Showing 15001 words to 18000 words out of 24315 words
Chapter 6 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
ne ya yi masa iso har cikin falon wanda ba ka jin komai sai sautin TV ta na waƙoƙin Mohamed zain na larabci.
“Assalamu aley...” saurar sallamar ce ta laƙe a maƙoshinsa ganin Anita ta fito daga wani ɗaki ƙugunta ɗaure da towel, ta na girgiza kai jiƙaƙen gashinta sai yawo yake.
Cak ta tsaya ta na kallon Bobby ,tun daga fararen fartun ƙafarsa har zuwa fuskarsa wacce ya fidda ma gashin baki ya bar saje kawai.
Fuuu ! Ta koma ɗakin da fito,Bobby ya fara kiran sunanta “Anita? Anita?” amma ba ta saurare shi ba.
Bai yi wani tunani ba ya bi bayanta,ya na shiga ya ganta tsaye ta baiwa ƙofa baya.
Ya ja wani dogon numfashi bisanin ya ida takawa dab da ita,kamar mai rawar sanyi haka hannunsa ke kyarma wajen ɗora shi kan ƙunta ya juyo da ita .
Hawaye ne ya gani cikin idonta su na shirin zubowa.“Ki yi haƙuri in zuwana ya ɓata miki rai,laifin ruhina ne da ya kasa sukuni saboda rashin ki a kusa da ni” cikin sanyin murya ya faɗi haka .
Anita ta kai hannu ta goge hawayen da suka yi nasarar zubowa kan kumatunta sannan ta ce “Bobby mi ya sa? Na yi kewar ka sosai! Na yi ta jira da tsumayen zuwan ka shiru sannan ba ka taɓa bani address ɗin ka ba .Har makaranta na je amma abu ɗaya suka faɗa min kai ɗan asalin Israel ne....” kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sa ta yin shiru.
Bobby ya jawota ya manna a ƙirjinsa ya na bubuga bayanta,haɓarsa ya ɗora bisa kanta ya ce “Je t'aime pour toujours ! Ina sonki na har abada!” Anita ta ɗan ɗago kanta suka tsura ma juna ido,a sannu a hankali suka dinga matsa fuskokinsu har Bobby ya yi nasarar sunkuyowa ya fara kissing nata.
Sumbata ce irin ta an yi kewar juna,zuciyoyin su har wani bugawa suke da sauri.
Anita ta yi saurin janye wa ta na mai cewa “Bobby koma falo ina zuwa” ya girgiza kai haɗi da jawota ya ci gaba da kissing nata.
Anita ta ƙara yin nasarar janyewa ta ce “Bobby Maman ta kusa dawowa daga aiki please ka koma falo” ba don ya so ba ya dawo nan falon ya zauna.
Kamar minti biyar Anita ta fito sanye cikin doguwar riga blue.Ta yi kyau sosai,ta sakar masa murmushi ta na mai buɗe frigine ta ɗauko masa ruwa ta tsiyaya a kofi ta basa.
Bobby ya karɓa ya sha,face da shi ta zauna suka fara taɓa hira.
Maman ce ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama ,Bobby ya yi saurin amsawa da “wa'aleykum Salam ya Ummi!”
Maman ta saki murmushi ta zo ta zauna,suka fara gaisawa yanayin shigar Bobby ta zata musulmi ne.Sosai ta ji daɗi,“Anita ki kawo ma baƙon abinci mana” cewar Maman.
Bobby ya ce “Alhamdullah ! Ban jin yunwa”
“Masha Allah! Bari na bar ku to” Maman ta faɗa ta na mai wuce ɗakinta.
“Maman na son musulmi,burinta kullum na auri ɗan addininta.Alamu sun nuna ta yi zaton kai ma ka na sallah ”
“Shi yasa na yi bincike kafin na tawo”
“Hum! Haɗuwar ku ta gaba doli ta gane kai ba ka da ma addini,don sai ta yi ta ma tambayoyi”
Bobby ya waro ido ya ce “ki ce tsugunne ba ta ƙare ba an saida Kare an sayi Biri”
Anita ta yi dariya ta ce “sosai kuwa don haka faɗi gaskiya tun yanzu”
“A'a zan yi tunani a kai” hira su ka dinga yi bisanin Bobby ya fito.
A waje ya tarar da Léo ashe bai tafi ba ya na nan dai zaune cikin mota.Har sai da suka hau titi sannan ya tambaya “Ya ne? Babu dai wata matsala ko?”
Bobby ya furzar da huci ya ce “eh to! Babu sai dai fa doli na koyi wasu abubuwan na musulmai muddin ina son in mallaki Anita ”
“Ai babu wani wuya zan nemo malami” da haka suka isa hotel ɗin,Bobby ya fita daga motar yayin da shi kuma Léo ya yi tafiyarsa.
Wanka ya yi sannan ya yi commande ɗin abincin da zai ci,ma'akaciyar hotel ɗin ce ta kawo.Bobby ya gyara zama ya na ci ya na taƙila waya har ya gama.Kiran Léo ya shigo,“ka shirya ƙarfe tara na dare zan zo na ɗauke ka zuwa inda za a koyar da kai” shi ne abin da ya faɗa ,Bobby kuma cike da murna ya amsa da “okay!”
★SENEGAL
Lokacin da Kawu Mansur ya dawo gida ya tarar duk su na cin abinci.Duk gaishe shi suka yi banda Bintu da ta kawar da kai gefe ta na mai ci gaba da harakar gabanta.
Ya dubeta ya ce “ke ba za ki gaishe ni ba ko? ” duk da ta san da ita yake amma ba ta juyo ba.
Zahra ta ƙyafito ta da hannu “Bintu Baba na yi miki magana ” “ke wai mene ne? Ban son takura” cewar Bintun ta na mai tashi ta nufi bedroom.
Kawu ya yi murmushin mugunta ya na jin burinsa na daf da ya cika.Wayancewa ya yi ya ce “ Allah ka shiryi Bintu duk yadda nake son yarinyar nan ta zama kamar ƴar uwarta ta ƙi,iskancin nata sai ƙara gaba yake kamar wacce sheɗan ya yi wa fitsari akai” ya na gama faɗa ya wuce ɗakinsa.
Ɓangaren Bintu zuciyarta har tafasa take tsabar takaici.Ƙululun baƙin ciki ya turniƙe mata wuya,kan bed ta yi tsalle ta faɗa ba tare da kakaɓe shimfiɗar ba ko ambaton Allah.
Lummmm! Wani sanyi ke ratsa gangar jikinta,sam ba ta damu da yanayin ba har sai da ya nune mata jiki ta koma liƙis.Kasa ta yi wa duk wata gaɓar jikinta sarƙa,kanta kuwa kamar mai mura haka ta ji ya kume wuri ɗaya ya zama ɗingimeme.
Haka kawai idonta ya fara fitar da hawaye,a haka wani bacci marar daɗi ya yi awon gaba da ita.Mafarkai ta fara na namun daji bisanin Kare ya dinga biyar ta da gudu har ya samu nasarar cizonta a ƙafa.Firgigit! Ta tashi ta na mai dafe kai wanda zuwa yanzu mugun sara mata yake ga kuma idonta har rufewa suke tsabar wani baccin da take ji.
Zahra ta shigo ta na mai cewa “ƙarfe tara fa har ta gota ko ba za ki je makaranta ba?”
“Bacci nake ji” cewar Bintu kamar za ta yi kuka.
“Ki tashi ki yi wanka zai sake ki”
“To jira ni kar fa ki tafi ki bar ni ” Bintu na gama faɗar haka ta tashi ta shiga toilet.
Bayan ta fito ta saka uniforme suka wuce islamiyya.Sam ba ta jin daɗin karatun kawai dai haƙuri ne take har aka taso.Ko da suka zo gida ba ta yi wa kowa magana ba ta shige ɗaki,wani baccin ta yi.Ba ta farka ba sai da Zahra ta tashe ta don yi sallah zhur.
Da kwandon masifa ta nufi ƴar uwarta,“tsabar baƙin ciki mutum na bacci ki zo ki tashe shi? Ina ruwan ki don ban yi sallah ba ke dai ba kin yi ba?”
Jikin Zahra ya yi sanyi,sam ta kasa gane kan ƴar uwarta a yau.Haka ta fita ta barta, Bintu kuwa rasa abin da za ta yi kawai sai ta fashe da kuka.Sai da ta yi mai isarta sannan ta je ta yi wanka,dakyar ta gabatar da sallar ta fito falo.
Abinci ta zubo ta rakuɓe can gefe ta fara ci kamar mayunwaciya.Duk kowa sai da ya yi mamakin yadda Bintu ta ci plate biyu na abinci har da hauda madarar bido.
Da lokacin makarantar marice ya yi,ƙememe ta ƙi zuwa nan ta shiririce wajen kallon tv.
Da dare,sun yi shirin bacci Zahra ta dubeta ta ce “Bintu don Allah ko za ki faɗa min abin da ke damun ki? Gobe Kawu ya ce zai kai mu gun Mama ban so ta ga wannan canjin da ki ka samu”
“Babu abin da ke damuna,kawai na yi kewar iyayena ne.Kin ga ni bacci nake ji sai da safe” Bintu ta faɗa ta na mai juya ma Zahra baya.
Ita ma a doli ta kwanta ta na saƙe-saƙen zuci.
Kusan ƙarfe biyun dare amma baccin ya ƙi ɗaukar ta,duk yadda ta so ya yi awon gaba da ita.Ta juyo ta na mai facing Zahra wacce ita tuni baccinta take.Shiru Bintu ta yi bisanin ta lumshe idonta,a nan take wata damina ta fara luluɓeta ta na sanyayya fatarta.A sannu a hankali ta fara shiga duniyar mafarki mai kama da gaskiya.
Tsikar jikinta ne ya yi wani mugun tashi, lokaci ɗaya ta fara jin amai yayin da kuma tsoro ke daɗa aurenta.Ta yi baya za ta gudu kawai ta ji an cirata sama ƙafafuwan ta na yi reto a iska.Ihu ta fara sai dai alamu sun nuna babu mai jinta don muryata sam ba ta fita.Timmm! Aka saketa ta faɗi ƙasa,bakinta ya fashe jini ya fara zuba.Mumunar hallitar nan ta ga ta dumfarota,Bintu ta rumtse ido ta na addu'ar Allah zare ranta ta huta da wannan masifa.
Hannunsa ta ji ya na shafar fuskarta,tamkar garwashin wuta haka tafinsa ke da mugun zafi.A karo na biyu ta buɗe ido ta kalle shi,idonsa ɗaya da ke can kusa da kumatu ya kafa mata,yayin da kuma yake wani juya ƙawon da ke gefe da gefen kansa.
Jikinsa duk gashi ne babu kyawun gani,murya na ɗan rawa ta ce “wane ne kai?”
“mijin ki ne?” ya bata amsa cikin wata ruɓaɓiyar murya ya na mai cire kayan jikinta.Tamkar wacce aka yi wa allurar kashe jiki haka ta gagara hana shi har sai da ya biya buƙatarsa.Ihun da ta fasa ne ya dawo da ita daga duniyar mafarkinta.Kalle-kalle ta fara bisanin da sauri ta sauka ta nufi falo don ɗauko ruwa ,tsit kake ji babu motsin komai.Kitchen ta shiga ta ɗauko ruwan ,hannunta har rawa yake wajen buɗe murfin sai dai kash ta na ɗaga butalin sama kamar magie ruwa ko ɗigo ɗaya babu.
Daga bayanta ta ji motsi,a tsorace ta waiga ta na fitar da wani sauti “haaann” sai dai wayam babu kowa ta na shirin ajiye butalin ta ɗauki wani sai kuma ta ga ya cika da ruwa da sauri ta kai bakinta ta shanye su tasss.
Innuwar mutum ta gani,a hankali ta fara ɗago kanta zuciyarta na halbawa sai dai kafin ta yi tozali da fuskar mamallakin innuwar wutar gidan ta ɗauke ɗifff.Ta buɗe baki da niyyar yin ihu ta ji wani kakauran hannu ya toshe mata baki tare da cewa “shiiit!”
Masu son ci gaba sai mun haɗe a PAID GROUP,400 ne kacal Hajiya .Ki tura ta wannan account 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
Talla
Assalamu alaikum,ina masu fama da shafar aljannu ko sihiri to ku matso kusa ga wani book na musamman da na ware domin wannan matsalolin a cikinsa akwai bayanai daki-daki akan ko wace matsala sannan da addu'o'in ta.Akwai su a rubuce sannan kuma da wanda za a saurare a samu waraka bi'izinillahi ta'ala.
*ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* ƙirƙirarren labari ne mai ɗauke da darussuka,masu cutar hauka,ko damuwa ko jinnu duk za ku samu addu'o'in ko wace matsala na karatun malumai da suka tsaya suka zaƙulo ayoyin Allah daga cikin Alkur'ani na dangane da ko wace irin cuta.
Uwanda ba su iya karatu ba za su iya saurare ko kuma su bayar wani ya karanta masu cikin ruwa.
A cikin wannan littafi na fitar da kalolin asiri uku wanda su ne aka fi samu.
Akwai masu fama da djinn ashiq bayyananne ko ɓoyayye irin wanda bai nuna alama ko kuma ya tashi.Da yardar Ubangiji shi ma zan yi magana akai tare kuma da karatunsa domin samun lafiya in Allah ya so.
Domin samun wannan littafi 400 kawai za ki biya na saka ki group +22795045822
[23/07 à 14:41] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆
```MRS SADAUKI```💫✍🏻
FCWA ☀️
*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂
*Page 15_16*
```Assalamu alaikum jama'a,ina yi ma kowa fatan alkhairi saboda yawan ƙorafin cewa babu kuɗi a yanzu a rage mana.To zan bayar da book one a free na *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI* book 2 kuma za ku biya 200 kacal😓 ga masu buƙata su yi min magana pc.
Katin MTN ko transfer,ƴan Nijar kuma carte airtel ko Moov ta 200f🙄```
Jikin Bintu ya fara yin wata irin kyarma, kamar ranta zai fita haka zuciyarta ke wani bala'in bugawa.Ƙiiii! Ya rinƙa janta har suka isa wani ɗaki,daidai nan hasken ya dawo ya kuma sakar mata baki.A wahalce ta juyo ta dube shi,Kawu Mansur ne tsaye ƙiƙam ya na aika mata wata muguwar harara bisanin ya yi gaba ya ɗauko wata system.
“Ki buɗe matakan tsaron da ke ciki,PA ya tabbatar min ke ɗaya ce ki ka san sirrin ubanki” Kawu ya faɗa cikin bayar da umarni.
Bintu ta haɗiye wasu yawu,tsoro take ya yi mata wani abu hakan ya sa jiki na kyarma ta fara buɗe duk wasu abubuwan da ke da code.Ta ɗago hawaye sai zuba suke yi mata,cikin rawar murya ta ce “na buɗe” Kawu Mansur ya wangale baki ya na mai ɗauke system don shi bai san komai ba da ya shafi boko.
“Fice ki ban wuri ki ka wani tsaya ki na kallona da shegun idonki” ya daka mata tsawa.Bintu har tuntuɓe take wajen fita,direct ɗakinsu ta wuce ta na mai fashewa da wani marayan kuka.
Hankali tashe Zahra ta farka daga bacci,“lafiya mike damun ki?”
“Kawu Mansur ne shikenan duka dukiyar mahaifinmu zai kwashe” ta faɗi haka cikin kuka.
“To mine ne na kukan? Kin ga don Allah ki bar zancen dukiya,ina ce dai wanda ya tara ta ma ya mutu ya barta balle mu da gado ne za a bamu” Zahra ta faɗa ta na jawo Bintu a jiki,ita kuwa sai kuka take kai kace yanzu aka shaida mata mutuwar Abba.
Washegari da kumburar fuska Bintu ta tashi tare da matsanancin ciwon kai.Halilu ya shigo har ɗaki domin dubata,ta wani yi banza da shi .
“Mene ne ya saka ki kuka? Zahra ta ce min ba ki da lafiya” ya furta ya na mai zama bakin bed tare da ɗan jan zanen da ta rufa da shi.
“Ka je ka tambayi maci amanar ubanka” ta faɗa sautin muryarta bai fita sosai.Halilu ya rumtse ido jin furucinta,“mi shi Baba ɗin ya yi miki? Na san dai ba zai dake ki ba”
“Don Allah ka fita ka bar ni ban son surutu”
“To ki tashi ki sha magani”
“Ban sha”
“Don mi?”
“Saboda jikina ne ba na uban wani ba”
“Bintu ni ki ke zagi?”
“In akwai fiye ma da haka zan yi”
“To na ji! Amma ki daure ki sha maganin,ko kuwa na kai ki asibiti ”
Bintu wacce tun shigowarsa ta rufe ido,ta yi saurin buɗe su ta na kallonsa kafin ta ce “kai a su wa?”
“Mijin ki” Halilu ya bata amsa,ita kuma ta ja dogon tsuki bisanin ta juya masa baya.
Fita ya yi ya sawo maganin ,cikin kofi ya jiƙa shi sai da ya narke duka sannan ya yi wa Bintu ɗuren shi.Duk yadda ta so ta ƙwaci kanta hakan ya cuttura saboda ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba.Babu jimawa gumi ya fara keto mata,a sannu ciwon kan ya fara sauka.Ta ja ajiyar zuciya ta na mai sake yin lamo a ƙirjinsa don har yanzu bai saketa ba.
Tafin hannunsa ya kai kan goshinta ya goge zufar,ta buɗe idonta masu kama da mai jin bacci ta saka su cikin nasa.Ya ɗan hura mata iska ya ce “ya jikin?” ta turo baki ta na hararen shi.Halilu ya ɗan ja ajiyar zuciya ya ce “Bintu ban so ki na tayar da hankalin ki akan dukiya,na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari ta salwanta ba.Ni ke nake so,ban damu da wasu kuɗi ba don haka da zarar na kammala karatuna duk wasu abubuwa za su dawo ƙarƙashin kulawata kin ga shikenan sai na mayar miki da komai”
Da sauri ta yunƙura tare da janye wa daga jikinsa,“bakin ku haɗe kai da mahaifin ka.Kamar ku na jiran mutuwar Abba duk ku ka dawo gidanmu alhalin babu wanda ya ce ku zo.Mama ba ta lafiya amma tsabar mugunta ta Kawu a gabanta yake cutar da mu, wannan ya saka ta gwammaci ta koma zaman asibiti.Na tsane ku dukan ku ban son ku,ban san ma ya aka yi mu ka haɗa alaƙar jini da ku ba”
“Kenan ba ki yarda da ni ba? Ko kuwa soyayyata ce har yanzu ba ki gamsu da ita ba? Bintu dube ni cikin ido”
Ta ɗago suka haɗa ido,sai kuma ta yi saurin sunne kai saboda ba za ta iya jurar kallon cikin su ba har wata zaiba-zaiba take gani da kuma wani abu mai kashe jiki.
“Ina son ki,kuma in sha Allah babu wanda ya isa ya cutar da ke ciki kuwa har da shi Kawun” jin furucinsa ya saka ta sake dubansa ya jinjina mata kai.
Wani ɗan sanyi ta ji ya ratsa sashen zuciyarta,duk da ba ta yarda ɗari bisa ɗari ba amma ta yarda da soyayyar da yake yi mata.
“Lilu....” sai kuma ta yi shiru,shi kuwa wani murmushi ne ya ƙwace masa ba ƙaramin daɗin sunan Lilun nan yake ji ba.Cikin zaƙuwa ya ce “mine ne Bintuna?”
Sai da ta yi ɗan jimmm sannan ta ce “da gaske ka na sona? Sannan za ka iya zama da ni a ko wane irin ƙuncin rayuwa?”
Sai da ya riƙo tafukan hannunta sannan ya dube ta cike da kulawa ya ce,“Babu wani hali da Bintu za ta shiga wanda Halilu ba zai zauna da ita ba,da ace za ki zama kuturwa,makauniya kuma kurma to ki saka a ranki ɗigo ɗaya na soyayyar da Halilu ke yi miki ba zai ragu ba”
Bintu ta zumɓuro baki ta na wani hararen shi,ya tambaye ta “mi na yi kuma?”
“Sai wani kiran kan ka kake da sunan ubanni,kawai ka ce Lilu ya fi kyau da daɗi” cike da yarinta ta yi maganar,wanda hakan ya saka shi yin dariya har sai da haƙoransa suka bayyana.
Bintu ta yi kasaƙe ta na kallonsa,ba ta taɓa sanin ya na da kyau ba sai yanzu,sai kuma ta kawar da kai.
Halilu na shirin yin magana Kawu Mansur ya shigo ɗakin.
“Uwar mi kake yi nan? Ke kuma ki tashi ki yi shirin makaranta don ubanki tunda ba kuɗin banza na zuba ba”Kawu ya faɗa ya na hararenta.
“Kawu ba ta da lafiya ne,yanzu nan ta sha magani”cewar Halilu .
“Ka