Showing 3001 words to 6000 words out of 24315 words

Chapter 2 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

126

kuma itaciyar ROUGEAU ,aikina shi ne haddasa hutar sha'awa ta hanyar tsafi” dubansa ya maida da jar bishiyar,daga bayansa ya waiga sai ya ga baƙar bishiya ce “ni kuwa sunana NOIRANT ,ni ce ke aman duk wani baƙin tsafi ”

Muƙut! Bobby ya haɗiye wasu yawu,burinsa ɗaya ya fita daga cikin wannan baƙin dajin.NATA ta yo fifike ta sauko ƙasa,Bobby ya ja baya kaɗan ganin ƙatuwar Mace a siffar bil'adama amma da fukafuki.
“Kar ka ji tsoro kyakkyawa,mu je na kai can gun sauran members” ta na gama faɗa ta ɗauke shi ta ɗora kan kafaɗarta bisanin ta tashi sama.Sun yi tafiya mai nisa,Bobby dai ya na ta baza ido ya na kallon duwatsun da ke kwance a ƙasa kamar da shi aka yaɓen wurin.



Ta na sauke Bobby aka saka masa kaya bisanin su shiga jirgi su dawo gida.Cikin zafin rai yake taka matakalen benen,Mamy na kiran sunansa sam bai tsaya ba.Ɗakinsa ya shiga ya fara watsi da kaya,sosai yake jin baƙin cikin duk abubuwan da suka faru da shi a yau.
Wata uwar tsawa Daddy ya yi masa,tare da ɗaga murya ya ce “Bobby ! Ka yi hauka ne ? ”
“Eh hauka nake! Daddy kawai don ina yin duk abin da ka ce shi kenan sai ka tsafa ni ? Na ji na yarda kai ɗan ƙungiyar asiri ne,ban damu ba wannan ra'ayin ka ne.Amma akan wane dalili za ayi min duk wannan shirmen?” bai rufe bakinsa ba Daddy ya ɗauke shi da wani mari wanda ya saka shi faɗuwa ƙasa bai shirya ba.


Da yatsa ya nuna shi ya ce “kar na kuma ji ka kira wannan da shirmen,in kuwa ka yi kuskuren yin haka zan guntsire ma halshe.So ka ke Father ya yi fushi da mu ko mi? Wannan abun da ka ke kira shirme to shi ne madogararmu,tun kakanni da iyaye.Ni ma gada na yi gun mahaifina,shi yasa kai ma doli ka karɓa in kuma ka ƙi to duk za mu hallaka sannan Mamynka ita ce ta farko da za ta su kashe”


Hankali tashe Bobby ya ɗago kansa wanda tunda Daddy ya maresa ya sunne,ya ce “su wa za su kashe ta? Daddy kar ka bari wani abu ya samu Mamyna in hakan ta faru mutuwa zan yi”
“kisan gilla za su yi mata kuwa,namanta za su rinƙa yanka wa su na ci har sai ta zama ƙwarangwal ta mutu” cewar Daddy ya na mai jan wata doguwar ajiyar zuciya bisanin ya ci gaba da cewa “ka na ji Bobby ? Duk wannan abun da nake wa kai ne fa! Ina son ganin ka cikin kyakkyawar rayuwa,kuma ta wannan hanyar ce za ka samu cikon burin ka wato Anita budurwar ka”


“ Daddy ka san Anita ne?”
“Eh na santa,Father duk ya bani labarinta”
“Wane ne Father ?”
“Shuganmu baki ɗaya na *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI*”
“Ka na nufin ya na da ƙarfi ne har haka? Har ya san mun yi soyayya da Anita?”
Sai da Daddy ya ƙyalƙyace da dariya sannan ya basa amsa da “duk yadda ka ke tunaninsa to ya wuce nan,shi ɗin fa ba mutum ba ne,komi ya na gani yanzu haka hirar da muke a yanzu duk zai samu labarinta”
“Daddy da gaske zan samu Anita ?”
“Eh za ka same ta Bobby muddin ka bi ƙa'idodin duk abin da za shimfiɗa ma”
Bobby ya yi wani murmushin farin ciki ya ce “zan yi komai akan Anita sai dai fa Daddy ban san gidansu ba?”
“Kar ka damu,mu da muke da Father duk zai faɗa ma.Mu je ka ci abinci”Cewar Daddy ya na mai jan hannun Bobby suka sauko ƙasa.
Umarni ya bada aje a gyara ɗakin Bobby ɗin,Mamy kuwa da mamaki ta ce “ya haka? Ka shiga da fushi ka sauko da murna?”
Bobby ya shagwaɓe fuska ya ce “ a bani abinci yunwa nake ji”


“Jansh? Janash ?” Mamy ta ƙwala kiran ƴar aikin nasu,da saurinta ta fito ta na mai amsawa “ki zo ki yi saving ɗin mu kafin ki ci gaba da aikin ki” duk suka samu wuri suka zauna,Janash ta zuba masu frite da niƙaƙen nama suka fara ci su na hira.
Daddy ne ke shaiwa da Mamy yadda lamarin tsafar da Bobby ya kasance a ƙarshe ya ƙara da “Ruhinsa na da ƙarfi sosai wannan ya sa Father cewa a fara tun yanzu don akwai jan aiki a gabanmu,sam ban yi tunanin Bobby zai fito da rai ba yadda na dutsen Barclay ya ƙi karɓarsa ”


“Kar ka ji komai,ai tun ranar da na haife shi na faɗa ma Ɗana waliyi ne ya na da wata baiwa ta musamman ”Mamy ta faɗa ta na murmushi.
Bobby ya ce “oh! Na manta bari na je na ɗauko wayata ina son jin su Kameel” ya faɗa tare da tashi ya nufi ɗakinsa.



Wayar ya ɗauko sannan ya fito zuwa filin training inda yake wasar mashi da ta doki.Cikin rumfa ya shiga sannan ya buɗe data, group ɗinsu na su uku ya shiga ya yi masu hi! Ai kuwa dama duk su na online su ka maido.Hira suka fara taɓa wa,hannun Bobby har rawa yake wajen rubuta masu abubuwan da suka faru.Tuni suka ruɗe wanda har ta kai su da bada wurin haɗuwa domin su tattauna.

Da sauri Bobby ya koma ɗaki ya shirya tsaf,cikin motarsa ya tafi can gidan shakatawar.Har sun zo,hannu ya basu suka gaisa sannan ya samu kujera ya zauna


“Mu fara cin abinci kafin ka bamu labarin al'mara ” cewar Kameel ya na dariya don shi sam bai yarda da maganar ba.
“Ni kam na ci abinci kafin na fito zan sha da lemu” Bobby ya faɗa.
Fadeel kuwa sam ya kasa cewa komai sai tunani yake in kuwa hakan gaske ne ya zama dolai shi ma ya je.
Bayan an kawo masu abubuwan da suke buƙata Bobby ya ƙara jadadda masu komai kamar dai can farko.


“Aboki ka ce ita mai gadin wurin mace ce,kuma wurin na da haɗari ? Kaiii ban yarda ba” cewar Kameel.
“Amma mi yasa Daddyn ka ya kai irin wannan wurin mai haɗari? AOKIGAHARA fa duniyar fatale ce,duk wanda ya shiga dajin ba zai dawo da rai ba,in ma ka fita da ran to fa a mahaukaci ne kawai” Fadeel ya faɗa cike da nutsuwa.
“To ni dai kam mun je,in kuma ba ku yarda ba sai ku shirya na kai ku ”
“abin da ke raina kenan,amma yadda Kameel ke da tsoro ina ga ba zai iya zuwa ba” Fadeel ya faɗa ya na dariya.
Kameel ya kai shawarma bakinsa ya ce,“in za ku je mi zai hana ni zuwa?”
“Bobby tunda haka ne yaushe za ka kai mu?” Fadeel ya tambaya.
“Duk lokacin da kuka shirya” Bobby ya basa amsa.
“Awa ɗaya ce daga nan zuwa AOKIGAHARA ina ga mu na iya tafiya yanzu” cewar Fadeel cike da zaƙuwa.
“Dare na iya yi mamu a hanyarmu ta dawo wa,ku dai bari har gobe” Bobby ya faɗa.
“Hum! Dama nace ƙarya ce,ga gaskiya nan ta bayyana sai kwana-kwana ka ke” Kameel ya faɗa don shi sam bai yarda ba.



“Ku tashi mu tafi” Bobby ya faɗa ya na miƙewa tsaye,“da motocin za mu je ko mu tafi da ɗaya kawai?” Fadeel ya tambaya.
“Mu je da ta Bobby kawai ,in mun dawo sai mu biyo ta nan ka ɗauki taka” Kameel ya faɗa.




Haka kuwa aka yi suka shiga mota ɗaya,Fadeel shi ne ke driving Bobby na gefensa yayin da Kameel ke zaune can gidan baya.
Hanyar da za ta kai ka dajin sam dama babu wasu gidaje sai irin uwannan mutanen maras galiho da suke ɗan buga gidan roba.Tafiyar awa ɗaya da rabi suka bisanin su kawo ƴar siririyar hanyar da za sada su da can cikin ainahin dajin.
“Mota ba ta shiga” cewar Fadeel ya na samun wuri ya yi parking duk suka fito.
Bobby ke gaba su na binsa baya,ko tako goma ba su yi ba suka ji wata irin ƙara ƙiiiiii! Suka waiga a tare mi za su gani? Hanyar shigowa ta rufe ruf....





★SENEGAL




Wasu ƴan mata biyu ne zaune kan capet,su na cin kayan marmari.Kallo guda za ka yi masu ka san ƴan gata ne,duba da yadda baƙar fatar su take wuwulniya ta na sheƙi kamar ka lashe.
A tare suka ɗago suka kalli ƙofar shigowar,“mtsss!” ɗaya daga cikin Twins ɗin ta yi tsaki,yayin da ɗayar kuma ta amsa sallama cikin sanyin murya ta na mai cewa “wa'aleykum salam! Kawun ina wuni? Ya hanya ya kuma iyali?”


Wanda ta kira da Kawun,ya ƙarasa shigowa ya na amasa wa ya ce “lafiya lau Zahra ,ya wajen ku fatan na tarar da ku lafiya?”
“Ba a sani ba! In ba tsabar iya yi ba ai ka gan mu ƙalau mine ne na tambaya? To Abba bai nan sai a tattare tsamokaran tsumman da aka kwaso ƙafa aka zo da su mtsw!”

Kawu ya ce “Bintu ina matsayin Yayan ubanki ki ke ja min tsuki? Eh lalle! Amma ba laifin ki ba ne,laifin wannan munafukar uwar taki ce da take koya miki fitsara”



Bai ida rufe bakinsa ba wata kyakkyawar mata ta fito ta na cewa “hayaniyar mi nake ji haka ne kamar ana yaƙin duniya?” su na haɗa ido da Kawu ta wani yamutsa fuska ta na haɗe rai ta ce “Yaya Mansur ne?”
“A'a ba ni ne ba! Wato Hajara bayan kin mallake ƙanena shi ne kuma ki ke koyar da ƴaƴansa mugun hali ko? ”
“Eh ta je ta...” uwar tsawar da aka daka mata ce ta sa ta yin shiru ta na turo baki haɗi da kallon Abban nata.


“Ya Mansur ina wuni? Ya su Inna fatan duk su na lafiya?” Abba ya faɗa cike da kulawa.
Mansur wanda suke yi wa laƙabi da Kawu ya haɗiye wasu yawun baƙin ciki ya na kallon gizner Ƙanen nasa wanda su biyu tal uwarsu ta haifa.
“Alhamdullah! Dama zuwa ne na yi tunda kai an shanye ka ba ka da ta cewa ka auro alaƙaƙai.Yanzu Ayub shikenan ka tsinke igiyar zumuncinmu? Yaushe rabon ka da ƙauye ? ”
“Don Allah Yaya ka zauna ,ko fa ruwa ba ka sha ba amma ka fara yin ƙorafi.Maman Twins haɗa wa Yaya abubuwan motsa baki” Abba ya faɗa ya na mai jawo hannun ɗan uwansa ya zaunar da shi kan salon.


Bintu ta yi wani saurin tashi ta na toshe hanci,sarai Kawu ya ganta.Momy kuwa ba don ranta ya so ba ta shiga kitchen,ba a jima ba sai ga ƴar aikinsu ta shigo da tray ta ajiye a gabansa.



Saboda mugun kari irin na Kawu ƙiri-ƙiri ya ƙi cin komai.Ji yake kamar ya shaƙe Abba ya mutu don ya gaji dukiyarsa.
“Don Allah Yaya ka yi haƙuri in sha Allah sati mai zuwa zan je ”
“Hum! Kullum haka ka ke faɗa,daga ƙarshe kuma ka ƙi zuwa”
“Wannan karon in sha Allah zan je kar ka damu”
“Zan koma,dama don na yi maka tuni ne akan haƙin da rataya kan wuyanka tunda an juye ma kwanya” cewar Kawu ya na miƙewa.
Abba ya yi murmushi,ya san halin Yayansa sosai.“Haba Ya Mansu kar sheɗan ya hana ka yin aikin lada,duba fa da niyyar kwana ka zo tunda ga kayan ka nan ma ka zo da su.Yi haƙuri ,Zahra tashi ki gyara masa ɗakin baƙi”
Da “to Abba ” ta amsa kafin ta miƙe,ta je ta ƙara gyara ɗakin sannan ta kwashi duk abincin da aka kawo wa Kawu ta kai masa can masaukinsa.
Abba ya fita dama wajen aiki zai je, Kawu kuwa ya na shiga ɗaki ya fiddo tarkacen layun da bokansa ya basa kafin ya maida su ya na dariyar mugunta.....



Share please
[16/07 à 08:07] MRS SADAUKI 💫: 🪆 *ƳAN ƘUNGIYAR ASIRI...*🪆
🪆
🪆🪆🪆🪆

```MRS SADAUKI```💫✍🏻

FCWA ☀️


*Gargaɗi* ban yarda a saka min book ta ko wace kafa ba sai da izini, youtube ko audio ban buƙata.Haka kuma ban yarda a juya min labari ba,ga masu shigar da ƙorafi hanya a buɗe take +22795045822.
*Ƙirƙirarren labari ne,ban yi shi don cin mutuncin kowa ba,wanda ya yi daidai da rayuwarsa kuma arashi ne*🙂


*Page 5_6*


Bayan Kawu ya ci ya ƙoshi ya yi kwance sai faman murmushi yake.Dare na yi ya fara aiwatar da aikinsa duk ya bi gidan ya turbuɗe da layu.
Washe gari Abba ya basa kuɗi masu yawa ya ce "ga wannan kafin na dawo" Kawu ya karɓa ba godi balle na gode ya saka aljihu .
Falo ya fito ya zauna kan kujera ya na kallon TV,Bintu ta Zahra ne suka fito cikin shigar kaya kala ɗaya don komai nasu iri ɗaya ne wannan ya saka ba kowa ke iya banbance su ba,sai da halinsu don Bintu fitsararra ce ta ƙarshen aji,ita kuwa Zahra babu ruwanta asali ma tsoro ne da ita.

"Ina kwana Kawu an tashi lafiya ?"
"Lafiya lau tauraruwa alhamdullah ya fama da mai mugun hali?"
Sai da Zahra ta ɗan yi murmushi ta kalli ƴar uwarta Bintu ta ce,"sai haƙuri Kawu"
"Kin fi ƙarfin ko gaishe da magajin ubanki to ina kwana?" Kawu ya faɗa ya na hararen Bintu .Ita kuwa baki ta zumɓuro ta na gunguni,"kin yi wa ubanki Ayuba da uwar ki Hajara shigiya fitsararra wacce sheɗan ya yi ma fitsari akai"
"Ni dai ba shegiya ba tunda da ubana kuma har aka kwaso jiki aka zo wajensa don cin banza..." Bintu ke faɗa cike da rashin kunya,Mama ta katse ta "Bintu mi na faɗa miki? Ban ce kar na kuma ganin kin yi wa babba rashin kunya ba?"
"Mama shi ya fara ja na fa" ta faɗa a shagwaɓe.
Jiki na ɗan rawa Mama ta ida sauko wa daga step ɗin ta na taɓa hannuwa "Yayan mahaifin naki ki ke faɗar shi ya fara jan ki?" Wani irin dundu ta kai mata a baya kafin ta balbaleta da masifa.
Kawu Mansur ya yi wani murmushin mugunta,ƙasan zuciyarsa fal farin ciki.
"Ya Mansur don Allah ka yi haƙuri ka san har yanzu ƙurciya ne da ita,duka 15years babu yawa"


"Ko ma dai mine ne ai ke ki ka koya mata,kin ga ma tafiyata" ya na gama faɗa ya shiga ɗaki ya a haɗe kayansa ya koma can ƙauyensu *Djifer*.Ɗansa babba Halilu ya tarbe shi,"Baba ya ya komai ya tafi daidai ?"
"Fiye da yadda ka ke tunani,kawai ka fara shirin zuwa kamun kifi gobe wanda za a yi masa girki"
Halilu ya washe baki ya ce "Baba har na matsu garin Allah ya waye wayyo daɗi "
"Ai wannan karon ba zai kubce mana ba,yadda na bi ƙa'idodin da boka ya ce tabbas zai zo.Wai ka ga yadda shegiyar matarsa ke min ladabi? Da zan tawo har da haƙuri ta yi ta bani hhhhh"
Halilu ya ce "Haba dai? Kenan ita tuni asirin ya fara aiki a kanta? "
"Eh sosai! Shi ma uban gayyar har wani rawar hannu yake da zai bani kuɗi inda can farko ne bai wuci ya bani dubu goma ba"



"Baba ka san kuwa ina son Bintu?"cewar Halilu ya na wani karkace baki.
"Mu bar wannan maganar ka ji! Bari na shiga daga ciki"
Halilu ya bi bayansa da kallo kawai ya na jin ko sama da ƙasa za su game Babansa bai isa ya hana shi auren Bintu ba.





A can kuwa ɓangaren Mama sosai take mugun shakkar Kawu Mansur ɗin.Sam zuciyarta ta ƙi sukuni,haka ta kira Daddy murya na ɗan rawa ta ce "Baban Twins Kawu fa ya yi fushi ya koma Djifer(ƙauyen su) ina ta basa haƙuri amma ya ƙi saurarena" yadda Abba ya ji hankalin matar shi a tashe ya ɗaga nasa hankalin babu shiri ya dawo gida.


"Kawai ka je Djifer ka basa haƙuri" cewar Mama.
Abba ya ce "ina da aiki sosai a office sai dai zuwa gobe,mine ne ya faru har ya yi fushin?"
"Bintu ce ta masa fitsara,ka san ba mutumci ne da ita ba"
"Ina take?"
"Sun tafi makaranta"
"To ki kwantar da hankali don Allah,zan je na basa haƙuri har gida"
"To Allah sa ya haƙura ɗin,sam zuciyata babu daɗi baban Twins"
Kumatunta ya ɗan bubuga tare da rarrashinta,dakyar ta barsa ya koma can wajen aikinsa.


Makarantar islamiyya ce suka tafi,ba wani sosai suke maida hankali ba ga karatun amma babu laifi sun iya karatun sallah.Zahra duk hankalinta ta tattare wuri ɗaya ta miƙa wa malam wanda yake karatu kan Tauhidi.
Bayan sun taso daga makaranta ,su na shigowa falo suka tarar da Mama ta rabka uban tagumi.
"Mama ina ta yin sallama ba ki amsa ba" Zahra ta faɗa ta na mai durƙusawa ta cire mata tagumin.
"Har kun taso?"
"Eh Mama" su yi gamon baki suka amsa mata.
"To ku je ku yi wanka ku ci abinci"
"Mine ne ke damun ki Mama?" Zahra ta tambaya.
"Babu komai kawai zuciyata ce nake jin ta yi min nauyi babu daɗi sai ƙunci" Mama ta faɗa kamar wata sakarya.
"Zai wuce Mama ki yi ta addu'a "


Ɗakinsu suka wuce ko wace ta yi wanka ta saka kayan shan iska.Su na cin abinci su na hira,Bintu ce ke bata labarin barkwanci da kuma na ban tsoro ita kuwa baiwar Allah Zahra har tsoratar take.


Da Abba ya dawo sosai ya yi wa Bintu faɗa ,kafin ya haɗe su da Zahra ya yi masu nasiha.Mama na daga gefe ta bi ayari ta yi shiru kai kace sabuwar musulunta.

Washegari
Ƙauyen Djifer Abba ya yi sammako.Daidai ƙofar gida ya parker motarsa sannan ya fito ya shiga bakinsa na shirin yin sallama ya ji ƙafarsa ta yi wani girrr.

Halilu da ke tsaye ya na wankin kifi ya ga komai sarai ya ce "ka shigo mana Baban Twins " Abba ya haɗiye wasu yawu dakyar sannan ya shigo,"babu kowa gidan?"
"Baba da Inna sun tafi gona,Habiba kuma ta na ɗaki ta na yi wa Tsohuwa tausa" Halilu ya basa amsa.


Abba ya sake matsawa ya yi sallamar da ya so yi tun a bakin ƙofa,aka amsa sannan ya shiga.
Mahaifiyar tasa wacce suke kira da tsohuwa ya gaida bisanin ya yi zaune,Habiba ta gaishe shi ita ma ta na fitowa waje.


"Ga ruwa nan a langa ki kai masa ya sha"
"Halilu daga zuwansa ?"
"Na ci uwarki ki ɗauka na ce"
Habiba na zumɓurar baki ta ɗauki ruwan wanda ainahi boka ne ya bado su ta kaiwa Abba .Cike da ladabi ta ce "an kwaso hanya ga ruwa nan Abba " ta ajiye a gabansa ta fita.


Abba ya ɗauki ruwan ya sha kaɗan ya ajiye.Ya na nan zaune sai ga Inna matar Kawu ta shigo,gaisawa suka yi ya na mai tambayarta "ina Yaya Mansur ɗin?"
"Ya shiga banɗaki yanzu ya fito"


Kawu Mansur kuwa ya na gun Halilu da ke faman gasa kifi sai barbaɗa magani suke su na hira ƙasa-ƙasa.
Abba da ya gaji da jiran shigowarsa ya fito ya na mai kiran sunansa.Kawu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login