Showing 24001 words to 24315 words out of 24315 words
Chapter 9 - Yan Kungiyar Asiri Book 1 Complete Hausa Novel
wai gida za ta kar ayi mata faɗa”
“Ok zan shiga wanka,in ta fito ki ce ta tsaya sai mu gaisa ” ya na gama faɗa ya yi sama.
Mardeeya ta shiga ɗaki,ta kalli Habiba wacce ta mayar da uniforme ta tuntsire da dariya ta ce “wai duk tsoron kar a dake ki ne ya saka duk ki ka yi wani iri?”
“Mu je ki kai ni don Allah ban son surutu?”
“Dad fa ya zo”
Gaban Habiba ya faɗi ɗaram! Haka kawai ta ji zuciyarta ta shiga wani yanayi.
Mardeeya ta ci gaba da cewa “mu je in ku ka gaisa sai na kai ki gida”
Jiki a sanyaye ta fito,kan kujera suka zauna su na jiran saukowarsa.
Kamar minti goma haka,Dad ya fara saukowa har ƙarar sautin takunsa ake ji.
Habiba ta ɗaga kai ta sauke su kan dattijon da tuni farin gashi ya fara yi masa sallama.Su na haɗa ido gudun zuciyarta ya kusan tsayawa,a haka ta daure.
“Barka da fitowa Bestie ” Dad ya furta ya na yi mata wani kallon ƙasa-ƙasa mai cike da kwaɗayi,Habiba ta buɗe baki za ta yi magana kenan Kameel ya shigo......
*Masu karatu yanzu ne ƙaddarar Habiba za ta soma,na san kun fahimci labarin na tafiya ne daki-daki a sannu a hankali ko wacce Star ta littafin zan zayyano irin ƙalubalen da ta fuskanta.Mun fara da Bintu mai namijin dare,sannan Habiba wacce a halin yanzu ta faɗa son Kameel yayin da kuma shi Mohan ke sonta shin ya za ta kaya?* Sai ku biyo NI cikin book 2 wanda a cikinsa ne duk lamurran za su faru,ita ZAHRA babbar Star ɗin ko ɓangaren ta ban ɗauko ba🤩
Masu buƙatar shiga PAID GROUP za su biya 200 kacal ta wannan account ɗin 3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ƴan Nijar carte airtel ko Moov ta 200f
*NB:* daga lokacin da na kammala book ya zama complete 500 ne farashinsa.