiki ko kuma dabi'a,
don haka a ko ina yara suka ga Inna za ka ji suna
Mama' Mama ina za ki? Mama kin dawo?
Mama kin ga wane ko? Hatta wasu iyayen yaran
da suka san Inna uwa ce a wurin 'ya'yansu, za ka
ji suna gaya mata laifin yaran nasu don nufin ta
taya su yi musu fada kan laifuffukan nasu kko
kuma kin da suke yi wa makaranta.
Cikin yaran da Inna ke yin mu'amallah mai
karfi da su akwai Mubarak da Mansur wadanda
su ba suna zuwa wurinta don cin tuwonta bane
a'a sukam ma yan gata ne a gidajensu
musamman Mubarak wanda shi shi kadai ne da
namiji a gidansu a wurin kuma ubanshi Alhaji
Mühammadu wanda a unguwar tamu duka babu
maigidan da ya kai nashi girma da kuma kyau.
To haka shima Mansur ko da suke da yawa a
gidansu gidan nasu na rufin asiri ne, su suna
zuwa wurin Inna ne kawai saboda gidannata ya
zamo wurin zuwan yaran unguwar har kuma sai
ka ji suna tambayarta Mama da wani abu ne mai
dan dumi in akwai ta ce akwai in babu ta ce sai
7


garin rogo, wani lokacin ma har sai ka ji tana yi
musu fada kan abin da tasan suna yi musamman
Mubarak, kusan kullum ya shigo za ka ji tana
tambayarshi kaje Makarantar ko yau ma ba ka je
ba? In yaje ya ce yaje in bai je ba ya dan tsuke
fuska yana yi mata bayani Mama ke ba za ki
gane ba ne? ta ce Eh, ba zan gane ba in ba ka
gaya min damuwarka ba amma in har za ka bude
baki ka gaya min ai zanfahimci daidai
gwargwado, tayi mishi nasiha
lyayena ba masu hali ba ne, amma a cikin
rufin asiri muke rayuwarmu, sana'ar Babana
sana'a ce ta rufin asii, kayañ miya yake sayarwa
a saman layinmu ba sni da tsawwalawa.kan
kayanshi, don haka wurin nashi matattara ce ta
cinikin yara.
Mallam ban tumatir, Mallatu han attarugu,
Mallam ban alayyaho, aikin ke nan. Don naka
inhar ban je Makaranta ko gidan Yaya Dijah ba
to yawanci na kan je wurinshi ne in rinka taya
shi in yana bada kaya in rinka karbar mishi kudi
saboda wasu yaran da tarbiya bata ishe su ba
sukan karbi kayan miyan su tafi ba tare da sun
ba shi kudin ba saboda ganin hankalinsi ya tafi
wajen masu kokarin ya ba su nasu.
Babana ba mutum ba ne mai dogon buri ko
mako game da kudi, don hakan kullum ya dawo

8

daga kasuwarshi ya kan tattara duk cinikin nashi
ne ya mika mata ko kuma ni ya miko min in
shirya su in je in ajiye su a inda nasan tana adana
kudi.
Shi kuma ba mai yawan sa ido kan abubuwa
ba ne, balle ka ji shi yana kididdiga ko tuhuma,
don haka kusan komai Inna ce take tafiyarwa
tana ganin wani rami a çikin gidanmu za ka ji ta
kira wani daga cikin samarin da suke shigowa
wurinta ta basu kudi ta ce maza suyo siminti ka
toshe mnin wannan wurin.
In kwata ce take nema ia cika zata sa su nemo
mai kwasheta ya gyara suyi ciniki ya kwashe ta
basu kudin suje su biya haka nan rufin kwano in
ta hango alamar zuwan damina zata basu kudin
foti su sayo su nemo mata mai hawa kwanon ya
kara bin kusoshi da fotin din maganin yoyo.
Haka nan kuma ko wata hidima ce ta taso
bata jiran Babana sai dai ta ce mishi an yi kaza
an yi kaza ko da kuwa ta sallah ce ko azumi ya
ce mata to, ko da kuwa a kan shi ne zata yi tayi
mishi tuni musamman da sallah, Mallam in fa
baka sayi yadi ka bada dinkinka yanzu ba zaka
rasa dinki, ya ce mata to don na rasa dinki
menene tunda dai ke da yaran kun samu ai shi ke
nan.

9


Tayi murmushi ta ce, Haba Mallam ana
hidimar sallah ai zan so nima in ga mijina fes in
Rara jin dadi da yiwa Ubangiji godiya, yayi
kamar bai ji ta ba. Inna da makwabciyarta Babah
Sumaye wani irin zama suke yi da yafi na 'yan
uwan da babu fahimta da kauna ta zumunci a
tsakaninsu dadi.
Kusan kullum sai wata fa shigo wurin wata
duk abin da suka girka sai sun aikewa juna, wata
rana ma ka ji daya tana cewa dayar in za ki yi
girki kiyi tare da nan gidan, don kasala nake ji ko
kuma aiki zai yi min yawa-za a yi abu kaza da
kaza su ce to.
To haka Babana yake da mallam Hodijo
ko'ina za su suna tare ko da kuwa Masallaci ne
kullum kuma naje karbo cefanen gidanmu, to
nakan hado ne da na gidan su Babah Sumaye.
Innata ba wata jaruma ba ce in dai a kan
neman kudi ne bata da wata sana'a da take yi ta
maida taro ya zama sisi anima tana cikin wadata
saboda halin mijinta na komai nashi a wurinta
yake ajiye shi bai da kuma matsala don ta ce
mishi ta kashe kaza kan abu kaza na hidima da
ya taso haka nan ita din gwana ce kwarai ta
shirya abinci mai dadi aci shima Baban nawa
mai son cin dadin ne.

10


Sannan ta iya zama da shi ta iya tarairayarshi
da tattalinshi duk da shi ba mai yawan magana
ba ne, ko yawan dariya amma in suna tare shi da
ita fuskarshi bata rabo da murnmushi, bini-bini
kuma za ka ji shi yana yawan ambaton sunanta
Ramatu.
Gidanmu karamin gida ne dan madaidaici,
dakuna hudu ne a ciki, ciki da falo guda daya
wanda ni da Inna muke ciki, sai dai-dai guda
biyu, daya Babana daya kuma tarkace na
kwandunan tumatir din Babana da sauran
kayayyakin Inna na aiki, kullum ka shigo
gidanmu daga zauren gidan ka ke soma shakar
kamshin turaren Innata.
Ana cikin hakanne aka wayi gari a gidan
namu Inna tana wani irin rashin lafiya da Babana
yayi ta zarya yayi ta zirga-zirga da dawainiya
mai yawa a kai, cikin wani irin farin ciki da
zumudi mai yawa.
Haka nan itama Babah Sumaye tayi ta hidima
aikin gidanmu gaba daya ya zama nata, ta rinka
kai kawo tana ta faman murna ashe, ashe wai
Innar tawa wani cikin ne da ita, ni kam nayi farin
ciki saboda ganin zan samu kani wata kila mace
watakila namiji, wanda dama nasan Babana yana
Son samunshi.

11

Sai dai kuma gabana ya fadi da na tuna da
irin haihuwar da Innan tayi shekara guda da ya
wuce inda ta kubuta da kyar.
Kankana, abarba, lemo da ayaba basa
yankewa a gidanmu, saboda kullum sai Mallam
Hodijo ya kawo ya ce a kawo mata saboda abin
sana'arshi ke nan a bakin asibitin garinmu.
Haka a ka yi ta fama da ita har dai ta samu
sauki ta wartsake ta koma kan al'amuranta.
Muna nan a haka har cikin Inna ya bayyana
ya fito sosai, dama kuma ita din mai katon ciki
ne ina jin ta rannan a hirar da suke yi tana gaya
mishi ni dai ban taba jin ciki irin wannan ba
Mallam, ko kuma don mutum ya fara girma ne
yake jin hakan oho.
Yayi murmushi ya ce, "Ramatu ke nan, kina
yar shekaru talatin da biyar kina gayawa kanki
girma da kuma ni ne nayi kuskuren ba ki nace
miki kin girma da kin ce.na hango wata yarinyar
ne a waje yáa sani kiranki tsohuwa."
Tayi murmushi ta ce, "Uhun! Mallam ke nan,
to tunda a ka yi auren yarinyar nan kuwa har
gata yanzu da juna biyu ai dole in kirawa kaina
girma ni da kaina."
Ya tayata murmushin kafin ya sake kallonta
Cikin natsuwa ya ce mata, ai ba Dija ce mizanin
da za ki rinka dubawa wajen gane girmanki ba,

12

ni za ki rinka dubawa ai ni ne ma'aurinki ya ya
ki ke a wurina? Shi ne maganarki, ya ya nake
kallonki? Shi ya kamata ya zama abin lurarki,to
in kuwa ni ne ban taba kallonki na gane
canzawarki ko bambancin da ke tsakaninki a yau
da na ranar da mahaifinki ya kira ni ya ce min in
dawo da yamma inga 'yar da yake da ita in tayi
min in kawo sadaki a daura min aure da ita babu
wata rana da nake wayar gari ko zan wayi gari
ban yi wa wannan mutumin kirki addu'a ba
Ramatu."
Ta kalle shi ta dan yi murmushi ta ce, Uhun
kai Mallam babu halin in kawo maka wata
magana sai ka kawo wannan zancen ya ce, Eh ai
bana gajiya da bada labarin ne saboda ya bani
abin da ban taba tsammanin samu ba na kar6i
aurenki cikin tsananin tsoro saboda nayi zaton za
ki bijire sai kuma ki ka zamo yarinya mai
albarka mai ladabi da biyayya, mai sanin darajar
iyaye da aurenki.
Tunda ki ka zo wurina ban taba ganin wani
al'amari daga gare ki ba sai na alheri." Shiru
Inna tayi tana sauraronshi sai da ya gaji ya canza
zancen don kanshi ni nafi zaton canjin da kike ji
din wata kila da namiji ne ai kin san gaba daya
haihuwar nan da a ka yi in ban da na farin sauran

13

shidan duk mata ne amma tunda kin ce kina da
damuwa to tashi kawai muje asibiti."
Tayi maza ta ce ka ji Mallam kuma shekaran
jiya ne fa naje awo suka kuma ce min babu
matsala, iyaka dai in dan rage cin gishiri da
barkono."
Haka rayuwar Inna da Babana take kullum a
cikin ganin alherinta yake, bai daga ido ya kalli
wani al'amarinta ba balle ya gano kuskurenta
baida wani labari wanda ya wuce na fadin
alherin mahaifinta saboda ba shi ita da yayi ba
tare da shi din ya neme ta ba ya kuma ba shi ita
tana da shekaru goma sha biyar a duniya, bayan
kuma gata da manema masu yawa da suke fatan
ganin an ba su aurenta.
Kullum Babana a cikin sayayyar haihuwar
Inna yake komai ya gani ya bashi sha'awa zai
sayo yazo da shi gida, rannan ina jin ta tana ce
mishi wannan kayan fa Mallam yawansu ya isa
haka.
Kuma ma ni sai nafi son a hakura da sayayyar
haka sai an ga an yi haihuwar tukuna saboda ni
dai Mallam zuciyata a tsinke take game da
haihuwar nan.
Yayi maza ya dago ido ya kalleta za ki fara
ko Ramatu? Kin san irin fadar min da gaban da
kike yi kuwa idan kina furta irin wadannan

14
kalaman? Kin sani sarai ai kin uma san abinda
kike yi in yi kike yi don in ji dadi kin sani, in ma
don me kike yi kin sani.
Kin sani sarai bani da kowa bani kuma da
yan 'ya'yannan naki amma sai ki rinka gaya
min maganganun da zan rinka hawa gadona da
daddare ina kasa yin bacci saboda lissafe-
lissafen al'amura. Tayi murmushi ta ce, "To kayi
hakuri Mallam bari in je in kawo maka
abincinka."
Bai saki fuska ba ya ce, To wane abinci kumna
zan ci ni yanzu bayan kin gaya min wannan
maganar."
Ta sake yin wani murmushin ta ce, "Kayi
hakuri Mallam ba zan sake yin ba amma da
wannan katon cikin nawa da wannan kwalliyar
da nayi don ka ji dadi in girka abinci don kai ka
ce ba za ka ci ba ai kai ma kasan in na soma
fushi zan dade ban huce ba, burabusko fa nayi
maka da miyar yakuwa, ta kuma sha kashi da
tantakwashin ga kuma nama ka gani?"
Ta zauna kusa da shi tana nuna mishi in zuba
maka? Ya ce To ko don tsoron kar kiyi fushi ai
zan ci Ramatu amma in don yunwar da na dawo
da ita ne ai ta tafi tunda taji irin kalaman ki tayi
maza ta ce ai ba zan sake ba kayi hakuri ya ce ya
wuce Ramatu.

15

Anyi hakan bai dauki wasu kwanaki da suka
zamo masu yawa ba na farka cikin dare naga
kofar dakin Innata a bude alhalin sanda zamu
kwanta ni da hannuna ne na rufe kofar har na
sanya mata salanta nayi kamar in gyara ruhuwata
da na fahimci zamewanta ne yayi dalilin
farkawar tawa saboda tsananin sanyin da a ke yi
har na juya da nufin komawa baccina sai kuma
na tuna ai ban ga Innata a wurin kwanciyarta ba
da sauri naji baccin ya sake ni nayi mika na bude
idanuwa sosai a kasa na ganta a durkushe da
gwiwoyinta a kasa ta dafa wata kujera 'yar
tsugune wacce dama ta zamanta ne a kicin
nantake na karan wartsakewa ina kara bude ido
don in ganta da kyau har nayi nufin saukowa in
da take sai ga Babana ya shigo dakin cikin sauri
rike da kwanon sha karami a hannunshi alamar
rubutu yaje ya yiwo mata daga wannan rubutun
dai Ramatu in bai yi ba sai kawai mu tafi asibiti
kin ga nakudar tayi tsawo kar muzo muyi irin na
wancan karon shima asibitin yana da amfaninshi
ai duk rama ce ta Ubangiji ta kawomasu bata dai
tanka ba.
Ya isa gare ta ya durkusa a gabanta shi ma
kan gwiwoyinshi karbi ki sha rubutun nan
Ramatu, bata motsa ba daga yanayin ta na

16

sunkuyar da kan da tayi tana kallon 'yan
yatsunta.
A hankali cikin matsananciyar taushi da
laushin murya ta ce mishi ka yafe min abubuwan
da nayi maka Mallama.
Ya kara zuba mata ido watakila ba wannan
ne karo na farko da tayi mishi irin wannan rokon
ba saboda jin da nayi ya ce mata, To ni wai me
kika yi min ne Ramatu da ki ke ta nanata min
wannan maganar? Ai ni ban san komai ba game
da ke in ban da alherinki shekaru ashirin din
aurena da ke sune shekaruna na jin dadi da
samun farin cikin rayuwa in ban da ke da wata
kila ban taba sanin jin dadi ba, na zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login