Showing 9001 words to 12000 words out of 26864 words

Chapter 4 - Halin Rayuwa Book 1 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

122

da muka girkan yawanshi ba
kadan ba ne, dandanonshi kuma ba wani mai
gamsarwa ba ne ko in da aiken nata da zuwan
Jumaren wane irin kwaba zan yi? Oho.
Duk da min karbi girkin abincinmu Babana
bai daina bada kayan miya a gidan Baba Hodijo
ba babu kuma wani abinda ya canza a tsakani ni

47

kam ma dai ban daina zuwa karban abincina ba
ina shiga gidan Babah Sumaye zata ce min ga
abinci can in za ki ci jeki ki diba in ce mata to
dama kuma hakan take yi min.
Haka nan duk wani abu na kulawa da take yi
min bai sauya ba, ina dawowa daga Makaranta
wurinta nake fara zuwa in tube kayana in canza
da wanda ke nan a wanke a goge in ci abinci in
yi wanka in yi sallah in yi shirin tafiya
Makarantar allo bayan na karbo cefane na kawo.
Zan iya cewa kwanon Babana ne kawai aka
cire shi ne kuma mai cin abincin da nake
kwabawa da sunan girki sai ko yaran da nake
turawa a cikin gidan wadanda rasa uwata da nayi
ya koya min lura da sa ido wajen sanin 'ya'yan
da ba Su da uwa a dalilin suma mutuwa ta
daukan musu ita kamar yanda ta daukan min
tawa kokuma a'a sakin uwar tasu aka yi aka bar
su watse a tsakar gida.
Duk.munin abin da na girka Babana bai cewa
komai, bayan sannu da kokari sai yayi bisimillah
yayi komai uku yayi hamdala ya ce in kawar ko
in nemi wadanda zan ba, in ce mishi to in je in
kawo mishi ruwa.
Zuwan da nayi gidan Yaya Dijah ne na bata
labarin dukkan abubuwan da suka faru har da
bayanin da Babah Sumaye tayi ina ji, shiru yayi

48

Dijan tayi cikin wani yanayi na nuna tsananin
tausayi ta ce uh'uhummn, Baba ina jin
tausayinshi in na tuna Inna na tuna halin da na
samu kaina a ciki a dalilin rasata da muka yi.
Sai in tambayi kaina to shi kuma fa yaya yake
ji? Ta dan yi shiru cikin wani irin nazari da
tunani mai zurfi, jimawa kadan sai ta dago ta
kalle ni idanuwanta sun kada sunyi jazur alamar
suna shirin fara zubar da hawayc, sai ta ce min
dama yayi auren kawai zata debe mishi kewa zai
samu abokiyar mu'amallah zai kuma huta da cin
wannan danyen abincin naki da ki ke kwabawa
bakya ci nayi maza na ce ina ci mana ai ba
danyen ba ne kuma kullum ya ci zai yi min
addu'a.
A wannan lokacin zan iya cewa bani da wata
matsala ko kuma damuwa da ta wuce ta bani da
uwa mahaifiya in ban da wannan ban rasa komai
ba, ban nemi wani abu na rasa ba, Babana yana
matukar sona yana kula da ni yana tattalina,
komai nake so yi min yake yi duk wani abinda
ya ba shi sha'awa saya min yake yi.
Fura da nono, kankana, gasasshen nama,
wannan kadan ne kusan kulllum zai saya min sai
in ni ce na ce ba zan ci ba.

49

Babah Sumaye ma a tsaye take a kan
al'amarina, kitso, wanki, kula da kai, tsaftace jiki
lura da tarbiya bata gaji ya min kan komai ba.
Ga dangin Innata da kusan kowane lokaci
hankalinsu a kaina yake, don haka ina yawan
tuna Innata ne a dalilin tsananin kauna da
shakuwar da ke gare mu amma ba don na samu
kaina cikin wani hali na wahala ba.
Rannan ina tare da Babana a gida yana
kishingide yana jan carbin shi a hankali cikin
natsuwa tare da sauraron kira'ar karatuna da
nake yi a gobe, sai da na kammala komai na
maida Alkur' anin nawa mazauninshi.
Bayan na gama addu'o'ina na shafa sai muka
shiga hira da Babana irin wadanda suka shafe
mu har na shirya zan tafi in kwanta sai naji ya ce
min ni fa da wata yar shawara na ce zan yi da
ke.
Da sauri na dawo na zauna cikin natsuwa ina
kallonshi cikin yanayin girmamawa da kuma
sauraro can cikin zuciyata kuma tunani nake yi
wacce shawara ce wannan da Baba bai da mai
bashi ita sai ni?
Ban sani ba ko ganin irin yanda na tattara
komai na mayar gare shi ne yasa shi mikewa ya
zauna ko kuma a'a shi ma hakanne yaga ya fiye
mishi daidai, kina jina ko Maryamu?

50

Nayi mazana ce mishi eh Baba can cikin
zuciyata kuma na kara girmama al'amarin da
Babana ke bukatar shawarar tawa a kai tunda
yayi dalilin da yasa shi ambaton sunana na
Maryamu' tunda nasan ba kasafai ya kan yi
hakan ba, saboda kasancewar sunan nawa suna
mai girma a wurinshi.
Mutane ne suka dame ni da maganar in yi
aure, nan da nan na tuna kalaman Yaya Dijah na
cewar duk randa ya sake yi min wata magana da
ta danganci aure in yi mishi in karfafa mishi
gwiwa kan yayi auren don shi ma ya samu
saukin al'amuranshi.
Bisa wannan dalili yasa nayi maza na ce
mishi to kayi auren mana Baba Inna fa wajen
shekararta uku ne yanzu da rasuwa kana ta zaune
kai kadai yin auren kuma zai rage maka wasu
damuwowin.
Ya bar abinda yake yi ya zuba min ido yana
kallona, kalamanki ne wadannan ko kalaman
yar uwarki? Don dai nasan ba ki da wannan
nisan tunanin, ban boye. mishi ba na kwashe
hirarrakin da muke yi ni da Yaya Dijah kan
rashin auren nashi. Yana ji na bai ce min komai
ba sai zuwa can naji ya ce min to bari dai kawai
in yi tunda kuma kuna ganin ya dace in yi amma

51

in ba haka ba ni bani da wata damuwa kan
hakan.
Tunda muka yi wannan maganar Babana bai
sake ce min komai a kan maganar ba, sai kwana
goma bayan nan na kammala wanke-wanke na
kife kwanukan nazo inda yakena zauna saboda
kiran da yayi, ga ni Baba.
Nayi mishi maganar cikin girmamawa, ya
kalle ni cikin wani yanayi da na kasa tantanc
wanne ne yafi rinjaye a ciki? Maganar nan tamu
ce nake ganin kamar zata tabbatą.
Nayi maza na tambaye shi wacce magana
Baba? Yayi maza ya rage fara'ar wace magana
kuma ki ke tambayata? Nayi sa'a cikin hanzari
maganar ta fado min, don haka nayi maza nace
mishi eh Baba na tuna ta na tuna kayi hakuri.
Ya dan yi shiru kadan kafin jimawa kadan ya
ce min, akwai wata yarinya nan da a ka nuna min
tana da dan fasali kadan an kuma ce wai tana da
ya'ya biyu da mijinta ya rasu ya barta da su, to
kin ga maganar ya'ya tunda marayu' he ai nima
ga ki sai tazo mu hadu mu rike ku musamman da
yake shi maraya rike shi ba karamin al'amari ba
ne akwai falala mai yawa a cikin al'amarinshi.
Na ce "Haka ne Baba."
Tun daga wannan lokaçin bai sake min wata
maganar ba sai a wata ranar Juma'a da safe
52

bayan na dawo daga Makarantar Asuba. Na
zauna kusa dashi na gaishe shi sai yarkalle ni ya
ce min to yi maza kije gidan "yar uwarki ki gaya
mata zancen nan ya tabbata an yi daurin auren
yau da asuban nan.
Nayi maza na ce "Lah, har an daura Baba?"
ya ce, Eh uwata an daura to me za a jira tunda
dai za ayi? Ai ita din na gaya miki yanda
al'amarinta yake, don haka da ta koka min
maganar aikin kafinta saina gaya mata tabi a
hankali da tayi shawara dani ma da bata sanya
kanta cikin dawainiya ba balle har taje tana
6acin rai, don haka ta tare kawai tazo ta fara
amfani da wadannan kayan har kafin kafintan ya
bata nata sai a kwashe wadannan din.
In har da wani lokacin da naji dar ko wani
faduwan gaba kan maganar auren na Babana to a
wannan lokacin ne ban san dalili ba sai naji ban
ji dadi ba, a ce amarya tazo ta shiga dakin Innata
tanana amfani da kayan Innar tawa da dai ace
yau ne yake neman shawarata to da na ce mishi a
gaya mata kawai ta jira kawai kafintan ya gama
mata aikin nata to amma babu halin in ce komai.
Yi sauri kije ki gayawa Dijah ki dawo sai mu
dan yi kwalimar da zamu yi wa gidan kar baki
su zo su ga kazantarmu ko kuwa? Na ce mishi
haka ne Baba.

53

Gidan Babah Sumaye na fara shiga tana
hidimarta cikin kwanciyar hankali iko sai
Ubangiji yau sai a ka wayi gari da maganar
daurin auren Mallam Bukar na ce haka al'amari
yake in kaga ba a yi abu ba to lokacinshine bai yi
ba Ubangji ya bada zaman lafiya na ce amin
Baba.
A maganar da muke yi ne nayi mata hirar
bayanin da Babana yayi min.
Cikin sauri ta dago ta kalle ni anya ayi haka
kuwa? To ko da yake dai duk yanda a ka yin
daidai ne fata dai a zauna lafiya amma kuma ai
ita Halima a sanina akwai akwatinanta da nasan
akwai muhimman al'amarinta a ciki a dakin an
fita da su ne? nayi maza na ce mata a'a suna ciki
ta ce, to maza je ki ki tito da su ki kawo nan in
Dijah tazo sai ta tafi muku da su gidanta.
Na ce, Mata to, da sauri na koma gida cikin
sa'a Babana ya zaga nayi maza na fitar da su na
kai mata, haduwa muka yi da shi zai shiga ni
kuma zan fita ina rungume da hotunan Innata
guda biyu a jikina, ina za ki kai wadannan?
Cikin natsuwa na ce mishi zan fitar ne a dakin,
tsawa ya daka min nayi maza naje na maida su
nazo na wuce shina tafi aiken da yayi min.
Dawowa gida nayi na samu tuni har Babana
ya gama kwalimar da ya ce zamu yi tare, dan

54

karamin gadon bonon Innata shi ya kawo min
daya dakin wanda da na baki ne dan akwatina
kuma yana karkashinshi.
Duk abubuwan da suke faruwa ina bi ne
kawai da kallo ba sosai suke yi min dadi ba, to
amma kuma har cikin zuciyata murna nake yi
Babana zai yi aure da za a tambaye ni abinda ke
SOsa min ran kuma ba zan iya vin wani cikakken
bayani ba.
Anyi hidima su girke-girke da dafe-dafe
saboda isowar amarya da 'yan rakiyarta Babah
Sumaye ce kuma ta jagoranci duk wani abinda a
ka yi tunda shi mijinta ne ma ya zamo wakilin1
Babana da ya karbar mishi auren itama Yaya
Dijah ba a barta a baya ba, don har da sayayya
tayi ta kawowa Babana wai a kara a cikin kayan
aure.
Yayi murmushi ya ce, wane kayan aure ne
ma? Ke dai tunda kin kawo wadannan din a bata
a ce mata 'yarta ce tayi kwalliya, to Baba ta fadi
tana murmushi, ya tayata murmushin tare da yi
mata addu'ar Ubangiji yayi mata albarka, ya
kuma jikan Mahaifiyarmu da rahamarsa muka yi
maza muka ce amin.
Ban fara gane irin fasalin auren da Babana
yayi ba sai bayan da 'yan buki suka watse mukai
saura daga ni sai Babana sai ko Amaryarshi a

55

gidan, lokacin ne na soma gane wani canji ya
same ni.
Dakin Innata dakin da nan ne a ka haife ni, a
cikinshi muka yi rayuwarnmu ni da uwata bayan
rasuwarta kuma nan ne wurin zamana komai zan
yi a cikinshi nake yi sai na zamo ba ni da halin
shiga cikinshi in zauna in sake ina shiga na dan
zauna sai a ce min to je ki waje ko.
Gashi kuma daga in da duk a fito nan nake
dosa saboda kwata-kwata ban ma saba da in da
aka maida ni din ba, ga shi kuma sai nake ganin
tanfar dakin da abinda ke cikinshi duka nawa ne
ko kuma na Innata amma a ka fitar da ni a ka
sanya wata a ciki.
An wayi gari da safe ina durkushe daga bakin
kofar dakin gaishe su nake yi a cikin barin jiki
saboda al 'amarin da idanuwana suka gani wanda
ba sabawa da ganin hakan suka yi ba.
Babana na gani kwance shame-shame kan
gadon Innata me rumfa da aka canzawa shimfida
a ka sanya sababbi, ita kuma zaune a gefen
gadon da daurin kirji a jikinta kanta babu dan
kwali jikinta babu riga sauri nayi na sunkuyar da
kaina kasa, ban lura naga halin da Babana yake
ciki ba balle in gane da rigar a jikinshi ko babu?.
Yana fita waje ya bar gidan naji ta kwalo min
kira, da sauri na amsa naje ina işa tayi maza ta

56

cafke kunnena ta rike bayan ta dirma min wani
nannauyan dundu da sai da yayi sanadin
gantsarewata.
Kina hauka ne ki ke shigo min da a fadi
sunan uwar miji gara na uwa mahaifiya. Da sauri.
Babana ya ce mata ko? Ta langabar da kai nuna
alamar girman maganar da zata yin, to wacce ta
haifan maka miji Mallam? Da wani abin da yafi
aure daraja ne?
Da sauri Babana ya ce mata babu shi babu shi
fa kam. Sai dai fa sanin hakan wurin mutane
kadanne a wannan lokacin, ta ce Uhun ai kuwa
dai wanda ya raina aure bai yi wa kanshi adalci
ba.
Bakuwar ta ce tayi sallama abinda yayi
dalilin katsewar hirar tasu, a ka shiga barka da
sannu da zuwa a'a ke Lantana 'yar taki ki ka tasa
a gaba nan za ki koya mata son miji? Amaryar
Babana da a yanzu naji an kirata da Lantana
nasan sunanta shi kam Babana Malama naji yana
kiranta.
Ta kyalkyale da dariya ta ce, to me zan jira
ita mace ai tun daga haihuwarta ake koya mata
tattalin miji da tarairayar aurenta, to ai shi ke
nan. Ta juyo gare ni da dariyarta ke 'yar amarya
bakinki da maiko.

57

Nayi maza na soma gaisheta tunda a jiya an
gaya min in rinka gaida mutane in na gansu
kafin nan ban damu da gaida kowa ba in ba 'yan
uwan Innata ba ne sai ko na Babah Sumaye.
Ke Yaacuwuna kawo musu dan abin nan
mana yayi maganar daidai ya mike ya kama
hanyar waje bayan sun gama yiwa juna gaisuwar
gajiya da fatan Ubangiji ya sanya alheri, a
zuciyata nace sai kirana da sunan Yaacuwuna
yake yi sunan da ya dade bai kira ni dashi ba
alamar dai yana cikin farin ciki mai yawa.
Miyar kajin dai saura aje na kawo musu
wacce Yaya Dijah ce tayi mana tare da timemen
biredin da yake kai na ajiye musu, suka bude
kwanon kawar tata ta fara uh'uh'uh ke da arziki
cikin lamarin nan naki fa wannan karon.
Suka soma cin naman miyar suna hirarsu ni
kuma ina can gefe daya a rakube saboda yanayin
da na gani a fuskarta, baki dan tsakura kika
sanma 'yar taki ba? Tayi maza takai tsokar da ke
hannunta baki ta lankwame kafin ta sake gutsuro
katon biredi ta dannan a kai ta kora da ruwan
shayi sannan ta soma yi wa kawar tata bayani
wannan 'yar tawa a rike take nan inda ki ke
kallonta bata cin komai a jikin kazasai cinya, ai
kuwa kin ga bana bata cinya ni in zauna haka ba
ko kuwa?.

58

Ke Lantana ke fa sharrinki yawa ne da shi
yaushe ki ka bata ta ce miki cinya kawai take ci?
Yanzu wannan fuka-fukin in kin bata sai ta ce
bata ci? Tayi dariya ta ce a'a to in ma sharrine
ubanta yayi mata ni kam yaushe nazo balle in
fara nawa? Shi ne ya kawo kaza dankwaleliya
gasasshiya.
Yasa hannu ya balle cinyoyin duka biyu ya
mika mata ya bar ni da sauran jikin wai abin da
take iya ci kenan a jikin kaza.
Kawar tata ta kyalkyale da dariya ta ce, Ai da
ga ni kasan Kura za ta ci Akuya 'yar tashi aî ta
kiwatu komai nata luwai-luwai da shi, ga ta
kuma dama tubarkallah, ke dai irin wadannan
mutanen sai anyi hakuri a ke iya zama da su.
Uhun ai kuwa ni nasan sai anyi hakuri kin ga
Ramatu! Ramatu!! Ramatu!!! Tana ambaton
sunan Innata tana kwatanta yanda sunan yake
fitowa daga bakin Babana, yayin da kawar tata ta
zuba mata ido tana kallonta
Abinda a ka kwana' ana gaya min ke nan,
labarinta ake ta bani ana yi ana karawa ni kuwa
ina ta uh, wannan anyi mutuniyar kirki, garin ba
ni labarinta hawaye suka soma zubo mishi, yana
kici-kicin share su ni kuwa nayi maza na rushe
mishi da kuka.

59

Kawar tata ta kwashe da dariya kafin ta ce
"Kuka gaba daya? Ta ce to me ki ke so in ce
mishi yana bani labarin matarshi yana share
hawaye ba sai in taya shi kukan mutuwar tata
ba? Taja wani mummunan tsaki ta juyar da kanta
can gefe.
To ashe ba ku' samu kun yi wancan abin ba
kenan? Ni kuma da nazo ne in ji yanda a ka
kwashe. Ta dago ido ta kalle ni. "Ke tashi ki
bani wui, kin wani tsare mutane da ido suna
magana kina kallonsu, na mike na nufi hanyar
fita daga gidan, tayi maza ta ce "Ina za ki? Yau
ga abinda ya ishe ni, yazo ya same ki a waje? To
ba wajen na ce kije ba dakinki za ki shiga."
Na shiga dakin nawa na zauna sai dai cikin
rashin sa'a nan din sai ya zamo nafi jin zancen
nasu.
Ni na rantse miki kar ki ce maganar wasa
dingishin nan da kika ga ina yi ba na iyashege, ba
ne, don ma nayi aiki da ruwan zafi sosai, gaba
daya suka kwashe da dariya, ke kice min kawai
mutumi garau din shi yake.
A*a kalau yake Lami, sannan kin san ya kwana biyu rabonshi da abin, kuma gaskiya hadin nata mai kyaune, komawa zaki yi ki sake karbo min.

60

Wari-wari ya soma shigo min daki, nayi
maza na waiwaya wurinsu don ganin abinda ke
faruwa, karan Siga ri na gani a hannunsu suna
zuka cikin mummunan faduwar gaba nayi
magana cikin zuciyata don kar su ji ni na ce
Sigari kuma?
Ke dai kar kiyi asa da wannanauren naki,
zawarcin shekaru bakwai fa ki ka yi wannan
karon kafin shi kuma kin yi na shekaru hudu har
da watanni ki ka yi aure muna murna auren yazo
ya kare a watanni uku kacal, kin ga in an hada
zawarcin shekara goma sha daya ke nan. To don
me za a hada bayan ga auren wata uku a tsakani,
wata uku wasa ne?
Suna hirarsu ni kam tuni zuciyata ta shagala
tunanin ashe mata ma suna shan taba
sigari, na dauka maza ne kawai...
Ban ankara ba sai naji hirar tasú ta koma
bayanin ai yarinyar bata da tarbiya, goyon
gwauro yayimata sannu a hankali na gane wai
maganata da Babana suke yi.
Tunda aka yi auren Babah Lantana kullum da
irin kawayen da ke zuwa wurinta wadanda
Babana zai yi ta hidima da su in ya fita kuma ka
ji suna hira mai ban mamaki gashi kuma wani
abin da ya fi komai bani mamakin shi ne daga ita

61

har kawayen nata ba ka raba su da wani mele a
gefen fuskarsu tamfar dai sun taba konewa.
Rannan na nemi izini wurin Babana da itama
Babah Lantanan don ya ce duk abinda zan yi ko
nake so ita zan rinka tambaya wurin Yaya Dijah
naje, muna zaune ni da ita yayin da "ya'yanta ke
cikin gida wurin Kakanninsu.
Ni 'yasu wannan mata da Baba ya aura rufa
ido a ka yi mishi ne ko? Ba fa yarinya ba ce ga
shi da ganinsu ita da kawayen nata kaga 'yan
duniya, an yi bilicin har an gaji an kode an yi
mele. Lokacin ne na gane melen da nake gani a
jikin nasu na tabon mai ne.
Kamar in ce mata ai ma na gansu suna shan
sigari sai nayi maza na kama bakina nayi shiru
saboda wa'azin Malamin Makarantar Asubaru da
na tuna, da ya yi magàna kan tona asirin mutum
bayan halin nashi bai bayyana kowa ya gane ba.
Ni dai fatan da nake yi Ubangiji yasa
maganar da wata makwabciyarmu nan baya tazo
tayi min ya zama ba gaskiya ba ne, cikin
natsuwa na tambayeta wacce irin magana ce?
Yaya Dijah ta kalle ni ta ce min cewa tayi wai
sun santa sani mai kyau, aurentaa shidana
Babanmu ne na bakwai,kuma wai "ya'yanta guda
biyun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login