Showing 36001 words to 39000 words out of 60085 words

Chapter 13 - Narjeesah Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

222



Ajiyar zuciya ta sauke tace, "to sai kin zo babu damuwa ni nasan gurin da zan ajiye ta, kuma zanyi wa Mrs barr magana nasan ba zaki samu wata matsalar ba indai akan wannan ne".

Sallama mukayi naci gaba da aiki na, haka kuwa tun da safe ita ce, ta tayar dani daga bacci, dole tasa na tashi muka fara shiri tare da parking ɗin kayan da zamuyi amfani dasu, zuwa tara da rabi Ashiru ya zo mukayi sallama da Ummey muka nufi airport, zuwa ƙarfe sha ɗaya na kira Mrs Nazeer ai kuwa da farin ciki ta zo ta ɗauke mu sai katafaren gidan ta, duk ma'akatan gidan nata maza ne sai "yam mata, masu ƙananun shekaru daga sha biyu sha ukku suke nan,

Wani haɗɗen falo, kafin kace wani abu har an cika muna gaban mu da abinci irin da ban_daban, sai da muka futa sannan muka ci abinci da abun sha, wata yarinya ce, ta kira tazo, ta durƙusa ƙasa idon ta a ƙasa tace, "gani ya shugaba ta".

Dariya naso nayi amman na dake, Mrs Nazeer ta ce, "jeki ki kai wannan baƙuwar can kusa da part ɗin ku kuma duk abunda take buƙata ki tabbar mata da kin yi mata shi, kada ki yarda ta nemi abu ta rasa".

Da sauri ta gyaɗa kai, tashi Amrah tayi taja trolley ɗin mu tabi bayan wannan yarinyar, mu kuma muka saka fira inda take tambaya ta, labari na da suna na, nayi dariya na ce, "to yan zun ya ke nan Mrs barr ta ce, kada na yarda ku rigata jin wannan ".

Dariya ta saka ta ce, "kai wato dai wannan Haulman ɗin ta riga mu a komai kuma tafi mu sa'a to mun yarda maji daga baya, amman kin san wani abu kuwa".

Gir_Giza mata kai nayi, ta ce, "kin ƙara burgeni fa, wallahi, saboda tun yanzun kin fara riƙon sirrin mu, tun da gashi Haulman bata kusa kin faɗi sharaɗin ta, ɗaya daman haka muke so, shiya sa, har yan zun muke tare da Mrs Yaseer saboda tasan komai namu sirrin mu babu wanda bata sani ba, amman har ila yau bata taɓa fitar da sirrin mu ɗaya ba, a gurin kowa, dan haka kici gaba da hakan ".

Dariya nayi muka ci gaba da fira, har sai da Mrs barr ta kira ta ce, mu ƙaraso gidan ta, ta dawo tun ɗazun tana fatan dai Mrs Nazeer bata san komai a kai na ba"

Dariya mukayi haka muka bi ta gurin ɗakin da aka kai Amrah gurin akwai nisa da inda muke, kanar ba gida ɗaya ba, muka kira ta muka fita da direba ta haɗamu tare da sha tara ta arziki, na ce ba zan amsa ba, Amrah ta matsawa ita ce ta amsa, mukayi sallama, direba ya ɗauki hanya sai gidan Mrs barr, him to ai sai naga gidan Mrs Nazeer ba wani gidan bane tun lokacin da muka iso bakin get ɗin gidan nake ji wani irin bugun zuciya sai da na rufe ido da addu'a ɗauke a baki na muka lula cikin gidan, get ukku a na huɗun ne muka tsaya, da sauri wasu ma'aikatan gidan suka zo suka buɗe muna.

Kallon Amrah nayi naga duk a tsorace take sai da na dafata nayi mata murmushin ƙarfin hali sannan ta, fita nima fita nayi baki na ɗauke da addu'a kayan mu aka amsa aka shiga dasu, muka ma muna biye da masu yi muna iso har cikin gidan, faɗar haɗuwar falon ɓata lokaci ne .

Muna isa tsakiyar falon kamar ance mu kalli gurin tv turus mukayi muka zaro ido waje cikin rawar murya na ce..........

*Comment and share*

*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

💐💐 *NARJEESAH* 💐💐

*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

3️⃣6️⃣⏯️4️⃣0️⃣



➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Cikin rawar murya na ce, "Amrah kin ga wani irin surprise kuwa, wannan tar ba haka, kai am very happy fa, har naji na rage yawan damuwa ta".

Ba komai bane a burin photon mune nida Amrah a lokacin da muka haɗu a royal hotel haɗuwa ta biyu muna murmushi a jikin photon an rubuta, *your welcome pretty and friend* da zaiba, kula ga flowers masu masifar kyau a gurin.

Kallon gurin kawai mukeyi, mun shagala da kallo, takun takalmi ne, na jiyo a bayan mu, ana sauko wa daga step juyowa mukayi, da murmushi ɗauke a fuskar mu, itama da murmushi ta ke tafe, tayi shiga ta kece raini.

Ta ce, "ku ƙasa ku zauna mana kamar wasu baƙi?"

Bayan mun zauna ne a saman manyan kujerun gurin da suka kusa make falon duk kuwa da irin girman sa, bayan mun gaisa ne kukun tane ya fara kai komo a gurin, abinci dana sha kamar hauka, har sai da nace, ya isa hakan, muka ɗan taɓa kaɗan, bayan mun ƙarasa ne tace, "please muje daga ciki na kaiki ki futa dan ina son yin magana ne da ƙawata, so sirri ne zamuyi" .

Tashi Amrah tayi dan taga irin kallon da takeyi mata, tare suka bar gurin, ta ɗan jima kafin ta dawo a kisa dani ta zauna tace, "yauwa sunan ki da labarin ki sister nake son ji domin nasan irin taimakon da ya kama ta na baki ".

Kallon ta nayi murmushi na sakar mata sai kuma na ɗaure fuska na ce da ita, "Mrs barr zaki ji suna na da labari na, domin nasamu mafita da sauri dan jina nakeyi kamar saman ƙaya nake, mafitar da zaki bani kuwa ita ce ta sakani naji ƙwarin gwiwar zuwa gurin ki, dan ina son yau idan nasamu mafita nayi amfani da damata gudun a bari ya huce".

Ajiyar zuciya ta sauke tace "to kafin nan naji sunan naki dana mijin ki da fari".

Dariya nayi nace, "NARSAL, shine suna na dana mijina, bana saken furta wa kowa Sunan mijina saboda, ina jin kishin wani ya mai_maita Sunan da bakin sa ".

Dariya tayi tace, "amman Sunan yayi daɗi kjn kuma burge ni da kishin da kike yi da badan nasan yanda nake jin kishin mijina ba, da nace, kin fini haukar kishi amman nj nasan kishi gaskiya ne, to yan zun dai muje ga labarin Auren ku".

Kallon ta nayi na sauke ajiyar zuciya na ce, "Munyi Auren soyayya ne nida shi kulawa muke baiwa jjnan mu, har mukayi shekara da Aure, to a watanni baya da suka wuce, yace, dani haihuwa yake so shi, nikuma ban shirya hakan ba gaskiya ina yar yarinya dani yasa na tsofe da wuri, shine yace zai nemi Aure ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba, aikuwa duk budurwar da ya nema, da Aure har gidan su nake zuwa da wuƙa da guba, nace, su shirya kwasar gawar yar su, idan suka yarda aka ɗaura Auren ta da mijina dan mijina nawa ne ni ɗaya, aikuwa sai a fasa, abun yana yi masa, ciwo duk yan da, ya ɓoye mani zan cen Auren sa, sai na gano sa, to shine ya sauya yake biyar matan titi, ni kuma babu ruwa na da karuwar waje dan matsayin kishiya na ɗauke ta, nasha korar masa matan bari ki shine yan zun, ya gudo wannan garin, kuma gashi har naga nasara, amman ta kubce mani" na ƙarasa zan cen da dafe goshi na.

Ta ce, "tab ai kuwa kin kawo kukan ki inda za'a share maki, ki kwantar da hankalin ki, zan kaiki inda ko sunan mace, yaji ko muryar ta, indai ba ke bace, zai iya ɗaukar ta matsayin mugun abu ke koda uwar sa ce, magana kuma sai kin basa, umarni, yan kin shigo cikin tafiyar mu, amman yan zun zan saka a kaiki gidan Mrs Yaseer da Mrs Naseer, Mrs Yaseer nake son ki jawo muna hankalin ta, a matsayin ki na baƙuwar mu nasan kina da dabarar yin hakan ".

Kallon ta nayi nace, "zan yi wannan ƙokarin amman ke baki bani labarin nasarorin da kika samu ba, ballema naji daɗin yin amfani da wannan nasarorin naki gurin shawo kan Mrs Yaseer ko ya kika gani? ".

Itama ni take kallo, tana saurare na har sai da na dasa aya.

Nisawa tayi tace, "ba zan ji shakkun sanar dake ba, NARSAL amman a takaice ne zan sanar dake ".

Gyaɗa mata kai nayi, a take ta soma bani labarin ta, har ƙarshe, ai kuwa tsalle na doka na ce, "dole ne nayi aiki da wannan damar yan zun ma kuwa, amman yau zaki kaini gurin ko? ".

Dariya takeyi har da tafawa ta ce, "kai NARSAL kin ƙara burgeni tashi dai kije ki gani wan nan Mrs Yaseer ɗin ko zata bamu haɗin kai, amman kiyi amfani wayon ki".

Tashi nayi, muka fito a jikin motar muka sami Amrah shiga kawai mukayi, direba yaja mu sai gidan Mrs Yaseer ai kuwa da farin ciki ta tarbemu, ta shigar damu cikin falon ta, turus mukayi, ganin mijin ta, zaune yana aiki da laptop ɗin sa, ɗago idon sa yayi muka gaisa dashi a daddare, tashi yayi ya bamu guri muka zazzauna.

Kayan motsa baki ta saka aka kawo muna, mukayi godiya kallon Miss Yaseer nayi naga ni take kallo, nayi murmushi na ce, "to ke ba sai ki sanar damu Mai gidan yana nan ba, kin fa mun zo mun takura masa fa? "

Dariya tayi ta ce, "to dan Mai gidan yana nan sai akace ko wane baƙin ne bana son su gan shi? ".

Cike da mamaki muke kallon ta Amrah cike da dariya tace, "to ke ba kya gudun nayi maki snatched ne madam, kowa ce, na ɓoye mijin ta ke kina nunawa? "

Dariya tayi tace, "ai kuwa tunda mijina ba mugun abu bane sai na nunawa kowa shi Aure fa mukeyi ba zina ba, ballema naji kunyar nuna shi, a gaban idon kowa ".

Dariya mukayi, ta ce, "nasan kin zone kiji ta baki na, kija ra'ayi na, na yarda muje gurin da zamu halaka baƙi ɗaya".

Da mamaki muke kallon ta, gashi ta ɗaure fuska ba alamar wasa, a tattare da ita, taci gaba da faɗar, "kada kuyi mamakin taya akayi nasan hakan, to a zahirin gaskiya tun farkon ganin ku da nayi da kuma yanda nake a natse ina iya gano cewar ke da wannan yarinyar Yaya da ƙanwa ne, kuma tun daga lokacin da na fahimci hakan sai na ƙara zurfafa tunana, a kanki da abunda kika zo nema,

Tabbas abunda kika zo nema yana nan a kusa dake ki natsu da kyau kada kuyi garaje, kibi komai a sannu zaki fahimci gaskiyar abunda kike son sani, yan zun ki tashi ku tafi kada ku daɗe anan dan kuna cikin tarko ne amman kisan abunda kika faɗa a kai na Allah ya bada sa'a".

Kallon ta nayi nace, "to kin san da hakan miye yasaka kike biye dasu, kuma kin san cewar hakan yanada illah babba, sannan a iya sani na, biyayya da ƙasda kai a gurin miji da nuna masa kulawa, tsabta tattalin iya girki iya ado kwalliya nuna masa yafi kowa a gurin ki, girma mawa, farin cikin sa shine naki baƙin cikin sa kin fisa shiga damuwa, samun sa shine naki rashin sa, tare kuke da muwa kina kwantarwa mijin ki hankali tare da addu'a sune suke saka, miji yaso mace, har yaji baya iya haɗata da kowa ce mace, to sakacin na miye? ".

Dariya tayi ta ce, "shi yasa nace dake keda yar uwar ki, kallon farko na fuskaci akwai abun da kuke nema, ku tashi kuje ".

Tashi tsaye mukayi, Amrah ta ce, "naga alamar sun tsoratar dake da yawa, kuma na fahimci cewar ke mace, ce mai sanin ya kamata Allah ya ƙara danƙon soyayya keda Yaya na ".

Da Amin muka amsa muka fito da mijin ta muka haɗu ya ce, "har kun fito Mrs Salman? To Allah ya bada sa'a".

Ganin irin yanda muka zaro ido waje nida Amrah kawai yayi murmushi ya raɓamu ya wuce war sa, ssi da ya shige ciki sannan muka dawo da idon mu a kan ta murmushi kawai tayi muna, tayi gaba abinta, tayiwa direban ta, maganar inda zai kai mu, tunda wancan direban yayi tafiyar sa.

Jikin mu a sanyaye muka shiga motar ita kuma ta komawar ta cikin gidan ta, muka ɗauki hanyar gidan Mrs Naseer, itama da farin ciki ta tarye mu, amman har yan zun nida Amrah bamu ce da junan mu uffan ba, ganin yanda muka shigo cikin yanayin damuwa ne, ya saka Mrs Naseer tace, "I hope everything is fine, kodai Mrs Yaseer tayi maku wani zan cen ne akan mu? "

Gir giza mata kai nayi, na sauke ajiyar zuciya nace, "Mrs Yaseer tayi nisa bata jin kira mijin ta ya kafe ta, ya hure mata kunne bata jin zata iya aikata irin hakan, ke a gaban idon mu ma cewa yayi baya hana ta kwashe_kwashen abokai ba? Shifa baya son ganin ta da ƙawa ko ɗaya fa, dan haka mu tashi mubar masa, gidan sa, haka kawai daga ganin mutum baƙuwar fuska sai ya yarda dashi? ".

Zaro ido waje tayi ta ce, "a gaskiya bai kyauta ba, amman ni banga wani laifin sa ba, ke nima fa nayiwa kaina karatun ta natsu, ba zan koma aikata irin aika_aikar da mukayi ba, abaya ba, dan haka kema ki janye kanki daga aikata irin wannan mugun nufi da kika tsirowa kanki"

Kallon ta nayi nace, "ke koda ni ɗaya ce a wannan tafiyar tunda nayi niyar cika burina sai ya cika, ba zan janye akan baka na ba, kuma ki rubuta ki ajiye ni NARSAL sai na baku mamaki ".

Na kalli Amrah na ce, "ke tashi muje ".

Da ido ta bimu sake da baki, Amrah tace, "idan ke gwiwar ki ta kwance, to mu yan zun muka ɗaura ɗamarar tun karar filin daga, dan nima sai na shiga a cikin wannan tafiyar mun bar ki lafiya ".

Fita mukayi sai kiran mu take tana mu tsaya, amman muka shareta muka nufi direban ta, nayi masa bayanin inda zai kai mu, aikuwa muna shiga yaja mu sai gidan Haulman direba ko parking bai gama gyarawa ba, na fito nayi cikin gidan da sauri, ai kuwa a tsakiyar falon muka sameta ta da sauri taja hannu na ta zaunar dani, taje ta ɗauko ruwan Ever ta bani nasha, ta zauna tayi murmushi tace "ita fa Mrs Naseer da wasa take yi maki, dan ta gwada ki ne taga ni, kodai Mrs Yaseer ta sauya maki tunani ne".

Kallon mamaki nakeyi mata, ta ce, "kwarai kuwa, ni nasan halin kowa daga cikin su, dan haka ki kwantar da hankalin ki, ke gama labari mai daɗin ji, yau da dare zamu tafi gurin nan ina fatan yan zun hankalin zai kwanta".

Murmushi dayi wanda har haƙora na suka bayyana, na ce, "haba yan zun naji zance nikam".

Dariya tayi tace, to jeki na nuna maki ɗakin da zaki zauna kafin na zo da dare misalin ƙarfe sha biyu na dare, sai ki shirya da kyau ".

Dariya nayi nace "Aa yau zan kwanta ne tare da wannan yarinyar saboda tsaro kin san yan zun akwai waya hannun ta, kada muyi sakaci".

Ta ce, "yauwa shiyasa kike ƙara shiga raina dan akwai ki da saurin fahim ta ".

Ɗakin da Amrah take ciki anan na shiga kwance na sameta, nima na zauna a kusa da ita, ita kuma ta ce, "idan kuna ɓukatar wani abun kuje kichin da kanku kuma idan kuna son miƙe ƙafa ku shiga duk inda kuke so, ni zan shiga daga ciki zanyi bacci na tun yanzun ".

Dariya mukayi ta juya ta fita, ni kuma wanka na shiga na sauya kayan jiki na, haka ma Amrah, zaga gidan muke son yi, ai kuwa muka fito nida Amrah mun sha yawo kafin mu dawo cikin ɗakin, waya na ɗauka na shiga cikin bayi, na kira mukayi magana na fito, nida Amrah mukayi sallar magriba muka zauna akayi isha'i mukayi, muka kwanta can misalin ƙarfe goma da rabi, muka tashi nida Amrah muka fito ta bayan wani corridor da muka gani da addu'a ɗauke a bakin mu, muka fita, ta jikin flowers muke bi cikin sanɗa cikin ikon Allah sai gamu a jikin ƙofar mai gadin gidan wanda Miss Yaseer ta bani a rubuce, a test message ɗin da tayo mani,

Ƙwan ƙwasa ƙofar ɗakin mukayi aka ɓude da sauri muka shiga cikin ɗakin aka rufe ana rufewa ta jikin window na hango security suna dube_dube, ajiyar zuciya muka sauke a tare glub ne aka kunna ɗakin yayi haske ta ko ina, mutum ne muka gani zaune akan sallaya ya bamu baya, kuma sallah ce yakeyi, kallon sa mukeyi amman gaban mu faɗuwa yakeyi, nikam harda dafe zuciya ta ina karanto duk addu'ar da tazo baki na, sallame sallar yayi, addu,oi yakeyi sai da ya jima kafin ya tashi tsaye ya ɗauki sallayar ya fara lunkewa, juyowar da zaiyi kawai muka saki baki da hanci muka zaro ido waje muna nuna mutumen da hannu,

Shima mu yake kallo ya zaro ido yana, kallon mu cike da mamaki kawai ya dafe kai yayi luuuu.... Ya tafii... Zai faɗi ƙasa kawai, aka taro sa kafin mu ƙarasa kaiwa gurin har numfashin sa ya ɗauke ɗab.

Cike da tsoro da kukan daya kubce muna, nida Amrah mukayi kansa, shi kuwa wanda ya taro sa, shine yayi dubarar ɗauko buta, ya ɗebi ruwa a hannun sa ya shiga yayyafa masa, ai kuwa cikin ikon Allah sai gashi ya fara buɗe idon sa ya sauka akan wanda ya yayyafa masa ruwan ya kafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login