Showing 12001 words to 15000 words out of 26864 words
take cewa na Alhaji Tukur ne mijinta
62
da ya rasu karya ne, asalin ubansu ne wai ba a
sani ba.
Kamar ya ya ke nan? Nayi mata tambayar da
ta zamo tamfar tuni a gare ta, cewar wannan
maganar ta wuce sanina, don haka tayi maza tai
gyara ta hanyar fadin mu dai mu bar wannaan
maganar kawai muyi abinda yake gabanmu. Shi
kuma Baba muyi mishi addu'a, na ce to. Muka ci
gaba da harkokinmu da muka saba yi in naje.
Rannan ina tare da Babah Sumaye da Jumare
da tazo mata kwana biyu hirarmu muke yi muna
wasanmu ni da ita sai naji Babah Sumaye ta ce
min, Ke Mero kina da wata matsala ne naga kin
yi wannan zubewar haka? Da sauri na dago ido
na kalleta.
Nan take kuma na maida kallon nawa ga
jikina da take fadin ya zube, me ki ka gani
Babah? Ta ce, Uh'uh gani nayi dai kamar kin
ragu kan in ce komai sai Jumare ta ce mata,
zama da wannan matar ta Baba ba wani dadi. zai
yi ba, da na shiga gidan fa ba ki ga irin kallon da
take yi min ba, kuma na rantse miki sigari na
sameta tana sha.
Babah Sumaye tayi murnmushi ta ce, shan
sigari wurinmu ne muke ganin shi kamar da
aibu, amma wurin mutanen Bauchi da Katsina ba
komai ba ne yin hakan face kwalliya, ko gaye
63
tunda za ki samu har 'yanmata a wurin kawance
suna sha, da haka ta kashe hirar tamu a kan
Babah Lantana.
Wani abinda na kasa hakura dashi in daina
yin shi shi ne shiga dakin Babah Lantana, ban
san dalili ba daga in da duk na fito sai na shiga,
sai dai in na shiga naga ledar dakinne nake
tunawa musamman ma da yake sau biyu tana
rankwashina a kan taka mata ledar da nayi da
kafata bayan kuma ni take sawa in goğe mata ita.
Yau ma nazo zan shiga kaci6is muka yi muka
hadu a Rofar dakin ni zan shiga ita zata fito, don
haka nayi maza naja na tsaya nan take kuma na
juya zan koma nawa dakin ita ma har ta nufi
kicin sai kuma naji ta ce min ke ni zo nan mana
in tambaye ki, nayi maza na dawo kusa da inda
take din kafin naja na tsaya cikin natsuwa ina
sauraronta.
Wai zaryar me ki ke yi min a daki ne? ba ki ji
kashedin da nayi miki ba ko? Ba fa za ki iya
hana ni komai ba, ni kuma da ki ke ganina fa ko
da Ramatu na samu a cikin gidan ba za ta takura
min da komai ba, don bata isa ba sai dai ma in
bata yi sa'a ba in korata waje, don kuwa da
shirina na shigo.
Jikina ya dauki rawa yayin da ita kuma ta
daga murya wajen yi min magana, haba wacce
64
irin jarababbiyar yarinya ce wannan babu hali ki
ganni da mijina a daki sai ki kama yi min zarya
ki ce biro, ki ce pencil, ki ce kudin jarrabawa. Da
ya ce ki rinka tambayata raina ni ki ka yi kina
ganin ban isa ba ko?
To ai kwa za ki gane ke ce ba ki isa ba
sakarya kawai, shashasha da ta gaji iyayi da
munafurci wurin uwarta, kai ke kam ta tafi ta
barki da mummunan abu za kuma ki sha wahala.
Taja tsaki kafin. ta wuce ta bar ni ina ta faman
bari ban saba jin irin wadannan kalaman ba balle
kuma a ce a kan Innata a ke yin su.
'Yan kwanaki kadan da zuwan Babah
Lantana gidanmu sai nayi matukar tsorata da ita,
ko maganarta naji sai gabana ya fadi, gashi bana
sanin lokacin da nake aikata laifin da take cewa
nayin, balle in rinka kiyaye mata ban saba da
mu'amalla ta tsawa da yawan duka ba, sai kawa1
aka wayi gari na tsunduma a cikinshi.
Yar tsarabar' da Babana ya saba kawo min
ina ci na kwalama bayan abincin gida na daina
samu saboda yanzu komai yazo dashi ita yake
mikawa wai ita ce mai bani, ita kuma sai ta cinye
ina kallo.
Hakan bai dame ta ba a farkon zuwanta
gidanmu, ban cin komai jikn kaza in ba cinya ba
ne amma bata cika kwanaki arba' in da zuwa ba
65
sai da na zama har kai da kafa ci nake yi, wanda
mu da sanda Innarmu take raye ba a sa sua cikin
miya.
A kowane lokaci a cikin yi min kashedi take
in kika ce abinda zamu yi da ke kenan to kuwa
laiie zamu sa kafar wando daya ni da ke a gidan
nan, ba kuma zata fito ta ce min ga abinda nake
yin ba wanda zai yi dalilin da za a sa kafar
wando dayan da ni ba.
Rannan ta cika sati shida da zuwa gidanmu,
wato kwanaki arba'in da biyu kenan, daga
Makarantar allo na taso don haka na biya ta
wurin Babana don in dan zauna mu dan yi hira
inji dadi, tunda shima mu'amullar tamu ta dan
sauya.
Bai bar ni na zauna ba ya ce min maza je ki
gida uwarki tana can tana jiran dawo erki tunda
in ba kin koma gidan ba ba dora girki take yi ba,
sai tayi ta jiran zuwanki.
Kamar in ce wa Babana a'a Baba bata jirana
ni bata sani ma wani aikin da ya danganci girki
tuna ta ma hana ni shiga kicina dalilin wan
naman miyarta yana bata, amma sai na kasa
cewa Babana komai, na kamo hanya ka na
dawo gida.
Naje na gaishe ta sannu da gida Babah, bata
amsa ba sai da nayi sau biyu sannan ta daga ido
66
ta kalle ni sai yanzu ki ka dawo? Ai ni da ke nea
gidan nan na wuce sumsum na shiga dakina na
zauna don yanzu na riga na saba da zaman
cikinshi.
Ban dade da zaman cikin nashi ba naji wata
murya tayi sallama, ban ji amsa ba iyaka dai naji
an kurma ihun da ya sanya ni nayi maza na yiwo
waje saboda firgitan da nayi, sai dai sabanin
yanda nayi zato abin tsoro ta gani ashe wai
murna ne haka don ganinsu nayi sun rungume
juna ita da bakuwar tata.
Nayi maza na koma dakin nawa na zauna a
zuciyata ina mamakin yanda babba zai iya
kwallara ihu irin wannan da sunan oyoyo ko
murna.
"Na rantse ko jiya sai da nayi maganarki
cikin zuciyata, ashe kina hanya Delu. Delu ta
ce "Ke Lantana juna biyu ki ka samu ne naga kin
habake kin zama wata danya?
"Juna biyu wane iri? Kalau dina nake shimna
dai maigidan na ji shi yana maganar waiko juna
biyun ne, ni kuwa bai sani ba yaushe rabona da
al'ada, na fashekara sai dai zan koma wurin
mutumin nan ko zai bani maganin da al'adan
tawa zata dawo.
67
Ta kyalkyale da dariya "Tana tafiya ne dama
ta dawo? Ai in ta tafi ta tafi ke nan in dai ba ciwo
ne yayi dalilin daukewar nata ba."
To ai nima ciwon ne. Delu ta sake wata
'yar dariyar kafin ta ce "Ke dai kin samu gida na
kuma yi miki murna don da gani ba sai an
tambaya ba kin yi shar da ke har kuruciya ta
dawo miki, kai ni'ima da dadi take, sai dai kawai
in bawa bai samu ba ya hakura Ubangiji ya samu
a danshinku."
"Kai Delu kenan, abin dariyarki yawa ne da
shi. Tayi maza ta mike ta shiga cikin daki ta
fito mata da abubuwanci da na sha da Babana
yake kawowa tana hana ni tana ci tana 6oye
saura don masu zuwa mata.
Haba, gaskiya ni'ima ir bayyana a jikinki
ke ki ce gara kawai yake shirya uiki ke in ban da
ita haihuwa lokaci ne da ita da sai in ce gianta ki
ka zo ki neme ta." Babah Lantana tayi dariya, ai
iya shegenki yawa ne da shi kina nufin lokacin
nata ya wuce ne a wurina? To bari mu gani.
"Ke ki ce aure sosai ki ka yi, ai tunda ki ke
aure ma ina ganin in banda aurenki na biyun nan
ba ki taba dacen aure irin wannan ba, sai aka
yi rashin dacewa aka tare mishi da dan zani, ai
daga rikicin cikin nan nc abin duk ya shiririce
68
zama ya ki dadi sai da aka rabu daga baya ma
yazo ya rasu.
"Delu ke nan to wa ya tambaye ki wannan
dogon bayani ko kuma duk a san jin naman a na
kawo miki ne ki ke kokarin yi min wannan
tonon asirin?"
Delu tayi dariya ta ce, "To gida mu biyu
tonon asirin me zan yi miki Lantana? Auren naki
ne ya bani sha'awa, ga shi kin yi fes da ke da
alamar shi mutumin bai da wata damuwa. Ta ce,
Eh to kamar dai hakan nake zato tunda zuwa
yanzu ban ga wata damuwa a wurinshi ba, shi ba
a musu da shi in kuma takamanki son kudi ne
ma to shi ke zai baiwa ajiyar ribar cinikin nashi
ya dauki jarin da gobe zai koma dashi kasuwa,
duk abin da ki ka ce kin yi da kudin kuma ba
magana zai yi ba.
In har ina da wani abinda ya tsaya min a rai
game dashi to yar shi ne sai ko matarshi da ta
rasu, kinga ita 'yar duk inda tayi yana bin ta da
kallo sau goma kuma in zai yi miki wata magana
to shida a kanta ne hudin akan uwarta da bata
duniya.
Yanzu haka akwai wani hoto na uwarta da ya
kakaba min a cikin dakin maganar hoton kawai
nayi kan ko za a cire shi ne a dana tunda dai mai
shi ta riga ta mutu kar kiga irin fushin da yayi, to
69
ga maganar wadannan yaran da nake so in dawo
da su gidan nan a matsayin 'ya'yan Yata da ta
rasu ta bar min su.
Kin san ba zai yiwu in ce mishi nawa ne ba
don ya ma taba tambayata su na ce mashi ai
tunda ubansu ya rasu danginshi suka kwashe su
suka tafi dasu ni ko zuwa bana yi ke ce mai zuwa
don na gaya mishi ke Yayata ce.
"Au, haba? Yanzu nan ni surukarshi ce? ta
ce, Eh abinda na gaya mishi kenan, ta ce to ai shi
kenan su kuma yara kin hadawa Alhaji Tanimu
ko? Tunda shi kam ya mutu ai magana ta kare,
sai mu tafi a hakan unda kuma abin ya zama
haka to bari ni kuma kiga abinda zan yi miki.
Zan je miki wurin Mallam na kan tudu a kan
damowowin naki duka sai mu ji abin da zai ce,
da sauri Babah Lantana ta ce ma to Delu na
gode."
"A'a ba kin gode ne maganar ba, saura kuma
in yi miki rana ke kiyi min dare, in taimake ki ke
ki samu mijinki a hannunki ni kuma kiyi min
iyashege menéne naku ban sani ba?"
"A'a to ni kam ai ba sanin yau ki ka yi min
ba, in ma ya ya nake kin fi kowa." "To ni kawvo
min abinda za ki kawo min in tafi." Ta tashi ta
shiga daki ta fito ban san nawa ta kawo mata ba,
70
amma naji ta tana godiya tare da fadin wannan
duka?
Ai babu komai kuma tunda ba wani nisane
damu ba zan sa miki kwano ki rinka turowa ana
daukar miki abincin dare, bakuwar Babah
Lantana Dela tayi ta godiya tamfar dai wacce
aka ce an baiwa kyautar kujerar Makkah.
Rannan na shirya zan tafi makaranta da safe a
bakin kofa na tsaya nayi sallama aka amsa min
na bude baki nace Babah zan tafi ne? tunda
abinda Babana ya ce in rinka yi kenan. Da
saurinta ta fito tana fara'arta har kin gama shirin
ne?
Na ce mata eh, ina kallon irin kallon da tayi
wa gidan amma ba ta ce min komai ba sai ta ciro
sule ta miko min, *"To ga sule nan sai ki sayi
abinda ki ke so ko? na ce, To. Na juya na tafi.
Ina dawowa gida ko amsa salamar da nayi
mata bata yi ba ta rufe ni da duka titim-titim ""Ni
ki ka mayar 'yar iska saboda kin ganni a gaban
ubanki ko? Ba kiyi min sharar tsakar gida ba ki
Rarasa min wanke-wanke ba ki ka kama hanya ki
ka tafi, ni baiwarki ce?
Nayi maza na ce, a'a. mara kunya kawai mara
tarbiya dama kin nemi zama lafiya dani da ya
fiye miki, ina canjina? Nayi maza na kara zaro
71
ido cikin tsananin tsoro a dalilin ban san tana
bukatar in kawo mata canji ba.
Ko duka ki ka kashe kudin da sauri na ce
mata eh, don kar ta ce na bata mata lokaci wajen
amsawa, ai duka kika kashe? Uh lalle ina da aiki,
ni Lanti ni Lanti in ban yi da gaske ba lalacewa
za ki yi a zo ana cewa ni ce sanadi wato a yanda
ki ke din nan kina iya kashe sule guda a wuni.
To in ba ki bi maza ba kuwa kiyi me? Tayi
wuf ta sake kamo ni ta tittime ni kafin ta sake ni
ta wuce ta tafi tana to kuma a bakin abincin
ranarki kin ji na gaya miki.
A wannan lokacin kusan kullum sai Delu tazo
gidanmu ta kawowa Babah Lantaa wani abu ta
kuma kar6i kudin wani ab1 da za a sake
karbowa kusan duk lokacin da taro kuma za kaji
ta tana tambayarta kina ganin wani ranii a tare
da shi?
Ta ce to abinka da wanda baya magana
wancan na sakawan dai a karo min shi, ta ce to
kin gane kyanshi ke nan ta ce eh.
Rannan Babana ya dawo daga wurin tumatir
din shi ta kawo mishi abincin shi ban san dalili
ba naji ya kwalo min kira da sauri na amsa na
fito ungo cokali Yaacuwuna zauna kici abincin
nan kin ji."
72
Cikin hanzari na gyara na zauna na kanma cin
abincin nan sa da na cinye shi tas na debi
kwanukan naje na wanke su na kife na sake
daukan tsintsiya na share wurin tas na dawo zan
wuce in shiga dakina sai naji Babana yana cewa
ni Malama in tambaye ki mana.
Da sauri ta ce mishi "Menene fa? ya ce, ba
ki lura da irin ramar da yarinyar nan tayi ba,
gaba dayanta fa ta zube kasusuwa sun bayyana a
jikinta, ita kuma fa ba mai kashi ba ce, ramar
tata tayi min yawa tun ina daurewa ina hadiyewa
har abin ya gagaren na gaji na furta.
Ita mai cikakkiyar fuska ta zama wata yar
siririya, in dai ba bata da lafiya ba ne yasa ta
zama haka ai akwai matsala babba ke nan a tare
da ita wanda ya kamata abincika.
Da sauri Babah Lantana ta ce, cikin hanzari
kuwa, gara ma a fara binciken tun yanzu, ke
Yacuna zo nan, ta sake zabura cikin hanzari ta
shigo dakin nawa ta taso ni a gaba ta tsugunar da
ni a gabanshi. To gata nan tayi bayani da
bakinta, yauwa bawa da bakinshi ai wuyan sai
dawa gare shi.
Ina dalilin wannan kiran da kika yi mata?
Babu halin' muyi magana ni da ke sai ki kira
yarinya ki tsomataa a ciki? Yarinya? Tayi
tambayar cikin wani yanayi na tsananin fusata
73
wannan ce yarinyar? Tafdijam, ba yarinya ba ce
mace ce. To menene bata sani ba Mallam? Ai da
kadan na fi ta sanin duniya wane sharri daa
makirce-makirce ne bata kulla min?
Tun farkon zuwana gidan nan fa kana ganin
irin karbar da tayi min amma me na mata? Gata
nan ai tayi magana da bakinta, ke ta zuba min
ido tana kallona ina ba ki abinci ko ba na ba ki?
Na ce kina ba ni.
Ta gyada kai to, ina zaginki ne ko dukanki?
Na girgiza kai tare da fadin a'a, ta ce to amma a
hakan ne ki kaje ki ka hada ni da ubanki a dole
ke ga mai uba ko? To mu ma da bamu da uban
ba kinmu a ke yi ba yasa a ka daukan mana su
masharranciya kawai.
Watakila shirun da Babah Lantana taga
Babana ya yi ne yasa ta tayi ta maganganu da
tashin hankali mai yawa, bai ce mata komai ba
yayin da ni kuma nayi matukar tsorata don gani
nake tanfar zata mike ta rufe ni da duka ne.
Har tayi ta gaji bai ce mata komai ba nima
kuma ban matsa daga inda ta durkusar da ni ba,
sai da a ka kira sallar Magriba ya mike zai fita
sai ya ce min je ki kiyi sallah nå ce mishi to.
Ina zaune a dakina bayan na idar da sallar
Isha'i naji shigowanshi a tsakar gida ya samu
Babah Lantana tana goge kafarta da dutse bayan
74
ta fito daga wanka naji shi ya ce mata "In kin
gama abinda ki ke yi kije gidanku sai nazo."
Ko da bana nan a kusa nasan ba karamar
firgita Babah Lantana tayi ba da jin maganar
tashi saboda irin na'am din da naji tace kafin
daga baya ta soma maganganu irin na borin
kunya "Ai gara haka, ni dama tuni na dade ina
jiran irin wannan maganar ta fito daga bakinka
ba ka furta ba ne sai a yau. To kuma sai me? Ai
ta fi nono fari in dai a kan wannan munafukar
yar taka ne ai yanzu kasa hannu da aure. Bai ce
mata komai ba har ta gani da maganganun ta figi
gyalenta ta fita.
Tana fita ya tashi ya fita shima bai wani dadee
ba sai ga shi ya dawo min da gasasshen nama,
nayi maza na karba na lamushe sabanin da da in
ya kawo min na rinka yanga kenan yana
rarrashina ina cewa an labta yaji yayi ta
karkadewa yana cewa to ungo wannan na cire
miki yajin.
Washegari ma haka tare muka karya gidan ya
zama gwanin dadi kusan kwana biyar babu
Babah Lantana alama na Babana bai bi bayan
nata ba tunda cewa yayi taje sai yazo, cikin
zuciyata babu abinda nake fata irin a ce ta tafi
kenan ba za ta sake dawo mana gidanmu ba.
75
Tun kwanaki ukun farko na barinta gidanmu
yanayin jikina ya soma sauyawa na soma
dawowa cikin hayyacina.
Rannan muna zaune ni da Babana tsiren
Salim mai nama ya kawo min ina ci ina korawa
da ruwan tea mai kauri sai kawwai muka ji
sallama, Babana ya amsa yayin da ni kuma na
dauki abinda nake cina shige dakina na zauna
cikin fargaba da faduwar gaba saboda sanin Delu
ce tare da Babah Lantana.
Cikin ladabi naji Babna yana yi mata gaisuwa
irin ta surukuta saboda gaya mishin da Babah
Lantana tayi cewar ita din yarta ce.
Kayi hakuri Mallam maigidan ne baya nan
sai dazun nan ya dawo ya samu Lantana a gida
na kuma yi mishi bayanin kwanakin da tayi a
gida shine ya hau ni da fada ina dalilin da zan
barta tayi ta zama haka ban dawo da ita ba?
Na ce, To naga baya nan ita kunma ta ce min
kace kana zuwa ya dai yi ta fada kan rashin
hankalin da ya ce nayi ita kuwa in ban da da
mutane a gidan nan yau da ta gane kurenta ba
kadan ba, don niyya yayi ya bata ka shi sosai, to
sai a ka rirrike shi, ya ce in. baka hakuri kafin Va
zo da kanshi.
Da sauri Babana ya ce mata, aa ba sai yazo
ba nima zan zo gidan, kuma ayi min godiya
76
amma gaskiya in ban da wannan bayani da ki ka
zo min dashi da kuma ganin girman surukuta ba
zan iya tozartata ba, wannan da cewa nayi ku
koma tare. To ina jin kunya.
Da sauri Delu ta yi ta magana tana ba shi
hakuri, "Ai shi ma maigidan ya ce ba karamin
abu tayi maka ba."
Kalamanta suka sanya har Babana ya shiga yi
mata bayanin abinda ya faru duka, a gabana tana
aibanta min yarinya har tana cewa wai da kadan
ta fi ta sanin duniya, me take nufi? Ni fa saboda
irin wadannan al'amuranne yasa nayi ta zama a
haka dagani sai 'yata, saboda bana son kananan
maganganu da fitina, ban saba da su ba.
Ni matata bata saba min