Showing 24001 words to 26864 words out of 26864 words
ashe ma baya nan ne
yasa na daina ganinshi.
Da hikima da jan hankali Umma ta shawo
kaina har nayi mata bayanin sabon halin da nake
ciki, ta ce uhun dama abinda take so ke nan ta
raba ki da duk wani wanda zai taimake ki, in ba
haka ba ita kuma Dija me tayi miki da aka ce
kafa miki dokar zuwa gidanta ita ma?
Kai wannan uba naki? Ta dan yi shiru zuwa
wani lokaci kafin ta sake cewa, to sai a hankali.
Kin ga in gari ya waye daina jiran abin
karyawarta, rinka zuwa nan kawai ki karya ki
tafi Makarantarki na te mata to.
Kashedin da tai tayi min ne yayi dalilin da na
gama abinda zan iya na dauki Jakata nace wa
Babah Lantana Baba a bani abin karyawana in
na dawo sai in gama.
Ta ce, a'a ai sharadin karyawa gama aiki, ko
nima da ki ke ganin kamar ina daga zaune ne
kawai nake ci ba haka ba ne, da amfanin da nake
122
yi wa uban naki ita kuma Asabe ita take girkawa
shi kuma sallau yana karbo cefanen.
Don haka kema sai kin gama naki nace to a
bani kudin makarantar ta dago ta kalle ni da su
zan biya wadanda za su karasa aikin in kin tafi
kin bar shi.
Na juya na kama hanyar fita daga gidan ina
tunanin lokacin da Babana kan goya ni a
kekenshi ya kai ni Makaranta, muna tafiya muna
hirarmu komai na gani a hanya na ambaci
sunanshi ya tsaya ya saya min.
Tun ma ba a ce lokaci ne nasu tsada su lemon
tsuntsu su malmo ba amma wai a yanzu sai a
hana ni abin karyawa da kudin Makaranta a kan
idonshi yana kallo ba zai ce komai ba.
A gidan Umma nasha kunun gyada
lafiyayyen alalan ganye sai da na koshi na dauki
jakata zan tafi, ta ce min in an taso ki biyo ta nan
kafin ki je gidan naki na ce to.
Muna tasowa gidan nata na fara zuwa, na
samu dafadukan shinkafa da wake mai manja ya
kuma ji busasshen kifi a ciki da dan yaji-yaji.
Na ci na koshi na nufi gidanmu, Babah
Lantana bata bani ba nima ban tambaya ba,
tunda dama ko nayi mata aikin duka ba kasafai
nake samun abincin da zan cin ba.
123
Kusan wannan satin abinda ya rinka faruwa
kenan, don haka har ranar Asabar ban saurari
aikin Baba balle in je ina jiran abin karyawanta
Umman ce kuwa ta koya min yin hakan da
yamma na shigo gida na samu Babana zuane kan
tabarmarshi an kawo mishi abincinshi.
Ina kike tafiya ne Yaacuuwuna? Na kalle shi
cikin ladabi na ce mishi, "Gidan Umma. i Ban
san yanda a karyi ba bai yi min fada ba, sai naji
ya ce min to dauki wannan abincin kici, na ce to.
Ina daukan kwanukan Asabe ma ta zaburo da
saurinta nima zan ci nima ban koshi ba Baba.
To ku ci mana, yayi maganar a hankali. Tayi
maza ta biyo ni, To ki ajiye mana. A ha ina za
ki kai? kan in ce zan ajiye sai ga, Babah Lantana
tazo ta fige kwanukan da ga hannuna ta tafi da su
tana fadin.
Aikin banza aikin wofi, ba ka iya komai ba
sai lalatawa mutum tarbiya, a ina ake yin haka?
stya'ya gansun-gansun kowacce a ka kaita gidan
miji zata zauna sai kuma a ce kullum sai an basu
sudin uba, to ban yarda ba".
Ta juya ta tafi, duk. da nasan ita ta koyawa
Asabe irin wannan iya shegen saboda kyashin
dan abincin da wani lokaci Babana rage min
amma ban damu saboda na riga na koshi.
124
An kai maka maganar yawonta ba ka ce
komai ba kazo kana rage mata abinci, don daurin
gindi duk abin da ta kwaso dai ai a kanku zai
kare kai da ita, yaja bakinshi yayi shiru, to balle
kuma ni.
Washegari da safe na sake tambayarshi zuwa
gidan Yaya Dijah cikin sa'a sai ya bar ni na tashi
cikin zumudi da murna naje na gayawa Babah
Lantana ta tabe baki ta ce sai kiyi ta tafiya.
A gidan Yaya Dijah ranar kamar zata lashe ni
don dadi saboda na dade sosai ban je ba itama
kuma yanzu bata cika zuwa gidan sosai ba tunda
Babah Lantana ta ce ta yafe amma wai babu
sauran mu'amallah a tsakani.
Muka yi hira na bata duk labaran da ke cina a
cikina, tunda yanzu na kara sanin darajarta,
kullum kuma kara sonta nake yi.
Da yamma da zan tafi gida sai ta debo
zannuwanta kala hudu da ta ce za su yi min da
wasu sabbi da ta dinka man kala biyu ta hada
min har da takalma guda biyu suma sababbi.
Nayi ta murna na dawo gida zuciyata cike da
farin ciki, na shiga daki na adana kayana a cikin
dan akwatina a zuciyata ina tunanin tun da jibi
ne Juma'a to sai jibin zan fara saka su.
Ranar Juma'ar ina tasowa daga Makaranta ko
gidan Umma ban biya na ci abinci ba na dawo
125
gida da nufin in yi wanka in yi kwalliya tukuna
don ta ganni fes.
Na gama wanka na shafa maina wanda shima
Yaya Dijan ce ta bani shi, na shafa hodata na
jawo akwati da nufin zaban wanda zan saka sai
kawai kaya suka ce dauke ni a inda ki ka ajiye
ni.
Kuka sosai na kama yi kafin naje na kai
maganar gun Babana, Babah Lantana tana ji ta
ce wannan shi ne sharri da ki ka kawo wa ki ka
nunawa? Kin nuna min? na girgiza kai kin
nunawa Babanki?
Na sake girgiza kai, to ai ma ba haka a ke
sharrin ba, in ma ita ta koya miki in kin zo ki
kala mana sata to bata koya miki daidai ba.
Ta wuce ta taf ta bar ni ina kuka, Babana
kuma yana yi min fadan yanda a ka yi aka bani
kaya nazo na ajiye su ba tare da su sun taya ni
murna ba, bakin ciki ne ya ishe ni na fita na tafi
gidan Umma naje na gaya mata.
Ita kam bata musa ba, hakuri tayi ta bani ta
kuma bani abincin da ta ajiye min na ci na koshi
sannan ta kawo wata atamfa ta ba ni ta ce in yi
kwalliyar Juma'ar da ita.
Sannu a hankali sai gidan Umma ya zame
min gida na saki jiki sosai da ita ta zame min
126
tamfar uwa babu abinda bata nuna min na
hidimar rayuwa.
Hatta wankan al'ada ita ta koya min shi sosai
na iya, ita ce kuma ta fahimtar da ni na gane ita
al'ada ba laifi ba ne ba kuma abin kunya ba ce.
Sai dai mutunta kai ne ka tsare ta in. kana
yinta kayi ka gama ba tare da wanda ka ke tare
da shi ya gane ba, ita Umman ce ta fahintar da ni
cewar dabi'a ce ta cikar halittar mace.
Tun daga nan ne na gane na ma daina yin
kuka, in na ganta tazo min. ina zaune da Umma
masa nake ci cikin sauri saboda tsoron da nake ji
na kar in yi lattin makaranta.
Sai ga Alhaji Mahammadu ya shigo har
wajen kicin din yazo ya tsaya, yana kallonta ni
ina ki ka samu yarinya ne?
Yayi mata tambayar bayan ya anmsa gaisuwar
da nayi mishi. Yarinyar nan ne yar gidan
Mallam Habu mai Tumatir, nan da nan fuskarshi
ta kara daurewa, dama kuma ba mai yawan
fara'ar ba ne.
Ba ku rabu da ita ba ke nan kamar yanda
ubanta ya ce ayi? Cikin natsuwa ta ce, ubanta ai
ba a ta tashi Alhaji, da sauri ya tambayeta, sai
tawa? Tayi shiru bata bashi amsa ba.
Mutum da 'yarshi ki ce ba a ta tashi, sai ta
wa? Wane zancen banza ne wannan? Marainiya
127
ce Alhaji, Umma tayi mishi magana cikin murya
mai taushi da nuna girmamawa, yayinda nake
bake can gefe cikin rawar jiki saboda yanayin
fuskarshi da kwarjininshi.
Duk abinda aka yin sharrin matar gidanne, ba
ka ga yanda yarinyar nan ta koma ba, bayan
rabata da Ahmad Mubarak da aka yi shi yasa na
dawo da ita.
Macce ce rauni ne da ita ga shi kuma ta fara
girma, in wahala tayi mata yawa abin ba zai yi
kyau ba, yunwa ai musiba ce kuma bayan mu
muke dubawa tare da rokon Ubangiji ya tsare
mana su.
A bankali ya ce, To amin. Alamar dai ya
sauko har ma ya gamsu da kalaman matar tashi.
Wuce ki tafi makaranta Maryamu in kin dawo
ki biyo ta nan kar fa ki ki zuwa na ce mata to,
har na wuce zan tati 'sai naji ya ce mata in da
canji nan wurinki bata sule biyu ta ce mishi eh
akwai, ta miko sule biyu nasa hannu biyu na
karba tare da yin godiya, na kama hanyar fita ina
jinta tana yi mishị karin bayani a kaina, har da
Innata.
Da yamma ban ki biyowa ta gidan ba ina
dawowa ta bani abinci na zauna ina ci, ta kalle ni
cikin natsuwa ta ce min kin ga ma Babanku dazu
sai yace min kullum in ki ka zo tafiya makaranta
128
in kin karya in ba ki sule biyu ki rinka cin abinci
a makaranta, na ce mata to na gode.
A wancan lokacin da nake magana akai sule
biyu kudi ne masu daraja saboda sule goma ne a
Naira guda daya, yayinda ita Nairar take daidai
da dalar Amurka.
Don haka sule biyu kudi ne tunda kuma ina
cin abinci in koshi a wurinta in zan tafi in na
dawo ma kuma za a samu in ci in koshin sai ya
zamo ko ta bani sule biyun ba na karba sai in ce
bar su kawai Umma, wata ran kuma in karbi sisi
wato rabin sule daya ko kuma in ce kwabo biyar,
ban sani ba ko ganin hakan da nake yi ne ya
sanya ita Umma fara yi min banki a wurinta.
To Hausawa suka ce wai yau da gobe bata bar
komai ba, ana tafe a haka sai ga shi har mun
gama aji uku mun kammala jarrabawa muna
cikin hutun da zamu shiga (SS1), ko kuma aji
hudu na Secondary a takaice dai na shiga Senior
Section.
Haka nan da ki da so da wahalar da komai da
lokacin girmana yazo sai na girma saboda
Hausawa sun ce wai in rana ta fito to tafin hannu
kuma bai kare ta.
A wannan lokacin na zama ba Asabe ba, hatta
Babah Lantanar na kere ta a tsayi, haka nan duk
da a hakan ma ban wuce a dake ni ba, amma dai
129
nayi matukar rage jin tsoronsu da nake yi tun ma
ba na Asabe ba wacce kuma dama ita ce tafi
kowa takura min ko dan maina Umma ta saya
min a cikin kudina sai ta dauke min ko ta kawo
wata kwalbar ta juye shi.
Ana cikin haka Mubarak ya dawo daga
hidimar kasar da ya tafi Ibadan, ni da shi ba ma
kula juna, ganin da nayi ya ganni bai nuna wata
alama ta zai kula ni ba, yasa nima nayi kamar
ban ganshi ba.
Sai dai hakan bai sa na daína shiga gidansu in
yi hidimomina da Umma ba, saboda na riga na
kudurawa raina babu abinda zai sa in sake dauke
kafa daga zuwa wurin Umma, matukar ina raye
a cikin hayyacina.
Don haka shiga gidan nake yi yana kallona
ina kallon babu mai cewa wani ci kanka ita kuma
Umman bata taba nuna ta gane abin da ke
faruwan ba, balle ta tàmbayi dalilin hakan zuba
mana ido kawai tayi.
A wannan lokacin zama tsakanina da Asabe
matukar baci, saboda muna iya wuni mu
kwana tare a daki daya babu wanda ya ce wa
wani ci kanka.
Muna cikin hakan ne kawai na dawo daga
wurin Yakumbo Halima na samu Asabe ta tsala
130
kwalliya cikin sabuwar atamfata da Umma ta
dinka min su kala hudu.
Cikin natsuwa na kalleta na ce Asabe wannan
ai tana cikin sababbin atamfofina da na karbo
daga wurin dinki." Wacce? Na ce wannan ta
jikinki tunda gama botin rigar nan da na sayo da
hannuna.
Eh ai na san taki ce aro na dauka ta zancen
nata, na ce To gaskiya ban yarda ba cire min ita
kawai tazuba min ido tana yi min wani irin kallo
baki yarda ba fa ki ka ce? Na ce eh ban yarda ba
ina ce tawa ce? Ba sai ki cire min ba kawai ni daa
kayana?
Ai, ke nan babu damar a ari kayanki ke ba
kya aron na mutane? Babah Lantana tasa ba ki
cikin maganar ban ji nauyinta ba na ce in na ari
na wani ya kwace kar ya bar min shi ni dai a cire
min nawa kawai.
To ba zan cire ba tunda abin naki iskanci ne
ana miki magana kina ba mutane amsa.
Na ce gaskiya sai kin cire ban yarda da aron
ba tunda ai ma ba ki tambayen ba in ban da na
ganta a jikinki kuma da ba za ki dawo min da ita
ba.
Me ki ke nufi da wadannan maganganun
naki? Abin da nake nufi ke nan ana diban kayana
131
ba da sanina ba ana salwantar min da nayi in na
yi tambaya a ce na kalawa wani sata.
Ko rannan ai nayi miki cigiyar doguwar
rigata ta shadda ki ka ce' rainin hankali ne ya na
tambaye ki ita shekaran jiya kuma sai muka yi
kacibis ni da kawarki Nuriya da rigar a jikinta da
na tambayeta in da ta same ta ta ce min canji ku
ka yi ke da ita ki ka bata wannan.
A fusace kwarai Asabe ta tambayen ke me ki
ke so ki ce min na yi miki sata ko kuwa me? Na
ce Oho ko ma a me ki ka fassara shi daidai ne,
tunda kin daukar min kayana na tambaye ki kin
ce ba ke ce ba ce nazo na gani a jikin kawarki da
ta ce ke ki ka bata yanzu kuma ga wata na gani a
jikinki kin dauka bada izinina ba kuma da kina
so kiyi musun ba tawan ba ce.
To ba ki da abin da zan .satar miki bari in
gaya miki, to sau nawa? Ta tambaye ta cikin
yanayin da ya kara fusatata.
Taja wani mummunan tsaki ta wuce wai zata
fita tayi tafiyarta, nayi maza na kama gefen zanin
da ke daure a jikin nata na rike ai babu in da za
ki da kayana a jikinki.
Riketan da nayi ne ya zama dalilin da ta juyo
cikin hanzari ta rufe ni da duka, nima nayi maza
na maida martani don haka dambe ya kaure a
tsakaninmu.
132
Kamar kullum yau ma Asabe ce mai galaba a
kaina a damben. Sanin da nayi babu mai raba mu
daga Sallau da ke zaune a gefe yana kallon
abinda ke faruwa har Babah Lantana da taci gaba
da harkokin aikinta tare da fadin, a to ai dama ke
ki ka barta ta raina ki, yasa da na ji zata azabtar
dani azabar da ta wuce ka'ida na same ta na
gantsara mata cizo da iyakacin karfina.
A gigice kwarai ta kurma ihu mai tsananin
firgitarwa nan take kuma ta sake ni.
Da gudu nayi nufin fita in bar gidan, caraf
Sallau yasa hannu ya rike ni, saboda umamin da
Babah Lantana ta ba shi na kar ya bar ni in fita.
Ina ganin yayi nasarar kama ni na soma
kurma ihu mai tsanani tare da kiran sunan Babah
Sumaye, ina rokon ta kawo min agaji, duk da
nasan ba zai yiwu ta shigo ba saboda wani rikici
da ya faru tsakaninta da Babah Lantana a kan
dukan da Asabe tayi min.
Maganar har takai Babana ya shaiga ciki ya
kuma nuna 6acin ranshi kan keta haddin
gidanshi da a ka yi a ka shigo har cikin gida a ka
yi fada da iyalinshi.
Yana fadin haka Baba Baidu ya ba shi hakuri
ya kuma yi mishi alkawarin Sumaye ba za ta
sake shiga gidanshi tayi wata magana ba.
133
Sumaye! A'a Tasallah, Babah Lantana ce mai
wannan maganar kafin ta koma fadin "Tafdijan!
A nonuwa ki ka cijeta? Ki rasa inda za ki cijeta
sai a nono don sharri da mugunta?
1o ai kuwa sai ta rama. Rike min ita tamau
Asabe ta rama wannan sharri da tayi mata, ta
sake yi wa Sallau bayanin.
Tashi ke kuma shashasha ji yanda ki ke bari
sai ka ce wacce a ka gutsurewa nonon gaba
daya, zo ki daidaici inda tayi miki ke ma kiyi
mata.
Asabe ta iso gaskiya ne har lokacin jikinta
yana rawa, alamar ba karamar wahala tasha ba.
Tun kafin ta dora bakinta a kan nonon nawa don
rama cizon da nayi matan na saki. fitsari a tsaye,
saboda tsananin tsoratar da nayi da abin da ke
shirin samun nawa.
Wayyo! Wayyo!! Abinda kawai nake iya fadi
kenan, yayin da zuciyata ke ta neman taimako
wurin Ubangiji.
Rike ta da kya inin rikon da ba za ta kubuce
mata ba, shi kuma yayi maza ya sake damke ni a
hannunshi irin rikon da a ke yi wa kazar kuku.
Sai kuma ta juyo tana kallona ai daga yau ba
za ki sake cizon wani ba a rayuwar...ba ta kai
Rarshen maganar tata ba sai ga Mubarak ya
shigo gidan a guje.
134
Kan ka ce meye wannan har ya kirbe Sallau
da wani irin gigitaccen naushin da ya kifar da shi
a kasa, nima na fada can gefe saboda
hantsalawar da nayi.
Shigowar da Mubarak yayi cikin gidanmu da
gudu yayi dalilin da mutane da yawa suma suka
shigo saboda sun dade suna jiwo ihun da a ke yi
daga cikin gidan.
Tankam gidan namu ya cika da Jama'a, sai
dai kuma cikar da aka yin bai hana Sallau shan
dukan tsiya a hannun Mubarak ba, saboda babu
wanda ya koma takan yin rabo.
Da gudu Babah Lantana ta suri tabarya tayi
kan Mubarak zata rafka mishi ita, samari suka yi
wuf suka café ta suna fadin.
"Haba Babah, haba Babah, da girmanki ki
bugawa mutum wannan a ka? Wannan ai ya
zama kisan kai ko kuma ta'addanci, ai rabo ne
yafi dacewa da ke.
Babah Lantana sai ihu take yi tana fadin an
shigo mata har gida ana so za a kashe mata da,
ana cikin haka sai ga Babana ya shigo ban san
wanda yaje ya gaya mishi ba.
Bakin ciki mai yawa ya bayyana a fuskarshi
saboda tsananin baccin da ke tare da shi duk ku
fita ku ba ni wuri. Yayi maganar cikin natsuwa
nan da nan kuma a ka yi ta fita.
135
Babah Lantana tana ganin haka ta soma rusa
kuka mai tsanani tana fadin "An keta mata
haddin cikin gidanta an keta mata haddin
aurenta, an shigo har cikin gida an ci mutuncin
iyalanta sakacin Babana yasa duk unguwar nan
babu mai jin shakkar shigowa cikin gidan shi
yaci mutuncin matarshi.
Duk wadannan kalaman da Babah Lantana ke
furtawa Babana yana jin ta bai ce mata kala ba,
bai kuma cewa kowa ci kanka ba, illa iyaka dai
da gari ya waye sai ya zartar da hukuncin da ya
ke ganin shi ne daidai a wurinshi.
Mu bi Maryam Abubakar cikin littati na biyu
mu sake shan wani labarin, kafin nan ina yi
muku fatan alheri.
Taku;
Hafsat C. Sodangi
Na gode
Tare suka fito da na (2)
136