Showing 18001 words to 21000 words out of 24315 words

Chapter 7 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

130

je can falo ina son ganin ka,ke kuma na baki minti goma ki shirya ” Kawu na gama faɗa ya fice.



Cike da tausayi ya dubeta ya ce “ki tashi ki shirya kin ji? Ni zan kai ki da kaina ” Bintu ta jinjina masa kai.Ya miƙe ya fita,ta bi bayansa da kallo bisanin ta je ta yi wani wankan.
Bayan ta fito ta je kitchen ta samu ruwan zafi ta gasa idonta,duk kumburin ya baje.Cikin uniforme ta shirya,ta zo falo ta yi zaune ta na jiran fitowar Halilu don tuni su Zahra sun tafi.




Daga inda take zaune ta na jiyo sautin muryar Kawu,alamu sun nuna masifar ce da ya saba yake yi wa Halilu.Ta nan zaune ya fito ransa a ɗan ɓace,su na haɗa ido ya sakar mata murmushi ya ce “tashi mu tafi” ta take masa baya har zuwa mota.
Shi ya tuƙa ta ya kaita makaranta,a hanya sai hirar soyayya yake yi mata ita dai sai dai ta mayar masa da martanin murmushi.





HABIBA

Tun da a ka sa ta makaranta ta fara wayewa,don yanzu tsakanin ta da hijabi sai in za ta yi sallah.Hullar gashin doki kuwa ita kanta ba ta san rabon da ta cireta a kanta ba,kamar ibada kullum ta na ga kanta.
Ƙawarta guda duk faɗin makarantar,sunanta Mardeeya ƴa ce ga shugaban ministan kuɗi.Abotar tasu ta samo asali ne tun ranar da ita Mardeeyar ta fara zuwa aji babu wuri sai ita Habibar ta yi mata nuni da kusa da ita shikenan suka ƙulla ƙawance.



Zaune suke su biyu,Habiba ta dubeta ta ce “yanzu da gaske ba ki iya girki ba? To in ki ka yi aure wa zai dafa wa mijin ki abinci?”
Mardeeya ta tuntsire da dariya ta ce “na yi miki kalar shiga kitchen? Hum! Ai ni yanzu haka ko wanka zan yi sai mai aiki ta cika min bawon wanka ta zuba kalolin sabulu da turare.Mijin da zan aura kuma ba ɗan nan ƙasar ba ne,Balarabe ne a facebook mu ka haɗu da shi”
Habiba ta waro ido ta ce “yanzu yadda ki ke baƙar nan sai Balarabe ya aure ki?”
“Ai sun fi son baƙar fata,ƙarshen week ɗin nan zai zo gidanmu ina gayyatar ki fatan ba za ki ƙin zuwa ba?” Mardeeya ta faɗa ta na kamo hannuwan Habiba alamar roƙo.
“Zan zo mana,dama ina son zuwa gidan ku ke ce ba ki bani ƙofa ba”
“Ko yanzu ki ke son zuwa sai mu tafi ai ba wani abu ba ne” cewar Mardeeya ta na mai tashi tsaye,Habiba ta washe baki ita ma ta miƙe.


Inda ake ajiye motoci suka nufa, Mardeeya ta buɗe wata latsetsiyar farar mota ta shiga ,Habiba ta zauna a gaba.
Cikin slow take driving ta na shan chocolat yayin da kuma bakinta ke bin waƙar Dadjou,a haka har suka isa katafaren gidan wanda a ƙofaf gidan har da jami'an tsaro.


Aka wangale gate ta cinna hancin motar ciki,ta samu wuri ta yi parking sannan suka fito.
Duk kurin da Habiba take da murnar su ma yanzu masu kuɗi ne sai ta ashe Kawu Mansur talaka ne in aka auna shi da mahaifin Mardeeya.



Cikin falon kalolin kugerun zama sama da guda biyar,ƙaton falo ne irin sosai ɗin nan.Tsabar ƙauyanci ya saka Habiba yin tuntuɓe ji ka ke tassss! Ta ture faux du fleure .
“Fatan ba ki ji ciwo ba?” Mardeeya ta tambayeta,Habiba ta girgiza kai a zuci ta ke cewa ‘oh! Ita ba ta damu da abun da na fashe ba ma’

“Ga ɗakina na nan” Mardeeya ta katse mata tunanin zucin,ta buɗe ɗakin ta shiga Habiba ta mara mata baya ta na mai cewa “mi ya sa ba a baki ɗaki can sama ba sai a nan ƙasa?”
“Ɗakin Dad da kuma Ya Kameel ne kawai a sama hatta Momy a ƙasa take zaune” Mardeeya ta bata amsa ta na mai cire takalmin ƙafarta masu tsini.
Habiba na shirin yin magana idonta ya yi tozali da ƙaton hoton wani Guy baƙi suluk,sai dai sajen da ya ajiye shi ya ƙayatar da fuskar tasa.
“Ya Kameel ne wannan,shi ne babba gidanmu,bayansa an haifi wasu duk sun mutu.Ni ce aka haifa ta ƙarshe kuma ni ce auta”
Habiba ta waigo ta dubeta,ita kuma ta ɗaga mata gira tare da cewa “Yes! Ko ya yi miki ne ki na son shi?”
Habiba ta ce “mi zai yi da baƙauya, wannan da ganinsa ƴan matansa ba su ƙirguwa”
Mardeeya ta ce “ai kuwa kamar kin sani ,don yanzu haka maganar da nake yi miki kusan kullum sai sun zo nemansa.Wasu ma har gyaran ɗaki suke yi masa,akwai kuma masu kwana a gidan nan duk domin samun soyayyarsa ”


Wani baƙin ciki ne ya rufe zuciyar Habiba wanda ba ta san dalili ba,kawai sai ta taɓe baki ta na mai ɗan ƙarewa ɗakin kallo.Komai na cikinsa pink ne tun daga bed ɗin har labulaye da kuma kujeru biyun da ke ajiye.
Takalmi ne kaloli a jere ras a cikin ƴar kwabarsu,haka ma hullunan mèche na gashin doki.Kan dressing mirror kuwa ba a magana,kai kace wani kantin kayan kwalliya da turarruka.


“In kin ga abin da ya burge ki kawai ki ɗauka” Mardeeya ta faɗa ganin yadda Habiba ta baza na mujiya ta na kallo.
“Ina son kayan kwalliya ,sai dai ban iya ba”
“Hhh! Ai babu wuya bari na yi wanka sai na nuna miki yadda ake yi” ta na gama faɗa ta shiga toilet ta fara wanka,babu jimawa ta fito ƙugunta ɗaure da towel fari sol.

“Ki shiga ki yi wanka,sai na yi miki kwalliyar”

“Mardee kar fa aje ayi min ta ƙi yi min kyau”
“Dalla Malama ki shiga kawai ki yi wanka in ba ta yi kyau ba ki ce ni ba Mardee Mohan ba ce” ta faɗa har da wani buga cinya irin yanda indiyawa kan yi, Habiba ta tuntsire da dariya bisanin ta shiga ta yin wankan.


Bayan ta fito ne Mardeeya ta tsantsara mata kwalliya,kai kace wata amarya.Cikin kayanta ta zaɓo wa Habiba wata shuɗiyar doguwar riga.Kamar wata ƴar tsanar roba haka ta fito ta yi tsaf da ita,hotuna ta yi mata bisanin ita ma ta shirya kanta.
“Yadda ki ka yi kyawun nan ina mai tabbatar miki in mu ka je gidan shaƙatawa sai an samu kyakkyawan saurayi ya wud da ke!”

“Mardee kar ki sa kaina ya fara hayaƙi mana”
“Allah gaskiya nake faɗa miki ”
“To ina za mu je?”
“Mu je mu sha crème glacée”


Direba ya kai su wajen shan crème glacée ɗin.Su Na zaune su na taɓa hira,Mardeeya sai bata labarin yadda suka haɗu da Balarabenta take a haka har suka ida suka fito.
Su na shirin shiga mota wani saurayi ya yi saurin ƙaraso wa gun su.Sallama ya yi masu suka amsa,ya dubi Habiba ya ce “don Allah in babu damuwa ina son lambar wayar ki”
“Banda lamba” ta basa amsa.
“Ba dai za a bani ba,to a sayar min ko nawa ne zan saya”
Ta ɗan saki murmushi ta ce “tukunna dai ban fara riƙe waya ba,karatu nake”
Saurayin ya dubeta,don Habiba ta kai shekara sha takwas.
Ɗan waigawa ya yi,ya ce “in babu damuwa to ku jira na je na sayo miki wayar na kawo miki,don muddin ki ka suɓuce min na shiga uku”
Ba Habiba ba hatta Mardeeya sai da ta dube shi,haɗaɗen gaye ne irin sosai ɗin nan.


“Ok bari mu shiga mota mu jira ka” Mardee ta faɗa,ya yi murmushi ya ce ya “na gode” wata jar mota da ke parker a gun ya shiga,su ma suka shiga suka zauna.


“Kin gansa kyakkyawa da shi”

Habiba ta taɓe baki a zuci ta ce ‘ai bai kai Kameel kyau ba’ a zahiri kuwa cewa ta yi “mun dace da shi ne?”
“sosai ma kuwa”
“Ni kuwa bai kwanta min a rai ba”
“Ki ƙara masa lokaci dai,duka fa yanzu ne kuka haɗu”
Su na nan zaune ya dawo,ya ƙwanƙwasa glass dakyar Habiba ta fita ta karɓi wayar bisanin su yi tafiyarsu.



★JAPON


Malami na musamman ne ke koyar da Bobby abubuwan da suka shafi Musulunci.Ba wai don ya yi aiki da su a karan kansa ba ne a'a,kawai dai ya na koyo ne saboda ya ci nasarar samun Anita.
Sosai ya maida hankali wajen koyon babbaƙu,bai ɗauki dogon lokaci ba ya fara iya tada baƙi tare da koyon karatun Alkur'ani mai girma.
Shi da Anita kuwa kullum su na maƙale a waya,tun ranar da ya je gidansu bai sake zuwa ba.




Garin yau ya tashi da hazo,luf-luf ko ta ina hadari ne ya gangamu ya yi baƙi ƙirin.Bobby kuwa a tsanake ya ke ƙara gyara ɗakin nasa saboda ziyara da Anita za ta kawo masa.Flowers ya zuba kan gado ya rubuta kalmar I LOVE YOU da babban harufa.

Komai ya shirya shi tsaf zuwanta kawai yake jira.Ya na nan zaune ya ji knowking,da mugun sauri ya je ya buɗe.Anita ce sanye cikin riga da wando ,ta harɗe gashin kanta a tsakiya.
Blue idonta masu kama da na mage ta ƙura masa,Bobby ya ja ya bata hanya ta shigo sannan ya rufe ɗakin da key.


“Waooo!” ta furta ta na kallon kwalliyar da ya yi wa ɗakin kamar ba hotel ba.Ya rungumeta ta baya ya ce “Oui je t'aime ! Ina sonki my Ani! ” dariya ta yi ta ce “ni ma ina sonka”

Ya sake ta,ya nuna mata wurin zama ta maƙe kafaɗa ta ce “a samar ƙafar ka zan zauna”
“oh! Hakan ya yi min daɗi” ya furta ya na mai zaunawa ,Anita ta hau kan cinyarsa.
Jus ya zuba a kofi biyu,ya miƙa mata ɗaya ya ɗauki ɗaya.
“Shikenan ka manta da ni,shiru ka ƙi zuwa wajen sati biyu kenan.Maman har sai da ta tambaye ni ko lafiya ?”

“Lafiya lau,ina nan ina ta fafutukar iya addinin Maman don ta bar min ke” Bobby ya faɗa.
Anita ta ce “Ka na nufin larabci ka ke koyo ko kuwa karatun?”
“Duka biyun”
Ta ƙura masa ido,bakin na ɗan rawa ta ce “dama har haka ka ke sona?”
Ya bata amsa da “Fiye da haka”

Anita ba ta san lokacin da ta yi saurin kwanto shi ba,ta na mai kai bakinta kan lips ɗinsa.Mai son kuka an jefe shi da kashin awaki! Bobby kamar mai jira ya yi mata kyakkyawan masauki akan ƙirjinsa....



Wacce ta shirya payement za ta turo 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaida biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte Moov ta 200f
[24/07 à 15:40] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆

```MRS SADAUKI```💫✍🏻

FCWA ☀️


*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂


*Page 17_18*


Yadda yake sarrafa ta a haukace ya saka tsoro yi wa Anita dirar mikiya a ƙawon zuciya.Ƙoƙarin cire gangar jikinta take,amma sam ta kasa saboda kamun sandar makauniya da Bobby ya yi mata.Mugun sonta sai ƙara bijiro da tsohuwar sha'awarsa yake,duk yadda yake ƙoƙarin controling kansa ya kasa .“Bo..b...byyy please ka bari har bayan aure” Anita ta faɗa cikin fizgar numfashi bayan ta ci nasarar zare bakinta daga na shi.


Ido tab hawaye Bobby yake dubenta,sam ya kasa yin magana .Rabon da ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayin tun ranar da ya kawar da budurcin Anita.
Hannunta ya yi saurin kamawa ya ɗora saitin zuciyarsa da take faman bugawa,ta sani sarai a wannan lokacin babu abin da Bobby ke da buƙata illa ta basa haɗin kai bori ya hau.Waiwayen baya da kwanyarta ke yi mata na uwar azabar da ya gana mata shi ke daɗa tsoronsa a zuciyarta.



Ta ya haɗiye yawu haɗi da jan ajiyar zuciya ta ce,“zan taimaka ma ka samu nutsuwa amma please kar ka kusance ni”
“Don mi?” ya tambaye ta hawaye na zubowa zirrr kan kumatunsa .
“Doli Maman za ta gane in na koma gida.Bobby tun bayan rabuwata da kai babu namijin da ya taɓa kusantata,hasali ma ban yi wani saurayi ba ka ga kuwa muddin mu ka yi sex zan sha wuya ne”


Da sauri Bobby ya girgiza mata kai ya ce “ba zan yi miki da ƙarfi ba, please Anita ki fahimce ni zan iya mutuwa fa” ya na faɗar haka ne tare da kuma kai hannu jikinta ya na sarrafata.



Ta rumtse ido gam,Bobby ya cirata cak ya ɗora kan bed.Sai da ya sha daga sosai kafin ya raba Anita da kayan jikinta.A halin da ta gansa kawai ya sa ta fashe da kuka,bai saurareta ba ya toshe bakinta ta hanyar saka nasa ciki bisanin ya fara kusantar ta.




Kamar wata amarya haka take kuka da faman fizge-fizge,an ɗauki ɗan lokaci kafin ya koma gefe.Cike da jin haushi Anita ta miƙe ta shiga toilet, Bobby ya take mata baya .
Cikin bawon wanka suka shiga,suka yi wankansu bisanin su fito su ci abinci da ke kan table.


Kayan jikinta ta maida sannan ta yi masa sallama ta fita.
Bobby kuwa wani tsadadden murmushi kawai yake saki,wata irin nutsuwa yake ji da salamar ruhi.Group ya shiga suka fara yin message shi da Fadeel don Kameel tun komawarsa Senegal ba kullum yake hawa online ba.



ANITA
ta na cikin mota ta na tunanin scène ɗin su da Bobby .Ta ci wuya ba laifi amma a wannan karon ta ƙudiri aniyar ba za ta barsa ba za ta dinga jure wa buƙatarsa.
Ta na isa gida ta tarar da Maman a falo ta na karatun Alkur'ani.
“Oh! Allah ” ta furta cike da gajiya bisanin ta zauna ta na cire takalmin ta .
“Ina shopping ɗin da ki ka ce za ki yi?” Maman ta tambayeta ta na mai ƙare mata kallo.
Gaban Anita ya faɗi,sam ta manta da ƙarya da ta yi wa Maman kan za ta be shopping ne alhalin don ta je gun Bobby ne.
“Am .. Eh...Su na can cikin mota Maman,amma mi yasa ki ka tambaye ni?” da i'ina ta yi maganar.
“Ina matsayin mahaifiyar ki bai dace na san inda ki ka je ba?”
“A'a ban ce ba! Kawai dai na yi mamaki ne yadda aka yi ki ka tambaye alhalin lokacin baya ba ki yin haka” Anita ta faɗi haka ta na mai kwashe takalminta ta nufi hanyar bedroom don gudun wata tambayar.

“Ya shi Mohamed Bobby ɗin ya na lafiya ko?”

Da mugun sauri Anita ta juyo ta kalli mahaifiyarta sai kuma ta shige ɗakinta ba tare da ta amsa mata ba.
Ta na nan zaune bakin bed Maman ta shigo.
“Anita ke yarinya ce! Ki na tunanin za ki iya yi min wayo? Dubi yanayin ki haka ki ka fita? Ina kwalliyar da ki ka yi ? Haka nan kawai ta goge?” Maman ta jero mata tambayoyin.

Anita ta ɗan rikice duk alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta.
Murya na ɗan rawa ta ce “Maman na sani ! Na je gun Bobby amman babu abin da ya shiga tsakanina da shi.Ko kin manta na faɗa miki shi ma musulmi ne? ”

“Ki yi hankali shi ne kawai abin da zan faɗa miki.Samun ciki a shekarun ki ba tare da aure ba shi nake guje miki.” Mama na gama faɗar haka ta fice.Anita ta ja wani dogon numfashi ta na mai faɗa wa kan bed ɗin ta yi kwance ta na kallon sama.





★SENEGAL



Kamar jaririn da aka haifa yau haka suka zagaye wayar su na dubawa.Habiba zuciyarta fal farin ciki yau dai ta fara riƙe abun da su Twins ba su taɓa samu ba a rayuwarsu.
“Na yi mamaki sosai da ki ka ce yau ne ku ka haɗu kuma har ya iya saya miki waya” Zahra ta faɗa.
“Ya na sona ne shi yasa ke ma da zarar kin samu mai son ki zai saya miki ” Habiba ta bata amsa.
Bintu ta ce “tun Abba na da rai kullum sai ya yi mana faɗa akan kar mu kula samari haka ma kar mu amshi abun hannun su to mi zai sa ta karɓa?”

“Hhhh! Hassada ta dai ku ke yi in na gane,to na gaba ya yi gaba iyeee! Ƴan baƙin ciki” ta na gama faɗa ta miƙe ta fita daga ɗakinsu dama ta shigo ne ta nuna masu wayar.
Twins suka kalli juna cike da mamaki, Bintu ta taɓe baki ta ce “Kin ga Zahra ki tashi ki ɗauki duk abin da ki ke so , Lilu ya ce zai kai mu asibiti gun Mama”
“Can za mu kwana?”
“Eh mana! Ko kin manta gobe weekend ?”
“Amman ai za mu je islamiyya ”
“Mtsw! Kullum ba mu na zuwa ba? Gobe ne kawai za mu yi fashi fa”
“Ok to” Zahra ta faɗa ta na mai tashi ta saka kayansu kala biyu cikin wata jaka.



Halilu da kansa ya zo ya yi masu magana suka fito ya sa su a mota ya kai su haɗaddiyar asibitin.
Ko ina tsaf yake babu ƙazanta,a asibitin ba su buƙatar ƴan jinya likitocin ne ke kula da duk patients.In kuma ka na son ganin wani sai weekend.
Da murna suka je suka rungume mahaifiyarsu wacce tsabar yadda ake kula da ita ya saka ta yi kyau.
“Mama don Allah ki koma gida ” cewar Bintu.
“Zan koma ƙarshen watan nan lokacin na iya tafiya da ƙafata ”
“Mun yi kewar ki sosai” Zahra ta faɗa kamar za ta yi kuka.
“Ni ma haka.Ya ya ƴan gidan? Fatan ba a takura maku?”
Bintu ta ce “Hum! Kawu zai barin mu haka nan ba tare da tsangwama ba? ”
“A'a bai da matsala ke ce ki ke takura kan ki” cewar Zahra.
Bintu ta ce “Mama wannan da ki ke gani ba ta san ciwon kanta ba.Ko kin san da Kawu ya tursasa ni sai da na cire masa code ɗin system ɗin Abba ?”
Mama ta yi murmushi ta ce “ki barsa shi da Allah ne! Haƙin zumunci kawai ya isa ya tambaye shi.Wai ban ma tambaya ba wa ya kawo ku?”
“Lilu ne!” Bintu ta bata amsa.
“Wane ne kuma haka?”
“Wai Halilu kin san yanzu soyayya suke” Zahra ta faɗa ta na tuntsira dariya.


“Kun ci abinci ne? ”
“A'a sauri muke kar Kawu ya dawo ya hana a kawo mu”
“Ok ku buɗe frigine akwai kaza da madara da kuma ayaba sai ku ci”

Da murna suka je suka ɗauko,su na ci su na yin hira har suka gama suka shiga toilet suka wanke hannu.
Hira sosai suke,bayan sun yi sallah isha'i ne wata nurse ta shigo ta kawo masu wasu ƙananan matala lakai-lakai guda biyu.
Bisanta suka kwanta da dare ya yi.
Bintu na cikin bacci ta fara jin sanyi na ratsa ta bisanin kuma wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login