Showing 6001 words to 9000 words out of 24315 words

Chapter 3 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

127

Mansur ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba,sannan ya zo suka gaisa da ƙanen shi.
"Ina dawowa gida aka ce min har ka tafi,shi ne na zo na ji in lafiya?" Abba ya faɗa .
"Hum! Ta ga dama ta baka dama ka zo?"
"Don Allah Yaya ka bar wannan maganar ai dai gani na zo ta ƙorafi ta ƙare"
Kawu Mansur ya ɗan washe baki tare da rungume Abba ya ce "har na ji daɗi ƙanena,Habiba shimfiɗa min tabarma can gidin bishiya mu yi hira ni da ƙanena "

Ganin murmushi kan fuskar Kawu Mansur sai Abba ya ji wata irin nutsuwa.
Kan tabarma suka zauna su na hira ,kafin Halilu munafiki ya kawo hasashen kifi babba da ƙarami "Baban Twins wannan ne naka ,Baba kai kuma ka yi haƙuri ka ci wannan tunda kullum ka na ci" cike da munafurci yake faɗa tare da ƴar dariya .
"Babu komai ka basa har da nawa ɗin,ka je ka ƙara kamo wasu sai ya tafi da shi can gida" cewar Kawu Mansur ya na kishingiɗa.

Abba kuwa a duniya babu abin da ya fi so kamar kifi wannan ya saka babu jira ya fara ci,ya ce "a'a Yaya wannan ma ya ishe ni" jin haka ya saka Mansur ɗaukar nasa shi ma ya bi bayan Halilu suka koma can bayan gida su na ƙyalƙyata dariya.


Tsohuwa ta fito waje,"tsabar mugunta a gasa kifi shi ne ba za a ban ba?" Ta faɗa ta na tako a hankali.
Abba ya yi saurin raba wa biyu ya bata rabi, tsohuwa ta fara ci ta na saka masa albarka.
Kawu Mansur ya na dawowa ya ga kifi a hannun tsohuwa da mugun sauri ya ƙaraso ya na cewa "Tsohuwa ba dai kifin ne ki ke ci ba?"
Abba ya ce "Ni na bata ya na ga hankalin ka duk ya tashi?"
Kawu ya haɗiye wasu yawu ya ce "a'a babu komai"
Sai marice lis Abba ya koma can gida.




★JAPON


“Kar ku ji tsoro ai dama haka ne ƙa'idar dajin da zarar ka shiga yake rufewa ” Bobby ya faɗa ya na saka masu murmushi bisanin su ci gaba da tafiya.
Kameel ya yi ihu ya na mai dawowa tsakiyar su Fadeel.
“Lafiyar ka?”
“Wlh ji na yi kamar an taɓa kafaɗata” Kameel ya faɗa .
“Ku Afirka wa Allah ya yi ku da shegen tsoro,mu uku ne kawai to wane ne ya taɓa ka ɗin?” cewar Fadeel cike da masifa.
“Oho! Dai ina na nan tsakiyar ku ba zan gusa ba,dama ku da Aljannu banbacinku kaɗan ne”Kameel ya faɗa ya na wani riƙe rigar Bobby shi da ke gabansa.


Duwarwatsu ne ta ko ina yayin da gayen ya yi kore tsanwa shar,dajin tsit ba ka jin komai sai kukan tsuntsaye da kuma sawun sawayensu. A haka har suka shigo tsakiyar dajin inda yake mai faɗin gaske."Ƙwaƙwaƙwa! Tsutsutsu! Tsitsitsi!" Kawai ke tashi kamar ana ruwa.
Kameel ya ɗaga kansa sama,ido huɗu suka yi da wani tsuntsun mai manyan ido ya tattakura ya fasa ƙara ya na cewa “wayyo! Aljani! Aljani! Ku duba ”
Su ka kece da dariya Bobby ya ce “mujiya ce fa! ” Fadeel kuwa ƴar bangar Kameel ya yi sannan ya ce,“haka ake aljani? Mtsw! ”
“Ku biyo ni wannan ita ce hanyar shiga kusurwar dajin inda bishiyoyi ke magana” cewar Bobby ya na mai yin gaba suka take masa baya,Kameel sai waige-waige yake a haka har suka iso ƙofar shiga NOIRA wanda yake tamkar kogo.
Yau babu mai gadi,Bobby ya fara shiga sannan Kameel a ƙarshe Fadeel .


“Hiiyihiyi! Zhumm!” haka kogon ya fara ɗaukar wannan sauti bisanin ya fara juyawa kamar majaujawa.
Mutane masu fararen shiga suka fara ketowa ta ko ina su na dariya,wacce sautinta kawai ake ji amma ba a ganin fuskokinsu sai ƙwarangwal.
Abin da bai kashe Kameel ba, lokacinsa ne kawai da bai yi ba.Wani uban tsalle ya yi ya ɗale jikin Fadeel wanda shi ma a tsorace yake.
Bobby ne ya fara magana “kar wanda ya cutar da su abokaina ne,kar ku matso kowa ya tsaya inda yake” ya na maganar ne idonsa na ɗaukar wani irin haske .
Da sauri duk suka fara ja baya,domin hasken ba ƙaramin cutar da su yake ba.
“Kar ku ji tsoro ina tare da ku” Bobby ya faɗa wa abokansa,“Bobby ka fitar da mu don Allah zuciyata za ta tsinke” Kameel ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba.
Fadeel ya wani cire shi daga jikinsa ya ce “ƙaton banza matsoraci! Buɗe ido ka ga yadda fatalwa ke tsoron Bobby saboda miracle ɗin da ke fitowa a idonsa”


Kameel ya buɗe ido ya sauke su kan Bobby wanda har zuwa yanzu idonsa ke fitar da haske kamar wanda aka saka masa ƙwan fitila a ciki.
“Matsafi! Bobby kai matsafi ne?” Kameel ya faɗa cikin ɗaga murya ya na waro ido.

Dirar mikiya NATA ta yi masu ta ɗauke Kameel da Fadeel ta yi sama da su, bisanin ta fara magana cikin fushi “ka aikata babban kuskure na zuwa da bare a cikin kogon NOIRA wanda babu mai shigarsa sai wanda aka yi wa wankan TSAFI.Wannan kusurwa ce ta musamman domin members kawai,don haka zan saka abokan ka gidan Yari in ka na son su to ka kawo sacrifice ka fanshe su” ta na gama faɗar haka ta jefa su Kameel cikin wata raga da ke can rataye ga icce.



Bobby ya ɗaga kai ya kalli abokansa sai ihu suke su na neman agaji.
Hasken idonsa sam basa iya yi wa NATA komai.
Murya na ɗan rawa ya ce “Ki yi haƙuri daga yau ba zan sake ba” Nata ta sauko ƙasa ta na mai komawa ƴar matashiyar budurwa ta ce “a wannan duniyar ba a san kalmar haƙuri ba,jini ake bayarwa a maimakonta.In ka na so na sauko ma da su to ka kawo jinin ƴan yara biyu da ba su balaga ba kafin nan da faɗuwar rana” ta na gama faɗar haka ta wani hura masa iska a fuska,Bobby bai tsinci kansa a ko ina ba sai a waje kusa da inda suka ajiye mota......
[17/07 à 11:26] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆

```MRS SADAUKI```💫✍🏻

FCWA ☀️


*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂


*Page 7_8*


Bobby ya dafe kansa ,ya na mai sake duba yanayin garin da tuni duhun magrib ya fara ketowa.Tunaninsa ɗaya ina zai samu yara biyun da za ayi sacrifice ɗin? Ya na mugun son abokansa sai dai sam ya rasa tudun dafa wa.
Keey ɗin motar ma ya na can ga Fadeel ,a hankali ya fara yin tafiya bisanin gundu.
Ya gaji sosai,sai dai yin gudun shi ne mafita gare shi.Sama da minti ashirin kafin ya zo bakin hanya wacce take tsit tamkar an shareta.
Bobby ya riƙe ƙugu ya na haƙi tare da waige-waige,bai da nisa da dajin AOKIGAHARA ɗin wannan ya saka yake iya ganin abin da ke faruwa.
Wasu irin gizai-gizai ne baƙi ƙirin suka haɗu daidai dajin kawai sai walƙiya yake.Gaban Bobby ya faɗi,in ba zai manta ba ya na ɗaya daga cikin abin da Sarkin ruwa ya shaida masa.Da mugun sauri ya koma,ya fara gudu kamar ransa zai fita har zo hanyar da za ta sada ka da dajin.
A buɗe take,kawai shiga ya yi har ya isa ciki.



Kogon NOIRA ya shiga,ko tako biyu bai yi ba ya ji muryar Nata a bayansa “ina yaran biyu da aka ce ka kawo?”
Bobby ya juyo suka haɗa ido da ita,muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya ce “ban san inda zan same su ba” Nata ta shiga ƙyalƙyata dariya har sai da ƙasa ta amsa bisanin ta ce “Sacrifice ya zama dolai,ko kum....” ba ta ida kai ƙarshen maganar ba ta ji murya Marlin bayanta.
“Nata ki kawo mana su can gaɓar Teku ”
Da mugun sauri Bobby ya juya ya na ganin mahaifinsa ne ya ji wani sanyi a ransa.Sai dai yadda fuskar Daddy take kicin-kicin ya saka Bobbyn shan jinin jikinsa.



NATA ta ɗauko Kameel da Fadeel uwanda tuni sun fara fita hayyacinsu ta kai su gaɓar Teku .Daddy na fita Bobby ya take masa baya har suka isa can gaɓar ruwan.
Tuni an cire ma su Kameel kaya an saka su cikin ruwa,Bobby ya yi tsaye kawai ya na kallon Mohan da Martan.


“Ka matso kusa” Daddy ya umarci Bobby ,a sanyaye ya matsa tare da jerawa layi ɗaya da su ya rufe ido kamar yadda suka yi.
Kogin na fara yin ruguuuu suka fara karanto ɗalasiman TSAFI.Bobby bai san ta yaya ba amma samun bakinsa ya yi da rera harafofin.
An ɗauki sama da minti goma sannan kogin ya kwanta.Duk wata ajiyar zuciya suka sauke,Bobby ya kalle su a zuci ya ce ‘ko mi hakan ke nufi?’


Kameel da Fadeel suka fito cikin ruwa fatarsu na wani irin sheƙi ba kamar lokacin da suka shiga ba.
Cike da murna Daddy ya rungume su ya na mai cewa “Barka da shigowa cikinmu yarana” ko wanensu murmushi kan fuskar shi ya amsa ma Daddy bisanin su je ga iyayensu.


Kogon NOIRA suka dugunzuma,aka ci gaba da yi masu sauran tsibace-tsibace.Fadeel ya ɗauki baƙin tsafi,yayin da Kameel kuma jan tsafi.Bayan sun gama zaɓa aka basu wasu ruwa cikin wata tsohuwar ƙwarya.Ruwan baƙi ƙirin suke,su na shan ruwa duk illahirin gangar jikinsu ta ɗauki caji suka fara jin banbanci su na jinsu a duniyar sama saboda pouvoir/can/ƙarfin ikon da aka basu.


Bayan an gama komai iyayen suka fito.Bobby ya ce “na ji tsoro sosai abokanai na yi zaton zan rasa ku ne” Kameel ya ce “to ga shi a yanzu mu ma an yi mana wankan shiga mun zama ɗaya”
Fadeel ya karɓe da “a'a fa,abin da na lura kamar mun fi Bobby ƙarfin iko”
“Eh haka ne saboda ni ba a bani ruwa na sha ba sai nan gaba”


“Nan za ku kwana ko kuwa?” NATA ta tambaye su.
“Yanzu za mu tafi”
“Yauwa saboda akwai meeting da za ayi ”
Ko da su Bobby suka fito ba su ga mahaifan su ba.Cikin motar da suka zo suka koma,sai da suka biya inda suka ci abinci Bobby ya ɗauki motar shi sannan duk kowa ya kama gabansa .





“Bobby?” ya ji muryar mahaifinsa, ya dawo baya ya na amsawa “na'am Daddy ”
“Dube ni cikin ido”
“Daddy ban iyawa,ka yi haƙuri ”
“Mi yasa to ka yi haka?”
“Tsautsayi ne”
“Ka san irin haɗarin da ka saka rayuwar ƴaƴan mutane? Ba don Allah yasa na shiga ɗakin sirri ba na ga alamar matsala da sai ya ya kenan? ”
“Daddy nace ka yi haƙuri ba zan sake ba” Bobby ya faɗa a shagwaɓe ya na mai ɗagowa ya kalli mahaifinsa.
Daddy ya ja wani huci ya ce “zan baka wasu ɗalasamai da za ka yi bita kafin lokacin da za a ida naka rantsawar,ban so a samu matsala Bobby .Abokan ka ga shi nan sun shiga gaban ka,sai sun fi ka saurin samun matsayi”


“Daddy ni fa ba wani son wannan abun nake ba”
“To ka manta da Anita kawai!” Daddy na faɗa ya miƙe tsaye,Bobby ya ce “No Daddy ina sonta sosai” murmushin gefen baki kawai Daddy ya yi .



Bobby ya shiga ɗakinsa ya yi wanka,ya canza kaya.Kwnonking aka yi ya bada izini,Janash ce ta shigo riƙe da tray .Kan ƙaramin table ta ajiye masa ta ce “ga abincin ka nan,Madam ta ce na tabbatar ka ci sosai”
“Fita!” shi ne kawai abin da ya furta,Janash ta fice da sauri.


Wayarsa ya ɗauko ya yi danne-danne sannan ya kara a kunne“Mamyyyy!” ya faɗa kamar zai yi kuka,can ɓangaren ta ce “ya ne Bobby? Ka ci abinci?”
“Ina ki ka tafi ba tare da na sani ba?”
“Wajen meeting ,ba zan dawo ba sai dare ya yi sosai”
Ya furzar da iska ya ce “okay! Na ji!” ƙittt ya kashe wayar .

Abincin ya ci bisanin ya fara aiki a system ɗinsa,a haka har dare ya tsala sosai a gajiye kwana ya ɗauke shi.



Ƙarfe biyun dare agogon Japon ta buga,a lokacin da kowa ke kwance ya na bacci su Daddy kuwa farke suke su na shagalin murnar samun wasu members.
Fadeel da Kameel tamkar wasu sarakai haka aka yi ta gaishe su.Kalolin jus kuwa babu kalar da babu wanda ainahi ana sarrafa su da jinin bil'adama.

Zoben tsafi aka baiwa kowanensu ya saka a yatsan tsakiya na hagun bisanin taron ya watse.


Washegari
Daddy ne tsaye kan Bobby da ke ta sharar bacci.A hankali ya fara bubuga kumatunsa ya na kiran sunan shi,Bobby ya yatsina fuska ya na mai buɗe ido.
Daddy ya sakar masa da murmushi,“tashi ka yi wanka ina son kai ka wani wuri”
Bobby ya yi wani tashi da sauri ya shiga toilet,a nutse ya yo wanka ya fito.Cikin suit farare ya shirya kafin ya je can falo inda Daddy ke jiransa.
“Bonjour la famille !” Bobby ya furta,Mamy ta ce “Morning Babyna” ya yi mata kiss a goshi ya ja kujera ya zauna,Janash ta yi saving nasu.


Bayan sun gama Daddy da Bobby suka fito,direba ya ja su a mota.Tafiya mai nisa suka yi kamar za su barin gari bisanin su isa wani ƙaton waje wanda aka yi masa doguwar ƙatanga kamar ta gidan fir'auna.


Ƙaton gate ɗin aka buɗe,“wooo! ” Bobby ya furta saboda aljannar duniyar da ya gani.Kusan unguwa guda ce Daddy yasa aka tsara masa haɗaɗen gida mai game da masana'antar shi.


Ma'aikata ne birjit ta ko ina,baƙaƙen fata sun fi yawa sai aiki suke tuƙuru.Duk tsayawa suka yi su na gaishe da su Daddy,cike da tausayi Bobby ke kallonsu har da mata da ƴan mata.



“Kar ka wani tausaya masu kuɗi suke so,duk yarinyar da ka gani nan to iyayenta ne suka kawota don yi aiki a biya su ” Daddy ya faɗa ya na mai jan hannun Bobby ya fara zagaye da shi.
“Amma Daddy su matan bai kamata ace su na aikin ƙarfi ba,wai su na ma cin abinci kuwa?”
“Akwai ma'aikatan da kawai aikinsu girki ne,wasu kuma wankin kwanoni.Maleek?” Daddy ya ƙwala kiran wani saurayi,da gudu ya ƙaraso “ka kai Bobby ko ina na wajen nan ,zan shiga daga ciki ai ka shirya komai ko?”
Maleek ya ce “Eh yalaɓai tun jiya da ka shaida min za ka zo na shirya komai”
Bobby ya bi bayan Maleek,ya na sake nuna masa wasu wuraren.



Daddy kuwa katafaren sashen ya nufa ,ya na buɗe ƙofa ya hangeta zaune kan gado cikin shigar kaya shara-shara.Ya lumshe ido ya na jin wani sanyi a ransa, Babyn ta haɗu sosai.Ta na ganinsa ta fara fari da ido kamar yadda Maleek ya shaida mata don saye zuciyar shugaban nasu.
Daddy bai wani ɗauki lokaci ba suka fara masha'ar shi da yarinyar da a haife ya haifeta.Wannan shi ne halin Daddy holewa da ma'aikatan shi wanda musamman ya ɗauki Maleek aiki don duba masa wacce zai rinƙa holewa da ita a duk ƙarshen mako.
Bayan ya gama biyan buƙatarsa ya shiga toilet ya yi wanka,ita kuwa tuni ta saka wasu kayan wanda suka ɗan suturta jikinta.




A gajiye Bobby ya ce “Mu je ka kai ni wurin Daddy ”
Maleek ya ce “Yalaɓai akwai wurin da ban kai ka ba,mu je lambu can za ka huta sosai sannan ga ƴaƴan marmari wanda za su sa yawun ka su tsinke”
Haka Bobby ya bi bayansa suka shiga lambun,Maleek da kansa ya rinƙa wanke su apple da sauran su ya kawo gaban Bobby .Ya na tsaka da ci wayarsa ta ɗau ƙara,ya na dubawa sunan Fadeel ne da sauri ya ɗaga “aboki ya ne? Mun zo gidan ku ba ka nan”
“Eh mun fita ni da Daddy ne,ya ne ko ta samu ne?” Bobby ya tambaya.
“Eh mun shirya shagali ne akwai ƴammata iri-iri har da Black Baby musamman na yi oder domin ka”Kameel ya faɗa ya na dariya alamu wayar a main libre/ hand free take.
“yaushe ne za ayi shagalin?” Bobby ya tambaya.
“Tuni an fara don wuni ɗaya za mu yi muna holewa, please ka bar Daddyn ka kawai ka tawo”
“Ok gani nan zuwa” Bobby ya faɗa ya na mai tashi tsaye,ya dubi Maleek ya ce “mu je akwai inda zan je”




Direban da ya kawo su shi ya tuƙa Bobby ,tuni ya shaida ma su Kameel inda za su haɗe ko da suka kawo mararrabar hanya ya tsinkayi motar Fadeel .
Da ɗan sauri ya fita ya je ya same su,ihu suka yi kafin Fadeel ya ja mota a guje sai waƙa ke tashi.
Gidan da suka ɗauka don yin shagalin suka yi tsinke,komai ya tsaru kan tsari.Black Baby kusan goma aka tanada saboda Bobby ,Fadeel ya zo dab da kunnensa Bobbyn ya ce “ka zaɓo biyu zafafa wanda za ka shiga da su,na ɗauki nauyin biyansu”
Bobby ya ɗan yamutsa fuska ya ce “babu wacce ta burge ni,tsantsaninsu ma nake”
Kameel da ya ji furucin Bobby ya ce “mine? Mi ka ke tsantsani?”
“Wai Black Baby” Fadeel ya basa amsa.
“Ina ƙawar ka wadda ka ce duk nacin namiji za ta iya da shi?” Kameel ya tambayi Fadeel shi kuma ya basa amsa da “ta na bisa hanya za ta zo”
“To ai shikenan,ita baturiya ce ƴar uwar ka hakan ya yi?”


Bobby ya ce “yes!” cikin wani ɗaki suka shiga Fadeel ya saka system ɗin da ke kula da duk wata Camera a gaba.
“Kameel ka lura da kyau ka zaɓa mana ƴammatan da suka fi ƙurciya domin sacrifice”
“Sacrifice? Ku tsaya,mine ne ku ke shirin yi?” Bobby ya tambaya.
Shiru duk suka yi,sai yanzu Fadeel ya farga ashe Bobby bai fara zuwa meeting ƙungiya ba.


“Bobby Babynka ta iso ga shi ta na kirana” cewar Fadeel ya na duba screen ɗin wayarsa.Bobby kuwa tuni ya manta da wani zancen sacrifice ya ƙura ma system ido ya na kallon haɗaddiyar babyn da ke tsaye bakin ƙofa.

“Jira na je na tarbota” cewar Bobby.....




★SENEGAL


Tamkar mai ciwon haihuwa haka tsohuwa ke saffa da marwa goshinta kuwa sai fitar da gumi yake.Kawu Mansur kuwa kukan jini ne kawai bai yi ba da ya je gun boka ya tabbatar masa da tabbas tsohuwa mutuwa za ta yi kuma aiki ya rushe ba zai kama Abba ba.


Tsakar dare sosai, tsohuwa ta fara shaƙuwa kafin wani lokaci ta ce ga garinku nan.A gaban idon Kawu Mansur ta mutu,ransa ya yi baƙi ƙirin.A duniya babu wace yake so sama da mahaifiyar shi,ita ɗin BANGO ce.
A cikin wannan daren ya kira Ayub sai dai bai ɗauka ba.


Washegari
Abba bayan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login