Showing 21001 words to 24000 words out of 24315 words
Chapter 8 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
zazzafar shafa mai shiga ɓargo.Ba ta san mine ne feeling ba sai a mafarki,tuni jikinta ya fara ɗaukar caji ta na jin daɗin yadda ake taɓa sassan jikinta.Lokacin da ya fara kusantarta tamkar ta yi ihu haka take ji don daɗi,a haka har ya gama ya sauka kanta.Daidai nan ta farka,da wani mugun sauri ta tashi zaune ta na mai dafe zuciyarta.
Toilet ta shiga ,sai ta lura duk ta ɓata jikinta.Duk da ba ta da wani dogon ilimi amma a makarantar islamiyya an yi masu bayani kan babin wanka janaba da na jinin haila da kuma abubuwan da ke sharhanɗa wanka.
A hankali ta kunna pampon ta yadda ƙarar ruwan ba zai tayar da su Zahra ba ta gabatar da wankan.Bayan ta gama ta yi alwala ta fito,a zaune ta tarar da Mama da sauri ta sunne kanta da ke ɗigar da ruwa.
“Je ki kwanta Bintu kin wani zo kin yi tsaye” shi ne abin da Mama ta faɗa.A hankali ta ja wata ɓoyayyar zuciya,ta yi tunanin Mama za ta tambaye ta wankan mine ne ta yi.
Kan katifa ta je ta kwanta,sai dai ta kasa yin bacci tunanin mafarkin nan kawai take yi wanda ba ta san dalilin yinsa ba .
Sai wuraren asubahi ta samu bacci,wanda a ƙarshe Zahra ta tashe ta don yin sallah.Ta na gama wa ta ɓingire bacci.
A zaune ta ganta cikin wani jeji mai furanni tsanwa sharrr.A gabanta kuwa wani kyakkyawan saurayi ne ya na sakar mata murmushi. Kyawunsa ne ya ja ta izuwa gun shi,kalaman soyayya ya fara faɗa mata ya na yi ya na shafar jikinta.
Kan cinyarsa ta hau,ta ɗora bakinta kan lips ɗinta daga nan suka fara sarrafa juna,ya na gaf da ya kusanceta ta ji muryar Zahra ta daki dodon kunnenta.
Kanta ya yi wani bala'in sarawa,cikin fushi ta tashi ta ce “mi aka yi ne?”
“Ki tashi ki yi wanka sai mu ci abinci ” cewar Zahra,a harzuƙe ta ce “ban ci ” sai kuma ta yi luuuu ta koma ta kwanta.
Idonta har wani dishi-dishi suke,cikin son ta koma baccin ya fara hura mata iska a fuska.Cikin sauri ya fara kusantar ta kamar abun yaƙi,ya na gamawa Bintu ta farka.
Wannan karon haka kawai ta ji hawaye na yi mata zuba ba tare da ta san dalili ba.Can ta tsinkayi Zahra a zaune kusa da Mama su na cin abinci,dakyar ta miƙe ta shiga toilet.Baƙin cikin ganin yanzu ma jikinta ya ɓace ya saka ta fashewa da kuka,bisanin ta sakarwa kanta shower.
Rigar da ta cire ta ɗaure kanta tamau don kar Mama ta ga gashinta a jiƙe.Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta fito,can gefe ta zauna ta shafa mai da turare sannan ta saka kaya.
Duk abin da take Mama na ankare da ita kawai dai ba ta ce mata komai ba ne.
Dakyar Bintu ta ci abinci, sam ta kasa sakewa saboda ƙuncin da take ji.
A can gida kuwa Kawu Mansur sai da ya yi kamar zai daki Halilu da ya samu labarin ya kai su Twins can asibiti.Inna ce ta yi ta faman basa haƙuri,ita kuwa Habiba ta na can maƙale da waya ita da sabon saurayinta wanda tuni ya saye mata zuciya.
Tsaf ta shirya cikin wasu riga da zane na atamfa,kamar yadda suka yi da saurayinta Haidar shi ya zo daidai inda ta kwatanta masa.
Su na tafe a mota sai yaba kyawunta yake,ita kuma banda juya ido da murmushin jin daɗi babu abin da take a haka har suka isa gidansu Mardeeya.
“Sai yaushe za ki koma gida?” Haidar ya tambaye ta .
“Ina ga sai bayan sallar magrib,don yanzu aiki ne za mu yi sai kusan ƙarfe biyar baƙon nata zai zo” Habiba ta basa amsa.
“Ok in kin gama sai ki kira ni,ki kula min da kan ki”
Ta washe baki ta ce “to in sha Allah!” sannan ta fito.
Mardeeya ta kira bisanin masu gadi su barta ta shiga,da ihu suka tarbi juna kafin Habiba ta aje jaka ta canza kaya sannan suka shiga kitchen.
Yau kam mai aiki gefe ta koma ta na kallonsu, lokaci zuwa lokaci ta na ɗan taimakawa da abun da ba a rasa ba.
Mardeeya kuwa sai murna take don tuni ta faɗa ma baƙonta da kanta za ta yi masa girki.
Sai bayan sallah azahar suka gama,Habiba na fitowa daga kitchen ta yi kiciɓis da Kameel ya shigo shi da wata farar Baby sun nufi can saman bene.
Wani takaici ne ya rufe ta ,a nan ta yi tsaye ta na kallon su har suka ɓace ma ganinta.
“Oh! Nan ki ka tsaya? Bari na je na yi sauri na yi wanka” cewar Mardeeya ta na mai rugawa ta nufi ɗakinta.
Sama da minti biyar Habiba na nan tsaye bisanin ,wata zuciya ta raya mata bin bayan su Kameel .
Can sama ta hau,sai dai ta rasa wane ne ɗakinsa don ɗaki uku ne a gun.Har ta juyo za ta tafi wani sauti ya ja hankalinta.Da saurinta ta kai kunnenta jikin ƙofar,ta wani waro ido saboda kalaman da suke fitowa daga bakunan masoyan.Bugun zuciyarta ne ya tsananta bugawa da ƙarfi,yayin da kuma ta fara jin tamkar da ita ne Kameel ke tarayya.Hannunta har rawa yake wajen tura ƙofar ciki,ba tare da wani tunani ba ta kutsa kai ciki.....
Masu buƙata shiga group 200 ne kacal kuɗin karatu,ki tura ta wannan account ɗin 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f
MRS SADAUKI 💫✍️
[25/07 à 11:46] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 19_20*
Habiba ta kutsa kai cikin ɗakin,cak ta tsaya ta na faman zaro ido ta na kallon Kameel da budurwarsa da ke ta sha'aninsu kan kujera.Sam ba su ma san ta shigo ba,suratai da kuma kalaman soyayya kawai suke amayarwa.
Ido na zubar da hawaye Habiba ta fito daga ɗakin.A sanyaye take saukowa daga step ɗin,direct ɗakin Mardeeya ta shiga ta samu bakin bed ta zauna.Tun da take ba ta taɓa ganin wannan lamari ba,ko a TV iya kiss ne kawai ta saba gani yau kam da idonta ba a mafarki ba sai ga shi ta yi kallon yadda ake tarayya.
Ta wani zabura ta na mai rumtse ido da sauri,bisanin ta buɗe ta kalli Mardeeya wace ba ta tsaya da yarfa mata ruwan yatsunta ba.
“Tunanin mene ne ki ke haka? ”
“Babu komai” ta bata amsa ta na mai tashi ta shiga wankan ita ma .
Bayan ta fito Mardeeya ta yi mata simple make-up ta zaɓo mata abaya irin na Makka .
“Waooo! Amma dai ba aro ki ka ban ba ko?”
“Kin ji ki da wani zance,to kyauta na baki” cewar Mardeeya.
Cike da murna Habiba ta saka rigar,ta kuwa karɓeta tsaf ta yi mata kyau.Mardeeya kuwa cikin wani mahaukacin Sahari ta shirya kai kace ba'indiya don ma dai fatarta na baƙa.
Falo suka fita,tuni mai aiki ta gyara ɓangaren da za a sauke baƙon.Selfie kawai suke da wayar Mardeeya,su na nan zaune har sai da ya zo.
A tare suka fita suka tarbo shi,suka yi masa iso ciki.Tamkar ƙaramar yarinya haka Mardeeya ke zuba masa shagwaɓa shi kuma ya na biye mata.
Bayan ta gabatar masa da Habiba ne sannan suka fara taɓa kalolin abincin da suka yi.
Nader sai santi yake ya na yaba abinci, Mardeeya duk da ba wata uwar ta tsinana wajen girkin ba amma ta ji daɗi sosai.
“Bari na tashi na baku wuri don ku zanta da kyau” cewar Habiba ta na mai miƙewa.
Mardeeya ta ce “fara yi ma hoto ni da Habiby kafin ki tafi”
Ta karɓi wayar ta fara yi masu hotuna bisanin ta je can ɗakin Mardeeya.Wayarta ta ɗauka ta kira Haidar ,kamar yadda ta ɗauki darasin shagwaɓa haka ita ma ta fara yi masa ai kuwa ta samu karɓuwa duk ta rikita Haidar.
“In ki na yin shagwaɓa sai ki sa na zauce” Haidar ya faɗa.
Habiba ta ɗan yi wani far da ido ta maƙale murya ta ce “ai na fi son haka Babyna,ko kai ba ka so ne?”
“Ina so mana sosai ,ji nake kamar ace ki na kusa da ni”
“Ko zuwa za ka yi ne?”
“Kin gama komai ne?”
“A'a sai zuwa an jima”
“To ki bari har ki gama my dear ”
Hira soyayya suka ci gaba da yi,ba su yanke kiran ba sai da Mardeeya ta zo nemanta.
Har bakin motarsa suka yi masa rakiya,mai gadi ya shigar da tsarabar da ya kawo mata bayan kuɗi da ya basu dukan su biyun.
Habiba har tuntuɓe take wajen shiga falon don duba kayan.Cike da mamaki take buɗe duk ledodin ta na mai tambayar Mardeeya “na ce halan kuɗi gare shi irin sosai ɗin nan? Dubi kayan nan fa sun fi 500k/mill kamar dai za a haɗa lefe”
Mardeeya ta saki wani murmushi ta ce “Yanzu dai ki duba wanda suka yi miki sai ki zaɓi ko kala goma.Kaina na yi min ciwo zan shiga daga ciki”
“Ki turo min hotunan da mu ka yi kafin ki kwanta”
“Na gaji sosai ki duba a status duk na saka su”
“Har da na Balaraben?” ba ta bata amsa ba ta shige cike.
Habiba ta shiga zaɓar wanda za ta ɗauka,kamar daga sama ta ji tsuki.Ta na ɗago kai ta yi arba da Kameel da budurwarsa da dukkan alamu kuma ita macen ce ta ja tsukin.
Kamar gumki haka ta tsaya ta na kallonsu,har suka fice.Hawayen takaici ta goge,ƙunci da ke naƙarƙasasar ruhinta bai hanata zaɓar kayan ba.Sauran kuma masu aiki suka shigar da su can ɗakin Mardeeya wacce tuni bacci ya ɗauke ta.
Habiba ta kira Haidar ya zo ya ɗauke ta ,su na tafe su na hira har suka kawo ƙofar gidansu.Haidar ya kama hannunta ya ce “yanzu Baby sai yaushe?”
“Gobe mana,ko ba za ka zo makarantar ba?”
“Zan zo mana,amma kafin nan ai za mu yi waya ”
“Ba ka gajiya da waya”
“Son ki ne silar haka”
“Hum!”
“Allah kuwa Baby ji nake kamar kar mu rabu”
Yadda ya yi furucin ya saka Habiba saurin kallon shi.
Haidar ya nitsa idonsa da kyau cikin nasa ya fara aika mata da wani mugun kallo mai kashe jiki.Hannunta da ke cikin nasa ya fara ɗan matsawa,Habiba ta wani jan ajiyar zuciya ta na haɗiye yawu muƙut! Sai kuma ta kawar da kanta.
“Ko na ture iyayena su nema min auren ki?” Haidar ya furta kamar mai shirin kuka.Da mugun sauri ta juyo ta ce “Aure kuma? Duka yaushe ne mu ka haɗu da kai shi ne ka ke min maganar aure?”
“Habiba shi muradin zuci babu ruwansa da jimawar masoya,kin san irin yadda son ki da sha'awar ki suke azabtar da ruhina?”
Ta maimaitata kalmar ‘sha'awa’ a zuciya.
Ba ta san lokacin da bakinta ya furta “mi ka ke nufi da sha'awa?”
“Buƙatuwa mana,ina son kasancewa da ke na ji ki rungume cikin ƙirjina ina kissing ɗin ki”
Zuciyar Habiba ce ta fara bugawa da mugun gudu,yayin da madubin idonta kuma yake hasko mata video Kameel da budurwarsa.Nan take jikinta ya ɗau rawa,da sauri ta fizge hannunta da ke cikin nasa ta tura ƙofa da niyyar fita Haidar ya tsayar da ita ta hanyar ƙara riƙota.
“Gida zan shiga ban cikin nutsuwata,in an jima za mu yi waya” ta furta cikin rawar murya,ba tare da ya sake cewa komai ba ya barta ta fita.Sam ta manta da ledarta wacce ta zubo kaya,shi ma haka.
Ta na shiga gida ta tarar da su Twins su ma sun dawo.Zahra na karatu yayin da Bintu ke yin hira ita da Halilu .Kamar zararra haka ta nufi ɗakinta wanda ita kaɗai ce mallakinsa,direct toilet ta shiga ta tsabtace jikinta.
Kan bed ta kwanta ta na tunanin abubuwan da suka shuɗe a yau, murmushi kawai take saki a haka har bacci ya ɗauke ta .
Bayan sallar magrib Haidar ya yi mata text akan ya na ƙofar gida ta fito ta karɓi ledarta.Kallabi kawai ta ɗora kan kanta ta fita,can nesa da gidan su ta tsinkayi motarsa inda ke da ƙarancin haske.
Tun fitowar ta ya ƙureta da ido ya na kallon shap ɗin ta mai tafiya da hankali duk wani lafiyayen namiji,har ta ƙaraso.Daidai ɓangaren da yake zaune ta tsaya haɗi da bubuga glass ɗin.Haidar ya buɗe tare da ziro ƙafa ɗaya.“Ƴan mata adon gari” ya furta ya na mai kallonta,Habiba ta ce “ina ledar take ban so Baba ya zo bai gan ni ba” hannu yasa ya jawo ledar ya miƙa mata ta ce “sai da safe ko?” “ɗan duƙo ki ji” cewar Haidar Habiba sokuwa ta ɗan rage tsawo kawai sai jin bakinsa ta yi kan lips ɗinta.
Kai ta girgiza ta bar gun da sauri shi kuma ya yi ta dariya.
Ta na ƙoƙarin shiga ɗaki muryar Kawu ta daki kunnenta “uban waye wancan mai motar?”
Gabanta ya bada ras! Ko kafin ta kai ga furta wata kalma Kawu ya zo gabanta ya sharara mata mari sannan ya nuna ta da yatsa ya ce “daga yau sai yau kar na sake ganin kin kawo min ƙato a gida.Ban shirya yi miki aure ba karatu za ki yi ki je can na baki aikin offishi,in kuma na sake ganinsa a ƙofar gidana za ki sha mamaki”
Da gudu Habiba ta ƙarasa cikin ɗakinta ta na kuka,ba ta yi jinkirin sanar da Haidar furucin mahaifinta ba.Shawarar farko da ya bata shi ne ita sai ta rinƙa zuwa wajensa su na yin hira,abun ka da zuciyar da ta kamu da so sam ita ba ta ga illar yin haka ba.
ƘAUYEN JOAL
Mohan ne hakimce kan kujerarsa ta alfarma,bayan ya gama ganin mutanen da ke zuwa wurinsa da sunan ya yi masu aiki shi ne ya zauna ya na hutawa.Ƙatuwar wayarsa ce riƙe a hannunsa,saƙon mataimakin shi mai kula da duk wani fice dashigar kuɗi ya fara dubawa bisanin na sauran mutane.Har zai ajiye wayar sai kuma ya nufi ɓangaren status,na Mardeeya ya shiga.Murmushi ɗauke da fuskar shi yake kallon ƴar tasa wacce ke zaune ita da mijinta na gobe ,hotunan ya ci gaba da dubawa har ya faɗa kan na Habiba.Zoom ɗin hoton ya yi ya na ƙare wa duk wani lungu da saƙo na jikinta kallo,a ƙasan hoton an rubuta my Bestie.
Mohan ya fiddo halshe ya wani lashi leɓensa na ƙasa kamar tsohon maye.Kusan shekaru biyar kenan da mutuwar matarsa,tun daga nan bai sake yin aure ba amma ganin Habiba ya saka jin kamar ya samu matar aure.
Screenshot ya yi na hoton,bisanin ya fita daga WhatsApp ya kira Mardeeya.
A shagwaɓe ta ɗauki kiran ta na mai cewa “Dad ka manta da ni ”
“A'a ku na raina,in sha Allah zan shigo gobe.Na ga ashe Nader ya zo yau”
“Wa ya faɗa ma? Cewa ya yi ko kai bai sanar ba ”
“A status ɗin ki na gani.Har da hoton Bestie”
Murmushi mai sauti ta yi sannan ta ce “Bestie Habiba ,ajinmu ɗaya a makaranta.Dad ka ga ƴar ƙauye ce ko ba ta dace na yi ƙawance da ita ba?”
“A'a ko ɗaya,ai kun yi daidai kamar Twins.Wane ne mahaifinta?”
“Dad na faɗa ma ƴar ƙauye ce ba su wani jima da dawowa birni ba.”
“Ok ! Ina Kameel ?”
“Ban ji ɗuriyarsa ba duk yau ƙila ya na can wajen dadiron shi”
“Mardeeyyya!” ya kirata da wata irin murya .
Kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah Dad abin da Ya Kameel yake yi daidai ne? Gidanmu kamar wata club haka ƴan mata ke shige da fice,da zarar na yi magana kuma ka ga laifina.”
“Ko ma dai mine ne ɗan uwan ki ,in ba ki rufa masa asiri ba wane ne zai rufa masa?”
Ta turo baki kamar ya na ganinta ta ce “in ni aka yi ma abin da yake yi wa ƴaƴan mutane har kashe mutum zai iya! ”
Dad ya murmusa ya ce “shi ɗin garkuwar ki ce! Ya ne kin ci abinci?”
“Eh na ci sosai yau Habiba ce ta yi mana girki mai shegen daɗi ka san ƴan ƙauye sun fi kowa iya abinci gargajiya”
“Ah haba? To gaskiya ni ma gobe a kira Bestie ta yi min girkin na ci na ji in ya yi daɗi sai na bayar da tukuici”
Mardeeya ta shiga ƙyalƙyata dariya bisanin ta ce “Dad ai kuwa zan faɗa mata kawai ka shirya gift ɗin da za ka bayar,don Bestie maƙura ce wurin girki”
Ido ya lumshe ya na jin sotayyar Habiba na daɗa hauhawa a birnin zuciyarsa.
Washegari
Kamar kullum direba ne ya kai su makaranta,su Twins ya fara ajiye wa sannan ya wuce da Habiba .
A bakin ƙofar shiga makaranta ta ci karo da Haidar.Ta waro ido ta na kallonsa,“tun ɗazu ke nake jira,so nake na ga kyakkyawar fuskar ki kafin na je aiki” ya furta cikin taushin lafazi.
Wani mayen daɗi ne ya rufe zuciyar Habiba,ta ce “na gode sosai masoyi”
Ya ce “ki shiga kawai ni zan tafi ki kula da kan ki,ina son ki” bai bata damar da za ta mayar masa da martani ba ya yi saurin tafiyarsa ya shige motarsa.
Habiba ta bi motar da kallo har sai da ta ɓace ma ganinta.Ta ja ajiyar zuciya bisanin ta shiga daga ciki.Saman bayan mota ta tsinkayi Mardeeya,da ƴar sassarfa ta ƙarasa.
“Bestie albishirin ki? Jiya na baiwa Dad labarin girkin ki ya yaba sosai ya ce na gayyato ki yau ki yi masa shi ma ya na son ci” Mardeeya ta faɗa cike da zumuɗi .
“Ki ce yau zan ga Dad?”
“Eh! Mu na sauka daga makaranta sai mu wuce gidanmu ”
“Da wane lokaci zai zo?”
“Bai sanar da ni ba,amma dai ya ce girkin kawai yake son ci”
Habiba ta saki murmushin jin daɗi,bisanin su shiga aji.
Bayan sun sauka kamar yadda suka tsara haka suka wuce gidan su Mardeeya.
Haɗaɗen girki Habiba ta shirya kala biyu,tuwon shinkafa da ɗanyar kuɓewa sai kuma tuwon macaroni da miyar ganye.Ɓangaren lemu kuwa mai aiki ce ta yi ,Habibar na kallonta don har yanzu ba ta ƙware ta wannan fannin ba.
Mohan kuwa tun da wuri ya shigo cikin gari, office ya fara zuwa ya rage ayyuka sannan ya zo gida .
Mardeeya ya tarar a daidai wurin da yake cin abinci kullum ta na gyara table ɗin.Da murna ta tarbe shi ta na mai cewa “yawwa Dad gwara da ka zo yanzu,Habiba na can na saka uniforme