Showing 1 words to 3000 words out of 24315 words
Chapter 1 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
[14/07 à 11:59] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...* 🪆
🪆
🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 1_2*
*AOKIGAHARA* shahararren daji ne a ƙasar Japon,wanda mutanen duniya sun yi itifaƙin cewa shi ya na ɗaya daga cikin hatsabiben dajika huɗu da suka yi shuran hatsari a duniya.Dajin zubar da jini,dajin fatalwa,shi ne laƙabinsa.
Mutane ne sama da ɗari jere rasa sun yi layi biyu,masu sanye da baƙaƙen kaya su ne a hannun hagun,yayin da uwanda suka saka jajaye suke hannun dama.Dukkansu da manya hulluna a kawunansu ta yadda ba a iya ganin fuskokinsu.Rugugin da tekun ta ɗauka ne ya saka su fara yin wani yare su na karanto wasu ɗalasamai “Kanzakhani yelolini,barhan yakulu,isbaryeyejanye” tamkar su na zuga shi haka yake yin sama ya na zafir kamar zai kamo sama bisanin can ya lafa ya yi tsit.
A hankali wani dattijo ya fito daga cikin ruwan ,a ƙalla zai kai shekaru sattin a duniya.Fari ne sol,ka na ganinsa ka Bayahude saboda gashin bakinsa da ya yi wani tsini da tozo.Fuskarsa a murtuƙe,ya zo ya tsaya a gabansu daga shi sai wani jan ƙyalle a ƙugu.
Shiru suka yi suka bar karanta ɗalasaman tsafin,daidai nan wata baƙar guguwa ta taso ta shiga saka wa mutumen nan da ya fito wasu fararen kaya tare da doguwar sarƙa har ta na shirin taɓo cibinsa.
Yaf! Yaf!Yaf aka fara yin wasu yayyafi,kamar haɗin baki a tare suka ɗago kawunansu da sauri har hullansu na fita su na mai furta “Shugaba Marlin! Shugaba Marlin! Shugaba Marlin!”
A hankali ya fara soma takawa,ya na bin ɗaya bayan ɗaya ya na tsaka tafukan hannunsu da wata aska.Tuni jininsu ya fara ɗigar da jini ya na ɗiga a ƙasa,a ƙarshe ya yankan nasa sannan suka je suka wanke hannayensu cikin Kogin.
*Bobby* cike da jarumta ya fito hannunsa riƙe da mashi,har ya nufi hanyar fita ya ji muryar Daddynsa “Bobby ina za ka je haka? Ko ka manta yau ranar murna ce shagali za mu yi?”
Bobby ya ce "Daddy training kawai zan yi ,ba zan jima ba”
Daddy ya gyara maɓalan suit ɗin jikinsa ya na mai cewa “babu inda za ka je,wuce ka canza kaya mu wuce ”
Bobby ya ɓata rai ya ce “wai Daddy murna mice ce? ”
“ta na samu ƙarin girma yanzu ni ne shugaba”
Mamy wacce ta fito cikin wata fitinaniyar doguwar riga wacce ko hannu babu ta ce “ chéri ka san Bobby bai son taron mutane kawai ka barsa,sai mu je mu biyu”
“waooo! Kin kyau muaaah” cewar Daddyn ya na mai zuwa ya rungume matarsa tare da sakar mata kiss,“na gode ta furta ta na godiya”
Ba don ransa ya so ba haka ya je ya shirya tsaf cikin baƙaƙen suit ya fito suka wuce.Babban shagali ne ake,duk wanda suka hallarci taron hamshaƙan masu kuɗi ne.Banda barasa babu abin da suke bankama,su na cashewa.Bobby na daga gefe ya na kallo kawai,shi sam bai son hayaniya.Aka riƙo hannunsa,ya ɗago kai sai ya ga Daddy ne.“Taso mu je na haɗa ka da abokaina ” ya miƙe ya bisa.
Wani waje na musamman suka shiga,Friends ɗin Daddy ne su biyu ko wane da Ɗansa.Bayan sun gabatar da kawunansu sai su ƴaƴan suka keɓe kansu.
“sunana Kameel Mohan”
“ni kuma Fadeel Martan”
“Bobby Marlin ne nawa sunan” ya faɗa ya na ɗan sakin murmushi.
Cikin ƙanƙanen lokaci suka yi mugun sabo kai kace wasu abokai ,wanda hakan kuma shi ne burin iyayen nasu wanda daga can gefe su na ankare da ƴaƴan nasu.
Baban Fadeel ne ya yi magana wato Martan ya ce “Na taya ka murna sosai da ka shigo tsagen mu ka zama shugaba kamar dai mu”
“Hhh! A kullum tunani ya na kan result ɗin ku,ina tambayar kaina ko cikin masu *Blue tsafi* wane ne zai zama zakara? Ashe kai ne” cewar Mohan wanda shi na sa tsafin kuma ya kasance *Jan tsafi*
Marlin ya murmushi ya ce “ duk na gode,Martan mi ya sa ka zaɓi *Baƙin tsafi* ?”
“saboda ni mugu ne na ƙarshen lamba,sannan ina samun kuɗi sosai a harakar don duk tsiyar mutum in na yi masa asiri ba zai warware shi ba”Martan ya faɗa wanda ya kasance Nasara ne.
Mohan kuwa shi baƙar fata ne asalin ɗan Senegal ne,ya ce "Ni kuwa abin da yasa na ɗauki *Jan tsafi* saboda a ƙasashenmu soyayya na wahalar da mutane,shi yasa musamman masu ɗawainiya da sha'awar wasu”
“Ni kuwa harakar Aljannun ruwa ita ta fi burge ne,saboda su na da cikon alƙawari ”cewar Marlin wato mahaifin Bobby.
“Ya kamata ƙungiyarmu ta samu ci gaba,a kawo sabbin abubuwa musamman saboda yaranmu da za su taso”
“eh kam! Wannan shawara ce mai kyau,a fara yin sacrifice ta yadda zamu samu kuɗi irin sosai ɗin nan”
“to ai dama ana sacrifice,kawai dai sani ne ba ku yi ba.Amma Ni na san da hakan saboda ina hulɗa da Aljannun ruwa" .
Ire-iren wannan hirarakin kawai suka yi ta yi bisanin taron ya watse kowa ya koma gida.
Bobby na kwance kan makeken gadonsa ya samu saƙon su Kameel akan yau za su fita da dare.Shi ɗin ba ma'abocin ƙiriniya ba ne kamar yadda duk ma'akasarin samari kan yi amma bai son baiwa abokan nasa kunya shi yasa ya ƙudiri aniyar zuwa.Ƙarfe tara cicif suka faka mota ƙofar gidansu,a nutse Bobby ya fito cikin shigar riga da wando na jeans blue da riga fara.
Fadeel ne ke driving,Kameel na gefensa yayin da Bobby ke can gidan baya.Sautin waƙar Céline Dion ke tashi,a haka har suka iso babban club ɗin.
“wooo! Dubi wata Baby kyakkyawa ta sha kyau” cewar Fadeel ya na daidaita tsayuwar motar,Kameel ya yi tsuki ya ce “ to kar ka bayar da mu mana,ka ja aji sosai”
“no yawuna sun tsinke doli na je gun ta” ya na gama faɗa ya buɗe murfin mota ya fita.
Bobby ya fito shi da Kameel suka samu haɗaɗen wuri suka zauna kan kujeru.
Serveur (irin masu aiki gidan abinci,wanda suke hidima da baƙi) ya zo ya ce “mi za a kawo maku?” Kameel na faɗin kalolin ababen kurɓewa shi kuma ya na rubutawa a jikin takarda,“shikenan abin da za a kawo banda abinci?”
“Bobby ko za ka ci wani abu ne? ” Kameel ya tambaya,ya girgiza kai ya ce “no! Ban buƙata in akwai sigari dai a kawo min”
Serveur ɗin ya ce “ok ku bani minti biyar” ya na faɗa ya yi gaba,bai jima ba ya zo ya didire masu abubuwan da suka buƙata.
Bobby ya kunna sigari ya na sha hayaƙi sai tashi yake,can ya ce “na tambaye ka mana Kameel,a can Senegal duk haka fatar ku take ko ya ya?”
Kameel wanda ke kwankwaɗar giya ya ƙyalƙyale da dariya bisanin ya ce “ana samun masu haske,amma mi yasa ka yi min wannan tambayar?”
“kawai dai ina tunanin yaya ƴan matan garin ku za su kasance ne,irin wannan baƙi kamar tukunya”
Kameel ya ɓata rai ya ce “ƴan ubanci ne za ka yi min? Hum! Ka san can farko na tsani Turawa saboda baƙar azabar da suka gana wa baƙaƙen fata”
“lokacin jahiliyya ne,amma ai baƙaƙen fata sun fi ƙarfi da juriya shi yasa ma nake son baƙar mace”Bobby ya faɗa ya na wani lumshe ido.Kameel ya ƙware da barasar da yake sha ya na ta yin tari bisanin ya ce,“ka na nufin ɓakar mace ta fi burge ka kan ƴan uwanka Nasaru?”
“Ni Bayahude ne fa,ina son mace baƙa sosai”
“halan ka taɓa tarayya da ita ne?”
“no ba haka ba ne,ni wannan harakar ba ta gabana?”
“pardon! Tu peux dire quoi exactement ? Ka na nufin ba ka taɓa sanin ƴa mace ba?” Kameel ya tambaye shi ya na wani tsure shi da ido.
Bobby ya girgiza kai ya ce “no! Ba haka ba ne,ka ga kawai abar maganar bani barasar na sha”
“Hum! Sha sai ka min bayani” ya cika masa kofi tare da miƙa masa, Bobby ya karɓa ya kwankwaɗe ya ce “ Kameel ka na son tuna min rayuwar baya ne?”
“A'a ina dai son sani ne”
“To je suis pas un puceau ! Na san mace amma ita ɗaya ce tal a duniya”Bobby ya faɗa ya na jin wani irin ƙunci na taso masa har ƙasan zuciya.
Kameel ya shiga yin dariya har da riƙe ciki ya ce,“ka na son raina min hankali ne ko mi? ” Bobby ya ɗan ware idonsa kaɗan,ya waiga inda su ka bar Fadeel ganinsa ya yi rungume da Babyn nan su na kissing da sauri ya kawar da kansa .
“aboki ya haka kuma? Ina za ka je?”
Bobby ya ɗan dafe kansa ya ce “ina ɗan jin jiri ne,bani keey na koma can cikin mota”
“a'a jira mu tafi kawai”Kameel ya faɗa ya na miƙe wa shi ma.
Bobby ya shiga gidan gaba ya zauna,yayin da Fadeel da budurwarsa suka zauna baya Kameel ya ja su.
A cikin mota sautin numfashinsu sosai ya takura Bobby,sam bai son ji ko ganin abin da ya shafi mu'amalar mace da namiji.Da sauri ya kai hannu ya buɗe volume duka ,sai kuma ya yi lamo cikin kujera a haka har suka iso gidansu.
Ko sallama bai yi masu ba ya fice ,ya na shigo wa babban falo Daddy ya kira sunansa “Bobby!” bai ko juyo ba balle ya tsaya,direct ɗakinsa ya wuce ya zube kan bed.
Daddy ya bi bayansa,gefen gado ya zauna ya fara shafar sumar kan Bobbyn bisanin ya ce “ya ne? Ya soirée ta kasance?” shiru Bobby bai ce komi ba sai goshinsa da ke tsatsafar da zufa.
Daddy ya ja wata doguwar ajiyar zuciya,ya na mai juyo da fuskar Bobby sai ya ga tuni ashe bacci ya ɗauke shi.
Fita ya yi ya nufi ɗakin sirrinsa,zigidir ya yi haihuwar uwarsa ya tsaya jikin madubi ya na karanta ɗalasiman tsafi.
Wani farin tsoho wanda gashin kansa yake kamar na giginya tsabar fari ya bayyana.Daddy ya lumshe ido sannan ya buɗe su ya na mai cewa “Father ina son sanin damuwar Bobby ne, wannan banzar tabi'ar ta shi na baƙanta min rai! Shi ne magajina wanda zai maye gurbina nan da wasu ƴan shekaru a haka mi zai tsinana wa ƁOYAYYAR DUNIYA ? ”
“Ba komai ba ne ke ɗawainiya da Bobby illa gubar soyayya da kuma sha'awa.Shekarun baya ya haɗu da wata ƴar Pakistan sun yi soyayya sosai wacce ta kai su da yin mu'amala tarayya,sai dai yadda Bobby ke da ƙarfi sosai ya rinjaye Anita ita kuma sam ba za ta iya juriyar hakan ba shi ne ta datse alaƙarsu.Bobby na son wacce za ta maye gurbin Anita sai dai ya na tsoron kar ita ma ta guje shi kamar waccan.Ɓangaren magie wato tsafi zuciyar Bobby na da girma sosai,RUHIN ALJAN zai yi wuyar ratsa ɓargon jikinsa!” Father ya faɗa cikin wata shaƙaƙar murya.
Wani tuƙuƙin baƙin ciki da tashin hankali ne suka rufe Marlin ,ya ce “mine ne mafita kenan?”
“Mafita ɗaya ce ka fara shirin rantsar da Bobby ayi masa wankan shiga ƙungiya tun yanzu.Sai an tsafa shi sosai ta yadda a nan gaba ba za mu sha wahala ba”
“Gobe zan shirya komi ba sai an ɗauki lokaci ba,yau babu meeting ana hutu ai da tun yau zan aiwatar da komi”
“A'a ba a tsafe Magaji da dare doli sai in zazzaɓin rana ya keto,za ku je can AOKIGAHARA ayi masa wanka da ruwan kogi daga nan sai ku je kusurwar dajin domin neman tabaraki” Father na gama faɗar haka ya ɓace.Daddy ya fita,ya koma cikin iyalansa.
A ɓangaren su Kameel kuwa can club suka sake komawa suka cashe ayarsu da ƴan mata.Sosai suka yi ta ɓarin kuɗi su na raye-raye,ƴan mata sun samu abin da suke so sai zubar da aji ake.
BOBBY
Wani mafarki ne ya yi mai kama da saƙo,ya na zaune kan kujera sai ƙoƙarin ɗora masa kambun sarauta ake amma abu ya cuttura.Tamkar ya hau kan garwashin wuta haka yake ji,so yake ya tashi amma kallon da Daddynsa ke yi masa ya ƙi basa wannan damar.
Kamar daga sama ya ga wata kyakkyawar sura ta bayyana gare shi,abin da ya lura shi kaɗai ke ganinta.Hannu ta saka ta kamo nasa tare da jansa ta fitar da shi daga cikin taron jama'ar,farin mayafin da ta rufe fuskarta ta fara ƙoƙarin cire wa daidai nan Bobby ya farka da wani matsanancin ciwon kai.
Washegari
Tun da suka yi breakfast Daddy ya shaida masa da akwai inda za su je.
Hatsabibin dajin suka je,tafiyar a jirgi suka yi ta.Kamar yadda Daddy ya yi tsammani tuni ƴan ƙungiyarsu sun hallara.
Bobby ya san da mahaifinsa na tsafi,ba baƙon abu ne gare shi ba amma bai yi tunanin layi zai kawo kansa ba.
“Bobby yau bikin ka ne,kar ka ji tsoron komi ina tare da kai.Duk wata matsalar ka za ta kau har Anita za ka manta da ita sannan ka samu wata wacce ta fi ta” cike da mamaki Bobby ke kallon Daddynsa,har zai yi masa tambaya sai kuma ya katse masa hanzari “ka cire kayan jikinka ka shiga ruwa ”
“Daddy...” da sauri ya ɗaga masa hannu,ba don ya so ba haka Bobby ya bi umarnin mahaifinsa ya cire kayan jikinsa ya bar ɗan ƙaramin wando.
Tuni members suka fara rera wakokinsu na ɗalasiman tsafi, Bobby ya shigar da ƙafafunsa girrr ! Haka ya ji kamar lantarki ya ja shi bisanin ya fara nutsewa a hankali cikin ruwan har suka kawo ga wuyansa,kansa na nutse wa suka ido huɗu....
[14/07 à 15:29] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 3_4*
Suka yi ido huɗu da kifi-mutum (irin kifayen nan masu rabin jiki na ƴan Adam ) fuskar Bobby ya riƙe gam nan take ya fara ganin wasu taurari na gifta masa.Ya ja shi can ƙasan ruwa,tuni numfashin Bobby ya fara barazanar ɗauke wa . Kifi-mutum wanda ya kasance Sarkin ruwan gaba ɗaya ya shaƙe wuyan Bobby na second uku nan take ya dawo hayyacinsa ya yi tsaye kan ƙafafuwan shi kai kace bisa doron ƙasa ne yake tsaye.
Ruguuuu! Kifaye suka fara ɓullo wa ta ko wace kusurwar kogin su na zuwa inda su Bobby suke,wannan ya saka ruwan motsawa su na zillo kamar za su taɓo sama.
Bobby na cikin ruwa amma ya na jin muryoyin mutanen da ya baro can gaɓar ruwa su na karanta ɗalasiman tsafi,wanda yake jin tamkar su na azalzala masa huta ne a gangar jiki.
Ga shi dai cikin ruwa yake tsumbul amma azababen zafi yake ji,ya na ratsa fatar jikinsa ya na shiga ɓargonsa.Idonsa ne abu na farko da ya fara ɗaukar caji,wani zuuuu! Nan take su ka canza launi su ka koma kore kamar na mage.
Sarki ya kwantar da Bobby bisa dutsen Barclay wanda a nan ne ake tsafar da bil'adama da ke son pouvoir/can/ƙarfin iko.Rawa dutsen ya fara yayin da fatar Bobby ta fara fitar da jini,wanda kafin ƙyaftawar ido ruwan kogin sun ɗauki launin ja.Tsit duk members ɗin suka yi da karanta ɗalasiman.Jikin Daddy ya ɗauki wani irin rawa kamar mazari hankalinsa ya tashi.
Ƴar kallon-kallon aka fara tare da yin zugum saboda wannan alama ce ta rashin sa'a.Kamar fitar tusa haka gangar jikin Bobby ya ɓullo daga cikin ruwa sam babu alamar numfashi a tattare da shi.
Father ne ya bayyana daga can tsakiyar ruwa dogon farin gemunsa na ɗigar da wani haske.“Kar ku jinkirta ku ɗauke shi ku shigar da shi NOIRA(wuri ne na musamman da ke cikin dajin wanda a nan ne duk hatsabiban hadarurruka ke ci) zai farfaɗo ku yi masa abubuwan da suka dace” ya na gama faɗa ya ɓace.
Mutum shidda ne suka ɗauki Bobby su na tafe su na yin wata waƙa kamar ta jinnu har suka isa kusurwar dajin.Tun daga bakin ƙofarsa gaban ka zai faɗi yadda wata ƙatuwar halitta ta yi bake-bake ta kace hanyar shiga.
Fukafukinta ta kaɗa hakan ya bata damar tashi sama ta shiga gaba su kuma su Daddy na take mata baya.Gidin wasu bishiyoyi uku masu kaloli ja,bulu da kuma baƙi aka kwantar da Bobby.
“Tun da ake kawo bil'adama ban taɓa ganin wanda ruhinsa ke da mugun ƙarfi ba kamar wannan.Shin ɗan wane addini ne? don bai yi kama da wanda bai da abun bauta ba” NATA wacce ta kasance ita ce mai gadin wannan kusurwar ta tambaya ta na mai kai hannunta ta shafi kumatun Bobby.
Wulk! Ya buɗe idonsa tarau kanta,da mugun sauri ta ja baya ta na mai ci gaba da kallonsa.
Cike da murna Daddy ya bada umarnin a fara karatu,duk suka lumshe ido su na jero ɗalasiman tsafi cikin salo.
Sayun bishiyoyin ne suka rinƙa ɓaɓakowa daga cikin ƙasa su na ɗaga Bobby sama yayin da kuma suke laulaye gangar jikinsa.
Ihu ya fara saboda tatsar shi suke kamar wata awara,an ɗauki kamar minti biyar kafin su yi ƙasa da shi nan kuma furanni suka fara zuba bisanin guguwa haɗi da cida.
Ruwa suka fara zuba kamar an karkata bakin ƙwayar,a na cikin haka dajin ya ɗauki wani irin duhu.Bobby ya yi saurin rufe idonsa saboda gane-ganen da ya fara yi,sai dai hakan ma da ya yi ba ta canza zane ba.Matattu kawai yake gani su na gifta masa sanye da fararen kaya,wasu kuma ƙwarangwal yayin da kuma wasu ke zo masa a siffar aljan-mutum.
“Daddy!” Bobby ya furta cike da tsoro jin hannu ya dafa kafaɗarsa,sai dai shiru Daddy bai amsa masa ba.Kukan Mujiya🦉 ne ya fara tashi busanin jemagu,da sauri ya sa hannu ya toshe kunnuwansa.
“shuuuwuu! Huuukmm! Rhooo!” sautin da ya fara ji kenan a kunne tamkar za a zaro amadun kunnensa.
Ya zabura ya miƙe tsaye ya na shirin guduwa,dajin ya washe ya dawo rana fayau.
Ido tulu-tulu Bobby ke kallon sawun namun daji da tsuntsaye,su Daddy kuwa sam ba su nan.Waige-waige ya fara,kamar daga sama ya ji muryar na magana “Sunana itaciyar BLUANT wacce ke sarrafa duk wani blue tsafi da ya shafi aljannun ruwa” kallon bishiyar ya yi sai ya ga launinta irin na sararin samaniya ne,daga gefensa kuma aka ce “ni