Showing 9001 words to 12000 words out of 24315 words
Chapter 4 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
dawo daga sallar asuba ya duba wayarsa.Jikinsa har rawa yake wajen maida kira ,da kalmar “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” ya sauke wayar daga kunne.
Mama da ke shafa addu'ar sallah ta ce “baban Twins lafiya?”
“Tsohuwa ce ta rasu?”
“Wace tsohuwar ? Innalillahi!”
“Ki je ki sanar da Twins su shirya za mu tafi Djifer” Abba ya faɗa ya na mai zama bakin bed hawaye na zubo masa.
Da kuka Mama ta zo ta sanar da su Kakarsu ta rasu su shirya za su tafi ƙauye.Zahra ce kawai ta yi kuka ta na yi wa kakarta addu'a yayin da Bintu ke masifar za su tafi ƙauye ita fa ba son zuwa take ba.
Cikin kayan atamfa suka shirya sannan kuma suka haɗa wasu kayan cikin akwati.Direba ya ja su zuwa ƙauyen Djifer,Abba ne zaune gidan gaba yayin da Mama da Twins ɗinta suke baya.
Ko da suka isa tuni ƙofar gidan ta cika da mutane .Halilu ne ya karɓi kayan su shi da abokansa suka shigar da su ciki,sai wani baza ido yake ya na kallon Twins ya na son banbance wace ce sanyin idaniyarsa don mugun kama suke.
“Wai lafiya kamar wani tsohon maye ka ke wani rarraba ido ka na kallona? Mtsw baƙauye kawai”
“Laaa! Bintuna,kin ga fa dama so nake na tantance ki sai gashi kin yi halin naki ” Halilu ya faɗa cike da fara'a don ba ƙaramin so yake yi mata ba.
Mama ta ce “mai hali ai bai fasawa,kin ga kowa ba shaida ƙwarai yake yi miki ba.Wajen masifa kawai ake gane ki”
Bintu ta turo baki ta na gunguni haɗi da hararen Halilu wanda sam ya kasa kawar da kallonsa gare ta har suka isa can cikin ɗaki.
Gaisuwa suka fara yi wa junansu,Inna da Mama ita kuwa Habiba kusan su Twins ta koma ta na yi masu sannu da zuwa.Zahra ce kawai ke amsa wa cikin sanyin halinta.
Kawu Mansur na ganin Abba ya je ya rungume shi ya na kuka,ya ce “ɗan uwana shikenan tsohuwa ta rasu, Allah sarki rabon ku ga juna” yadda yake kuka kamar wani ƙaramin yaro sai ya baiwa kowa tausayi.
Abba na kuka ya fara rarrashin Yayansa tare da jajanta ma juna.
Gawar tsohuwa aka fiddo wacce tuni an yi mata wanka an suturceta.Sallah aka yi mata bisanin a ɗauke ta zuwa maƙabarta ,a gaban kabarin Kawu Mansur ya zube ya na kuka dakyar aka rarrashe shi suka dawo.
Bintu duk a takure take,sam ta tsani mutane ita rayuwarta ba ta son takura.Tsukin da ta yi ya cika buhu, can ta miƙe ta fito waje.Zahra da Habiba suka biyo ta,ta ɗan taɓe baki ta ce “Su kuma kalar al'adar tasu kenan an yi rasuwa amma shinkafa da miya aka dafa”
“Eh kin san jiya da Abba ya zo duk ya kawo su,to babu wake a ciki” Habiba ta bata amsa,Bintu ta ce “shi ne kuma ba ku iya sayen waken?”
“Bintu don Allah ki yi shiru,kar fa ki manta mutuwa ce ba wani buki ba” cewar Zahra.
“Ke ni zaman gidan nan ya ishe ni,dubi tsabar munafurci ba su tashin yin kuka sai sun zo nan mtws! ”
“Ku zo mu ci abinci”Habiba ta faɗa ta na ɗauko tray guda na shinkafa da miya.
Ba su yi breakfast dama,Zahra ta tsugunna ta fara ci ita kuwa Bintu kallon hadarin kaji ta fara yi ma abinci kafin ta ce “Ni kifi nake so” Zahra ta ɗago kai ta na kallonta,Habiba ta ce “bari na faɗa ma Halilu sai ya kamo miki ”
“Da gaske?”Bintu ta tambaya cikin jin daɗi
“Eh jira ni” cewar Habibar ta na mai fita ƙofar gida,ta kuwa ci nasarar ganin Halilu da hannu ta yi masa alama ya zo.
“Bintu ce ta ƙi cin abinci wai kifi take so”
Halilu ya washe baki “ok ce ta jira na kamo sai ki gasa mata”
Habiba ta dawo ta shaida ma Bintu yadda suka yi da Halilu ,ba a ɗau lokaci ba kuwa ya dawo hannunsa riƙe da manyan kifi har uku.
Habiba ce ta gasa duk suka ci,sai a lokacin Bintu ta ɗan saki ranta ta na mai cewa a zuci ‘ashe su na da kirki’....
[19/07 à 10:00] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 9_10*
Kawu Mansur ne zaune a gaban boka ana yi masa bugun ƙasa.
“Aikin ka na da girman gaske! Haɗarinsa kuma shi ya fi komai cakwalkwali.Ba zan ɓoye maka aikin nan ya fi ƙarfina,amma in ka ji za ka iya zan haɗa ka da babban malami Mohan sai dai fa shi aikinsa ba maganar kuɗi ce ba” bokan ya faɗa ya na kallon Kawu Mansur wanda zuciyarsa ta ƙeƙashe babu ɗigon imani.
“Ko ma mi yake buƙata zan basa muddin buƙatata za ta cika.Yadda ya yi sanadiyar mutuwar maifiyata to tabbas shi ma doli ya bi bayanta.A ina zan samu shi Mohan ɗin?”
“Nan cikin Senegal yake a wani ƙauye da ake kira Joal sai ban tsammanin ya na nan saboda duk ƙarshen shekara su na haɗuwa can ƙasar Japon domin a ƙara masu ƙarfin iko”
Maganar boka ta sanyaya zuciyar Kawu Mansur,sai yake ganin tamkar ma har burinsa ya cika.
“Zan je na tambaya” ya furta ya na sakin wani murmushi.
“A'a ba sai ka je ba,jira na kira maka shi ta madubin tsafi” bokan ya faɗa tare da tashi ya ɗauko wani madubi da yake rufe da jan ƙyalle.
Ya shafi madubin ya na ambaton surkulle,babu jima wa muryar Moha ta bayyana “Ya aka yi bokan bokaye? ?”
“Aiki ne aka samu ranka shi daɗe,talaka ne shi bai da kuɗin da zai iya biyanka da su wannan ya saka na ga gwara ayi masa aikin daga nesa kamar yadda ka saba”
“In ya amince da sharaɗin to ya rubuta ya ajiye ɗan uwansa zai mutu a yau ba sai gobe ba” Mohan ya faɗa,ko kafin ya rufe baki ya ce “na yarda” kalmar yarda da ya furta ya saka boka kifar da madubin tsafin.
Kawu Mansur ya koma gida,nan ya tarar da Abba su na ta shirin kowa ya gida kasancewar tuni an yi sadakar bakwai.
Har mota suka yi masu rakiya,Halilu wanda ke ta ƙoƙarin ya saye zuciyar Bintu wani awarwaro ya bata ta ƙi karɓa duk da a ido ya yi mata kyau.
Ta na shirin shiga mota ya kamo hannunta tare da saka mata shi,ta wani harare shi kamar idonta za su faɗo ƙasa.
Direba ya yi wa mota key suka fara sharara gudu sai da Abba ya yi masa magana sannan ya rage.
Das! Das! Das! Haka sautin bugun zuciyar Abba ke ɗan canza yanayin bugawa.Hannu ya kai da niyyar kunna ƙira'a amma wani abun mamaki tamkar wanda sanƙarau ya kama haka hannun ya sandare.
Wata ƙatuwar Mujiya ce ta dira a gaban motar tare da fara bugun glass ɗin ta na son fasa shi.Bakin Abba ya kasa furta komai ,sai kai da yake faman girgizawa.
Babu mai ganin Mujiyar sai shi ɗaya,kamar ƙyaftawar ido motar ta kife.
Kasancewar har sun fara shigowa gari ya sa suka samu agajin gaggawa.Abba da direba an mutu nan take,Mama ta samu kariya a ƙafa yayin da Twins kuma suka sume don firgici.
Kawu Mansur na samun kira,ya kwashi duk ahalinsa suka tafi can asibitin da aka shaida masa.
Kuka yake wiwi kamar ransa zai fita,a ƙasan zuciyarsa kuwa tamkar ta saurayin ango.
“Ga gawarwakin can a mutuware ,ka sa hannu sai a baka su” wani likita ya faɗa ya mai miƙa ma Kawu Mansur wasu takardu.
Mai gadin gidan gawar ne ya yi masa iso har ciki.Gawar direban aka fara buɗe wa bisanin ta Abba,da sauri Kawu Mansur ya ja baya ya na kallon ɗan uwansa babu ido sai gurbinsu.
Muƙut! Ya haɗiye wasu yawu bisanin ya fita.
Da kuka Mama ta farka,su Twins ta gani ko wacce kwance sanye da ƙarin ruwa.
Abba ta fara kira ta na gwanjin kuka,Inna ce ta fara bata haƙuri sai dai ta ƙi yin shirun.
A can waje kuwa Kawu Mansur ya kira dangi da abokan azirki domin sallatar gawa.Har aka kai su makwancinsu ya na tunanin ta ya aka yi Abba ya rasa idonsa sai dai babu damar tambaya don ya na tsoron abin da zai je ya komo.
Su Twins ko da suka farka suka samu lafiya.Tare da mahaifiyarsu suka shiga kukan rashin Abba don ƙiri-ƙiri Kawu ya shaida masu rasuwar.
Sati guda currr ta yi a asibiti sannan aka sallamo su.
Kawu Mansur da iyalansa tuni sun babakere da komai na Abba,sai abin da ya ce ake zartarwa.Ya cire su Twins daga makaranta a cewar shi tunda Habiba ba ta yi boko ba su ma ba za su yi ba.
Mama na zaune Zahra na bata abinci a baki,hawaye suka zubi mata shaaa.
“Mama don Allah ki bar kukan nan tunda Abba ya riga ya mutu,a yanzu addu'ar mu yake buƙata”Zahra ta faɗa ta na goge mata hawayen.
“Shikenan kuma sai a gurgantar maku da karatu? Babban baƙin cikina da ba zan iya tafiya ba da wlh tuni mun bar gidan nan”
“Dukiyar ubanmu fa? Shikenan sai mu tafi mu bar masa? ”Bintu ta tambaya.
Mama na shirin magana Kawu Mansur ya fito cikin wata gizner fara .Fuska ya turniƙe ya na mai cewa “uwar mice ce kuke faɗa?” duk shiru suka yi sai Bintu ce ta murguɗa baki ta na cewa “abin da kunnuwan ka suka ji” yatsunsa biyar ya sauke mata a fuska.
Ta fasa ƙara ta shiga rera kuka kamar amaryar lalle, da sauri Inna ta fito wacce ke kitchen ta na yi masu girki.
“Kawun yara za a fita?” ta tambaya ta na wasar baki,kallonta ya yi sai ya ga ta ƙara yi masa kyau sam bai taɓa sanin haka Inna ke da kyau ba ashe talauci ne ya nakasata.
“Eh zan tafi can office ,kin san na ɗora wani yaro akai shi zai rinƙa yi min aiki kafin Halilu ya kammala karatun sai na ɗora shi matsayin tunda dai ni ban yi boko ba”
“To Allah tsare ya maido ka lafiya,irin wannan ɗawainiya da kake Allah biya ka .Da wani ne ai banzatar da Iyalin ɗan uwan zai yi” Inna ke faɗa cikin kalar tausayi ta na kallon su Mama.
Kawu ya fice bayan ya amsa addu'ar da ta yi,ita kuma ta koma kitchen.
“Mama sam abin da Baba ke yi bai kyauta ba,duba fa ki ga ya hana Twins zuwa makaranta.Ina ma laifin ya ce su dinga koyar da ni har na cimma masu?” Habiba ta faɗa wacce ke taya mahaifiyarta aikin.
Shiru Inna ta yi kafin ta ce “kuma fa kin kawo shawara,ina ga haka za ayi bari har ya dawo”
Cike da murna Habiba ta ce “yauwa Innata!”
Girkin suka ci gaba da yi har suka kammala,Habiba ta zo falo gun Zahra su na ƴar hira yayin da Bintu ke can gefe sai cika take ta na batsewa a zuci kuma ta na zagin Kawu Mansur.
Wanka Inna ta yi,ta zaɓi kalar kayan atamfa cikin na Mama ta saka sannan ta fito falon.“Sannu Hajara ya ƙarfin jikin?” Mama ta dube ta sannan ta ce “alhamdullah!” “ko a zuba miki abincin?”
“A'a ban jin yunwa”
“To babu damuwa,Zahra ki kuna mana kallo mu kalli dandali” cewar Inna ta na kallon Zahrar.
Cike da ladabi ta ce “toh!” ta tashi ta fara harhaɗa wayoyin ta kunna masu Arewa24.
Ana suka shiririce har lokacin cin abinci ya yi,Inna ce ta zuba ma kowa kafin su je su yi sallah.
Bintu kuwa kan bed ta kwanta,tunani take yadda duniya ta yi masu juyin waina.Ta ja wani ƙyaci,Zahra da ke karatun Alkur'ani ta ɗago ta dubeta “ke lafiyar ki?”
“twin yanzu saboda Allah mafarkina na zama cikakkiyar lauya ba zai cika ba?” kawai sai ta fashe da kuka.
“Haba Bintu ya kike yin abu kamar wata ƙaramar yarinya wacce aka cire daga mama? Ina ce dai a gaban ki ranar nan malam ya ce ilimin boko iyakar mu da shi nan duniya ne.Ki gode Allah da bai hana mu zuwa islamiyya ba,kuma Kawu ai tamkar Uba yake a wurin mu?”
Cike da takaici Bintu ta jefe ta da pilow ta ce “je can wawuya,ni bai haife ni kuma har abada ba zan ɗauke shi matsayin Uba ba” ta na gama faɗa ta tashi ta shige toilet.Shower ta sakar wa kanta ta na ta faman kuka.
Kai kawai Zahra ta girgiza bisanin ta ci gaba da yin karatun.
Kawu Mansur sam bai da yarda wannan ya sa ya ƙara Camerorin tsaro fiye da can farko.Bai iya komai ba,sai dai yaronsa ne ke yi masa aikin shi kuma ya na daga gefe.
Sai zuwa marice ya shigo gidan,bayan ya yi wanka ya ci abinci Inna ta same shi da maganar da suka yi da Habiba na zancen su Twins su koma makaranta.
“Zan yi tunani akai” shi ne abin da ya faɗa.
“Wane tunani kuma? Don Allah kawai ka amince”
“Ina baƙin cikin zuba kuɗin da za su yi karatun ne”
“Haba Kawun yara,su fa kuɗin nan ainahi na ubansu to miye da ka zuba masu?”
Cike da ɓacin rai Kawu ya fita.Ana daf da yin kiran sallar magrib ya saka direba jansa a mota,ba su zarce ko ina ba sai ƙauyen Djifer.
“Ka tsaya nan ka jira ni ina dawo wa” Kawu ya faɗa ya na mai bin wata hanyar da za ta kaisa gun bokansa wanda a yanzu ya na cikin aminansa.
“Mansur ne? Ai kuwa kamar ka shiga zuciyata ina son ganin ka.Da akwai wata matsala da na ga ta na tunkaro ka” boka ya faɗa.
Kawu Mansur ya samu wuri ya zauna ya na mai cewa “ai kuwa dai ita ɗin ce ta kawo ni,ina son ayi min asirin da zai saka kaf ma'aikatana da su kansu ahalin gidan su dinga shakkata da mugun tsorona”
“In dai wannan ne babu matsala an gama”
“Yauwa sannan ina son ka haɗa ni da wannan malamin Mohan”
“Sai wani sati mai zuwa yake dawowa ” boka ya basa amsa.
Kuɗi ya basa kafin ya koma gida,shi kuwa boka tun a daren ya fara aiki...
★JAPON
Da sassarfa Bobby ya iso gare ta,“Salut!” ya furta ita ma ta mayar masa da “Hi!” ya ɗan murmusa bisanin ya tara mata hannu.Sai da ta kalle shi da ƴan ƙananan idonta bisanin ta saka nata hannunta.A hankali suka fara tafiya hannunsu sarkaye da na juna,Bobby ne ya ce “kin zo kin tsaya kamar wata baƙuwa”
“Eh to mice ce ? Ban san kowa ba a nan sai wanda ya gayyace ni kuma shi ne nake kira”
“Kenan ni ba ki sanni ba?” Bobby ya yi mata tambayar ya na mai tsayawa da tafiyar,ta kalle shi cikin ido kafin ta ɗan girgiza kai.Ya kama haɓarta ya ce “yauwa ko ke fa! Sunana Bobby ke kuma fa?”
“Sabitry”
“Jolie nom! Nice name” ya furta daidai nan suka shigo ɗakin show ɗin.
“thank you”
Wurin zama suka samu suka zauna,sai ƙoƙarin kiran lambar Fadeel take yayin da shi kuma Bobby ke ɗan baza ido ya na kallon masu rawa.
Muryarta ya ji “Tu veux danser?/Ka na son yin rawa ne?”
Ya ɗan yi murmushi ya ce “pourquoi pas? Surtout avec une charmante comme toi/mi zai hana, musamman da kyakkyawa irin ki”
“ok allons-y” ta faɗa tare da tashi tsaye,Bobby ya miƙe shi ma tare da jan hannunta suka fara yin rawa irin a hankalin nan su na kallon juna cikin ido.
“An taɓa faɗa miki ke ɗin kyakkyawa ce?”
“Hum! In ma ba a taɓa ba ai ga shi kai ka faɗa”
“Gaskiya ki na da kyau, musamman idon ki am...da kuma laɓan ki” Bobby ya faɗa ya na mai ƙura ma lips ɗinta ido,Sabitry ta ce “Allah sa dai wannan zancen naka har zuci yake”
“Don mi?”
“Saboda dayawan maza mayaudara ne, musamman in su na son kwantawa da mace”
Bobby ya ɗan saki murmushi ya ce “ba cewa na yi ina son ki ba fa! Kawai na ce ki na da kyau”
“Daga ƙarshe kalmar so ɗin ce za ta biyo baya”
“Shikenan mu yi dai rawar,ko kin gaji ne?”
“In na gaji mi za ayi?” ta tambaye shi idonta ƙur cikin nasa.
“Eh to! Na kai ki ɗaki ki kwanta”
Wata dariya ta yi ta na mai kai hannunta kan fuskar shi ta ce “wai gaske? Hutun zan yi ko kuwa dai?” sai maƙe masa ido ɗaya.
Bai ce mata komai ba ya ja ta zuwa wani ɗaki,kai kace wata matarsa haka suka holewarsu.
Bobby ya dubi Sabitry ko ƙyaftawa bai yi,“ya dai irin wannan kallon?” ta tambaye shi.
“Ina mamaki ne kawai yadda ki ka jure min” dariya ta shiga yi kamar mahaukaciya kafin ta ce “Wai da gaske,halan budurwar ka raguwa ce”
“No matata dai”
Da sauri Sabitry ta dubi hannunsa sai ta ce “ya aka yi ban ga zoben aure ba?”
“Sai nan gaba za mu yi aure ” ya bata amsa.
Sabitry ta ɗauki jakarta dama tuni ta kimtsa ta tashi ta fita,Bobby ya yunƙura zai tashi wayarsa ta ɗau ruri.
Daddy ne,ya na ɗagawa ko magana bai yi ba Daddyn ya ce “Bobby duk rintsi ka nemo yarinyar nan da ka kwanta da ita,in kuma ku na tare kar ka bari ta gusa gani nan tafe” ƙittt ya kashe wayar,zuciyar Bobby ce ta fara dakan tara-tara.
*Uwanda suka shirya za su iya fara yin payement don free page na dab da ƙarewa 400 ne kacal za ki biya kuɗin karatu book na ɗaya da na biyu ,ki tura ta wannan account ɗin*
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank
Sai ki turo min da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin mtn,ƴan Nijar kuma carte Moov ko airtel ta 400f.
MRS SADAUKI 💫
[20/07 à 17:10] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 11_12*
Da mugun sauri Bobby ya fita,duk da bai san taƙamaimai mine ne ba amma ya san Daddy ba zai kiransa kan banza ba.
Cak ya tsaya ganin Sabitry na fizge-fizgen ƙwatar kanta gun Kameel da ya yi mata wani mugun riƙo.
“Mais lâche moi! Ka sake min hannu!” shi ne abin da take ta faman faɗa,kowa na ɗakin taron ya tsaya cak ya na kallonsu.
Muƙut! Bobby ya haɗiye wasu