Showing 30001 words to 33000 words out of 60085 words

Chapter 11 - Narjeesah Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

207

akayi mai gadin gidan Salman shi aka baiwa wannan aikin har da wayar da zai riƙa kira yana sanar da abunda yake faruwa, da yake mutumen yana da hali mai kyau shine yayi ta sheda wa Mai martaba abunda ke faruwa.

Bayan wata biyu Mai martaba ya kira mu yake sheda muna cewar Salman zai zo gurin mu duk yanda akayi mu hanasa tafiya har sai idan shine ya kira mu ya bada umarnin barin sa ya tafi, ya tambaye mu cewar ko Salman yanada gurin sauka a garin mune, muka sheda masa cewar eh amman bamu san unguwar da zai sauka ba, dan yana da gidaje a garin mu harda motoci dan haka yanada masauki.

A gidan Salman kuwa wani irin ciwo ne ya taso masa, wanda yayi kamar zai mutu, sai shure_shure yakeyi ma aikatan gidan ne suka samesa a hakan da sauri suka kira wayar Haulart duk da kuwa irin tsoron ta da sukeyi, sukayi shahadar kiran ta, sai da taga damar ɗauka ta ɗauki wayar cikin masifa, take tambayar su miye?".

Cikin tsananin tashin hankali direba ya ce, "ranki ya daɗe wallahi yallaɓai ne bai da lafiya sai shure_shure yakeyi! "

Kashe wayar tayi cikin minti talatin ta iso gidan ita da guard ɗinta, da sauri ta shigo cikin falon turus tayi ta kafesa da ido tana ya tsinar fuska, wani uban ashariya ne tayi, cike da masifa ta kira waya, ana ɗaukar wayar tace, "abunda aka faɗa ya tabbata, kuma ance ko na barsa ya aikata ko ni na mutu, gashi ina da tsananin kishi, amman tunda ni rashin aikata abun zai shafa, to nayi ƙoƙarin samo yarinyar da aka ce, har ankai photon ta, a gurin bokon kuma ya sheda muna cewar ita ce, kuma nasa an sato yarinyar har ankawo ta wata hotel, kuma yan zun zan saka akaisa a ƙofar hotel ɗin a jiye sa a hakan kamar yanda aka ɓukata, nikuma zan koma na cika ɗayan aikin ".

Magana akayi mata, daga can ɓangaren, kawai ta kashe wayar da gudun ta ta fita, tare da body guard dinta ta shigo su huɗu suka ɗauki Salman suka fita dashi, maigadin ne ya kira Mai martaba ya sheda masa, ai kuwa aka bisa daman shima nashi ma aikatan suna biye da duk wani motsin Salman da matar sa.

Ban san ya akayi ba, nu dai Kawai mun ya ankawo Salman tare da jami'an tsaron sa, airport mukaje muka ɗauko su, a hotel suka sauka, sai da ya kwana biyu ya fara magana, kuma tun daga lokacin bamu sake zuwa inda yake ba saboda umarnin Mai martaba, sai dai ya kiramu yace, Salman zai koma mu kaisu airport, tun daga lokacin Salman bai sake zuwa nan garin ba sai wannan karon .

Amman fa matar sa wani sabon salon ta ɗauka duk wata macen da ta samu labarin cewar Salman ya kalla sai taga bayan ta, da sai an nemeta an rasa, kai abun ma harda abokan Salman bata bari ba, amman ban san miye yasaka mu bata rabamu da Salman ba, har tsayin wannan lokacin duk da tasan da cewar muna tare dashi, saboda duk inda Salman ya saka ƙafa tanada masaniya, akai abu kamar aljana".

kuma har yan zun sakamakon Salman baya haihuwa yake nunawa, amman kuma sai gashi Shuraim yazo a matsayin ɗan Salman, wanda kusan kullum matar Salman har a internet tana posting din Salman da result ɗin rashin haihuwar sa, anayi mata like, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa Salman da "yan uwan sa yakeyi ba him! "

Nisawa jafar yayi ya ce, "NARJEESAH kinji tarihin Salman kuma har yan zun Salman tutar sa a gurin kowa tsaye take, koda kinyi ƙarar Salman ba zaki samu biyan buƙata ba, sai in da Matar sa zaki kai ƙarar sa"

Kowa shiru ya yi Amrah ce, ta ce, "Antyn Nargeesah dan Allah kada ki kai ƙarar Salman saboda idan har mutane suka kalli Shuraim duba na hankali zasu fuskaci cewar ɗan Salman ne, to masu kawo wa Salman hari kina ganin kamar yanda muka rasa sanin inda Shuraim yake ba zasu ji daɗin kashe muna yaro ba?, ki duba da kyau kada kiyi abunda zai janyo mu rasa ganin Shuraim

Kallon su nakeyi zuwa can nace, "wallahi nikam nadawo ai nahin Narjeesah ta marar ɗaukar reni masifaffiya, kuma ni ban wani ji tausayin wannan mugun ba, koda banyi ƙarar sa ba, sai na rama abunda yayi mani! "

Dariya sukayi Nusaiba ta ce, "da mun bani har mu, dan nikam ba zan iya mantawa da halin ki ba, Anty Narjeesh".

Hindu ce ta ce, to yan zun a ina ne zamu nemo Shuraim? dan da alama Shuraim baya gurin Salman dan naga hankalin sa a tashe yake ".

Umma ta ce, "ku jira sa yazo muji ta bakin sa, idan Shuraim yana hannun sa, sai hankalin mu ya kwanta".

Kowa ya yi na'am da maganar Umma.

Nace, dan Allah Jafar da Aliyu ku saka mugun nan ya bani takar data, dan nikam ba zan iya zama dashi ba".

Kallona sukeyi suna dariya, Humaira ta ce, "ai lokacin da muka haɗu dashi munji yana faɗar akwai igiyar Auren sa a kanki kuma ba zai iya tsinke ta ba, kuma acikin labarin da kika bada ya ce, idan kika yarda ya dawo cikin rayuwar ki, kin makaro".

Tsaki kawai nayi, na share su fira muka chanza saboda sun ga bana son maganar Salman, sai dare suka je gida bayan sun zaga iyayen su, da iyayen Halima.

Yau ma kasa bacci nayi, tun da safe Amrah da Nusaiba suka kawo mani abun kari amman na sheda masu sai zuwa anjima dole suka ɗauke, suka fita sai ƙarfe goma na fito tsakiyar falo na ƙara gaida Umma na zauna ina kallon labaran da Umma take kallo, Amrah da Nusaiba suka fito suka zauna muka fara labari Umma ganin mun cika ta da surutu ne ya saka tabar gurin ta koma warta cikin ɗaki.

Labari mukeyi na yaushe ne zamu je gurin Inno mu dubo ta ita da Yaya sai dai muna gudun haɗuwar mu da wannan mutumen wanda ya so sace, Shuraim yana jariri,.

Amrah tace, Aunty gashi kuma, Shuraim ɗin baya hannun mu, da munje kawai tun da mun gano mahaifin Shuraim ko".

Nusaiba ta ce, "Allah yasa da Daddyn Shuraim zamu yaga ɓarawon yara ya kaisa kotu ayi muna maganin sa".

Harara na ɓallawa Nusaiba na ce, "uban waye zai je da wannan mugun garin mu, kisa ya raina ni, wallahi ni, bazan yarda yama ga fuskar hakuri a gareni ba dan banda shi kuma bana jin tausayin sa, ko na ƙwayar zaira ai bani ce, na saka ya aurowa kansa annobar da tafi ƙarfin sa ba ehe! ".

Gimtse dariyar su, suke yi Amrah ta ce, "Anty nifa wallahi matar Salman nake son gani kin san ko dan saboda miye? "

Gir_giza mata kai mukayi ni harda su mere mata baki, tace, "saboda yan da result ɗin Salman na asibiti yake nuna cewar baya haihuwa kwata_kwata gashi kuma ansamu akasin hakan shin wai nikam anya ma kuwa ita mutum ce, kuwa, shin tanada tunani kodai kwanyar kifi ne da ita? Shin da tasa aka nemoki ta ƙarfin gaske ta haɗaki da mijin ta, idan har da gaske takeyi, tana kishin kamar yanda tace, to ai koda umarnin duniyar zai bata, ba zata ji wuyar yin saba, irin yanda ta baro gidan ta, garin su, ta ƙetaro cikin local, ta satoki bataji wahalar komai ba, kuma ta haɗaki da mijin ta abanza da yofi, duk dan cika umarnin bokan ta, gashi kuma ya shirga mata uwar ƙarya".

Dariya Nusaiba keyi harda dafe ciki da kwan tawa, Nusaiba ta ce, "itafa mutuwa take tsoro ba wai kishin mijin ta bane ya sakata aikata hakan ita da bokan kida humai ne na bugawa a jarida, tunda sun bari har Salman ya kusan ci wata mace, ta daban bai karya tsafin nasa ba, da yace, zata mu ba".

Nikam ban ce dasu uffan ba, har suka gama, zuwa nayi na ɗauko abin karin kumallo na na karya, na, mukaje kowa yayi wanka muka saka ankon Humaira, muka fito zamu gidan, su Hindu, gurin Umma muka nufa muka sanar da ita, ai kuwa Umma ta soma faɗa, mutum da Auren sa akan sa, yake wannan shigar mayafi a kafaɗa, kuma anbi jiki da turare, kuma bada izinin miji ba, za'a fita ko? ".

Duka Umma muka tsare da ido Umma ta ce, "ni ku tafiyar ku ku bani guri kukayi mani tsaye kamar wasu itace".

Dariya mukayi muka fito nikam na ce muje dai nikam bazan wani takura kaina ba".

Tafiya mukayi, mun fito daga cikin gidan ke nan, sai ga motoci har ukku ajere parking sukayi a gaban mu, sakin baki mukayi, ganin mutane sun fito harda mace, sai Salman, a take su Amrah suka saki murmushi ni kuma na ɗaure fuska na ɗauke kai na juya zan tafiya ta kawai naga mutum a gaba na, saura kaɗan nafaɗa a jikin sa, da sauri nayi baya, cike da masifa nace, Malam miye hakan? "

Kowa kallon mu yakeyi harda su Amrah, wannan budurwar ce, mai kama da Salman da namiji suka iso gurin kallo ɗaya nayi masu, na gane su waye, wato Salma da Muhseen ne, hannu ta bani tana dariya, tace, "madam kiyi hakuri mu ɗan gaisa mana, sai ki kaini masauki nasan zakiyi tarbon baƙi ko? ".

Kamar ba zanyi magana ba, kuma dai naga ai ba ita ce tayi mani laifin ba, nace, "da ace ke ɗaya kika zo da kin ga yanda ake tarbon baƙi dan kin zo gidan karamci amman sai kika zo da mugun mutum kin kuwa ansamu naƙasu anan gurin".

Murmushi tayi ta ce, "to ai dai mu baƙin kine kuma ga Muhseen bro ɗina ne ku gaisa".

Kallon shi nayi banyi magana ba, shiko dariya yake gimtsewa, Amrah ce ta ce, dasu "bisimillah ku zamu mu shiga daga ciki".

Kallon su nayi na ce, "idan kika kaisu suka gaisa da Umma ki fito mu wuce, dan ni kam va zan shiga ba, tafiya ta kawai zanyi, kuma ki shaidawa mutum ya dawo mani da yaro na ehe! ".

Da sauri duk suka bini da ido Salman ya ce, wai kina nufin har yan zun Shuraim baya hannun ki, kuma kike zaune hankali kwance? "

Da sauri na dawo da ido na akan sa, nace, "kana nufin Shuraim baya hannun ka da gaske na rasa shi ke nan innalillahi wa inna lillahir rajiun, na shiga ukku ni Narjeesah waye wannan azzalumin da ya rabani da farin ciki na, Salma ce, ta dafa ni cikin kaɗuwa tace, "bani photon yaron na gani ".

Nusaiba ce, ta basu wayar da sauri Muhseen ya ansa ya Cuba photon Shuraim da sauri Salma ta ansa, shima Salman ansar wayar yayi ya juya cikin tsananin tashin hankalin, da sauri Salma ta ce, "kiyi hakuri yau muma zamu fara namu bin ciken yan zun kuwa zaki iya komawa cikin gidan ki zauna ga wannan wayar zan riƙa kiran ki muna magana ".

fasa fitar mukayi muka dawo cikin gidan muka zauna jagwab, kuka mukeyi har Umma ta fito ta same mu a hakan, zama tayi ta ce, "kuka ba shine mafita addu'a ita ce mafita a gare mu dukan mu".

Su Salman kuwa wata unguwar suka nufa sunayin parking suka fito da gudu suka shiga cikin gidan, saman kujera suka zazzauna Salma kuwa kaiwa takeyi tana dawowa, tana cizon baki, ta duƙule hannun ta ɗaya tana ɗan dukan tafin hannun ta,

Muhseen ya ce, "sister babu wanda zai ɗauki yaron nan face, masu bibiyar bro, amman wallahi, duk wanda ya yi wannan aikin da wata manufar yayi ba wai dan ya san da sanin cewar wannan yaron yana da alaƙa dashi ba".

Salma ta juyo ta fuskan cesu tace, "bros nikuma nawa hasa shen ba kowa bane ya ɗauki wannan yaron ba, face, ya fahimci yanda kayi saurin yarda da yaron har ya raɓeka, bayan kowa yasan cewar kai ba ma'abuci dariya bane ballema mutum yayi tunanin kana ƙaunar yara har haka ba, dan haka zamuyi bin ciken mu ta ƙar ƙashin ƙasa, dafatan zaka bamu haɗin kai kasan cewar ka babban lauya kuma wannan case ɗin kai ya shafa ba lallai bane ka iya aikin nan ba, dan haka ina son duk abunda kaga, mahaifiyar yaron nan tayi kayi mata uzuri kuma kasani ko ma miye da sa hannu na".

Kallon rashin fahimta sukeyi mata, amman sai ta sakar masu murmushi tace, "ku yarda dani bros".

Gyada mata kai kawai sukeyi, amman duk basu fahimce taba, cikin wani ɗakin ta shiga ta kira waya ta ɗan daɗe tana magana, kafin ta fito ta zauna tana kallon su".

Zaune muke bayan na gama yiwa Umma bayani, shiru tayi tace ke da Amrah ne zakuyi wannan tafiyar kuma duk zaku iya kuwa? "

Amrah tace, "addu'ar ki kawai muke buƙata ".

Addu'a Umma tayi mana, ita da Nusaiba suka rako mu, har ƙofar gida muka ɗauki hanya.........

*Comment and share*

Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

💐💐 *NARJEESAH* 💐💐

*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

3️⃣1️⃣⏭️3️⃣5️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a hanya nida Amrah muna janye da trolley din mu guda biyu da muka ɗauko daga cikin kayan da suke ajiye a waydrop wanda duk Daddyn Shuraim ne ya ajiye su, to a cikin sune muka ɗauki biyu daga ciki.

Tafe muke hankali kwance illa jimamin barin gida da su Umma mukeyi, muna ƙarasa wa a bakin titi mota na jiran mu, muna zuwa aka buɗe muna muka shiga muka ɗauki hanya sai airport koda mukaje komai angama, muna shiga kawai mukeyi jirgin ya ɗaga sai Abuja, tunda muke a rayuwar mu wannan ne karon farko da muka shiga filin jirgi harma muka hau jirgin a gaskiya munji daɗin hakan.

Muna sauka muka fito wani mutum ne ya tarye mu, muka shiga cikin motar da yazo da ita, muka ɗauki hanya, a gaskiya Abuja babban gari ne, tafe muke muna kalle_kalle a wayan ce, saboda tsaro, badan tsoro ba.

Wata unguwa ce muka shiga gidan kam ɗan madai daici, dashi yayi kyau yana ajiye mu yayi gaba abun sa, mukam tare da kayan mu muka shiga cikin gidan, babu kowa a cikin falon gidan muna ta sallama sai daga baya wata, mata ta fito da fara'ar ta tana yi muna lale mar haban da zuwa, ajiyar zuciya muka sauke, nida Amrah.

Matar ta ce, "ku shigo daga ciki mana kuka wani tsaya nan kamar wasu baƙi".

Dariya mukayi muka ƙarasa shiga cikin falon gidan akan kujera muka zauna muka gaisa da matar wadda a ƙalla zata kai sa'ar Inno, bayan mun gaisa ne aka ciki muna gaban mu da abinci dana sha, kai komai sai sam barka, ƙasa muka zauna mukaci muka ƙoshi, aka kwashe kayan matar tace, "to ku tashi na nuna maku ɗakin ku, kuyi wanka ku futa, ko? "

Murmushi mukayi mata, muka ɗauki kayan mu muka shiga cikin ɗakin da takaimu ta fito, a bakin gadon muka zauna muna sauke numfashi, Amrah ce, ta fara shiga wanka ta fito nima na shiga tare da ɗauro alwala muka sauya kayan jikin mu mukayi sallah muka zauna muna futawa, har mukayi sallar magrib da isha'i muka fito falon muka ƙara gaisawa da matar har take cewa"Amrah kodai anan zaki zauna dani kin ga ni ɗaya ce a gidan nan yara na duk sunyi Aure su ukku mata, Abida Asiya Lamra, sai maza ne kawai suka rage mani kuma duk suna gurin aikin su, kin ga na samu wata Autar mata ko? ".

Dariya mukeyi tun lokacin da ta fara maganar itama tana dariya Amrah tace, "eh fa zan kuwa zauna dake Ummi kin ga sai Anty Narjeesah da Auta Nusaiba su daina yi mani dariya suna cewa ni kam basu san a wane matsayin nake ba, niba ga yar fari ba, kuma niba Auta ba".

Dariya muke yi harda tafawa na ce, "Amrah ai dai mun riga ki sanin matsayin mu, nifa wallahi yau naga, kin zama wata irin shagwaɓaɓɓiya da ke sai uwar shagwaɓa kikeyi, kai mun gode Allah da yasa ba kece Auta ba da mun shige su wallahi ".

Dariya mukeyi, fira sosai mukayi da Ummey kamar ba gobe, kwanan mu ukku a gidan mun saki jiki da Ummey sosai, yau ne mukayi shirin zaga gari ni da Amrah direba ne ya jamu sai wani haɗaɗɗen hotel muka isa, yanayin parking muka fito nida Amrah, munyi shiga ta alfarma, wani gurin futawa ne muka nufa muka nemi kujera muka zazzauna Amrah taje tayo muna order abin sha ni kuma ina zaune ina dan na wayar hannu na, Amrah ta dawo ta zauna, muka soma fira, muna ɗan kallon gurare kaɗan_kaɗan, har aka kawo muna abin sha, wasu matane su ukku suka zo a kusa da kujerar mu suka zauna, kowa ce daga cikin su, tayi shiga ta kece raini, ɗayar ma harda gilas a idon ta ga manyan wayoyi a hannun su, da sauri ma'aikata gurin suka soma kawo masu gaisuwa tare da abinci da lemo, suna ajiyewa suka bar gurin, sai a lokacin ne wasu daga cikin ma zauna gurin suka fara kai masu gaisuwa mukam ikon Allah muke kallo.

Bamu ƙarasa mamaki ba, naga ɗayar tayi nuni da gurin da muke zaune, ai kuwa da sauri wata yariya tayo gurin mu, muna ganin hakan muka ɗauke idon mu, daga gurin su, muka fara kallon wani gurin, budurwar ta ce, "am excuse me please ana son ganin ku a gurin can".

Kallon juna mukayi nida Amrah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login