Showing 6001 words to 9000 words out of 26864 words
eh Baba. Ya ce, To ai
ina ganin sai kiyi shiri ki soma zuwa
Makarantarki, kin ga kin dade ba ki je ba, in ma
kin ga ba za ki ta bokon ba shi ke nan amma ta
allo kam da ta Asuba sai ki rinka zuwa na sake
ce mishi to Baba.
32
Jimawa can ya sake kallona cikin natsuwa ni
a ta bokon aji nawa ki ke ne? a wancan lokacin
da ba a cika sanya yara a Makaranta kafin
cikarsu shekaru bakwai ba, saboda bin ka'idar
hannun dama ya taba kunnen hagu kafin a dauki
yaro a Makaranta sai na ce mishi aji uku.
Yayi maza'ya ce, A'a to ashe ma kin fara nisa
ina ganin har ita sai ki koma don ki samu ki
gama aji shidan ki koyi karatu da rubutu da dan
turancin kai yara asibiti.
Ban amsa ba saboda jin nauyi a dalilin gane
in da maganar tashi ta dosa, iyaka dai nayi shiru
don komawa kan karatuna da na bari nima yafi
min don zai rage min zaman kadaicin da nake
ciki.
Kwana biyu bayan nan na soma zuwa
Makarantar boko wanda sai da naje ta allo kafin
nayi hakan gab ake da fara jarrabawar canjin aji,
a lokacin da na koman sai, dai da yake dama can
ina cikin yaran ajin masų fahimta gashi kuma ina
da kawata da muke benci daya Hasiya Jibrin, sai
na samu hayewa zuwa aji hudu.
Rannan na dawo daga Makaranta na shiga
wajen Babah Sumaye karbar abincina na zauna a
nan wurinta ina ci muna hira tana bani labarin
al'amuran da take ganin ya kamata in sani, na
gama na mike na kai kwanon gun wanke-wanke
33
na hada da kwanukan da na samu a wurin na
wanke su tas, na kife na wuce bandaki nayi
wanka na fito na wanke uniform dna na shanya.
Na shiga dakinta na shafa mai na dauki
kayana da ke wurinta na fito ina rungume da
allona, na ce mata za ni Makaranta Babah, ta ce
a'a sai kin karbo min cefane, ajiye allon anan
kiyi gudu ki karbo min cefane ki kawo min sai ki
tafi, na ce mata to. Nayi yanda ta ce din kafin na
tafi makarantar.
Mu'amallah ta uwa da 'yartga Babah Sumaye
take yi dani, yanda take tafiyar da ni sanda
Innata take raye haka a!'amarin yake, har yanzu
sai dai ma kari.
Don yanzu tana sa ido sosai a kaina hada
kayanki kiyi wanki, in ce to. Dauki kibiya ki
tsefe kanki, tunda ba wani son kits ake yi ba
in ce mata ban iya ba ta ce in gama abinda nake
yi in kawo kibiyata tayi min tsifan kowane
lokaci a cikin yi min fada take, sai dai in bata ga
nayi laifi ba ko da kuwa a gaban waye.
Ina ganin har dan hakanne yasa Yakunbo bata
dadewa bata zo wurinta ba, in tazo kuwa ta rinka
yi mata godiya ke nan, ita kuwa Yay. Dijah
kusan kullum in zata zo zata riko mata wani
abun hasafi ko dai sabulun wanka dana wanki ko
kayan tea.
34
A wannan lokacin a gida na daina barin
Babana yana sharar tsakar gida da kicin, ina idar
da sallah nake fita in yi komai in gama abin da
ke bukatar wanki in wanke na gyarawa in gyara
tunda ba wani kwanannen datti ba ne a gidan.
Sai kaga nan da nan nayi na gama na shiga
wankana, yawan abubuwan da Yaya Dijah kke
kawo mana kwana da yawan maganar da take yi
min kan fita kullum aje sayen abin karyawa
kowa yana gani yasa na rage sai in ce Baba muci
abu kazan da muke da shi kawai ya ce min to.
Kullum na gama shiri zan tafi Makaranta sai
Babana ya ce min matso nan in gyara miki hodar
nan taki, in ce to. In matsa yasa gefen rigarshi ya
goge min fuskata kafin ya umarce ni dasa hannu
in dauki Naira daya a cikin kudin da suke dakin,
lokacin nan kuwa Naiara daya ba karamin kudi
ba ne a wurin yara, don kuwa tana iya sayen
waina ta sayi biskit har ta hada da kwalbar lemo
wani lokaci ma har da alawa don haka kudi sosai
nake zuwa da su Makaranta.
Ina tare da Babana a gida duk da Innata ta
rasu yana matukar kula da ni, wai abin da yake
yi min din ma sanda Inna take nan bana samu,
don kuwa ita mai kwaba ce mai kulawa kuma da
tarbiya, iyaka dai kawai zama kusa da Inna da
35
yunwa yafi zama a inda bata nan cikin daula da
da na sha.
, Babana ya dawo daga Masallaci sallar asuba
ya zauna ya gama laziminshi da addu'ar da zai yi
ya gama ya shafa nima na shafa tunda a kusa da
Sinl nake zaune na soma gaishe shi kasancewar
ranar ta Lahadi ce ya sani gyara zama kusa dashi
tunda ba Makarantar boko zani ba.
Zan gama abin da zan yi ne in tafi makarantar
allo wannan kuwa sai wajen tara. Daga ido nayi
na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba,
ya ce Na' am Mamana, na tambaye shi yanzu duk
addu'o'in da muke yiwa Inna suna zuwa inda
take?
Yayi maza ya gyada kai tare da fadin da
yardar Ubangiji kuwa, kin san ai akwai wasa
ayyuka na sadakatul jariya masu gudana da dan
Adam kan bari a duniya ladar ta rinka kaiwa a
gare shi a bayan rayuwarshi daga cikin irin
wadannan ayyuka da ladansu bata yankewa
akwai 'ya'ya na gari.
Ba kina sallolinki a kan kari ba? Nayi maza
na ce mishi eh babu, ba kya kuma sabon
Ubangiji da gangan, na girgiza kai nuna lamar
a'a, ya ce To in sha Allahu in kin yi addu'a ladan
zai kai gareta ga kuma Yayarki da take zaune a
dakin aurenta, tunda a ka yi aurenta ba'a taba jin
36
wani abu na rashin jin dadin game da ita ba, kin
gani? Cikin yardar Ubangiji addu'o'inku za su1
rinka kawai gare ta.
Na sake kallon shi a hankali na ce mishi
menene sabo Baba? Ya zuba min ido kafin ya
gano ta inda zai Bullowa lamarin, irin su karya,
gulma da shiga harkar da ba taka ba, da
bijirewa iyaye ko zina da makamantansu kin
gane?
Nayi maza na ce na gane, kusan kullum sai na
lissafawa kaina laifuffukan da Babana ya lissafa
min a matsayin zunubi ko sabo, don kar in aikata
su saboda kar in aikata su su zama sanadin da
addu'o'ina za su daina kaiwa ga Innata.
Kusan kullum na zauna tare da Babana muna
hira zai yi min nasiha da cewar in kasance mai
gaskiyaa kan al'amurana in kuma tsare
mutuncina kar in yarda wani yayi min wayo duk
abin da na gani naji ina so in gaya mishi ban da
karbar abin hannun wani ita mace bata da wata
daraja komai kyanta in har bata zama mai kamun
kal da tsare mutuncin rayüwarta ba, in ce mishi
to din ba tare da na san mé maganar tashi take
nufi ba har na gane komai.
Rannan na idar da sallar Asuba ina ta doki da
zumudin Babana ya shigo in ba shi labarin da ke
37
Cina a raina, yana shigowa na soma gaishe shi ba
tare da na jira ya kai mazauninshi.
Cikin natsuwa na kalle shi na ce mishi Baba
zan yi sadaka yau, ya kalle ni cikin natsuwa ya
ce sadakan me kike son yi uwata? Na ce ko na
meye ma Baba jiya da daddare nayi mafarkin
Inna wai tazo gidannan na ganta lullube da
fararen kaya tana kallona tana ta faman
murmushi ni kuma sai tambayarta nake yi Inna
dama ashe za ki iya zuwa wurinmu shi ne tunda
kika tafi baki taba zuwa kin duba mu ba, ni da
Babana?
Ina maganar tana kallona murimushinta kawai
take yi ni kuma ina kurarin matsawa kusa da ita
don in taba ta ina cewa Inna kiyi mini magana
mana har zan taba tan sai kawai naga ta 6ace sai
kuma kawai naga ra farka daga baccina.
Cikin natsuwa ya zuba min ido a allona
lokaci mai tsawo bai kawar da idamuwanshi daga
gare ni ba har na fara jin tsoro ko yayi fushi ne
saboda maganarta da nayi mishi tunda ya sha ce
min in an tunata ayi mata addu'a kawai basai an
yi zancenta wani ba har zan buda baki in bashi
hakuri tare da alkawarin ba zan sake yi mishi
hirarta ba sai naji ya ce min jiyan da kika yi
mafarkinta ai jiyan ta shekara.
38
Nayi maza na daga ido na kalle shi a firgice
saboda razanar da nayi sai ya ce min kin gani in
ha ki manta ba ta rasu ne ranar sha tara ga waran
Jimada Thani, to yau ma ai shataran ne ko
ashirin ga watan.
Na ce Haka ne Baba, lokaci mai tsawo ya
dauka yana yi mata addu'a tare da sauran
Jama'ar Musulmi da suka rigaye mu baki daya
in kuma tamu cikawar tazo to Ubangiji ya
azurtamu cikawa da kyau da Imani.
Nayi maza na ce amin Baba tsawon lokaci
muna zaune shiru babu wanda ya sake furta wata
magana sai na bude baki da nufin fadin abinda
ke kai kawo cikin raina a hankali na soma yin
maganar cikin yanayin girmamawa da tsoro don
kar ya hana ni abin da nake nufin fadin tunda
yasha gaya min cewar maimakon yawan
ambaton Inna da yawan maganarta mu rinka
yawan yi mata addu'a kawai.
Zuba min idon da yayi yana kallona shi ne ya
kara tabbatar min da cewar ni yake sauraro, don
haka cikin natsuwa da ladabi sai na buda baki
nace mishi Baba tafiyar ta Inna ta fara nisa duk
da a lissafi ne kawai Inna ke da shekara guda a
yanzu in a kewa da kadaicinta ne mun kai wani
matsayi da ba zai yiwu mu kwatanta ba.
39
Duk da haka shekara gudan lisafin ma lokaci
ne mai tsawo da yawa in ban da tafiyar tata bata
dawowa ba ce da yanzu ta dawo ko kuma damun
soma sa rai da dawowan nata.
Cikin natsuwa ya ce min eh, Maryam ai tafiya
taia wata irin tafiya ce da dadewa bai sawa a
dawo da dadewa kansa a dawo ai da mu ma
iyayenmu sun dade da dawowa.
Nayi maza na ce haka ne Baba, kamar in yi
mishi wata maganar sai kuma naga to bari kawai
in ja bakina in yi shiru.
Kamar in sake yin wata maganar sa kawai
naga bari kawai in ja bakına in yi shiru.
A wannan lokacinne na shiga aji shida na
Makarantar Primary na fara girmia har Babana ya
fara barina ina tafiya gidan Yayc Dijah ni kadai
don yi mata wuni. Ina matukar son awa gidanta
saboda yanda na lura na gane bata da wani
wanda take so da kyautatawa irina.
Kullum naje gidanta to bata gajiya da tattalina
da tarairayata komai na ce mai kyau ne cewa
take yi in dauka tana ganin na kwana biyu ban je
ba zata shiga aiko kanen mijinta suzo su ga
lafiyata, in kuwa naje bayan aiken nata zan
gamu da fushinta kan dadewan da nayi ban je ba
kullum a cikin yi min nasiha take tana ganin zani
aikata kuskure zata yi maza ta gyara min.
40
Yanda Yaya Dijah ke sona da ji da ni haka
shima mijinta yana ganina zai fara murmushi ina
Inna take? Zo maza ga Mamanki tazo.
Sanin da yayi kullum naje gidan Yaya Dijah
zata tasa ni a gaba da aikace-aikace har da su
hidimar girki wai kar in girma ban iya aikin
mace a gidanta ba, yasa yana ganina zai je yayi
sabon cefane ya kawo ko da kuwa ba a ranar
suke bukatar cefanen ba sai ya ce in na girka in
tafi mana dashi gida muyi amfani da shi ni da
Baba.
Ina son Yaya Dijah da mijinta ina kuma
matukar son 'ya'yanta Inna da Abbati, ina son su
irin son da ba zai kwatantu ba, saboda gani nake
tamfar su din su kadai sune dangin da nake da su
sai kuma nake kallonta kallo irin na uwa, ganinta
nake tamfar ita ce madadin Innata da na rasa.
Dangin mijinta kuma 'yan uwa saboda suna
sonta kowane lokaci kaje'gian sunanan aurenta
aure ne na soyayya, fahimta da kuma kyautatawwa
juna, don haka gidanta gida ne na farin ciki da
kwanciyar hankali, kudi masu yawa ne kawai ba
su da su amma suna cikin rufin asiri.
Ni da Yaya Dijah kamannin da ke tsakaninmu
ba wasu masu yawa ba ne, ba su wuce wadanda
zaman ciki na kasancewa shakikai ke haddasawa
41
ba, yayin da nake matukar kama da Innarmu ita
kuma kama da Babanmu take yi.
Haka nan ko a halayenmu mun bambanta
mace ce mai matukar hakuri bata kuma da
kwaramniya.
A wannan lokacin saboda na riga na fara yin
wayo na fara fahimtar me nake ciki sai na zama
babu abin da nake so nake fata da buri irin in
ganni nayi haddar Alkur'ani mai girma a dalilin
kullum sai Malaminmu na Alkur'ani yayi mana
bayani kan falala, girma da kuma darajar
mahaddata Alkur'ani a ranar alkiyama su da
yayensu.
Sai na zamo ina matukar kwadayin nima
iyayena musamman ma Innata da nake rayuwa
cikin tsananin kewarta da begenta su samu irin
wannan matsayin a gobe kiyama.
Kowane lokaci a cikin taka tsan-tsan nake na
kauce wa aikata laifi musamman yin karya da
duk wani abin da Mallaminmu ya ambata cewwar
laifi ne don in samu in zama ya ta kwarai
saboda ya ce mana ya'ya na kwarai suna daga
cikin sadakatul jariya da mutum ke bari a duniya
wanda ladansu ba su yankewa a gare shi.
Rannan ina tare da Babana a cikin gidanmu
da daddare a kishingide yake a kan tabarma
yayin da yake jan carbinshi a hankali cikin
42
natsuwa idanuwanshi a kaina suke tare da
natsuwar shi saboda sauraron haddar da nake
kawowa na suratul 'ANKABUT".
Sai da na kai karshe na sake kallonshi cikin
natsuwa kan in gaya mishi abinda nake nufin
gaya mishin sai ya ce min kina da murya ta
karatun Alkur'ani Maryamu, kar ki yarda ki
daina, kar ki yarda kiyi wasa ta basirarki na ce
mishi to Baba, kan in yi wata magana sai ya sake
bani umarmi na in maimaita surar, ya ji ta dá
kyau.
Sau biyu na maimaita sannan yayi murmushi
ya ce a'a lalle hadda ta zauna sai kiyi ta tilawa
kar ki yarda kina yin sake don shi Alkur'ani
kana barinshi sai shima yayi nesa da kai, don
haka ki dage da tilawarshi. nayi maza na ce to
Baba. Yi mana addu'a, na sake cewa to nayi
muka shafa sannan muka je muka kwanta.
Rannan da safe muna aikace-aikacenmu a
gida ni da Babana kafin ya fita kasuwarshi nima
in tafi Islamiyyata tunda ranar ta Asabar sai naji
ya ce min ni Mero ba ki iya komai ba ne cikin
girke-girken da ki ke cewa 'yar uwarki tana nuna
miki?
Nayi maza na bar abinda nake yi na kalle shi
Cikin natsuwa da zumudi na ce mişhi Baba duk
abincin da nake zuwa da shi gidan nan fa ni nake
43
yi Yaya Dijah zama kawai take yi tana kallo in
taga zan yi wani abu ba daidai ba ta gyara min.
Shiru yayi yana kallon wuri guda nuna alamar
a cikin tunani yake, na bar abinda nake yi na
sake kallonshi tare da tambayarshi mene ya
faru Baba? Kaji miyar bata yi dadi ba ne?
Yayi maza ya gyada kai uh'uh ba haka ba ne
Mero tunani dai nake yi na in har ke ce da gaske
ki ke yiwo mana wannan girkin to ai gara in
hutar da wadannan yan uwa namu da suke ta
faman dawainiya damu shekara guda har da
wasu watanni tunda mahaifiyarku ta rasu ba su
taba hutawa da hidimarmu ba.
Don haka in har za ki iya to sai in sauke musu
nauyin girkinmu su rinka.yin nasa kawai in rinka
kawo cefanenmu kina yi mana.
Nayi maza na ce eh Baba gara kawai muyi
hakan can cikin zuciyata murna nake yi da
zumudi saboda babu abin da nake so nake kuma
sha'awa irin in ganni ina girki ni kadai ba tare da
ana nuna min ba wai ni a dole na iya.
Wannan maganar da muka yi da Babana bata
wani dade ba don ko kwana bakwai bata yi ba,
naje karbo cefane kamar kullum yanda na saba
ni ke zuwa wurin shi in karbo cefanen kayan
miya gami da su manja ko man gyada da maggi
44
in kai ma Babah Sumaye shikuma Baba Hodijo
yayi abin da ya saura tare da hatsi.
Ina tsaye ina jiran ta gama hada min in dauka
in kawo mata sai kawai naga ya miko min ledoji
guda biyu, ungo ki kai mata daya ke kuma ki
girka mana daya.
Gabana ya yanke ya fadi tamfar dai' ba ni ce
na ce mishi na iya girkin ba. Zaro idanuwa nayi
ina kallonshi yayin da shi kuma ya ci gaba da yi
min bayani, na riga na yi wa Mallam Hodijo
bayanin komai, don haka kaiwa ita uwar taki
kunshi daya ki rike daya.
Kije ki girka mana abinda ki ka san shi ki ka
fi iyawa kin gane ko? Na ce mishi to Baba, na
kamo hanya ina dawowa gabana sai faduwa yake
yi ban taba yin girki ni kadai babu wani babba a
wuri ba hasalima kafin rasuwar Innata bana
shiga kicin da sunan ya yi girki ko da kuwa na
wasa ne.
Babah Sumaye ta zubawa cefanen ido tana
kallo yanzu nan bawan Allahn nan da gaske yake
yi sai ya raba girkin nan? Ta dan gyada kai tare
da fadin to ai shi kenan tunda haka ya gani
daya,
amma menene'? Ai mun riga mun zama
dan abincin da a ke sa mishi guda nawa yake?
Ban da haka ma kullumn fa cefanen nan a
wurinshi ake karbo shi amma ya ce wai
45
dawainiyar da ake yin tayi yawa, ni dai nafi
zaton ko subutan bakin da nayi na ce a gaya
mishi ga wata bazawara na saman mishi ne duk
ya kawo hakan.
Ni kuma ba nayi hakan ne don na gaji a sa
mishi tuwo ba a'a ko kadan ba haka ba ne nayi
mishi tallan bazawarar ne don ganin hankalinta
da natsuwarta shi kuma yana ta zaune a haka yau
kusan shekara daya da rabi da rasuwar Ramatu,
wanda wasu da kyar suke jira ayi arba'in sai
kawai ka ji sun daura aurensu.
Yanda dama ban san anyi wannan magana da
Babah Sumaye ta rattaba min ba haka a yanzun
ma da ta rattaba min ban nuna naji ko na gane
inda Zancen nata ya nufa ba, balle in furta wata
kalma.
Sa hannu kawai nayi na dauki leda guda daya
na juyå da nufin fita daga gidan saboda nima ban
san dalili ba sai naji maganar ta dan sosa min
zuciya ina fita daga gidan dai ina jinta tana cewa
bai fahimce ni ba ne, ban gaya mishi hakan don
ban damu da rashin da aka yi ba sai dai don
sanin da nayi cewar yanda duk muka kai da son
Ramatu to babu yanda za muyi tunda ta riga tayi
tafiyar da babu dawowa a cikinta sai dai kawai
muyi ta binta da addu'a.
46
Ina shiga gida na juye kayan cefane na kama
wankewa sai da na gama tsaf naja na tsaya ina
kallon kicin din wanda rabon da a girka wani
abinci mai muhimmanci a ciki har an, manta sai a
lokacin ne kuma naji na dibibice na rude na rasa
ta ina ne ma zan faro?
Na zubawa murhun ido ina tuñanin yanda ma
za a yi in hada itacen su kama su zama wutar da
zata kama ta girka abincin da zai nuna zama
tuwon da za a ci.
Tsawon lokaci ina tsaye a wurin nan ina
tunanin ta inda zan faro sai ga Jumare ta shigó da
saurinta. Babah Sumaye ce ta ce in zo in ga
abinda kike ciki da cefanen da ku ka zo da shi in
taya ki girkin da za ki yi.
Nayi maza na ce mata gashi nan saboda
taimakon nata yazo min ne a daidai lokacin da
nake bukatarshi.
Duk da taimakon da Jumare ta kawo min da
aiken da Babah Sumaye tayi-tayi na ayi kaza kar
ayi kaza abincin