Showing 3001 words to 6000 words out of 26864 words
da ke
kina yi mini biyayya kina tattalin farin cikina,
kina kyautata min, ban taba yi miki umarni kin
ki bi ba, ban taba cewa ga yanda za ki yi kin ce
a'a ba.
A kullum ckin kiyaye bacin raina ki ke, to me
zan ce miki? In har akwai abin da ki ke yi min da
ki ke kuntatawa rayuwata ai bai wuce irin
wadannan kalmomin naki ba, tunda kin san me
suke nufi a gare ni, kina yi min nuni ne da zan
iya komawa in da na baro har gara ma wancan
lokacin ban taba danddanar wani madandani da
ya kwadaitar da ni son rayuwar duniya ba kamar
yanzu, to suma na yafe miki tunda nasan kina
17
cikin wani hali ne yasa ki ke yi mini hakan.
Ubangiji ya raba ki da wannan ciki lafiya.
Ni da nake kwance shiru a kan gado nake ta
faman kukan sharbe na kasa saukowa daga kan
gadon saboda tsoron kar a ce min in fita waje ba
wai don tsoron daren ba sai don tsoron kar a
hana ni ganin halin da Innata ke ciki saboda
nasan a duk lokacin da Babana ya shigo dakin
Innata ba a barina in shiga in ma ina ciki zan yi
sauri in tashi in fita tunda nasan ko ban yi hakan
ba ita Innan zata sani ni ce cikin zuciyata na
amsa addu' ar tashi na ce amin.
Mallam yayi maza ya ce na' am Ramatu me ki
ke son 6aya min? me ki ke so in yi miki? A
hankali ta ce mishi Mama ce. Gabana ya yanke
ya fadi jin ta ambaci sunana. Cikin natsuwa ya
ce mata "Eh, me Maman nawa tayi?
Ta sake rage murya kafin ta ce mishi, ka
baiwa Innata rikonta zata rike maka ita kamar
ina raye.
Cikin nutsuwa ya ce mata, In har ina raye to
a'a duk inda zan shiga zan shiga ne tare da ita,
zata rage min kewarki yayi maza ya share wasu
zafafan hawaye da suka zubo daga idonshi. Ita
din ai kama da ke take yi, kina raye ma nakan
kalle ta in yi mamakin kamanninta da ke balle
kuma in kin tafi kin bar ni.
18
Wasu hawayen suka ci gaba da zubowa daga
idanunshi har suna jika rigarshi, ban taba yi miki
karya ba, ba zan yi miki a wannan lokacin ba,
zan dai yi miki alkawari a duk lokacin da na
hango wata alama ta katsewar rayuwata, to cikin
taimakon Ubangiji zan mika mata ita.
Yana gama fadin hakan yayi maza yà miko
wata Jaka ya dauko wacce yasan nan Inna take
tara kayan haihuwarta yana cikin haka sai ga
Babah Sumaye da Baba Hodijo sun shigo alamar
kofar gidanmu ma a bude take sun kuma san da
abinda Inna ke ciki.
Mallam Bukar ga motar nan fa a waje mun
samota, da sauri Babana ya ce, To mu tafi."
Yasa hannu ya daga Inna ya tsaida ita, Babah
Sumaye ta daura mata zani tana fadin "Iko sai
mai shi." Gaba daya cikin ya tattara ya dawo
kirjinta.
Tuni na sauko daga kan gadon ina ta faman
kuka ina rike da hannun Innata wacce itama ta
kama nawa hannun ta kankame a cikin nata.
"Sake ta mu tafi, muje ki shiga gida ki samu
Jumare ku kwanta tare tazo tana nan a ciki, ki
kuma daina wannan kukan da ki ke yi, kiyi mata
addu'a kawai in Ubangiji ya kawo saukin
lamarin da sassafe sai ki ga mun dawo tare da
19
sabon yaronmu ko yarinya. Ki samu wata 'yar
uwar.
Wadannan duka kalaman Mama Sumaye ne
don haka na dan samu natsuwa har na wuce na
shiga cikin gidan nasu naje na samu Jumare
muka kwanta mu kuma namu gidan aka sa
kwado a ka kulle shi.
Jumare 'yar kanwar Babah Sumaye ce da ke
yawan zuwa wurinta, ta girme ni da shekarun da
suka kai hudu, don haka ta fini wayo tana ganina
ta ce min ke share hawayenki kizo muyi
kwanciyarmu haka ake yi in za a haihu gobe za
ki ga sun dawo da sabon yaro ko mace ko namiji,
wanne ki ka fi so?
Na dan yi shiru wai zan yi zabi, nan da nan
kuma naji bani da wani zabi bana ma dokin
abinda za a haifan tunda naga wahalar da take
ciki, bukatata kawai in ganta ne ta dawo gida
lafiya.
Duk da kalaman da aka yi min na Inna
haihuwa zata yi ba daga kwanciyata nayi bacci
ba saboda na riga na tsorata da abinda na gani,
daga baya ne kawai da yake shi bacci 6arawo ne
ya sadado yazo ya dauke ni.
Farkawa nayi daga baccin nawa a dalilin nayi
ya ishe ni ga kuma hasken rana da ya cika dakin
da sauri na diro daga kan gadon na fito dakin da
20
gudu, gidanmu nake nufin zuwa inga o zanga
Inna da sabon yaron da aka ce kan safiya zata
haife shi Jumare na gani a zauren gidan ta rabe
tana leke.
Nima na tayata yin leken don in ga abin da
take gani, cincirindon jama'a ne gaba dayansu
kuma maza babu mace ko daya gashi kuma
yawan nasu yakai inda ya kai.
Can gefe ga yara 'yan saffa suma maza mafi
yawancinsu kuka suke yi. Da sauri na kalli
Jumare meye a ke yi? Ta kara lekawa tana
kokarin tantancewa kamar fa rasuwa a ka yi
amma ban sani ba.
Muna cikin haka sai ga makara an fito da itaa
daga cikin gidanmu da mutum shimfide a ciki,
ina kallo a ka yi sahuana sallar amma wai ban
gane Innata ce a ciki ba, ina ji Jumare tana gaya
min wanda ya rasunne a ciki, na kuma ga zanin
Innata lullube kan likafanin amma kwata-kwata
ban kawowa kaina cewar ni ce na rasa Innata ba
saboda ban taba zaton zan rasata a wannan
lokacin ba, ban taba zaton zata daukan min
mahaifiyata ta raba ni da ita kamar yanda tayi wa
daruruwan yaran da ba za su kidayu ba.
"Waye ne ya rasu Jumare? nayi tambayar
cikin tsananin tsoro da firgita ba wai don ina
zaton abin ya kasance ne a kan Innata ba, sai dai
21
kawai don naga abin da ban taba gani ba, wanda
kuma yayi matukar tsorata ni.
Na sake yi mata tambayar mai yawa na sake
yi mata tambayar da sauri ta ce min, "Ke ban
sani ba. Saboda itama ta shiga wani yanayi na
kuma yarda har a yau dinnan na yarda Jumare
bata san Innata ake sallata ba.
Ban san yanda aka yi ba ina ganin an dauki
makarar nan an tafi da ita din, bin Jama'a sun bi
bayanta cincirindon yara suka yi ta dalewa kan
manyan motoči za su bi don yi mata rakiya na
kama kuka sosai da sosai Jumare tana bani
hakuri.
Daga baya ne kawai na soma jin matan da ke
wucewa ta bayangidan za su shiga gidanmu,
suna fadin "Ikon sai Ubangiji! Ashe Ramatu ce
ta rasu?
Ban san yadda a ka yi ba, ganina kawai nayi a
cikin gidanmu Yaya Dijah tana kankame dani a
jikinta tana ta faman kuka, bai yiwuwa in tsaya
kwatance ko bada labarin abinda ya faru. illa
iyaka dai kawai an yi zaman makokin Ina na
kwana uku cikin matsananciyar kewa da jimam
da addu'o'i ba daga wurin mu ya'yanta ko
mijinta ko danginta ba kawai. Har daga wurin
Jama'a masu yawa da suka santa ko suka Ji
22
labarinta wurin kira da mutanen da suka san
rayuwarta.
An watse daga zaman makokin Inna, 'yan
uwa da abokan arziki duk suka watse aka bar mu
daga mu sai mu a gidanmu, ina nufin daga
Babana sai ni sai ko Yaya Dijah da take nan bata
koma dakinta ba.
Muna zaune gaban Babanmu ni da Yaya
Dijah da take tashe da tsohon cikinta in ban da
kuka babu abinda take yi, ni kam nayi kukan na
gaji na bari watakila don ban gama fahimta ba
ko gama gane girman abinda ya same ni shi yasa
na hakyra da kuka na koma zare ido.
To yaya za ayi ai sai hakuri kawai, ita kam ai
ta huta wajen haihuwa.ta rasu banda haka kowa
alherinta yake fada, dubi kuma irin mutanen da
ta samu, kiyi hakuri kawai ki bar kukan muyi ta
addu'a Ubangiji ya gafarta mata, muka ce
Amin.
Duk da hakurin da Babana ke ta bayarwa na
muyi hakuri sau biyu ina ganinshi ya buya a
dakinshi yana nashi kukan.
Rannan da safe Yaya Ibahim yazo gaishe mu
dama kuma tunda a ka watse zaman makokin bai
taba fashin zuwa gaisuwar ba, suna gama
gaisawa da Babana yayi tasa mishi albarka. Da
zai tafi kuwa sai ya ce mishi in ka taso daga
23
kasuwar ka biyo ta nan ka tafi da matarka taie
gida ta huta a dakinta, sai kayi ta hakuri da ita.
Ya ce, To Baba yayi mishi godiya ya tashi ya
tafi, rannan da yamma Yaya Dijah ta koma
dakinta ba a wani dade ba kuwa ta haihu, ya
mace ta haifa, Yaya Ibrahim ya sanya mata
sunan Innarmu daga mu har Babanmu muka yi
murnar alherin da yayi mana.
Babah Sumaye ce taje ta zauna mata tayi
mata biki har tayi arba'in saboda Yaya Ibrahim
da iyayenshi sun ki yarda da dawowanta gida
suka ce tunda babu, Inna to me za ta dawo gida
kuma tayi?
Sannu a hankali sai mutuwar Inna ta rinka
shigarmu tana ratsa tsoka da kashi da bargo da
zukatanmu, gaba daya ta makurkusa mu ta canza
mu daga yanayin da duk muke tun ma dai ba
Babana ba.
A farkon al'amarin ni kam ma gani na rinka
yi tamfar karya ne tana can asibitin. ne kawai
watarana zata dawo wani lokaci kuma in rinka
jin tanfar wani mummunan mafarki ne da zan
farka in ga al'amarin ya sauya in da duk abin ba
haka ba ne amma ina?
Sannu a hankali sai kwanakin suka fara tafiya
daga daya har a ka je uku a ka yi bakwai har aka
kwana arba'in ban ga Inna ta dawo ba, babu ita
24
babu dalilintà sai dai yan uwanta da abokan
arzikinta su dan zagayo su duba mu a duk sanda
za su tafi kuma hakuri ne dai suke ba mu tare da
fadin Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa, ya
kuma sa alherinta ya bita, amma ita kam shiru
kake ji.
Wannan shi ne abinda yafi komai ba ni tsoro,
a wannan lokacin sai na zama babu abinda nafi
so irin in zauna in yi ta kuka saboda na riga na
fidda ran sake ganinta tunda ban taba ganin
randa tayi tafiyar da ta wuni ta kwana ba tare da
ta tasa ni a gaba ta tafi dani ba.
In ban da kewarta da kadaicin babu abin da
yafi komai damuna, ko ina yayi min fadi gani
nake tanfar ni.kadai ce a raye babu wani abinda
nake ji in ji na gani su balle in ji dadinshi in
tsaya bayani, na kewar da Inna ta bar mu a ciki
ma to na 6ata bakina ne na kuma san duk yanda
nakai da jin wani abu' kan rasata da aka yi to
Babana yafi ni, illa iyaka dai kawai shi baya
cewa komai.
In bani nayi mishi maganarta ba, ba ya yi
mini. In na cika kawo mishi zancenta ma sai ya
ce min yawaita yi mata addu'a zai fi yawaita
hirarta amfani in ce mishi to.
Tunda Inna ta rasu ba mu taba dora tukunya a
gidanmu da sunan yin girki ba, Babah Sumaye
25
ke sanya mana abinci rana da dare kamar yanda
ta rinka yi sanda Innarmu ke rashin lafiya.
Abin karyawa kuwa sayo mana nake yi wata
rana koko da kosai, wata rana waina da miya
wata rana shayi da burodi.
Kullum dai ni Babana yake tambaya me nake
so? In gaya mishi ya ce in je in da kudin suke in
dauko inje in saya, in na tati kan in dawo sai in
samu yayi sharar tsakar gida da kicin har da
wankin bayan gida muna gama karyawar sai in
tattara kwanukan da muka yi amfani da su in
wanke su in kife in uye ruwan wanka in je in yi.
Innata ma mata ce mai matukar tsabta, don
haka har bayan bata nan din ma ba ma iya barin
gidanmu da datti, kullum ka shigo tšab zaka
ganshi, kamshin turarenta ne dai a yanzu babu
shi a gidan.
Gidanmu gida ne na Jama, 8, kafin rasuwar
Inna amma a yanzu da bata nan wuni muke yi a
ciki babu wanda ya leko mu har yaran ma sun
daina zuwa dan gara gara ma Mansur jifa-jifa ya
kan shigo ya gaida Babana, ni kuma ya kawo
min dan wani abin lasawa.
Don haka nima ban cika zaman cikin gidan
ba in Jumare tana nan in shiga gidan Babah
Sumaye in bata nan in je wajen Babana in taya
shi sai da kayanshi sai ya taso in debo mishi
26
kwanduna mu dawo gida in shiga wurin Babah
Sumaye in karbo mana abincinmu mu zauna
muci tare a kwano daya ni da shi.
A duk ranar Juma'a kuma yakan sani in
shirya in je in gaida dangin Innata mafi yawanci
nafi zuwa gidan Yakunbo Halima wacce ita ce
yar Inna da take bi in naje wurinta wannan
Juma'ar sai wata Juma'ar, kuma in je wajen
Yaya Dijah.
Babana yana mutunta Yakunbo saboda sona
da take yi, sai dai duk da haka bai yarda ya bata
rikona ba duk da har turowa tayi a rokar mata
shi ya bata ni.
Sai ya ce a bata hakuri gani nan dai a tsakani
ai duk na ishe su. Tunda Yaya Dijah tayi arba'in
kusan duk sati sai tazo gidanmu sau biyu in zata
zo kuma takan zo mana da lafiyayyar miya
wacce take yi mana da naman kaji ko kayan
cikin saniya wata ran har ta kirbo mana sakwara
wai mijinta ne yake yin cefanen ya ce tayi ta
kawo mana mu rinka ajiyewa ko biredi ma rinka
ci da ita shima zuwanshi biyu wurin Babana kan
maganar ya basu ni.
Ya kalle shi yayi murmushi ya ce to in baku
ita Ibrahim kai da matarka ga kuma 'yarku sai in
kara muku da ita ni fa? In zauna ni kadai? Ai ba
zan iya ba.
27
Surukuta mai dadi Babana yake yi da Ibrahim
da kawai ya maida shi saboda yayi sa'a shima
Ibrahim din mutumin kirki ne ga sanin darajar
surukuta.
Don haka Baba yana sonshi yana kuma son
diyarshi da ya yi wa Innarmu takwara da ita ba
kadan ba har ma sai yayi mata lakani yake
kiranta da suna.
Rannan ina jin Babana yana cewa Ibrahim
din ka gayawa Dijah ta daina zirga-zirga da
yarinyar nan a kan hanya tana diban mata sanyi,
ya dan yi murmushi cikin girmamawa ya ce, Ai
ba komai Baba, Babana ya ce a'a ta zauna aa
dakinta kawai zuwan nata ba wani dadi ne da shi
ba tunda maimakon tazo ayi wata magana da ita
sai tazo ta wuni tana kuka gara ta hakura kawai
ta zauna a dakinta ya ce to Baba, ya tashi ya tafi
tun daga nan sai ya zama kannenshi ne suka
kawo mana duk wani abin da za su aiko mana da
shi ita kuwa ta koma zuwa jifa-jifa.
Inna ta rasu ne cikin watan Jimadah Thani,
sannu a hankali sai gamu mun iso cikin watan
Sha'aban har shima ya kusa zuwa karshe mutane
sai shirye-shirye da dokin isowar Ramadan suke
yi mukam a gidanmu ba a shirin komai.
Da Inna tana nan da mu ma muna nan muna
ta shirye-shirye abinda zuciyata take ta gaya min
28
kenan sai dai ban gayawa Babana ba saboda
yawan ce min da yake yi mata addu'a yafi yawan
hirarta amfani.
Ana gobe za a fara Azumi Babana ya bani
sugar mudu bibbiyu da madarar (Peak) dozin
dai-dai ya sani na bi yayun Inna mata da ke
gidan aurensu na kaiwa kowacce nata na gidan
Babanta kuwa shi da kanshi yaje ya kai musu
haka nan gidan Baba Hodijo.
Yaya Dijah kuma mu ma ta aiko mana da
abubuwa masu yawa kala-kala kuma masu dadi
na kamun Azumi.
Washegari kuwa mai alfarma Sarkin Musulmni
ya bada sanarwar ganin watan Ramadana mai
albarka don daukacin Musulmi maza da mata
suka yi niyyar daukan Azumi.
Sanda Inna ke raye na kan yi Azumin amma
ba mai yawa ba, ban san dalili ba a wannan
lokacin sai Babana ya ki yarda sai da nayi tayi
mishi kuka ya bar ni na dauka har watan ya kai
ashirin kuwa ban yi abin da yafi guda bakwai ba.
Shiga goman karshe da aka yi ne ya nuna
gabatowar sallah karama daga ko'ina sai aiken
kayan sallah ake yi min dangin Inna maza da
mata zai wuya a ce ga wanda bai yi min ba, sai
dai kawai na wani yafi na wani haka kawayen
Inna da Iyayen 'ya'yan da ta saba yi wa kitson
29
sallah da lalle kyauta, Babah Sumaye ma Yaya
Dijah da mijinta kam ba a maganarsu ga kuma
Yakunbo.
Babana ya tara kayan a gabanshi yana
dubawa, idanuwanshi suka cicciko da hawaye ya
ce, Wannan duk arzikin Ramatu ne Ubangiji ya
gafarta mata na ce mishi amin Baba.
Mun wayi gari a gidanmu ranar sallah kamar
yanda ta kasance a gidajen sauran Musulmi baki
daya, sai dai mu kam maimakon walwala da
farin ciki irin na sallah samun kanmu muka yi
cikin matsananciyar kewa.
Mutuwar Inna ta zamo mana sabuwa saboda
ganin babu kowa cikin kicin din gidanmu, da
yanzu tana nan tana fama da cincirindon yaran
dake karbar abincin sallah a kofar kicin dinta
wanda yawanci burabuskon gero take yi da
miyar yakuwa saboda shi ne mafi soyuwar abinci
a wurin Babana, sai kuma tayi masar shinkafa da
miya don rabo na sosai da sosai wanda ni zata yi
ta aika ina mikawa sai wadanda suka san da
burabuskon nata ne zaka ji suna aiko ni ki
gayawa Ramatu ta fa sanmun burabuskon nan
ina so, in ce musu to.
Yau kicin dinmu shiru babu kowa a cikinshi,
na shiga cikinshi har na gaji ina ganin kamar zan
30
ganta a mazauninta ban ganta ba, babu ita babu
dalilinta.
Ga fa kwanukan abinci nan an tara mana zo
ki zabar mana wanda zamu ci ki fitar da saura ki
samu masu ci ki basu don kar ya lalace nayi
maza na ce to Baba.
Nazo na dudduba na dauko kwanon
Yakunbo, tuwon shinkafa ne miyar kuka da man
shanu da yaji, ga kuma naman da nayi zaton na
Talo-Talo ne a ciki na ce mu ci wannan Baba ga
kuma masa da miya.
Mansur ya kawo na Yaya Dijah, kwan doya
ne da cincin mai nama da gasasshiyar kaza, sai
miya a wani kwano su na adana mana sauran
zan fitar in baiwa yaran da suke so ya ce, To.
Duk da lodin kayan sallar da ke gare ni ban
wani yi kwalliya ba,bayan wankan da nayi sai da
Babana ya ce min to gyara jikinki mana
Yahcuwuna kiyi kwalliya kamar sauran yara,
sannan naje nayi.
Nayi kyau ba kadan ba, ga kitsona da Babah
Sumaye tasa a ka yi min sun sauka har kafadata
na shiga gidan taga kwalliyata ta kuma aike ni
gidan su Jumare na kai musu abincin da tayi har
da gidan Yakunbo saboda mu'amallah sosai suke
yi a tsakaninsu.
31
Kwalliyar sallah sosai na rinka yi muka kuma
yi yawon sallah ni da Jumare wacce take ganin
ita din budurwa ce tunda 'yanmata a wancan
lokacin sha hudu ne sha biyar in an yi tsanani
sha shida wacce ta makara sosai sha bakwai.
Har gidan zoo Jumare ta kai mu muka kuma
samu goron sallah, osai wurin dangi da kuma
masu son Jumare.
Tun sanda Innata ta rasu ban sake zuwa
Makarantar boko ba, ko kuma ta Alkur'ani, ina
zaune ne kawai a gida bana komai tanfar dai a ce
da gani har Babana nawa mancewa muka yi da
ana zuwa Makarantar sallah da sati guda.
Ina tare da Babana, labarin yawon sallarmu
da Jumare nake ba shi yana jinjina kai cikin
yanayi na nuna alamar murna da gamsuwa don
dai ya kara min jin dadi da na gama sai ya kalle
ni ya ce min, gobe kuma ina za ku ke nan?
Nayi dariya na ce babu, ai hidimar sallah ta
Kare tunda yau sallah na da kwana bakwai.
Ya sake kallona ai kuwa dai haka ne hidimar
sallah ta kare kenan, na ce