Showing 42001 words to 45000 words out of 60085 words
wani abun, amman bari kiji yanda abun yake, na shigo cikin kune da tsabar wayau na da ɗaukar fansa, da ceto yaro na, Haulman tun kafin nazo garin nan nasan ki da ƙawayen ki da halin ku baki ɗaya, sai dai sam ban riga da nasan halin Miss Yaseer ba, sai da naji daga gareku, him! Haulman kama Dila sai an shirya tunda shi sarkin dabara ne, shi yasa sai da na shiryo na shigo cikin ku,
Tun ranar da kika sanar dani cewar Sunan ki Haulman ne, na fahimci Sunan ki ne dana Salman, ma'ana Haulart Salman, shine kika haɗa farkon sunan ki da ƙarshen sunan Salman, wato Haul Man, ni kuwa shi yasa na , buɗe sunan naku wato Haulart Salman, nayi dariya nima shine na sanar dake, NARSAL wato, Narjeesah Salman, kin ga na ɓatar dake, tun daga nan nabaki labarin dana ƙir ƙira, da kaifin basira ta, dan na daki cikin ki, naji sirrin ki, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, nasan komai naki kuma na sami yarina ƙarin farin ciki harda mahaifina na".
Na nuna Baban mu, da hannu na, da sauri Nusaiba ta kafe sa da ido ya sakar mata murmushi ya rungume ta, haka gurin kowa yake mamakin taya hakan ta faru.
Kallon Yaseer nayi nace, Yaseer a jiya dana tafi gidan ku, kai da matar ka, ban san tan da akayi kuka gane wace, ce niba, kuma narasa taya akayi har kuka san shiri na wallahi badan matar ka, tayo mani test ba, akan kada na yarda da nadamar Miss Naseer ba, da kun saka asiri na ya tuno, amman Allah ya kyauta, Haulart ni ban taɓa kawo wa kaina cewar zaki iya sace, Shuraim ba, saboda nasan baki san niba, baki san wace ce niba haka Shuraim duk da kuwa kammanin Salman da ya ɗauko, na manta cewar kina bibiyar duk wani motsin Salman, kuma na manta cewar zaki iya aikata komai akan Salman, sai da aka lurad dani hakan na fahim ta, koshi kuwa sai da su Jafar suka tuna sar dani cewar har na manta yanda akayi kika sato ni kika haɗa da mijin ki har zan kasa fahim tar, aikin ki? ".
Cikin da razana take kallona, nayi dariya na ce, "kwarai kuwa ban san kammanin ki ba, amman nasan labarin ki, sai da Salma ta turo mani photon ki dana kwayen ki iri daban_daban da bayanin garin ku da shige da ficen ku, da gurin da kuke zuwa, da yanda al'adar ku take, dan haka ne, aka shirya mani wannan tafiyar wadda ban san wanda ya biya kuɗin jirgi da direban da suke zirga_zirga damu, ke harma da gidan da muke zaune, nidai nasan Salma ce ta tsara, amman ita da waye shine ban sani ba, Salma ya abun yake, a ina kika sami wannan shawarar?
Dariya Salma tayi tace, "am dafatan duk kuna biye damu, to a zahirin gaskiya kowa yasan bana shiri da matar Yaya Salman ballema nasamu photon ta, dan bana jin zan iya ajiye photon ta, a waya ta, haka zalika ni ko kallon ta bana son yi ballema naji labarin ta, to abunda yasaka na ce, ita ce zata iya aikata hakan saboda, nasan yanda take bibiyar rayuwar bro, kuma nasan yanda bata son ya raɓi kowa ne, ɗan adam nasan zatayi tunanin yana da alaƙa dashi duk da, kuwa a lokacin shi kan sa bro da Anty Narjeesh basu san, alakar dake tsakanin su ba, har sai kusan ɓatan Shuraim da kusan wata ɗaya koma fiye, tun lokacin da bro ya sanar dani komai, kuma ya tabbar mani da cewar ya ɗauki Shuraim a ranar kuma a ranar aka nemesa aka rasa, to kawai na fahimci cewar aikin Haulart ne, shi yasa na nemi shawarar wanda zan Aura a lokacin, shine ya taimaka mani, haka, Muhseen shima ya bada tashi gudumawar, a gurin wanda zan Aura ne nasami photon su da bayan su cikin sauƙi ba tare da nasha wata wahalar ba, amman kuma ma sauki da direbobin da ke zirga_zirga da ku da gidan da kuke zaune ba aiki na bane, aikin Muhseen ne, Muhseen kai muke saurare".
Gyaran murya Muhseen yayi yace, "a lokacin da na fahimci miye Sister Salma take shirya wa ita da Narjeesh, shine na, sanar da direba na ya ɗauko su a hanya ya kaisu airport, kuma a hannun Salma na anshi photon su Anty Narjeesh naje, gurin abokin karatuna a airport domin ina son yayi masu komai a cikin sauri kuma Alhamdulillah nasami yanda nake so, haka na kira abokina kuma amini na, Al'amin akan buƙatar su Anty Narjeesh su zauna a gurin Ummeyn su, kuma yayiwa abokan mu bayani sune zasu riƙa kaisu duk gurin da na kira na faɗa ina bukatar aikaisu, ai kuwa haka, suke bin umarnin na, sun bamu haɗin kai ɗari bisa ɗari, harda su sauya suna akan sunayen "yan kauye wannan ke nan".
Salma taci gaba da faɗar, "tun daga lokacin muka fahimci su Anty Narjeesh sun sami nasarar shiga a gurin su Haulart muke neman yanda zamuyi, su sami ɗaukar Shuraim, gashi mun sami labarin tafiyar dare ne, duk hankalin mu a tashe yake, mun rasa mafita, gashi duk mun haɗu a guri ɗaya nida Muhseen da Yaya Jafar da Yaya Aliyu da ita Anty Narjeesh da Amrah da muke waya, dasu, suna sanar damu halin da ake ciki, na tabbar da cewar Shuraim yana gidan kamar yanda Miss Yaseer ta sanar da ita, gaskiyar lamarin, ai kuwa kamar daga sama, Bro ya fisge wayar ya kashe idon sa yayi mugun ja saboda ɓacin rai, duk sai da muka tashi tsaye, muna zarar ido, cikin ɓacin rai yace, "haba taya zaku riƙa ɓoye mani halin da ake ciki bayan mata ta da ɗana da "yar uwar ta suna cikin hatsari, kuma kun san irin matsanan ciyar damuwar da nake ciki,? A gaskiya kun ɓata mani rai ku tashi muje gurin su Mai martaba dan duk abunda ake faɗa tun daga farko har ƙarshe munji komai! ".
Haka muka doshi ɗakin Mai martaba duk da kuwa yawan mutanen biki da suka cika ko ina na cikin gidan, a can ne, Mai martaba yayi muna faɗa sosai shida Dad shine muka shirya zuwa Abuja kuma Alhamdulillah mun iso da wuri, bamu san lokacin da Bro ya baro mu ba, amman ya kiramu yace, na kira Anty Narjeesh akan cewar duk abunda sukeyi su isa ɗakin Mai gadi, a cikin daren, to kunji abunda ya faru".
Murmushi nayi nace, "Allah sarki sannun ku da ƙoƙari" anan ne Daddyn Shuraim ya ce, "a lokacin dana zo gidan, sai na shigo cikin sanɗa batare da kowa ya ganni ba in, banda yara na, masu, kare lafiya ta, shine na shiga cikin gidan na zubawa Haulart maganin bacci a cikin ruwan lemon da ta a jiye ta shiga toilet, ina kallon ta ta jikin labule har ta shanye duka anan ne bacci ya ɗauke ta, ni kuma na baro ɗakin naje ɗakin mai gadi dan jiran zuwan su, ai kuwa suna zuwa na ɓude masu ƙofar na ɓuya, kasan cewar yasan da zuwan nasu tun kafin nazo, to anan ne, suka gane cewar mahaifin su ne, kuma shima ya ƙarasa dawowa cikin hayyacin sa"
A Nan ne yaci gaba da basu labarin har zuwa yan zun da komai yake faruwa a gaban kow.
Cikin sauri Miss Naseer ta nufi gurin Miss Yaseer da niyar dukan ta, cikin tsawa mijin ta ya ce, "haba dai tun kafin kiji naki saka makon, to tun da kin so jin naki tarihin bari kiji".
Turus tayi tana kallon mijin nata, kamar wata hauka sabon kamu,
Ya ce, "to duk abunda kika ji Salma ta faɗa nine wanda take magana a kai kuma nine na basu information a kan ku, kuma nine na basu tarihin ku, da halayyar ku, kuma Yaseer da Nazeer dani kai na duk kowa ya bada gudu muwar sa, a cikin wannan aikin, kuma Salma da kike gani ita ce nayi niyar Aure ita ce muka haɗu da ita a shari'ar da sukayi ta farko wadda na bata, rigata, ta rufe jikin ta, saboda kallo ɗaya nayi mata, a lokacin suna baƙin zuwa wannan ƙasar, kuma ni ban san ya ya, akayi ba kika shigo rayuwa ta, har na Aure ki, dan haka yan zun ina yi maki albishir da cewar, an ɗaura Aure na nida Salma yan zun haka, ita a matsayin mata ta, take".
Wani irin uban ihu tayi ta zube a ƙasa sai ihu take zubawa tana ba zai yuyu ba.
Kukan mutum ukku da ihun su kawai kake jin yana tashi a gidan dan duk sun cika wa mutane kunne, ihu Nazeer ya ce, "Shin yan zun guguwar ta zo ne ko da sauran ta? ".
Da sauri Miss Nazeer ta ce, "aa kada ka ce komai a gurin nan na roƙeka da ka tausaya mani! " sai gir giza kai takeyi.
Wata uwar tsawa ya daka mata ya ce, "yan da kika rabi da iyaye na, mata ta da yarana da kowa sukaji baƙin ciki kema sai kinji fiye da hakan shegiya muna fuka azzaluma! ".
Mai martaba ne yayi gyaran murya ya buɗe taron da addu'a, bayan ya ƙarasa ne, ya ce, "tabbas Allah shine mai iko akan komai, gashi Allah ya baku aron dama kunyi watsi da ita, to bari kuji Salman da wannan yarinyar Narjeesah ni ne, na saka aka ɗaura masu, Aure tun lokacin da tsafi gaskiyar mai yin sa, ya saka, aka sato yar mutane da niyar cin zalin ta, na riga su, a gurin domin nine na saka aka bar hotel ɗin da aka yada su, kuma wannan yaron da ake rigima a kan sa, ɗan halak ne gaba da baya" anan ne Mai martaba ya basu labrin komai har zuwa yau ɗin nan.
Ham dala kowa keyi duk da ni da su Yaya Jafar dasu Amrah dasu Humaira da su Salma mun san da wannan zan cen wanda basu sani bane kawai suke cike farin ciki, saɓanin mutum ukku, wato Haulart da wanda a tare suka wani ƙurma uban ihu suka bushe da dari suka fara yaga kayan jikin su, sukayi waje da gudu suna ihu, duk abunda suka gani sai sun daka, cige gashin kan su sukeyi, wata irin uwar guguwa ce ta taso, ta tur nuƙesu tayi sama dasu.
Mutane kuwa kowa yayi ta kan sa da gudu.
Nan nauyar ajiyar zuciya kowa ya sauke, Mai martaba ne ya ce, "to kun dai ga ƙarshen masu shirka, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tasa tukunyar ko zafi ba zatayi ba, dan haka muji tsoron Allah a duk inda muke, ku kuma Allah ya saka maku da alkhari, gabaki ɗayan ku, Salman kuna sakaci da addu'a duk da nasan ka da ƙoƙari, kuma ita ƙaddarar mutum duk inda yake sai abun nan ya shafesa, sai dai saboda addu,oi abun ya zowa mutum da sauƙi, Allah ya ƙara bamu kariyar sa baki ɗaya ".
Amin, duk aka amsa Mai martaba ya sake cewar, ku tashi kowa yaje ya shirya yau zamu bar garin nan, kema Salma bikin da ya rage sai kuje ku ƙarasa, Narjeesah da mahaifin su, a maida su gidan su, dan hankalin Umman su ya kwanta".
Kowa ya amsa da "Insha Allah".
Dad ne yakewa Shuraim wasa, yana faɗar, "abokina zaka bimu ko? ".
Ai kuwa da sauri ya tashi ya gudo ya haye jikin Amrah ya ce, "gurin Umma zani, ita ne mai yi mani wasa, tana siya mani kayan wasa kuma tana sakani nayi bacci na mai daɗi... "
Ai kuwa dariya aka saka masa, tashi mukayi, cikin farin ciki nida Nusaiba mukayi waje, Amrah tana riƙe da hannun Shuraim sukaje suka janyo trolley ɗin mu, suka fito shima Baban mu, ya ɗauko kayan sa, duk kowa yayo waje, motoci aka shiga, nida, Humaira Hindu Amrah Nusaiba Shuraim mota ɗaya Yaya Jafar Aliyu Baban mu mota ɗaya, Salman Salma Muhseen Dad Mom motar su ɗaya, Mai martaba mota ɗaya Naseer Yaseer Nazeer Miss Yaseer motar su, ɗaya.
Haka muka ɗauki hanya sai gidan su Ummey muka ɗauko kayan mu, mukayi mata, sallama muka rabu cikin jimamin juna, tana tsokanar Shuraim, haka muka nufi airport, jirgi muka hau dukan mu, yan yola, cikin ikon Allah muka sauka lafiya, yaron Yaya Jafar ne yazo da motoci muka shiga sai ƙofar gidan mu, ai kuwa Shuraim da Nusaiba da gudu sukayi cikin gidan, mu kuwa dariya mukeyi masu, muka mara masu baya.
Umma ce zaune tana famar kiran wayar mu amman shuru, duk hankalin ta, ya tashi kamar daga sama taji muryar Shuraim yana kiran Umma..... Umma...., ai kuwa da sauri ta buɗe idon ta ganin Shuraim ya shigo da gudun sa, ƙofar falon ma da ƙarfin sa, ya turo yayo kan Umma cike da farin ciki ta cafe sa, ta rungume tana dariya Nusaiba ba ce, ta shigo itama ta rungume Umma tana dariya, ahaka muka same su.
Hindu ta ce, "kai Umma sune kawai kike yiwa oyo amman banda mu".
Sai a lokacin ne Umma ta ɗago idon ta, ta kallemu taga kowa ya zauna yana murmshi, ta ce, "to bayan kun nemo muna wannan mai saka mutane kuka ya hana su cin abinci? ".
Dariya mukayi Humaira ta ce, "ai dole ne muyi kuka Umma, kema fa kawai kinyi dauriya ne, amman fa abun babu dama".
Dariya Umma tayi tace, "Humaira ungo wannan na ce gidan ku".
Dariya muka shiga yi, a dai dai lokacin da su Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Baban mu suka shigo bakin su ɗauke da sallama, amsawa Umma tayi ai tana ɗaga ido, kawai sukayi ido biyu da Baban mu, cikin wata irin zabura Umma ta tashi tsaye, ta zaro ido tana murza idon ta ta gani ko mafalki ta keyi ne, da sauri muka ƙarasa inda take muka riƙe ta, sai jikin ta, ke rawa bakin ta sai mur_mar yakeyi ta kasa furta kalma ɗaya.
Nusaiba ta ce, "Umma a zahiri ne ba a mafalki bane , Baban mune da kan sa, wanda kowa aka sanar dashi mutuwar sa, ashe yana a raye wasu ne dai suka mutu".
Zaunar da Umma mukeyi Amrah tace, "a gidan Daddyn Shuraim muka samesa a lokacin baya cikin hayyacin sa, sai da idon sa ya sauka akan Anty Narjeesh san nan yadawo daga cikin hayyacin sa".
Kuka Umma ta fashe dashi, shima Baban kukan yakeyi ganin hakan ne ya saka Yaya Aliyu ya ce, "dan Allah ku dai na kukan nan haka, kada ku saka kowa ya kama kukan, tun da Allah yasa Baban yana a raye kuma an samesa ai sai godiyar Allah ".
Share hawayen su, sukayi, kowa yayi shiru sai Shuraim ne ke wasa a jikin Umma yana jan jelar gashin Umma, yana dariya.
Tashi Umma tayi tace ku tashi Amrah keda Nusaiba ku kawo abinci muje na nuna maku, komai".
Abincin aka kawo bayan anci ansha ne, Amrah ta labar tawa Baban komai wan da yayi kuka sosai, shi kuma ya ce, sai sun koma gida zai basu labarin abunda ya sani game da hatsarin, kowa yayi na'am da hakan.
An ajiye maganar tafiya gobe laraba da safe, ai kuwa su Yaya jafar sukace duk tare za'ayi wannan tafiyar dasu, dan haka sukayi sallama suka tafi tare da matan su, mu kuwa cikin farin ciki muka kwana ga Shuraim a jikina.
Yau tun da mukayi sallar Asubahi, bamu kwanta ba, muka shiga haɗa kayan tafiya, Umma kuwa suna kichin ita da Auta da Shuraim.
Bayan mun gama shirin mu, mun ci abinci su Humaira suka zo daga baya su Hindu suka zo, muka shiga fitar da kayan mu, motar Yaya Jafar muka shiga muka ɗauki hanya.....
*Comment and share*
*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
💐💐 *NARJEESAH* 💐💐
*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*ELEGANT ONLINE WRITERS*
_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_
*Hahhhh😂🤣 Narjeesah team kun fa sakani dariya, a page biyu, 36/40 41/45, haba dai har kun manta cewar mutuniyar taku, irin gidan da ta fito gidan mata huɗu gidan makirci? Tafa san ta kan kishi da iya zaman da mutane, kuma, cikin Shuraim shine ya saka ta, ta dawo wata irin shiru_shiru da ita, amman kowa yasan Narjeesah bata dama, haka Amrah, dan haka nasan yan zun kun gane dalilin da yasa, sukayi, acting ta maida Sunan ta NARSAL*
*Ina godiya sosai da Comment ɗin ku da sharhin ku, kuma ina ƙara godiya da addu'ar ku, sosai*
4️⃣6️⃣⏯️5️⃣0️⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Tafe muke a cikin motar Yaya Aliyu Hindu na gefen sa, nida Amrah da Shuraim muna a baya, kowa ka kalli fuskar sa, a cikin farin ciki yake.
Yaya Jafar kuma shine ke driving Humaira tana gefen sa, Baban mu da Umma da Nusaiba suna baya, kowa yana cike da farin ciki idan ka kalli fuskar sa, amman Baban mu ba zaka gane wane yanayin yake a ciki ba.
Shuraim sai surutu yakeyi, yana faɗar, "yeeee! Mun hau mota zamuje yawo, Uncle ka siya mani giwa da zaki inyi wasa dasu, mu shiga ta cikin wannan jejin muyi ta faɗa, da... Da... Dami ma ake ce masa Anty? "
Dariya mukeyi, Yaya Aliyu ya ce, "nikam ba zan iya siya maka giwa da zaki ba, amman inda kace, na siya maka doki ka hau zan iya kayi ta su guda" da dariya ya ƙarasa zancen.
Haɗe rai Shuraim yayi Hindu ta, juyo tana dariya tana kallon Shuraim ta ce, "kada kayi fushi nawan bari na anshi wayar sa na kira maka Daddyn ka, nasan shi zai siya maka su, ko? ".
Kwallar idon