Showing 21001 words to 24000 words out of 26864 words

Chapter 8 - Halin Rayuwa Book 1 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

123

kadan sai
naji Mubarak ya ce to amma Umma ya ya za ayi
da kannan ta samu saukinshi?

106

Kin ga wani ruwa-ruwa ma inda yake
gangarowa ta bayan kunnenta ko sai dai kawai
ayi aski? Da sauri na daga kai na kalle shi cikin
wani irin yanayi na mummunar faduwar gaba.
Kamar Umma ta gane halin da na shiga, don
ni kam duk da wahalar da kannawa ke ba ni ina
Son gashina.
Aski kuma Ahmad.Mubarak don ka ganta a
haka ko? ai maraici ne da uwar ta tana nan da
yanzu wata santaleliyar budurwa ce.
Yayi murmushi ya ce, budurwa kuma Umma?
Ta ce, eh to ai bana shekara ina ganin tsakanin
sha uku da sha hudu ta ke, ai kuwa kaga da ba
haka ta ke ba tunda duk da wahalar da take ciki
na kazanta da yunwa ai ta dan mike.
Don haka ba za a aske, mata kanta ba, bari in
gama abinda naké yi kawai na aikin abincin nan
sai in duba mata shi.
Ta mike ta shiga kicin tana aikin girkinta
suna hirarsu da Mubarak ni kuma ina gefe a
zaune a cikin hirar tasu ne na fahimci Mubarak
ya kammala karatunshi na Jami'a ne a bana.
Ta gama aikin abincinta ta rarraba ta baiwa
kowa nashi ta kalli Mubarak ta ce mishi, To ba
ni wuri mana ba ga naka can an kai ba, ko za ka
tasa ni a gaba ne sai na wanke mata kan kana
kallo?

107

Yayi maza ya ce, a'a Umma na zauna kina
Son zaman nawa ne? ta ce a'a bana so, ya ce to
ya mike yayi tafiyarshi.
Ta kalle ni cikin yanayin kamewa sosai shiga
kicin kici abincinki ga shi can na ajiye miki sai
ki fito in gyara miki kan naki.
Na daga kai na kalleta da niyyar cewa na
koshi, yanayin da na gani a tare da itan ya wuce
na a kawo mata wani wargi, don haka na mike
na shiga cikin kicin din na samu abincin da take
ci shi ne nawa.
Shinkafa ce da dankalin turawa da miya, ga
kuma nama zuku-zuku har guda uku ta zuba min
a kai. na kama ci sai da na cinyeta tas na fito da
kwanon nazo gun wanke-wanke da nufin wanke
kwanon da naci a ciki na hada har da kwanuka
da tukwanen da na smau a wurin na wanke shi
fes na kife.
Ina gamawa ta kira ni to zo daga nan mu gani,
naje in da ta ce din wanda gaba kadan da inda
nayi wanke-wanken.
Ni da Umma ta fara wanke min kai ina
tsugune sai da ta kai ma nayi zaman dirshan
sosai a kasa, ta wanke kurarrajin tun suna fari
har sai da suka zama ja tun ina jin dadin wankin
da ake yi musu har suka koma yi min zafi.

108

Tana yi kuma tana yi min fada in ba ka da
mai yi maka abu ai yi wa kanka ka ke yi, ina
dalili za ki zauna da wannan kazanta haka, ji
wuyanki fa, ji bayanki ta gogo inda take nufin da
hannunta ta nuna yanda datti yayi .mujimurji a
tafin hannun nata.
In uwarki tana da laifi ai ke ma kina da naki
na sakarci, Umma ta gama wanke min kai
sannan ta kama cuda ni da soso da sabulu, wuya,
baya, kirji, ke tafi can ni tsaya in cuda ki da kyau
ina ruwana da nonuwanki?
Kunyarta ta kara kama ni ta gama abinda take
ganin ya dace tayi min ta mike da nufin barin
wurin.
Kiyi wanka mai kyau kowane lungu a jikinki
ki wanke shi, ki goge kafarki sai ki cikin gida ki
same ni na ce mata to.
Nayi wanka da wadataccen ruwa naji dadi
irin wanda na dade ban ji ba, na fito na shiga har
cikin dakin Umma na tsuguna, ta kalle ni ta ce,
Ga daki can nasu Rukayya shiga ki shafa ki
dauki zanen da ke kan gadon ki daura sai ki zo
in sanya miki magani, na ce mata to.
Ni da na shiga gidan su Mubarak tun wajen
sha dayan rana:ban fito ba sai bayan Azahar,
kusan ma za a yi La'asar ina rungume da 'yan

109

kayana da na wanke suka bushe ta hana ni canza
na jikina da na sanya a gidan ta ce in je da su.
Rannan kwana nayi ina wani irin bacci mai
dadi, ashe-ashe dama can ba kwanciyar kasa ko
rashin abin ruhuwa ke hana ni yin bacci ba, masi
far kwarkwata da kurarrajin nan ne yafi komai
takurawa rayuwata.
Sa idon da Mubarak yayi kan karatuna da ma
duk wani abin da ya shafi al'amarina sai na dan
samu saukin wasu al'amura, kullum za ni
Makarantar boko da ta allo sai dai na daina zuwa
ta Asuba da ta dare saboda ayyukan da na kan yi
da safe kafin in je ta bokon.
Da daddare kuwa Babah Lantarna ta ce ba
Makaranta nake zuwa ba, gun samari nake zuwa,
don haka na bari.
Sanin da Babah Lantana tayi na ina yin lattin
Makaranta Mubarak zai zo har zauren gidanmu
da bulalarshi ya fita dani yasa ta fita harkar hana
ni karatun, tunda tayi tayi Babana yasa baki ya
hana shi yin hakan ya ki.
Don haka ko baya nan "zuwa Makarantata
nake yi saboda ba ta ganewa.
Rannan ya dawo daga tafiyar da yayi da
Babanshi kasancewarshi wanda ya karanta zane
zane yayinda shi kuma Babanshi Alaji
Muhammadu yake dan kwangila yasa tun bai
110

gama karatun nashi ba yake matukar taimaka
mishi kan ayyukan nashi.
Ina zaune a zauren gidanmu ni kadai
littafaina na Makaranta nake dubawa, yayinda
naji motsin shigowa da sauri na daga ido don
ganin wanda ya shigo din.
Ban san lokacin da nayi murmushi ba, ashe
ka dawo? Ya dan saki fuska kadan ashe kina
zuwa Makaranta? Ai daga can nake amma me
yasa yau ba ki je ba? Cilkina ne yake tayi min
ciwo yanzu ma ya dan lafa min ne na fito.
Ciwon ciki kuma? yayi tambayar yana mai
kallon cikin idona yayinda ni kuma nayi maza na
kaucewa kallon nashi. Kin sha magani ne? nay1
mishi karya na ce eh, to zo muje gida.
Nayi kamar zan yi musu, sai naji ya ce ai ba
ki da kirki, Umma ta ce min ba ki taba zuwa kin
gaisheta ba. Kunya ta kama ni gaskiya ban
kyauta ba, irin hidima da dawainiyar da tayi da
kazantata ga shi kuma hakan ya zama sanadin
warkewan kan nawa.
Kurarrajin ma duk sun warke, kwarkwata
kuma ta mutu nima kuma tun daga ranar ban
sake fashin wanka ba, balle wanki ko zan yi ana
zagina sai nayi.

111
Sabulu kuwa bana tambaya a irin kudin break
din da suke bani nake saye har da man shafawa
na (Vaseline) ina adana abina.
Tashi muje, ban musa ba na ce to. Yayi gaba
yayin da ni kuma na bishi daga baya, kai tsaye
nayi nufin wucewa cikin gidan kamar yanda
naga rannan mun yi sai na same shi a tsaye a
zauren gidan, shigo nan.
Na shiga kofar da ya ce in shigan maimakon
in ga dakin zaure kamar yanda nasan dakunan
zaure wani lafiyayyen falo na gani mai dauke da
wasu kofofi guda biyu wadanda suke rufe komai
na wurin kamshi yake yi.
Yau ke ba bakuwar Umma ba ce wurina ki ka
zo, yana fadin hakan ya wuce ya shiga daya
daga cikin kofofin ian da ke rufe bai wani dade
ba sai ga shi ya fito rike da wata leda mai kyau a
hannunshi. Zauna mana kin ja kin tsaya a tsaye
ko kina tsoro ne? ban yi magana ba, na nemi
wuri na zauna a gefen kujerar da ya nuna min,
gwada wannan in gani. Sandal ne mai kyau na
asalin fata, don zuwa makaranta na karba cikin
farin ciki na gwada a kafata kamar donni a ka yi
shi.
Ya kalli kafar bayan ya mike tsaye ya juya
zai shiga daya kofar yana tafiyar yana fadin nayi
zaton haka shi yasa na saya miki shi.

112


Bai wani dade a ciki ba nan ma sai gashi ya
fito da tire a hannunshi, gasasshen nama ne mai
zafi har yana tururi tare da wuka a gefen tire din
yazo ya zauna a kasa kusa da kujerar da na ke
yana yanka naman da wukar.
Sauko kici, na ce a'a na koshi. Ya dago ido
ya kalle ni ya dan yi wani irin dan kankanin
murmushi da bai kai a kira shi murmushin ba,
shi kuma ba yake ba ne.
Ya maida hankali kan abinda yake yi kin taba
ganin na shiga gidanku sanda Mama take nan ta
bani abu na ce na koshi?
Shiru nayi ban ce mishi komai ba, raini ne
babba na gaba da kai ya baka abu ka ce ka koshi,
ko da ka koshin sai kaci kadan don yasan
girmamawa ne ya sa ka yin hakan.
Don haka sauko ki ci ban sake yi mishi musu
ba, ya ci kadan ya mike yą bar sauran in kin
cinye ga kankana nan ki shnaye, ya shiga dakin
da ya fara shiga ya dan dade bai fito ba har na
gama abinda nake yi.
Naji tsoron kawar da tiren tunda ba zan shigar
da shi in da naga ya fito da shi ba, don haka na
mike na bar komai a wurin na fito waje cikin
sa'a babu kowa a wurin, don haka maimakon in
shiga wurin Ummanshi gidanmu kawai na dawo
nayi zamana.

113

Ni da kaina nasan na samu sassauci ba wai
wani canji na samu a gidanmu ba, amma yar
tsabtar da nake yi wa kaina tana yi min dadi tana
kuma yi wa Yaya Dijah.
Har Yakumbo Halima ma da ta ganni sai da
tayi min maganar gashi kuma a yanzu ba sosai1
nake jin yunwa mai tsanani ba.
Saboda in dai Mubarak yana gida to ka'ida
ne a wuni zai bani wani abinda zan ci mai dadi
ko da kuwa sau daya ne.
Kwanaki hudu bayan wannan ranar sai ya
kasance ranar ta Asabar ce ina gida da safe
bayan na kammala ayyukana na dauko allona za
ni Makaranta, sai kawai muka gamu da Mubarak
yanzu ne lokacin zuwa Makaranta? Yayi min
tambayar yana kallon agogon hannunshi.
Sai yanzu na gama ayyukana, na ba shi amsar
a natse. Ki ka gama ki ka fito ba ki yi wanka ba?
Sau nawa zan gaya miki wanka biyu ya kamata
ki rinka yi?
Ban amsa mishi ba, to in dai Makarantar
Baba Mallam za ki je bai fi saura minti talatin ba
a tashi, don haka wuce muje ki gaida Ummata da
nake ta fama da ke kina kakkaucewa.
A gidan su Mubarak kin yarda nayi in fara
shiga dakinshi, kafin in shiga wurin Umman
tashi, don haka muka rabu shi ya shiga wurinshi

114

ni kuwa na wuce cikin gidansu wajen Umman
tashi.
Tana ganina ta somna murmushi alamar taji
dadin ganin nawa, Maryamun Mubarak. Nayi
maza nasa hannayena duka biyu na rufe idanuna
saboda kunyar yanda ta hada sunan nawa da
nashi a wuri daya.
Kurarrajin sun warke ko? nayi maza na ce
mata eh, bata tambayi kwarkwatar ba sai ta ce ai
gashi nan da gani an san kin samu saukinsu, don
har jinin jikinki ya fara dawo miki, muga kan
naki.
Na matsa kusa da ita na bude mata shi don
ban jin kunyar bude shi a yanzu, babu shakka
yayi kyau yayi tsaf, gashi ne da ke mai kyau sai
rashin kulawa, ki kula da kanki kar ki jira sai an
ce kiyi.
Kitso a kai a kai kin ji ko? na ce to Umma.
Na maida dankwalina ina daure kan nawa, sai
naji ta ce min, Yaya cikin naki dai? Mubarak ya
ce min kwanannan kina yawan ciwon ciki?
Na ce yayi sauki, na dauka karshen maganar
kenan sai naji ta sake tambayata, kina ganin wani
abu ne bayan kin yi ciwon cikin?
Da sauri na dago kai na kalleta cikin
mummunar faduwar gaba nan take kuma na sake
sunkuyar da kaina.

115

Na ce kina ganin wani abu ne bayan ciwon
cikin yana fito miki ta jikinki? Kuka na kama yi
mata kamar yanda dama kukan nayi tayi lokacin
da na fara ganin nashi.
Ai ba abin kuka ba ne Maryamu, hali ne da
dabi'a ta kowacce mace a kan haka a ka halicce
mu, hakan kuma alama ne na girma.
Sai ki kara natsuwa ki kuma kara kama kanki
kar ki yarda wani namiji ya kusanci jikinki daga
yanzu kuma kar kina yarda lokacin sallah yana
wuce ki ba ki yi ba.
Don ta hau kanki, haka nan Azumi in dai na
ganin shi kuma za ki yi wanka tai tayi min
bayanin yanda zan yi wankan, sai dai ban ji
komai ba saboda kukan da nake yin ya tsananta.
Mubarak ya shigo ya same mu da Umma, bai
tsaya ba ya juya ya fita saboda shigowar nashi
bai sata ta daina maganar da take yi min ba.
Tashi ki share hawayenki ki wanke min
wadancan kwanukan, sanya umarni na aiki a
cikin maganar ya sanya ni hanzarin mikewa naje
na kama aikin da ta sani, na gyara wurin fes na
debo su na kawo mata, to ungo wannan gyara
min shi, na ce To. Nasa hannu na karba na gyara
shi na mika mata.
In ce ko uwar taki tana koya miki girki ne? na
ce a'a a gidan Yaya Dijah nake yi, Umma tayi

116
maza ta ce iko sai Ubangiji, har na mance Dijah
tana garin nan tana nan a nan inda muka kaita?
Na ce, eh Umma sai dai mijinta yayi nashi ne
a can ciki suka koma, tayi addu'a kafin ta
tambaye ni, ni yanzu 'ya'yanta nawa ne? na ce
uku mata biyu namiji daya.
Hira sosai muka yi da Umma har ta gama
abincinta ta zuba min nawa naci na koshi wanda
tuwon shinkafa ne miyar shuwaka sannan na fita
na koma gida.
Da yamma ina cikin gida Mubarak yazo yayi
sallama da ni na fito na same shi a zaure, leda ya
miko min nasa hannu biyu na karba nayi mishi
godiya na juya cikin gida.
Dakinmu na fara shiga na zauna a kasa ina
cicciro abubuwan da ke cikin ledar, kayan mai
ne guda biyu da a ka rubuta 10.0.6 lotion a jiki
da sabulanshi suma guda biyu, sai hoda da tur
are duka na 10.0.6 din ne.
Sai sabulan wanki da kwalin omo shima guda
biyu, sai wata leda da ta bani sha'awa sai dai ban
san meye a ciki ba, na shiga kokarin budewa
don in gani.
Sai kawai Asabe da ke kwance a kan gado
tayi maza ta fige tana fadin "Lahhh! Kan uba,
lalle yau an kama ki wannan ai iskanci ne, ya
sayo wannan ya kawo miki, da gudu ta fita ta

117

kaiwa Babah Lantana ta barni nan a zaune jikina
yana ta faman rawa saboda an ga abin iskanci a
wurina.
A to, ai ni kam dama na fada ai na gayawwa
ubanta abinda suke yi bai kula zancen ba ne in ta
dauko mishi cikin shege ai yasan abinda yake
ciki.
In banda isklanci ace har abin jinin al'ada
saya mata yake yi? Na sake tsorata, tsoro kuma
mai tsanani. Maimakon in tuna na dade ina ganin
Asabe tana yi in saki zuciyata sai na zauna nayi
ta kuka.
Babana yana dawowa kuma Babah Lantana
taje ta kai mishi audugar al'adar nan da Asabe ta
dauke cikin sayayyata ta nuna mishi a matsayin
huijar da zai gasgata maganar da take fadi, na'
cewar ni din lalacewa muke yi da Mubarak
tunda har ga shi yasan ina al'ada yana saya min
abin amfaninta.
Bakin ciki mai tsanani ne ya same ni, irin
wanda ba zan iya kwatantawa ba, gayawa
Babana da a ka yi na rinka ganin tanfar wani
gagarumin laifi na aikata irin wanda ba a taba
aikatawa ba a duniya.
Rannan Babana ya buge ni duka irin wanda
ba a taba yi min ba a rayuwata, karo na farko
kuma da ya taba taba jikina da sunan duka.

118

Sai dai ni kam ba azabar da na sha ne babban
matsalata ba, irin kukan da na ganshi yana yi da
hawayenshi.
Na samu kaina cikin kunci mai tsanani da
bakin ciki, nayi dalilin da Babana ya zubar da
hawayenshi a kaina, to ni kuwa ina zan shiga in
tsoma rayuwata in ji dadi?
Da yake akwai al' amarin kuruciya mai yawa
a tare da ni, a lokacin sai na rinka jin tanfar eh da
gaske ne iskancin da ake cewa nayin nayi shi
tunda a ka ga wannan abin a wurina, donni a
lokacin ban ma san asali menene a ke nufi da
iskancin ba.
Tsawon lokaci ban sake yarda wani abu ya
sake hada ni da Mubarak ba, ko da kuwa wane
iri ne komai kuma kankantarshi, ko a waje ya
hango ni ya soma kirana ko kokarin zuwa in da
nake zan ruga da gudu in tafi in ba shi wuri.
Zauren gidanmu da kofar gidanmu kuma
Babana ya hana shi zuwa, sai dai shima bai san
dalilin faruwan hakan ba.
Ana cikin haka ne kuma muka rubuta
jarrabawar mu ta gama aji biyu zamu tafi uku a
tsawon wannan hutun babu abinda ya hada ni da
Mubarak, bana ma ganinshi ko da kuwa a kofar
gidansu ne in da wani lokaci yakan zauna tare da
samari abokanshi.

119

Sai dai maimakon rabuwa da Mubarak din da
nayi ya zama sanadi da zan samu wani sauki ko
sassauci wurin Babana, tunda yayi min hukunci
na yarda ya bani umarnin fita hanyarshi nab
umarnin da ya bani ban samu sassaucin ba.
A gidan ma wani kuncin na sake shiga na
koma zama cikin yunwa ga rashin abubuwan da
da na daina nasa su Asabe tayi matukar tasa ni a
gaba babu halin in yi magana kan komai sai
Babah Lantana ta ce, To ba taga tana jini ba.
Bakin ciki ya kama ni in mance da wanda
nake ganin Asabe tana yi, kusan kullum sai tayi
min duka, duka kuma irin na zalunci irin wanda
babu mai ceto ko mai tambayar dalilin yinshi sai
ta gaji kawai ta bar ni don kanta.
Rannan na dawo daga makarantar allo a
lokacin nan an kai kusan watanni shida da
faruwar abinda ya farun, sai kawai gani ga
Umman Mubarak a hanya ta fito gaida mara
lafiya a makwabta.
Rike baki tayi tana kallona, haba ke kuwa
Maryamu, me yayi zafi haka da ba za ki shigo ki
gaishe ni ba? Na sunkuyar da kaina cikin wani
yanayi da ni kadai nasan abinda na shiga, in don
Ahmad Mubarak ki ka daina zuwa wurina shi
kamma ai ba ya nan...

120

Da sauri na kalle ta sai dai ban san lokacin da
na dago na kalletan ba, ta ce eh ya tafi hidimar
kasarshi yana can Ibadan inda aka tura shi, dama
yana son kin tafiya Ibadan dinne yayi a nan kusa
saboda ke da kuwa ki ka biyewa sharrin da
mutanen gidanku suka yi mishi nasa shi ya kama
hanya yayi tafiyarshi.
Wuce muje gidan ai dama na dade ina neman
in gan ki ko da kuwa a hanya ne ba mu gamu ba
sai yau.
Kunya da nauyin Umma yasa na bita, to wai
me yayi miki ne a ka ce yana yi miki iskanci?
Shiru nayi na sunkuyar da kaina kasa na soma
yin kuka.
Yana taba ki ne? nayi maza na girgiza kaina
alamar a a, sun gan shi ya rungume ki ne?
sake girgiza kai nuna a'a, ya gaya miki wata
magana ne suka ji? Na sake nuna a'a, to
menene?
Ta tsare ni da tambayoyi, na kasa cewa komai
har dai ta gaji tace duk mai yiwa dan wani sharri
dai zai gani a kwaryarshi, tunda ni kam ai an ce
ba a shaidar mutum amma ni zan yi wa Ahmad
Mubarak shi ba mai irin wannan iya shegen ba
ne, to yaushe ma ya kula wata da har a ka zo a ka
samu ubanshi ana yi mishi togaciya a kanki?

121
Ga dambun zogale can nayi da za ni gaida
mara lafiya, debo kici, na ce na koshi. Ta galla
min harara tare da daka min tsawa, ke tafi ki
debo bana son iya shege.
Na debo nazo na zauna ina ci ita kuma tana
kara jaddada 6acin ranta kan abinda a ka yi wa
Mubarak, kewar Mubarak din nima ta kara kama
ni, musamman da na gane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login