Showing 15001 words to 18000 words out of 26864 words

Chapter 6 - Halin Rayuwa Book 1 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

124

da irin wannan kace-
nacen ba, ba kuma zan yarda in saba da su ba, a
yanzu da girmana da komai. Gaskiya ne Mallam,
wannan maganar taka ita ce gaskiya in ban da
rashin hankalinta ita wannan yarinya ai 'yarta ce
yanzu ita marayunne da ita ba hawa-hawa?
Ga nata na kanta ga kuma na yarta da su
kuma babu uwa babu uba, to don me ba za ta
rike wannan da kyau ba, shi al'amarin duka ai
yiwa kai ne, kayi hakuri in naje gida kuma zan yi
mishi bayanin da kayi min duka.
To na gode Yaya, in ji Babana, ina ita uwan
take? Babana ya kwala min kira saboda jin Delu

77

tana kirana, don haka na fito nazo na durkusa na
gaishe su, uh'uh uh lalle yarinyar ta zube amma
ba ka ga kamar har da macijin ciki a ciki ba
Mallam?
Ina ganin a nema mata maganın macijin
cikin, ka san shi shegen abu ne sai yayi ta ci a
ciki ba a sani ba šai dai ayi ta tsotsewa ana
motsewa a tsaye ba a kwanta ba, tana maganar
tana tafiya bayan tasa hannu biyu ta karbi abinda
ya bata na alheri tayi godiya.
Bho Kwana biyu bayan dawowan Babah Lantana,
Babana bai sake mata ba, itama kuma ta shiga
Cikin natsuwarta sosai.
Rannan sai ga Delu tayi sammakon dawowa
tun Babana bai fita kasuwarsh1 ba, suna gaisawa
naji tana ce mishi maigidanne ya ce in zo in kara
duba ku in kuma kara baka hakuri don babu
abinda ban gaya mishi ba da na koma ranshi ya
baci sosai hankalinshi yayi mummunan tashi ya
ce wannan ai nema take ta zubar mishi da
mutunci.
Ya dan yi murmushi kadan are da fadin a'a
haba, ai ba a haka ka hukunta wani kan laifin da
wani ya aikata maka ba adalci ba ne, ita kam
mace ai dama kowacce da irin halinta ba a kuma
yin shaida a kanta iyaka dai kawai akwai wacce
tafi wata dama-dama.

78

Haka ne Mallam, suka ci gaba da yan
hirarrakinsu irin na surukai kafin yayi mata
sallama da cewar zai tafi kasuwa ta sake sa
hannu biyu ta karbi alherin da ya bata tare da
godiya.
Sai dai yana barin gidan ta juya wurin Babah
Lantana, uh'uh'uh kai wannan miji naki da
taurin kai yake, bai rusunawa kan ra'ayinshi, ga
shi da kafiyar tsiya bai kuma damu ya fadi
abinda ke ranshi ba, ko da kuwa yasan hakan zai
iya batawa wani rai.
Babah Lantana ta ce, Uhun, ai ba ki ma sani
ba, tunda muka dawo din nan fa bai saki jikinshi
da ni ba, ba ya ma yarda ya hau gado ya kwanta
sai kawai yayi shimfidarshi a kasa.
To me ki ka ce mishi? Zuba mishi ido kawai
nake yi in na nuna mishi na damu ai sai ya rinka
yi min irin wannan wulakancin. Ai ke ce ma
Lantana da wautarki ba ki tàbbatar kin kama shi
a hannunki ya kamu ba za ki fara kawo mishi iya
shege.
Wannann aiiya shege ne, don me za ki tasa
mishi 'yarshi a gaba? Tasata nayi a gaba Dela?
Babah Lantana ta taso, Delu ta ce, ai ke dama
haka ki ke, in mutum ya ce zai gaya miki gaskiya
sai ki zabura ki ce za ki yi fushi don ba kya
Sonta.

79

Wannan kuma a kan wannan yar tash1 in ba
ki yi hankali ba komai ma zai iya faruwa, kar ki
ce ba komai ma zai iya faruwa kar ki ce ban gaya
miki ba, yanzu dai ga wannan shi wancan
mutumin ne ya ce a kawo miki ki samu gero
kwaya bakwai ki hada da wannan garin maganin
ki make shi a gefen bakinki sanda ki ka tabbatar
kin shawo kanshi zai kula ki sai ki kwana da shi
gari in ya waye sai ki juye har da yawun baccina
faranti ki shanya shi a dakinki kar rana ya taba,
sai ya bushe sai ki dake shi lukui-lukui shi za ki
rinka zuba mishi a abinci da komai ma ko da
kuwa ruwan da zai sha ne.
Ta ce mata to, Delu na gode babu kuma
addu'ar da za a yi ko? Da sauri ta ce, a'a za ki yi
addu'a mana kar ya ji kar ya gani, abinda za ki
rinka fada ke nan tayi maza ta sake yin godiya.
Delu da kanta tazo ta samu Babana ta roke
shi wai ya yi wa wata yarta da ke gidan miji
taimakon ta samnu zaman lafiya da mijinta,
saboda kullum a cikin barazanar korarta yake, ga
ta kuma da kananan 'ya'ya har guda biyar.
Ina jin Babana yana gaya mata cewa in ban
da kananan 'ya' yannan da a ka ambata ba zai yi
ba, don mata ba wani kirki ne da su ba, suna
samun kan namiji to su kuma sai rashin imaninsu
ya tashi.

80

Delu ta ce ina za a yi haka Mallam ita da take
neman yanda za a yi ta zauna a kan 'ya'yanta?
To a dai gaya mata in ta samu yanda take so ban
yarda ta zalunce shi ba, in kuwa tayi haka ita da
Ubangiji da sauri ta ce zan gaya mata Mallam, ai
don ma ba ka santa ba ne.
A kan idona Babana ya rinka yin rubutu a
jikin allon karfen shi yana wankewa sai a bayan
idonshi in ga Babah Lantana ta kafa kai ta
kwankwade shi tas.
Ni ina kallo ko Yaya Dijah ban taba gayawa
ba, balle wani can daban saboda kullum naje
gidanta ta ganni sai tayi kuka 'yar magana ba
mai tsanani ba in na gaya mata itama tayi ta kuka
don haka na koyi kame bakina.
Ban kuma tabbatar jagwalgwalo da aikin da
yake yi wa kanshi ya kama shi ba sai a ranar da
nake sharar tsakar gida da safe yayin da shi
kuma yake cikin dakin a kwance a kan gado.
Naga an yiwo fito da wani hoto babba waje,
gilas dinshi ya tarwatse.
Da sauri na nufi inda hoton ya fadi cikin
tsananin tsoro da fargabar kar abinda nake zaton
ya tabbata, ina daga hoton gabana ya fadi, jikina
ya dauki rawa 'shi ne hoton Innata da zamanshi
a dakin ya dade yana tukurawa rayuwar Babah

81

Lantana bata samu yancin yin yanda take so da
shi ba, sai yau.
Ina cikin tunanin Baba bai san ta cire mishi
hoton shi ba sai na jiwo ta tana ce mishi ni fa na
Cire wannan jarababben hotonn da a ka kakaba
min a daki.
Shekara da shekaru tana can a kwance har
kashinta yayi fari amma ka ajiyewa mutane ita a
wuri tana nema ta rinka yi musu fatalwa, wannan
in banda ni din ni ce ai da bata bar ni na zauna a
dakin ba, to kullum na hafa ido da ita sai na zare
mata nawa nima in kuma ce mata kurwata kur
taci kanta tasha bakinruwa.
Ban ji ya ce mata komai ba, to balle uma ni
na dai sunkuya kawai na dauke hoton na kuma
tsince gilasan da suka fashen har suma ban zubar
ba, kulle su nayi a wani tsumma naje na adana su
a cikin kayana na zauna nayi kuka sai da na gaji
na share hawaye.
Tunda Babah Lantana ta samo kan Babana ta
Kara bayyanar da kiyayyar da ke tsakaninta da
Babah Sumaye da mijinta, tun farkon zuwanta
dai dama bata yarda tayi wata mu'amallah da su
ba, sannan duk wani lokacin da wata magana ta
taso da ta shafe su za ki ji tana yawan aibanta su
ko ta kira kirkinsu da Babana ke fadi da kirkin
munafukai.

82

Nan take kuma ta shiga rattabo mishi
aibobinsu, a yanzZu ta kaima ta raba Babana da
Baba Baidu cin abincin da suke yi da daddare
ban dai san yanda a ka yi ba gani kawai nayi sun
daina. A bakin Babah Sumaye kuma naji tana ta
fadin, ai mace shu'uma ce in ka gamu da ja' ira
tosai dai addu'a kawai, amma in ba haka ba
yaushe? Yaushe za a zaci za a yi haka?
A wannan lokacin ta kai ma ko makarantata
ta boko bana samun zuwa a kan lokaci, karatuna
na Alkur'ani kuwa tuni tasa kafa ta shure shi ko
a gida ta ganni ina karatun Alkur'ani zata shiga
zage-zage tana fadin ai Ubangiji ya riga yayı
magana a kan irinku masu yi don ace su ya tashi
ni ki bani wuri, munafuka kawai.
Ni da na rayu da Innata ina wanka safe da
yamma har bayan ta ma a haka nake ina tashi
nayi ayyukana na safe zan yi wanka kafin in tafi
Makaranta in na gama komai zan kwanta ma zan
sake yi kafin zuwan Babah Lantana gidanmu na
dauka ka'idar rayuwa ne yin hakan.
A yanzu duk na daina saboda babu halin ta
ganni nayi wanka ko zan yi sai ta ce wai kishi da
ita nake yi ranan har tana zaunar da ni tana vi
min bayanin da ki ke ganina ina wanka safe da
yamma ba ra'ayina ba ne yin hakan fitinar ubani
ce ta kan sa ni, in ban da haka babu abin da zai

83


sa in yi ta jika jikina da da ki ke kwaikwayona
ke a wane dalili ki ke yin naki?
Irin wadannan kalaman nata suka sanya ni na
zamo sai in yi kwana uku hudu ban yi wanka ba
balle ayi maganar wanki ga shi a yanzu tsanin da
ke tsakanin gidanmu da na su Babah Sumaye ya
rikida ya zama wari tunda takai ma har Babana
ya kafa min dokar shiga gidan.
A wannan lokacin kuncin da nake ciki ya kai
in da yakai kusan kowane lokaci a cikin yunwa
nake yawo ga kazantar jiki da na kaya gaba daya
na hade na zama babu kyan gani.
Tuni Asabe ta dawo gidanmu a zama, sai dai
ta dawo ne a matsayin 'yar da Yayarta ta rasu ta
bari ba a matsayin ita ta haifeta ba ni da Asabe
kai daya muke a tsawo sai dai ta dan fi ni kauri
kadan saboda ta girme ni idonta a bude yake
kwarai saboda za ka ji manya-manyan
maganganu a.bakinta.
A wancan lokacin da ban san komai ba game
da al'ada saboda kuruciyata ita bata jin kunyarta
a wurinta na fara ganin ta saboda bata damu da
kintsa kanta tayi ta gama wani na kusa da ita bai
sani ba.
Tunda Asabe ta dawo gidanmu da zama
al'amura suka kara tsananta a gare ni dakina da
dah nake yawan zama a cikinshi saboda kuntatar

84


da nake yi a tsakar gidan yanzu ba ni da halin yin
hakan in ji dadi saboda ni da ita ne a ciki
gadonmu ma daya dan kankanin motsi zan yi ta
rufe ni da duka babu mai cewa ya isa balle aje ga
tambayar dalilin dukan.
Ni kuwa a kwance muke a gado da daddare to
matse ni take yi a jikin bango da kuma zan ji
tsananin yakai tsanani in dan yi motsi sai kawai
tayi min gula da gwiwar hannunta. In nayi kuka
Babah Lantana ta fito ta kare min tanadi tana
fadin ai duk bakin cikinki ba ki isa ki kori Asabe
daga gidannan ba ina zamnan ubanki ne ita kuma
tana zamana yauwa in takamar ki maraici itamna
marainiyar ce ta uwa da uba, bata da kowa sai ni
din nan da ki ke ganis
Don haka babu in da zata yauwa yarinya 'yar
kankanuwa da ke sai bakin cikin tsiya tunda
Asabe ta dawo gidannan ki ka dauki karan tsana
ki ka dora mata me ta tsare miki ne haka?
Duk abinda ke faruwa kuma Babana yana ji
amma sai ayi a gama bai ce komai ba, kamar ba
ya nan a gidan.
Tunda Asabe ta dawo gidanmu Delu ta rage
zirga-zirgan karbowa Baba Salamatu
abubuwanta sai Asaben ce mai karbowa kusan
kullum sai ka ji ta karbo nata wani lakanin
85


asirin saboda duk samun Babana da tayi bai ishe
ta ba tana neman kari.
Rannan ina daga dakina a zaune ina hangen
su Babah Lantana ce ta kama wani kii mai rai ta
shake shi yayin da Asabe ke rike da wata 'yar
kankanuwar làya da taje ta karbo mata a hannu.
Yana bude baki sai kiyi maza ki jefa layar a
ciki in ji Babah Lantana Asabe ta amsa da to.
Hakan kuwa a ka yi wahala tana isan kifin
nan ya hangame bakinshi Asabe tayi maza ta jefa
laya a ciki nan take kuma suka yi maza suka
kama balkin nashi suka matse suka sa zaren lilo
suka daure tamau. To dauki maza tun bai mutu
ba kije da sauri ki jefa shi a cikin rafin nan na
kasan layi yan uwanshi su cinye shi a haka.
Da sauri Asabe ta ce mata to, ta kuma suri
ledan da suka jefa kifin tayi waje da shi don kai
wa rafin da ta gaya mata.
A yanzu ta kai a ko a waje naga Babana ko
na same shi a wajen tumatirinshi ba ya iya sake
jiki yayi magana da ni balle yayi min wani
taimako, don haka nima sai ban cika zuwa in da
yake din ba.
Don haka a yanzu sai na zama kan dakalin
gidanmu ne wurin zamana ko kua in yi zamana a
cikin zauren gidanmu kan tsohuwar tabarmar
Innata da nake shimfidawa.

86

Rannan na samu naje Makaranta daga can na
saci jik na wuce gidan Yaya Dijah a dalilin
itama a yanzu bana tambayar zuwa gidanta a
kyale ni saboda wai ita ce take kara koya min
iya shegen da nake yi.
Ina zaune a dakin nata ina cin abincin da naje
na debo a kicin dinta yayin da ita kuma take
share hawayen da ke zuba a idonta a dalilin
zancen da take yi min ashe abin da matar nan
tayi wa Yakunbo Halima ke nan da taje gidanmu
kan maganarkı?
Shiru nayi ban amsa ba, sai taci gaba da
magana cikin tsananin kaduwa da mamaki
tamfar a lokacin ta fara jin zancen, wai ta
kawowa Yakunbo Halima diga da cebur ta ce
mata taje kawai ta tono Innarmu a inda a ka
binneta tazo ta rike ki tunda nata rikon bai yi ba
an raina?
Na ce Eh nayi shiru ta gyada kai to babu
darnuwa ba zamu je nu tono ta ba amma kowa
zai tafi inda taje din lokaci ne kawai wata rana
kuma sai labari Baba ya bada ke ya ki? Ya hana
ni ke ya hana su Yakunbo amma ya kasa hana
wulakancin da a ke yi mana a kanki na kullum
mutum ya ganki sai yayi kukan bakin ciki.
Ta dan yi shiru kafin zuwa can ta sake cewa
ko da yake dai shima ba jin dadin zaman nan

87

nasu yake yi ba, yana dai yin shiru ne kawai
tunda gaba daya ya zube Baba mai tsabta amma
duk ya zama wani iri ta soma kuka sosai.
Na mike na ce mata zan tafi, tayi maza ta bar
kukan da take yi ta koma tambayata tun yanzu?
Ki tsaya mana in taya ki tsifan kanki ayi miki
kitso. Na.ce a'a in nayi kitso zata gane na biyo ta
gidannan ta gayawa Baba.
Da sauri Yaya Dijah ta zaro ido tana kallona
Baban ya hana ki zuwa wurina ne? nayi maza na
ce mata a'a amma ai ban ce mishi zan zo ba daga
Makaranta ne kawai na biyo, da wannan bayanin
ne ta dan samu natsuwar zuciyarta ta tashi taje ta
kawo kudi ta bani nasa hannu na karba na juya
zan tafi tana bina tana yi min magana ki adana su
kina kashewa a hankali kar kuma ki rinka zama
da datti, gobe gari yana wayewa ki tsefe kanki
kije kiyi kitso na ce mata to na wuče na tafi.
A farkon zuwan Asabe gidanmu na sha ganin
Babah Lantana tana feshe mata kanta da sheltox
din da Babana ke kawowa gida saboa kashe
sauraye da sauran kwari saboda kwarkwatar da
take fama da su amma daga baya da suka yi sa'a
tata kwarkwatar ta mutu saura kuma suka dawo
kaina sai Asabe ta ce wai ba za ta rinka
kwanciya da ni a gado daya ba don kar in sanya
mata kwarkwatata a kanta.

88

Babah Lantana ta ce kwarai kuwa ina ma ake
haka me kwarkwata da mara ita su hau gado
daya su kwanta? Don haka ta bani zabi tsakanin
abu biyu ko dai in tsaya ta aske min gashin kaina
tayi min malu saboda kwarkwatar da ke kam
nawa tayi yawa ba zai yiwu a tsaya yin wahalar
taba ko kuma in dawo Rasa in rinka yin shimfida
ina kwanciya.
Ita Asabe tana kwana a gado duk da ban bude
bakina nayi zabin ba hukuncin da Babah Lantana
ta zartar min ke nan dawo da ni kwanciyar kasa
kan wata tsohuwar tabarma saboda na ki yarda
in tsaya ta mayar min da kaina tal kwabo.
A wannan lokacin ko da gaske Babana ya
daina Sona ne kamar yanda masu yaran suke
gaya min? ko kuma a'a masifar da take balbale
shi ta ita ne baya so yasa duk abinda zata yi yake
zuba mata ido ban sani ba, duk abinda take yi bai
cewa komai hakan kuma bai sa ya tsira daga
masifar tata ta bar shi ya zauna lafiya ba.
Ko cinikinshi ya kawo mata kamar yanda ya
saba in har bai kawo da yawa ba sai tayi mishi
fada gashi babu halin ya ce mata a cikin kudin
nan ayi abu kaza, sai ta ce a wane kudin? A irin
hidimar gidan nan ne wani abu zai rinka raguwa
a wadannan 'yan kudin da ka ke kawowan.

89


Kullum sai ta tasa shi a gaba ya bata kudin
cefane daga kudin aljihunshi amma kuma bata
yin girkin kullum in tayi miya guda daya to bata
sakewa ko da kuwa bata yi dadi ba sannan ko
zata kwana uku to sai ta kare kafin a sake wata.
A wannan lokacin ne na samu kaina cikih
wani irin hali da ya tabbatar min da maraicin
uwata da nake ciki na rasa Inna na rasata kuma
irin rashin da na kara ganewa cewa rashi ne
nahar abada bani kuma da mai yi min maganin
halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasatan da
nayi.
Kullum dai Yaya Dijah da su Yakunbo
Halima suna yawan gaya min cewar wata rana
zai wuce sai dai in bada labari to amma yaushe
ne wataranan zai zo? Wannan ita ce tambayar da
kullum ta ke tsayawa a raina don gani nake amar
ba zai kare ba tunda kullum abin nata karuwa
yake yi.
Ina makale a zauren gidanmu kuka nake yi
saboda bakin cikin kalamin satan da Babah
Lantana tayi wai ni na shiga dakinta na diban
mata kudinta saboda kawai tayi min bincike
cikin kayana taga kudina da nake 6oyewa ina
tsakura a hankali ta kwashe wai nata ne alhalin
Yaya Dijah da 'yan uwan Innata ke ba ni.

90

Don haka wai in fito mata da duk sauran
kudin nata ma da bata gani ba, bayan kuma ni ko
shiga dakinta bana yi ta kuma san hakan.
Asabe tazo zata wuce ni da kwano a hannunta
a rufe nayi zaton ai kanta a ka yi tana isowa inda
nake sai kawai naga ta saki kwanon a kasa tayi
maza ta kama ni tana fadin gata Babah ga ta nan
na kama miki ita.
Sai kawai naga Babah Lantana ta shigo
zauren ashe damà tana makale a kusa, hannu ta
saka ta kama ni ta rike wani irin riko mai
tsanani, ta shiga jana zuwa cikin gida ni kuma
ina ta ihu saboda sanin da nayi cewar zan sha
wahala ko daga jin irin kamun da tayi min.
Muna shiga gida ta takarkare ta sakar min
wani irin azababben dundu da yayi sanadin da na
durkusa a kasa nan take kuma tarufe ni da duka
tana kuma yi min tambayoyi ni na kashe miki
uwarki ne da za ki tasa ni a gaba da masifa? Kiyi
min sata kar in yi magana? Ni nan da ki ke
kallona ubanki ma ba tsoro yake bani ba balle
wasu can banza a banza in na gama dukan naki
kije yau ma ki nuna musu ina nan ina jiransu su
zo Su same ni don ni nan da ki ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login