Showing 18001 words to 21000 words out of 26864 words
ganina warki
ce daidai nake da mazaunan kowa.
Ki min sata ki ce kar in yi magana? Inaki ka
min sauran kudin? Sau nawa kina yi min sata ina
91
kyale ki? Eye? Haka kawai ni da gidan mijina
kin takuramin kin hana ni sakat kin ishe ni da
fitina wai a kanki ke kadai a ka fara maraici ne?
iye ta sake rufe ni da wani irin duka har ina
fitsari a jikina amma bata fasa ba.
Sai ga Babah Sumaye ta shigo kai haba wace
irin musiba ce wannan? Wannan wane irin duka
ne da bai karewa haka? Haba yarinyar nan kin
san tana nan fa ki ka aurar mata ubanta kin kuma
zo mata gidansu kin tasata a gaba da masifa
bayan ke ga taki kin kawo kina rike da ita a ina a
ke haka ne dan gida ya wulakanta agola ya
zauna lafiya in ban da wurin azzalumai irin ki?
To ki. rama mata mana tunda kin shigo da
kanki shugabar munafukai.
"Ba zan rama mata ba zamani ne zai tantance
komai shi ne zai yi dalilin da sakamako zai hau
kanki don ba za ki dauwama a haka ba."
Bakin cikina ne zai kashe ku munafukai
mijina kuma ba ku da yanda za ku yi dani a kan
shi yana sona. Babah Sumaye ta ce, wane bakin
ciki za a yi da ke Lantana? Matar da ta gama
rayuwarta a gwagwarmayar rashin gaskiya, yau
ana nan gobe ana can duk in da a ka je din kuma
sai an yi cinta? Menene naki ba a sani ba? Har
dakin da ki ka zauna ki ka haifi shegun 'ya'yanki
an nuna min, babu wani abinki da ban sani ba,
92
wai ma Mallam Habun muna nan muna yi mishi
addu'a Ubangiji ya fitar da shi daga halin da
yake ciki, ya bayyanar mishi da ke ya gane
asalinki, ki kawo shegiyar yarki gida ta sake
amma ki hana yarinya sakat, to ana me ina
dalili? Ta juya ta fita ta bar Babah Lantana tana
fadin ai tunda ki ka kulla min irin wannan
sharrin to hukuma ce kawai za ta raba ni da ke,
za kí san kin iya sharri.
Tana kuka tana kurma ashar ganin da nayi
Babah Sumaye ta fita ta bar ni da ita cikin
wannan hali yasa nima nayi maza na fita na bar
gidan saboda ban san abinda zata yi min ba in ta
dawo hankalinta ta gane ni ce a zaune kusa da
ita.
GidanYaya Dijah naje tana ganina ta soma
kuka me ki ka yi mata tayi miki wannan azabar
kai yau kan abin ya ishe ni haka da sauri ta aika
a kira mata Yaya Ibrahim, yana shigowa ya
ganni tun kafin tace mishi komai ya zuba min
ido yana kallonä wai me kike yi wa matar nan
ne?
Saboda Allah me zata yi mata? Tayi tambayar
cikin yanayin kuka, a'a zata yi mata mana haka
kawai zata yi tayi mata irin wadannan abubuwan
ne wane irin mugun hali ne haka? Shi halin dan
wani da uwar wani kuma ai sai a hankali sannan
93
ba ka marawa naka baya ko da kuwa zaluntarshi
ake yi musamman idan ka san shi ne karami shi
yasa nake yawan gaya miki ita uwa ki ninka yi
mata fada kina nuna mata muhimmancin ta rinka
girmamata.
Kalaman Yaya Ibrahim ne suka yi matukar
rage karfin fushin Yaya Dijah amma duk da
haka sai ta nemi izininshi don muje gidan tare.
To babu laifi amma ban yarda in kin je kiyi
fada da ita ba, kiyi magana da ita cikin natsuwa
don kiji abinda ke faruwa cikin natsuwa da nuna
girmamawa gare shi ta ce to.
Duk da mummunan karbar da Babah Lantana
tayi wa Yaya Dijah tabi umarnin mijinta nata
tabi al'amarin a hankali.
Ina wuni? Ta kalleta a lalace au gaisuwa za ki
tsaya yi ai na dauka za ki rufe ni da duka ne
kawai, ban zo dukanki ba amma nazo ne in ji
laifin da take yi miki kike yi mata irin wannan
azabar, a'a aha aji kawai abin zai tsaya ai na
dauka za ku yi fushin zuciya ne dawo da uwar
taku kawai, haba yara kun tasa ni a gaba sai ka
ce ni na kashe muku ita a yi min sata a hana ni
yin magana.
Yaya Dijah ta kalleta a lalace ta ce me ki ke
dashi da uwa zata satan miki? Ke da kika tare a
gidanmu ko gadon kwanciya ba ki da shi a kan
94
gadon uwarmu fa ki ke kwanciya duk wani abin
da yake gidan kuma nata ne har yanzu ban ga
naki ba. Gorin da ki ke yi mana kuma na mu
tono ta to ba zamu tonota ba don bamu taba
ganin in da aka yi hakan ba sai dai kema za ki je
in da taje din da ana tonowa kuma to da mijinta
ya riga kowa tono ta don da bai kwaso ki kin zo
kin addabe shi kin addabi iyalinshi da
makwabtanshi ba.
Ta tashi zata fita daga gidan yayin da Babah
Lantana ke ta faman zagnta tana hadawa har da
Innarmu da Babah Sumaye tare kuma da jaddada
ita ubanmu ma ba tsoro yake bata ba balle wani
can banza a banza.
Yaya Dijah ta ce tunda mijinki ma ba komai
ba ne a wurinki ai kowama lada ne sai dai kanki
ki ka yi wa tunda miji ai aure ne aurenki ki ka
wulakanta mai auren kuma ya tanadi maganin
irin ku, mara mutunci wacce bata san a
girmamata ko mu din kuma ba tsoronki muke yi
ba kina cin darajar ubanmu ne kawai."
Nabi bayanta ta shiga gidan Babah Sumaye ni
kumana zauna a kan dakali ina jiran fitowar tata
tun da yanzu bana shiga gidan.
Babana yana dawowa ta kwashe bayani na
karya da gaskiya duka ta gaya mishi gaba daya
maganganun da Babah Sumaye ta gaya mata da
95
na Yaya Dijah ta hada duka ta ce Yaya Dijan ce
tayi mata su.
Babana yayi fushi mai tsanani wai ta raina shi
ne yasa ta iya buda baki ta 7agar mishi matarshi,
in ba haka ba ai matarshi uwarta ce da sai ta kai
mishi karar abinda ya farun taga abinda zai yi,
kan wannan maganar sau biyu Yaya Ibrahim ya
rako Yaya Dijah suka baiwa Babana hakutri, sai
ya ce wai shi ya wuce a wurinshi amma sai an ba
Babah Lantana hakuri tukuna ita kuwa Babah
Lantana da aka bata nata hakurin sai ta ce to ya
wuce amma daga yanzu babu sauran mu'amallah
a tsakani.
A wannan lokacin saboda tsabar samun wuri
ba Asabe kadai ba 'ce a gidanmu har da wanta
Sallau wanda gansamemen saurayi ne sosai, sai
kawai a ka bude mishi daya dakin aka sanya
mishi sabuwar katifa, shi kuma Babana ya zama
bai da wani wurin da zai dan shiga ya rauna sai
dakin Babah Lantana kawai da wannan gırma
nashi kuma bai hana shi ma ya dora hannu a
jikina ba da sunan dukan wai shi ma ina yi mishi
laifi.
Rannan na fito waje ina zaune kan dakalin
kofar gidanmu, kuka nake yi saboda al'amuran
sun ishe shi wahala tayi min yawa duk wani
taimako da da a ke yi min an daina gaba daya
96
makwabta sun fita harkata saboda kowa haushin
Babana da dabi'arshi ta fada a kan mata a ke ji a
kan kuma rashin gaskiya.
Na shagala babu abinda nake yin sai kukan ta
hanyar sharbe yayinda na sunkuyar da kaina
kasa ina kallon 'yan yatsun hannuna ban ji wani
motsi ba balle in san wani yazo in da nake sai da
naji ya buda baki yana tambayarta ke Maryam
me ya same ki ki zama haka?
Nayi maza na dago kai na kalle shi duk da na
dade bana ganinshi, kallo daya nayi mishi na
shaida shi, Mubarak ne ya girma yayi kyau
gayenshi yayi matukar karuwa sai kamshi yake
yi.
Nayi maza nayi shinu saboda ganin irin kallon
da yake yi min me ya hana ki tafiya Makaranta
yau Talata? Baniya ce mishi komai ba saboda
ban san me zan e mishi ba, tashi ki shiga gida
kije kiyi wanka ki wanke kayan jikinki kar kuma
in sake ganinki a gida a ranar karatu kin ji ko?"
ban ce mishi komai ba ya wuce ya tafi bayan ya
ga tshina zuwa cikin gida.
Tun daga ranar ban sake fitowa waje na
zauna ina kuka ba sai dai in yi zamana a zauren
gidanmu ranan ma ina wani kukanne a cikin
zauren a dalilin Babah Lantana ta ce wai tana
97
shirin duba ni saboda ta gane na fara bin maza
shi yasa babu halin ta aike ni sai naje na dade.
Ban san yanda aka yi yasan ina cikin zauren
ba sai ganinshi kawai nayi yana tsaye a kaina,
yau ma kuka ki ke yi? Yayi tambayar cikin
natsuwa yayinda fuskarshi take daure sosai wai
me ke faruwa ne a gidan nan naku? Ban ce mishi
komai ba ban kuma daina kukan da nake yi ba.
Yau ma ranar Makaranta ce ba ki je ba jiya,
na ce makarantar taku ban same ki ba
Malamarku ta gaya min ba kasafai ki ke zuwa
ba, nayi magana aa Ummana ta bani wasu
labarai marasa dadi a kan matar Babanku kar ki
yarda ta hana kikaratu ungo wannan ki share
hawayenki ki fyace majinar da ki ke mayarwa
ciki kina shanyewa.
Nabi umarnin da ya bani nasa halu karba
na kai hancina, kamshi mai dadi irin kamshin da
ke tare da shi ne, ina gama fyace majinar yasa
hannu ya karbi hankicin ba tare da ya ji kyamar
majinar tawa ba ya miko min ledar da ke
hannunshi karbi wannan kici yanzu ina kallo
nasa hannu na karba ba tare da nayi musu ba,
saboda sanin alakarshi da Innata shi da Mansur.
Iyaka dai na dade sosai ban ganshi ba na
kuma san yana canne wajen hidimar karatunshi.
98
A sanina sanda Mama take raye kina cikin
wadanda ake yi wa kyautar tsabta a makaranta to
don me kika yarda ta maida ke haka? Ga ki da
kokarin karatu duk kin daina, ai ba ayin haka ita
rayuwa ai bata tabbata a wuri daya komai
canzawa yake yi, wani mutumin da ya yi wa
rayuwa irin fahimtar da yayi mata ma sai ya ce
Tt is the law of nature and condition of all thing
for all things are craselessly changing. Komai
da ki ke gani zai wuce wata rana kuma sai
labari.
Kalamai masu dadi har ban san sanda na
Cinye mneat pie din da ya kawo min tare da lemon
gwangwanin, ba gashi kuma dama ya same ni
cikin bukatar abin saboda ko karyawa dama ban
yi ba.
Natsuwa tazo cikin zuciyata har ña fara baiwa
Mubarak amsar tambayoyin da yake yi min, ni
kina aji nawa ne? na ce biyu, to ki shirya gobe
zan tsaya a kofar gidanmu don in ga wucewarki
da safe kin ji ko?
Na ce mishi to, yanzu shiga gida kiyi wanka
ki wanke wannan kayan jikin naki ki daina zama
cikin kazanta ba ki ga yanda ki ka zama ba ne?
ban ce mishi komai ba na mike na shige cikin
gidan, sai dai wanka da wankin da ya ce in yin
99
ba su samu ba, a dalilin wai ba za ta bani sabulu
ba.
Rannan tun dare nayi wanke-wankena saboda
in samu damar tafiya makarantar da wuri, amma
da garin ya waye a kaga ina shiri sai a ka sake
taro min wasu kwanukan da ban ma san ta inda
suka fito ba, na gama shara da wanke bayan gida
nazo na same ta cikin ladabi na ce a bani abin
karyawa in na dawo daga Makaranta zan yi
sauran aikin.
Da sauri ta juyo tana kallona da wani
bawanki ne a gidan zan da zai yi miki aikin?
Na tsaya ina kuka saboda ganin Babana a
wurin ko zai tausaya yasa baki cikin maganar,
sai kawai naga ya tashi ya shiru takalmanshi ya
suri kwandonshi ya fita aimar wai wajen
tumatirinshi zai tafi.
Ganin haka yasa na bar kukan da na fara na
sunkuya nasa hannu da nufin daukar
fatattakakkiyar jakata in tafi saboda in bi
umarnin da Mubarak ya bani sai naji ta ce ai kin
bar kukan ne munafuka? To ai babu inda za ki
sai kin je kin yi min wanke-wanke nan.
Na ajiye jakar a tsakar gidana kama yanke-
wanke, sai kawai naji muryar Mubarak daga
cikin zauren gidanmu yana kwala min kira.
100
Da sauri Babah Lantana ta.fito tana tambayar
waye a nan? Waye ne mai keta min haddin cikin
gida? Suna hada ido da shi taja ta tsaya tana
kallonshi tare da sharbebiyar bulalar da ke rike a
hannunshi yana gaisheta yana kallona.
Tayi maka laifi ko? Ya ce eh, Makaranta nace
taje bata je ba, a to ai ga ta nan, ta wuce ta tafi
dakinta. Daga inda yake din ya kira ni, na taso
na tafi bayan na wanke hannuwana da kafafuwa,
bata kula ba saboda watakila tayi zaton dukan
zai yi min tunda ta ganshi da sharbebiyar dorina
a hannunshi.
A zauren gidanmu ya tsare ni babu alamnar
wasa a tare da shi na duba naga bulalar Baah
Lantana bata gama karasa girman tashi ba,
amma irin jin jikin da nake yi in tayi min duka
da ita to balle kuma wannan.
"Me yasa nace kije Makaranta ba ki je ba?"
ban 6oye mishi komai ba, nayi mishi bayanin
komai don tsoron kar ya ce na raina shi yayi min
duka.
"To wuce muje na." na wuce muka je din,
shagon unguwarmu ya kai ni ya saya min sandal
da littattafai da biro ya kuma kawo sule biyu ya
bani "Ki ci abinci a Makarantar, ki kuma yi sauri
kar ki tsaya a hanya." Na ce mishi "To."
101
Sanda na dawo daga Makarantar hana ni
abincin da Babah Lantana tayi bai wani daga
min hankali ba, saboda a koshe sosai na dawo
gida.
Tun daga wannan lokacin karfe bakwai da
rabi nayi in Mubarak bai ga wucewata ba zai
tako yaZo zauren gidanmu ya tasa ni a gaba ya ce
in wuce in tafi Makaranta, komai kumaa na
Makarantar yi min yake yi, kan ka ce meye
wannan? Sai ya zama shi ne babban abokin
gabar Babah Lantana.
Kusan kullum sai ta kai maganarshi wurin
Babana, wai yayi misi kashedi a kaina don
lalata ya' yan mutane yake yi, Asabe ma wai ta
ki yarda dashi ne yasa ya rabu da ita ya dawo
kaina. Sai dai ban san dalili ba, bai ce mata
komai ba, nima bai taba yi min Wa magana ta
kashedi a kan shi ba, ban kuma zaci ya taõa
tunkarar Mubarak din da maganar ba.
Rannan ina zaune a dakina ina jin Babah
Lantana tana cewa Babana waidama ya bayar da
rikona ga dangin uwata da suke raina mishi
kokarinshi a kaina, ko ma don ya ga uwar da za
su yi min tunda shi basa ganin kokarinshi.
Ya ce, mata a'a inda duk zai zauna zai zauna
tare dani, ta tabe baki ta ce, ai sai kayi ta zama
da itan tunda baka jin shawara, yar
102
kankanuwarta da ita maza sun fara yaudararta da
abubuwa tana binsu kana kallo an baka shawara
ka ki dauka, in ta zama budurwa kuwa tafi
karfinka taje ta dauko maka abin magana babu
ruwana, tunda ko a yanzun wannan yarinyar ai
ba na zaton in nayi rantsuwa a kanta nace ba
budurwa ba ce zan yi kaffara.
Bai dai ce mata komai ba har tayi ta gama
tayi shiru.
Ina zaune a zauren gidanmu kwarkwatar
kaina ce ta dame ni ga wasu kurarraji ma su
ruwa da wari da kaluluwowi a bayan kunnena da
keyata, ni kaina nasan ina cikin wani hali da
kwarkwatar nan saboda ko a makaranta ni
kadainake zama a benci saboda yara guduna
suke yi kar in sa nusu kwarkwata.
Don ba ta buya ba yanzunnan ne za ka ganta
tana bin jikina ko rigata ko hijabi ban da haka ga
bashin da nake yi, kan haka sai ya zamo min jiki,
duk inda na zauna in yi ta tsigota ina kashewa.
In kuma a cikin mutane ne nasa hannu cikin
sa'a na kamo ta to sai kawai in saketa a kasa
cikin hikima ba tare da na tsaya kasheta ba kar
wani ya ganni.
Ina zaune a zaure susa nake yi da hannayena
duka saboda dadi har yawu yana diga daga
103
bakina, jifa-jifa kuma in na kamota sai in sata a
kasa in kashe tayi kwas, na shagala ban san
lokacin da ya shigo ba sai kawai idona ya kai
kan kyakkyawar kafarshi da ke cikin wani
kyak.kyawan takalmi budadde, wato open shoe
A hankali nabi tsain kafar tashi da kallo zuwa
jikinshi har kawó kan fuskarshi, da sauri na
sunkuyar da kainà kasa daga dukkan alamu
kuma na abinda na gani a fuskarshi ya dade a
wurin yana kallon abinda nake yi.
Shi ke nan shima zan rasa shi shima zai fara
guduna yana jin kyamata a dalilin tsananin
kazantata ga kwarkwata kamar yanda sauran
yara da nutanen gidannu suke kyamata, na
mika haninu a hankali na jawo kazamin
dankwalin nawa na sake kulle cukurkudadden
kan nawa ban yarda na sake dsoa ido na kalli
fus karshi ba, fatana kuma da burina bai *e na
inga kafarshi da ke kusa dani ta motsa ta bar
Wun n ba.
Ba zan yarda in sake hada ido da shi ba, abin
da zuciyata ke raya min ke nan.
Wanke hannunki kici abincin da nazo miki
da shi. Cikin wata irin murya mai sanyi yayi
min wannan maganar, ban motsa daga yanayin
da nake ciki ba saboda wani 1irin yanayi da na
smau kaina a ciki na tsananin jin kunya.
104
Tashi mana kije ki wanke hannun." Na ce,
"To. Na mike da nufin in na shiga gidan ba zan
sake fitowa ba, sai naji ya ce, Ko kuma muje
gida kawai." Naja na tsaya kaina a sunkuye na
ce, a'a sai dai iyakar abinda zan iya yi ke nan
tunda shi ne a ta kusa da kofar shiga gidanmu.
Uh'uh ki ka ce min? za ki yi musu daru ne'?
cikin natsuwa ya jero min tambayoyin ban san
yanda aka yi ba sai kawai naga na juya na kama
hanyar zuwa gidan su Mubarak.
Ba wani nisa ne sosai a tsakaninmu ba, sai dai
duk da haka ba zan iya tuna rabon da in shiga
gidan ba, watakila ma tun Innata tana raye.
Sashin gaban gidan shi ne bangaren da
Mubarak yake, amma bai tsaida ni a nan ba can
cikin gidan ya wuce da ni wurin Ummanshi, tana
ganinmu ta saki murmushinta mai ban sha' awa,
Ahmad Mubarak bai fita ba ne?
Cikin natsuwa ya ce mata, Na fita Umma
dawowa nayi, to sannu da dawowa, Ubangiji ya
Rara shiryar mih da kai ya kuma yi wa kokarinka
albarka. Yayi murmushi amin Umma, Umma ba
ki ga Maryam ba ne?
Umma ta sake kallona, Maryam? Cikin nuna
alamar tunani kan ya ce mata komai kuma sai ta
kama salati, uwa ce wannan? Yayi maza ya ce
mata eh Umma, ta zuba min ido tana kallona tare
105
da jinjina al'amarin yanzu Meron Ramatu ce ta
zama haka? Cikin sauri ya sake cewa, eh Ummna.
To Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa ya ce
amin Umma.
To zauna mana, ta nuna min wuri nabi
umarnin da ta bani. Umma! tayi maza ta ce
na'am Ahmad Mubarak menene?
Sha'awar mu'ammalarsu tayi matukar kama
ni cikin zuciyata, na ce nima da Innata tana nan
da haka zamu rinkayi da ita.
Umma kan yarinyar nan nake so ki duba ki ga
wani abin mamaki, naji kamar in ruga da gudu
don tsananin kunya, da énsan abinda yasa ya ce
in zo gidansu ke nan da ban yarda na biyo shi ba.
"Muga kan naki Maryamu. Na dora hannu a
kan nawa cikin yanayin sanyin jiki sai dai ban
iya kin bin umarnin da ta bani ba, zuba ido tayi
tana kallon kan nawa babu alamar damuwa a tare
da ita, ki duba ki gani Umma wai kan mutum
mai rai ne wannan.
Umma tayi murmushi ta ce, eh ai babu komai
anyi yafi haka maraici babu abinda bai sanyawa,
wata rana kuma sai labari.
Ya ce, Haka ne. suka dan yi shiru yayi: da ni
kuma kaina ke sunkuye, 'yan mintoci