Showing 12001 words to 15000 words out of 24315 words
Chapter 5 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
yawu bai ma iya furta komai ba.Fadeel da ke can gaban Camera ya ga abin da ke faruwa ya fito da sauri,can ɗakin suka koma su duka.
“Sabitry dama duk abin da ki ke da tsafi ki ke amfani ban sani ba?” Fadeel ya yi mata tambayar ya na mai dafe goshi.
Kameel ya ce “Allah ya yi sa'a ta na fitowa na ci karo da ita,ba don haka ba da shikenan ta saka rayuwar abokinmu cikin cakwakwali”
“Wai don Allah mine ne ke faruwa,kaina ya ɗaure! Daddy ya kira ni ya ce kar na bari ta gusa ku kuma ku na wani zance”Bobby ya tambaya ya na son samun haske.
“Bobby wannan yarinyar da ka ke gani muguwa ce,za ka iya kiranta da BOKANYA kai tsaye.Duk ƙarfi da juriyar da aka ce ma ta na da to tsafi ne,da zarar ta kwanta da namiji babu shi ba zaman lafiya sannan ƙarfin jikinsa za ta dinga tatsa su na saffara abubuwan tsafinsu” Kameel ne ya basa amsa.
Bobby ya yi masa wani kallo irin kamar ban gane ba, wannan ya saka Kameel ci gaba da cewa “ni ma na fahimci haka ne saboda ƙarfin iko da nake da a duniyarmu” kafin wani ya sake yunƙurin yin wata magana aka turo ƙofa.
Daddy ne,fuskarsa ta yi jawur.Wani gigitacen mari ya ɗauke Sabitry da shi wanda ya saka ta faɗuwa ƙasa wanwars ba ta shirya ba.Gashin kanta ya cakumo ya ɗagota sama,kuka ta fara ta na basa haƙuri.Bakinta ya taɓe ya saka yatsansa manuni wanda yake ɗauke da zoben tsafi a ciki.Kamar yadda gashi in ya shiga cikin ruwa ko mai yake yin sama haka wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga bakin Sabitry ya na shiga zoben Daddy.Can ya yi yarɓi da ita ya na mai cewa “Ƴar iskar yarinya! Ke kin yi kaɗan ki taɓa rayuwar yarona wanda tun kafin ya zo duniya nake kula da duk wani motsinsa saboda mugayen mutane irin ki” ya gama faɗa ya fita.
Jiki babu ƙwari Sabitry ta fice,yayin da su Kameel kuma suka samu kujeru suka zauna.
Fadeel ne ya ce “ban taɓa sanin da tsafi take aiki ba,sai yau.Shi ma ɗin don yanzu ina cikin ƙungiya ne”
“Kenan in mutum na cikin ƙungiya ya na iya gane duk wani mai amfani da asiri ko tsafi?” Bobby ya tambaya.
“Eh sosai! Da ace Kameel bai ganta ba da shikenan ” cewar Fadeel.
“To ai ni ma ina cikin ƙungiyar ko?” Bobby ya faɗa,a tare suka kece da wata irin dariya bisanin Kameel ya ce “kai fa dutsen Barclay bai karɓe ka,wanda kuma shi ne yake babban jigon ƙungiya ”
“Sai nan gaba sannan ka shigo sawun mu ka ƙara haƙuri ”
Bobby ya ɗan taɓe baki ya ce “ni fa ban wani damu da harakar tsafi ba,kawai don ban son baiwa Daddy kunya ne”
“Ko ma dai mine ne mu je mu yi shagali” cewar Fadeel tare da miƙewa,su ma suka mara masa baya.
Bobby wuri ya samu ya zauna kawai,sosai ya yi mamakin ta yadda aka yi har Sabitry ta ɗauki hankalinsa alhalin shi duk matan duniya su da maza duk ɗaya suke a wurinsa in ka fidda Anita.
Ya lumshe ido tare sakin murmushi,a hankali ya furta “ina son ki Anita ” bugun zuciyarsa ne ya ji ya amsa.
Sosai aka yi shagali aka cashe bisanin duk kowa ya kama gabansa.
Bobby na zuwa gida Daddy ya tarbe shi da pasport ɗinsa wanda tuni an yi masa VISA .
“Ga shi gobe in Allah ya kai mu jirgin ka zai tashi zuwa Pakistan,na yi magana da mutumena ya yi bincike kan Anita ya gano inda take.Lambar wayarta da address ɗinta duk a wajen shi za ka samu” Daddy ya faɗa ya na miƙa masa pasport ɗin.
Wani tsallen murna Bobby ya yi,ya rungume mahaifinsa sannan ya shiga sumbatarsa ya ce “na gode sosai Daddy bari na shiga ciki na haɗa kayana”
Mamy wacce ke zaune kan salon ta ce ,“My Prince tuni na haɗa maka komai ya na cikin trollyn ka,fatana kawai ka more rayuwar ka.Ina son ace ko da ka ke dawo wa ƙasar Japon ace kai da Anita kun yi saka zoben alƙawari in son samu ne ma ace da Baby a cikinta”
Dariya duk suka shiga yi, Daddy ya mirza sumar kan Bobby ya ce “to ka ji dai don haka ka sa himma! Je ka yi wanka ka zo ka ci abinci”
“Ban jin yunwa,zan dai huta ne don na gaji sosai” Bobby ya faɗa ya na mai haurawa sama passeport ɗinsa a hannu.
Bayan ya yi wanka ya shiga group ɗin su na WhatsApp ya shaida wa abokansa.A nan ne shi ma Kameel ya sanar da su za su koma Senegal shi da mahaifinsa.Fadeel duk sai ya ji babu daɗi sam sai babu yadda za su yi....
★SENEGAL
Sai da Kawu Mansur ya danne zuciyarsa sannan ya bar su Twins domin su ci gaba da karatunsu.Habiba wacce ta fita daga boko tun primary malami ya ɗaukar mata ya na koya mata a gida,sannan kuma ɗaya ɓangaren Zahra na koyar da ita.
Sosai ta maida niyya wannan ya saka,Kawu biya mata kuɗin makarantar ita ma sai dai irin ta ƴan gayu ce mai masifar tsada.
Ranar farko da Habiba ta shiga aji,sai ta zama banban da sauran.Duk da dai kowa uniforme ce a jikinsa amma duk ƴan matan sun sha kwalliya sun zubo gashi,wasu gashin doki ne ma amma banda ita.
Yadda ta ga ana kallonta ya saka ta gane bai rasa nasaba da burkiɗeɗen hijabin da ke jikinta.
Bayan ta dawo gida ta baiwa Zahra labari,“Habiba kar ki biye masu ki ci gaba da shigar da ki ka saba mana.Kin ga ni da Bintu After dress muke ɗora wa a saman uniforme ko ke ma ita ake nemo miki?”
“A'a ina son ni ma gashin kaina ya koma dogo har ga baya ”
“Wai kin ɗauka gashin kansu ne? To na doki kuma babu kyawu saka shi”
“Ni dai kam ya burge ne zan shaidawa Baba ya bani kuɗi sai ki yi min rakiya na sayo”cewar Habiba ta na jin son ganin canjin rayuwarta.
“Ok babu damuwa,yanzu dai mu yi karatun Alkur'ani zuwa dare sai na koya miki lesson”
“Kai na gaji sosai ki bari zuwa dare ni ma sai na koyar da ke”
Zahra ta maraice fuska ta ce “don Allah Habiba ki tausaya ki faɗa min ko da aya biyar ce” ba don ta so ba ta yi wa Zahra ƙarin karatu kasancewar ita Habibar ta na da ilimin addini.
“Ku zo ku ci abinci,ina Bintu ?” ina ta tambaya ta na mai ajeye trayn abinci a tsakiyar falo.
“Ta na ɗaki,wai kanta ke ciwo” cewar Zahra .
“To ku zo ku fara ci,bari na tasheta ta zo ta ci abinci sai ta sha magani” Inna ta faɗa ta na mai nufar ɗakin su Bintu.
Tsakiyar gado ta tare da ita ta yi rub da ciki,“Bintu? Bintu?” ba tare da ta amsa ba ta ce “taso ki ci abinci sai na baki magani” kai ta girgiza ta ce “ban jin yunwa” Inna ta ce “kin sha magani ne?” ta girgiza kai alamun a'a,da sauri Inna ta fita babu jimawa ta dawo hannunta riƙe da kofin ruwa da kuma magani amma ƙememe Bintu ta ƙi sha sai da Inna ta je ta kira Halilu wanda a yanzu ta fara jin tsoronsa.
Fuska ya haɗe cikin bayar da umarni ya ce “ki tashi ki sha” kuka ta fashe ta na mai cewa “ni ba zan sha ba, chocolat nake so”
Halilu ya dubeta sake da baki ya ce “kenan lafiyar ki lau?” kai ta ɗaga masa ta na shagwaɓe fuska.
“To tashi ki shirya mu je mu sayo” da murna ta sauka daga bed ɗin ta shiga toilet ta wanke fuskarta.
Gaban madubi ta tsaya ta shafa mai da hoda sannan ta juyo ta dubi Halilu wanda duk inda ta yi idonsa na kanta,Inna kuwa dama tuni ta yi tafiyarta .
“Ka fita ina son canza kaya” ta faɗa a sanyaye.Halilu ya maƙe kafaɗa ya ce “a'a ba zan fita ba,kawai ki canza na yi miki alƙawari ba zan kalle ki ba”
Bintu ta turo baki,zumbulele hijabi ta saka ta yadda ba za a ganin ƴar ƙaramar rigar jikinta ba.
A jere suka fito,su na daf da shiga mota suka ji muryar Kawu Mansur kamar aradu “gidan uban waye za ki kai min Ɗa? ” a tare suka juyo su na kallonsa.
Bintu ta taɓe baki bisanin ta kawar da kai gefe,“Baba za mu tafi mall ne ba za mu jima ba”cewar Halilu cike da nutsuwa don yanzu ya ƙara wayewa.
“Ita ta dawo kai ka tafi”
“Lilu wuce mu tafi don Allah rana sai gasa ni take” Bintu ta faɗa a mugun shagwaɓe,wanda ya saka Halilu tattaro hankalinsa kanta.
Murmushi ne ya suɓuce masa jin da sunan da ta kira shi,uwa uba kuma yanayin maganarta.Bai san lokacin da ya buɗe mata ƙofar mota ba ta shiga,shi ma ya zagaya ya zauna ya yi wa motar key suka bar Kawu Mansur tsaye sake da baki.
A cikin mota Halilu sai surutu yake zuba mata kamar Akun kuturu,har suka isa mall ɗin.Kai kace wata Baby haka ya ɓata kuɗinsa wajen saya mata kayan maƙulashe da kuma wani ƙaton Teddy pink.
Lokacin da suka dawo sun tarar Kawu Mansur na ta balbalin masifa kamar zai tadi gidan.Ko kaɗan babu tsoronsa a fuskar Bintu ,ido cikin ido suke kallon juna da ita.
A zuciye ya kifa mata mari ya na mai cewa “shegiya mai ido tsakar kai,ke ga ƴar iska wacce ba ta samu tarbiyya ba.Dama ta ya ya barewa za ta yi gudu ɗanta ya yi rairafe.Amma zan yi maganin ku ke da munafukar uwar ki” ya na gama faɗa ya sa hannu zai karɓe ledar hannunta,da sauri Halilu ya tare shi ya na cewa “Bintu shiga ɗaki gani nan zuwa”
Idonta sun yi ja amma ba ta yi kuka ba,wata uwar harara ta banka wa Kawu bisanin ta wuce ciki.
Zahra ta bi bayanta,falon sai ya rage Kawu da iyalansa.
“Baba wannan abun da ka ke sam ba ka gyara min,ka yi kowa sanin irin mugun son da nake yi wa Bintu .Da ya ya na yi na samo soyayyarta? Aiki na yi tuƙuru babu dare babu rana sannan na samu ta fara saurarena,amma shi ne kake rushe min ginin da na tsara”
“Halilu rufe min bakin ka,mahaifin ka ne fa.Kuma ai ba ka fi shi sanin daidai ba,abin da ba ka sani ba rabin dukiyar Marigayin Ayub Bintu ce kawai ta san inda take sannan akwai takardun da doli sai ta saka hannu sannan su zama mallakinmu.Ko ka yi tunanin banza yasa har yanzu ni ban fito da mugun halina ba? ” Inna ke faɗa ta na matsowa kusa da Ɗanta.
Halilu ya ce “ni dukiya ba ta gabana Inna ,wlh na fi son Bintu fiye da duk komai na ƙyalƙyalin duniyar nan.In kuka kwantar da hankalin ku ni nan da kaina zan karɓo komai,ya kuke gani in na aureta?”
Kawu Mansur wanda takaici ya rufe da sauri ya yi gaba,ɗakinsa ya shiga .In akwai abin da ya tsana to ya na bayan zur'ar Ayub ,ba don gudun zargi ba da guba yake zuba masu duk su mutu.
Safa da marwa ya fara ya na tunanin malam Mohan da aka ce masa gobe zai shigo Senegal.Kamar wani zararre ya fara magana shi ɗaya “zan yi maganin ki,gobe in Allah ya kai mu ƙarfe bakwai na safe a Joal zai yi min! Hum! Haba! Duk za ku ci ubanku ”
Halilu kuwa ɗaki ya bi Bintu nan ya tarar su na rigima ita da Zahra akan teddyn da ya sayo.
“Lilu wai ita ma sai an saya mata ko kuma ta toye shi” Bintu ta faɗa ta na dariya har dimple ɗinta ya lotsa.
Halilu ya dafe goshinsa ya ce “oh! Shaf na manta da komai iri ɗaya ku ke yi,Bintu laifin ki ne amma in sha Allah da dare zan sayo mata”
Sai a lokacin Zahra ta saki ranta, toilet ta shiga don lokacin makaranta ya kusa.
Halilu ya zauna kusa da Bintu ya ce “ina sonki sosai” ta dube shi da sauri yanayin fuskarta na canzawa.Ya ja dogon numfashi ya na shirin kamo hannunta ta yi saurin tashi,“zo ki zauna babu abin da zan yi miki ” ya faɗa ya na mai kafeta da ido.
Ta maƙe kafaɗata haɗi da turo baki gaba ta ce ,“ni dai don Allah ka fita”
“Don mi?”
“In dai ka na sona ka fita”
“Hakan shi zai sa ki yarda ina son ki?” kai ta gyaɗa masa da sauri shi kuma ya miƙe,ta gabanta ya wuce ya yi ƙoƙarin yi mata kiss a goshi ta ture shi ya yi dariya fita.
Zahra na fitowa ita ma Bintu ta shiga ta yi wankan,sannan suka shirya suka tafi islamiyya.
Ko da suka sauko tuni har Halilu ya sayo wani teddyn da murna Zahra ta ɗauke shi ta na cillawa sama.
“Wai sai yaushe Mama za ta dawo?” Bintu ta tambaya.
Zahra ta ɗan tsaya da abin da take sannan ta ce “Sati ɗaya ta ce”
“Ciwon ƙafa ya ƙi ci ya ƙi cinye wa kamar wacce aka asirce” Bintu ta faɗa cike da damuwa.
“Zato zunubi ne” Zahra ta faɗa.
“To Malama na ji,yanzu dai zan kwanta”
“Ana shirin yin magrib ɗin?” Zahra ta tambayeta,ko dubanta ba ta yi ba balle ta bata amsa haka ta yi kwanciyarta ba ta jima ba bacci ya ɗauke ta.
Sai bayan sallar isha'i Bintu ta tashi agajiye.Wanka ta fara sannan ta yi sallolinta ta fito ta ci abinci sannan ta wuce wurin su Zahra da suke karatu ita da Habiba.
Washegari
Kamar yadda Kawu Mansur ya yi alkawari hakan ce ta kasance.Tun da safe ya tashi direba suka je Joal,sai dai ga mamakinsa duk uban sammakon da ya yi akwai uwanda suka riga shi.Ko wane cikin gizner sai ƙamshi ke tashi,da Kawu ya ga alhazzai sai da ya raina kansa.
Haka suka yi ta jira da ɗaiɗaya ake shiga har layi ya zo kan Kawu Mansur.
Kansa ya fara shigarwa ya buɗe baki da niyyar yin sallama sai kuma ya yi shiru sakamakon aljannar duniya da ya gani.Ɗakin tarben client ɗin kai kace fadar Sarkin Makka tsabar haɗuwa da kyau.
Can bisa wata kujera ya hangi wani baƙin mutum a zaune ya hakimce hannunsa riƙe da wata ƙatuwar lula mai haske .
Muƙut! Ya haɗiye wasu yawu kafin ya ƙarasa,da hannu Mohan ya yi masa nuni ya na mai cewa “ba a kallon cikin idona muddin ka na son tsira da ganin ka”.Kawu Mansur ya zauna kan capet ɗin a gabansa,ya wani sunne kai.
Mohan ya ci gaba da cewa “mi ke tafe da kai?”
Kawu ya yi gyaran murya ya ce “dama aiki nake son ayi min kan wata yarinya....” kafin ya ida Mohan ya ce “ta na da taurin kai ne,sannan duk da ƙarancin iliminsu na addini mahaifinsu ya koyar da su yadda ake riƙe Tauhidi shi yasa bokan ka ya gagara aiki a kanta.Amma tunda ka zo nan komai ya wuce ”
“Ina son a aika mata baƙin aljani wanda zai hanata shaƙat har sai duk dukiyar da ke hannunta ta dawo gare ni” Kawu Mansur ya faɗa.
Mohan ya ce “ba ma tura aljani haka kawai sai da sharaɗin aure”
Kawu Mansur ya ɗago,da sauri ya mayar da kansa zuciyarsa na bugawa saboda ganin kamannin Mohan ya canza daga nan bil'adama sak.
Cikin rawar murya ya ce “kamar ya aure?”
“Na ɗaura masu aure da aljanin,zai rinƙa amfani da ita kamar yadda ma'aurata ke yi har su haifi yara” Mohan ya basa amsa ya na mai kallonsa.
Kawu Mansur ya washe baki ya ce “ai hakan ya yi don ina so a ƙarshe ya haukatar da shegiya”
Mohan ya ce “ƴar ɗan uwan ka ce ko?”
Kawu Mansur ya gyaɗa kai,Mohan ya ce “ok ka na iya tafiya”
“Ba ka faɗa min nawa zan bayar ba”
“Sai in na gama aiki ake biya”
Kawu Mansur ya fito zuciyarsa fara tasss.....
400 ne kacal za ki biya domin karanta littafi na ɗaya da na biyu na wannan littafin wacce ta shirya za ta iya tura kuɗinta ta wannan account ɗin
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank
Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN na 400,ƴan Nijar kuma carte Moov ko airtel ta 400f
[22/07 à 07:37] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 13_14*
Tamkar daren sallah haka Bobby yake ji.Tun da ya sauka a filin jirgi Léo ya zo ya tarbe shi ya kaisa can inda zai zauna.Cikin shiga irin ta ƴan Pakistan ya shirya har da wani ɗora farin rawani akai,sai kuwa ya yi kyau sosai.
Léo ya miƙa masa duk wasu takardu masu ɗauke da bayanai kan Anita ,sannan ya ce “ka kula da kyau kamar yadda na shaida ma mahaifiyar Anita musulma ce,mahaifinta kuma Kirista ne don zan iya ce maka ma kusan kowa ya san shi a garin nan saboda yawan wa'azinsa da kuma taimakon da yake raba wa al'umma”
Bobby ya saki ɗan murmushi ya ce “kar ka damu Léo duk zan kula,salamu aleykum! Shi ne gaisuwar musulmi ko? ” Léo ya jinjina kai alamar eh,Bobby ya ci gaba da cewa “Mohamad shi ne wanda suka fi so duk duniya,saboda shi ne shugaban annabawan su” Léo ya ce “annabawan mu dai! Ya na gaban Annabi Musa ”
Bobby ya ɗage kafaɗu ya ce “sunan fa ina Bayahude ne ,amma da za ka yi min tambayoyi kan annabinmu ban sani ba” Léo ya ce “don mi?” “saboda ni ban yarda da ko wane irin addini ba” Bobby ya basa amsa ya na mai ɗora baƙin gilashi a fuska ,da sauri Léo ya cire shi ya na mai cewa “no! Kar ka saka shi”
“ok mu je ka ajiye ni”
Harabar hotel ɗin suka fito,Léo ne ya tuƙa su har zuwa wani haɗaɗen gida mai zagaye da furanni.
“Ka sauka ka ƙwanƙwasa,zan jira ka a nan”cewar Léo .
Bobby ya fita daga mota ya je ya yi knowking ,an kai minti biyu kafin wani ya buɗe alamu sun nuna dai mai gadi ne.
Bobby ya yi masa sallama bisanin ya tambaya “wajen Anita na zo” Cike da wata irin murna ya buɗe masa gidan.
Bobby ya sa kai,mai gadin