Showing 21001 words to 24000 words out of 60085 words
sun fara magana,
Sai naji sam wannan ba hausa irin tamu bace, dan hausar su bata fita kamar Umma na.
Mutumen yace, "yarinya kiyi hakuri ki anshi jarabawar ki, idan kina son ki tsira da mutumcin ki to ki yarda a ɗaura maki Aure a yanzun idan kuma bakya son wannan Auren anshrya maida ke karuwa, to ni kuma mutumen daya turo nu yace, kiyi hakuri ki anshi wannan Auren dan kuwa mukam mu sai da mukayi istahara akan Auren kuma munga babu wata illa idan kin yarda da ƙaddarar Allah to ki ashi Auren nan da hannu biyu ".
Kallon sa nayi na ce, "bawan Allah kadubi girma Allah ka tausaya mani ni marainiya ce kuna ƙaramar yarinya ce!"
Murmushi mutanen ya yi yace, "shekarun ki nawa ne yan zun? ".
Da sauri nace, "sha biyar".
Ya ce, "shin kin mance, cewar NANA Aisha yardar Allah ta tabbata a gareta, shekara nawa akayi mata Aure? Shin ke nan ke a yanzun uwa ce ko? To kiyi hakuri ki ɗauki Auren nan kada ki bari ayi zina dake".
Kalamai masu shiga jiki akayi mani, dole na yarda na amshi sadakin dubu sittin aka ɗaura Auren wanda nake jin kamar wuta aka ɗaura mani a jiki tashi sukayi bayan sun gama saka mani albarka da adduar kariyar Allah da wasu ruwan addu'a da suka bani, nasha ina kuka, suka fita, wasu matan ne suka kawo mani wani abun kamar zuma da kuka na nake sha saboda muguwar yunwar da nakeji ga tsoro ta ko ina, bacci ne ta ɗauke ni ban sake sanin inda kaina yake ba.
A cikin wani ɗaki mai duhun gaske na tsinci kaina, hannuwa na a ɗaure haka ido na da baki na, na rasa ya ya numfashi na zai iya fita a sauƙaƙe.
Jin motsi nayi a kusa dani, a take nayi yun ƙurin guduwa, kawai naji an janye mani ƙafa, na faɗi ƙasa Ashe akan katifa ne, ƙafa ta aka raba biyu, aka ɗaure a wani gurin da ban san miye ba, sai kawai naji saukar mutum a jiki na, Ashe ma ko kayan jiki na an cire, hannu na duk suna a ɗaure haka nayi ta dukan mutumen amman ina koda ba a ɗaure nake ba ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya ba, kawai ya afka mani.
Tabbas wannan itace baƙar rana a gareni yau nice akayi wa fyde tabbas babu wani bam banci wannan fyde ne! .
Sai da na kusa sumewa aka ƙyaleni, zuciya ta naji tana batun bugawa, naji duniyar ta isheni naji na tsani kaina da kowa ma na cikin duniyar nan!.
Bayan wani lokacin haka aka sake afka mani, haka dai nayi ta kukan zuci wanda yafi wuta zafi, da ƙuna, bayan kamar wani lokacin sai naji an fita, kuma an dawo, sautin murya naji, kamar haka:-
"Yarinya badan mace ɗaya bace, tsari na ba dana, ajiye ki koda a wani guri ne, kodan wannan abun da nayi maki, amman yanzun ga kuɗi nan, masu yawa ki nemi lafiyar ki, kuma kije ayi maki wankin mara, bana bu'katar ganin fuskar ki, kema ba zaki ga tawa fuskar ba, kisani nayi maki nisa, har abada, kuma bazan sake ki ba, kije kawai haka nan dan ni bana iya sakin mace, idan lokacin da mace takeyi, ya kai zaki iya neman wanda zai rabaki da Aure na, koda yake baki san sun nan mijin ba, zaki iya samun duk sunan da kika fi tsana a duniyar nan, kice shine mijin ki, sai a taimaka maki amman kafin ki nadawo zaki iya aikata hakan idan kuma Allah yasa nadawo cikin rayuwar ki, tofa babu wannan zan cen ya roshe,
Ga sabuwar waya nan nasan baki da ita dan na lura kuruciya na damun ki, kasan cewar ki mai tarbiya yasa har na kusan ceki, duk da banga fuskar ki ba, nasan baki son rasa wannan darajar taki, shi yasa kika tsaya baki damu da wata duniyar ba da ruɗin duniya, yanzun kije na baki wayar nan, da ƙuɗi gasu nan a cikin ƙaramin akwati sannan kuma harda wannan gidan duk sun zama mallakin ki da motoci guda biyu dake cikin gidan nan ke da duk wani abunda yake gidan nan.
Na baki dan kiyi jinyar jikin ki, duk da kin iya boye mani budurcin ki, ni mijin ki kawai nasan sirrin ki, duk da baya a gaba na.
Ni ma sakani akayi ina tare da security masu duba ko na cika aiki na ne?,
Babu wanda yasan da cewar wannan gidan nawa ne, amman ke haka kawai, naji na baki shi a kyauta.
Kuɗin nan kuma nasan zasuyi maki amfani, zan buɗ maki baki, kiyi magana nasan kina da buƙatar ki zageni, kuma idan kika sake kikayi mani mugun zagi him! ".
Allah Allah nakeyi ya buɗe mani baki, dan yanda zuciya, ta take ingiza ni jin nakeyi kamar na haɗe zuciya, na mutu.
Hannun sa ya saka ya bud'e mani baki, ai kuwa abunda na fara faɗa shine, Allah ya isa na mugu azzalumi, kuma kamar yanda ka batawa marainiya budurcin ta, Allah yasa wannan abun ya hanaka jin daɗin rayuwa, Allah ya isa na, kuma wallahi na tsaneka na tsani duk wani abunda yake naka ne, ka ɗauki tsiyar ka, bana buƙatar komai naka, nagode wa Allah da yasa banga wannan mummunar fuskar taka ba, azzalumi kawai".
Ya ce, "ya Isah haka! idan kika sake zagi na, sai na ƙara maki abunda nayi maki, koma fiye".
Na ce, "azzalumi kawai, mai cutar karamar yarinya wadda take da buri masu yawan gaske inyi karatu inyi aiki inyi kuɗi masu yawa na ginawa Umma gida da Inno da Yaya banda Mama dan na rama abun da take yi mani na rowa da hassada".
Naji yayi yace, "ko yanzun ma zaki iya cika burikan naki, duka tunda ba kashe ki nayi ba".
Da ƙarfi nace, "Allah ya isa na!, ka ruguza mani komai amman sai na rama wallahi ko ba yau ba, na murguda masa baki duk da kuwa kasan cewar baki".
Fita kawai naji anyi, ina ɗaga hannun na naji, a kwance harda ƙafa ta, hannu na saka na yaye abunda aka rufe mani fuskar ddashi, sai da na runtse idon, saboda haske.
Ina duba jikin na, na fashe da kuka na janyo dan kwalin da na gani gefe na rufe jikin na dashi.
Kuka kawai nakeyi da takaicin yanda naga, jikin na, Ashe bani da komai a jikin na, kuma glub kunne haske ta ko ina.
Allah ya isa kawai nake ja masa, na ɗauki alwashin sai na rama.
Tashi nayi daket da jan ƙafa ina cije baki, na shiga gurin da naga an rubuta toilet na duba banga bokitin wanka ba, sai bahon wanka, tunowa nayi da wani siries din film a take nakoyi komai nayo wanka na fito,
Sallah nayi ban ma san adadin sallar da banyi ba, nidai nayi ta kwana biyu, abinci naga an ajiye mani, naci, nadawo tunanin abunda zan sama a gida idan na koma gida, bacci ne ya ɗauke ni, ina tashi da zazzaɓi na tashi, naje nayo wanka haka dai na kasan ce har tsayin kwana biyu ni ɗaya ina jin na sami sauƙi na fito sanye da kayan jiki na, ƙasa na sauka na falon gidan na kalla har kichin naje bayan na fito ne, na kashe komai na gidan mai aiki da wuta, makullai kawai na ɗauka da nagani a cikin wani ɗan akwatin ƙarfe, na fito gidan na rufe a harabar gidan, motoci biyu na gani na buɗe get ɗin na rufe naje na binne akwatin na ɗora dutsi natashi na fara dube_dube gabas kudu yamma arewa ina tunanin ina ne hanyar gidan mu?.
Kawai na saka kai ina tafiya ina wai wayen gidan dana fito, a gurin bushiyar lemon tsami, na tsaya ina futawa na ƙara ɗaukar hanya ke nan, wata motar tazo taja wani wawan burki a gaba na, kafin na gudu han an turani cikin motar an shaƙa mani wani abun bacci ya kamani ban tahi falkawa ba, sai a cikin ɗakin Inno.
Ɗakin naji yana juya mani, na dafe kaina, da ƙarfin gaske, Inno da Yaya ne keta tofa mani addu'a, har nadawo cikin hayyacina, kuka na fashe dashi dan nasan, asiri na ya tonu, Kuka kawai nakeyi, tambayar duniya sunyi mani nace masu babu komai, kuma ni ban san komai ba.
Kyaleni sukayi, koda na fito tsakar gida cewa akeyi yawo na naje, nadawo, tun ina damuwa har na daina damuwa, ranar na tambayi Inno yaushe ne nadawo gida, shine take bani labarin anyi nema na ba dare ba rana duk ba a ganni ba, har kwana bakwai nikam tsoro ne ya ƙara kamani, kuma da aka tashi gani na a cikin layin mu ka tsince ni bana cikin hayyaci na har sai da na kwana ɗaya a gidan na falka.
Nan ma Inno tayi tambayar duniya amman nace mata nima ban sani ba, bayan wata biyu ciwo ya kamani ni har ma na manta da abunda ya faru dani saboda hauka irin tawa, na ɗauka cewar komai ya wuce ashe matsala babba na nan, ciwo nakeyi kamar zan mutu, Mama ta ce, " da alama dafuwar ta nuna, ciki ya bayyana idan ba a yarda ba aje asibiti ayi awo ai kuwa cikin satin akaje asibiti rest din farko ciki wata biyu, aikuwa ƙarya tawa nayi, abu kamar wasa ƙaramar magana sai ta zama babba, duk inda akaje ciki wata biyu wasu harda sati ɗaya suke faɗa.
Tabbas na shiga cikin matsanan cin damuwa da tashin hankali, na rasa ya ya zanyi da rayuwa ta ne inji daɗi, kullum cikin kuka nake tun daga wannan ranar ne, Mama da iyalan ta da yaran Yaya su biyu suke zagi na aka bi duniya dani, kawu kuwa dasu goggo cewa sukayi babu wanda zai haifa masu shege a cikin dan gin su, itama Umma kawun ta da matar sa sun zo sunyi rashin mutuci, harda su cewa a zubar da cikin aikuwa su Mama dasu kawu suka dage sai an zubar dashi, ni kuwa tunowa da nayi cewar fa wannan cikin ba shege bane da uban sa duk da ban san waye uban nasa ba, to wallahi ba zan yarda ba.
Aka kaɗa aka raya naƙi yarda su yaya Halilu harda dukan tsiya sukayi mani amman naƙi yarda shine suka ce, zasu barni amman nasani duk ranar dana haihu to sai nabar masu gida Inno kuwa tace, babu inda zani ai gidan uba nane dan haka ciki itama bata yarda a zubar dashi ba, rigima sosai akayi a gurin.
Tun daga wannan ranar ne na daina shakkar a zageni mutum na zagi na sai na sakar masa magana, su yaya kawai nake tsoro, aiki kuwa ina shan sa hardai Mama wadda take bani aikin wahala kuma ina yin sa, gashi duk abunda ta dafa duk yan da nake son abun nan bata bani, kuma nikam bana ma biye wa abinta saboda bana son gori dan tace ita bazata iya bani abunta ba, saboda ita ba zata iya ciyar da shege ba, da uwar shege, a ranar dana haihu kuwa a ranar aka koremu, wai anyi rabon gado bamu da gado cikin gidan sai gona, wadda aka siyar aka bamu dubu ɗari biyu da saba'in"
Kallon su Umma nayi dasu Jafar nayi murmushi wanda yafi kuka ciwo na ce, "Umma kinji yanda akayi wallahi ni ban san fuskar sa ba, muryar sa kawai na sani koshi dan munyi musayar magana ne! "
Hawaye masu zafi nake sharewa.
Umma dai shiru tayi cike da mamaki tace, "ki sani baiwa ina shareki bane, wallahi ko bacci banayi saboda ke, kullum na kwanta da tunanen wane hali kike ciki nake kwana nake tashi, kuma ganin ki ɗakin Inno duk da kasan cewar tana sonki ina kula da yanayin da kike ciki, rashin kunyar miye zan nuna dan an taɓaki ai duk wanda ya nuna yafika son ɗanka to kai yake so, mahaifin ki yana kula da tarbiyyar ki, haka Inno to ni kuma saboda rashin godiyar Allah kulawar miye kike so nabaki eye! ? Itafa duniya kaƙi naka duniya taso shi kaso naka duniya taƙishi, dan haka ni ina godiya da kulawar da kike samu, a gurin wannan mutanen.
Kuma ko a gidan mu haka na taso Mama na ko kallon inda nake batayi saboda alkunya, amman mutane suna kula dani sosai dan haka ni ba ƙin ki nakeyi ba ina son ki, kuma daga yau ina son duk abunda yake damun ki, kizo ki sanar dani, saboda alfarmar da mahaifin ki yayi ta nema a kanki kuma nima yan zun na gane sakaci na ne da rashin kulawa dake yasaka wasu abubuwan suka faru dake da kuma ƙaddarar rayuwar ki".
Duk shiru mukayi muna sauraren Umma har ta gama maganar tayi shiru sai hawaye nake sharewa.
Murmushi Amrah tayi tace, "Yaya Jafar Yaya Aliyu Anty Hindu Anty Humaira, zan ƙarasa maku labarin nan ta labarta masu komai har zuwa yau ɗin nan, cike suke da al'ajab.
Aliyu ya ce, "to ke nan Narjeesah matar Salman ce ko? kuma Maman Shuraim ko? ".
Ɗaure fuska nayi nace, "ni kotu zan kai shi ko kuma ya bani takarda ta, kuma duk da haka sai an bi mani haƙƙina! ".
Jafar ne ya ce, "Narjeesah Salman mutumen kwarai ne, amman duk da haka akwai gagarumar matsala! ".
Kowa faɗar, " Matsala! Matsala!! Matsala!!! Kuma? in banda Aliyu, dan da alama yadan komai.
Jafar ne ya sharce zufar da ta zubo masa yayi yace, "eh matsala babba ma kuwa dan baku san waye Salman ba, amman yan zun zaku sani, keda kike cewar zakiyi ƙarar sa ki saurara da kyau kiji wane ne Salman da har kike takun saƙa dashi, ke da kanki zaki baiwa kanki amsa".
Salman........
*Comment And share*
*UMMU Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
💐💐 *NARJEESAH* 💐💐
*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*ELEGANT ONLINE WRITERS*
*Alhamdulillah Am back*
_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_
2⃣1⃣⏮2⃣5⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Salma Muhammad Yunus, ɗane a gurin Alhaji muhammad Yunus ɗan gidan Mai martaba, Yunus, mahaifin Salman bayan kasan cewar sa ɗan Sarki tofa shi jakadan nageria ne a ƙasar london, a can aka haifi Salman amman mahaifin sa yana nan nageria, kuma mahaifin Salman yake jira ya zo ya anshi sarautar sa dan shine ake so a masarautar shi kuma yace baya buƙatar sarauta sai dai a baiwa Salman shima Salman ya ce, baya so sam, to har yanzun rigimar da akeyi ke nan.
Salman ɗan gata ne gaba da baya, mahaifiyar sa, Hajiya Lamrat "yar gidan sarauta ce, ita kuma babbar masarauta a can london ɗin aka Auro ta, shi yasa Salman baya son zuwa nageria sai da Mai martaba ya nuna ɓacin ransa akan rashin zuwan Salman gurin sa, sannan iyayen suka shiryo suka zo, Salman yanada ƙanwa Salma da Autan su Muhseen, wannan zuwan nasu a nageria shine na farko a tarihin rayuwar su, Salman da ƙannen sa.
Tunda Salman yazo nageria sam baya da farin ciki shida ƙannen sa, suka takurawa iyayen su akan su zasu koma koda ba tare da iyayen su bane, amman Mai martaba, yace shi bai san zan cen ba, sai dai iyayen su koma, abakin aikin su abar masa yaran nan sai sun saba zama tare dasu, a take duk suka a za rigimar sam su basu yarda ba, an wani zo an takura masu, jin furucin su Salman ne ya ƙara har zuƙa mai martaba inda ran sa yayi munmunan ɓaci, a take ya baiwa mahaifin su umarnin bai son ya sake kwana ƙasar nan, yau_yau ɗin nan yake da wannan ɓukatar, iyayen su Salman badan sun soba, dole sukabi umarnin Mai martaba suka tafi a ranar.
Tunda iyayen su Salman suka bar su, shike nan suka rufe kan su a cikin ɗaki basu basu sha, kai sam basa ma fitowa, har sai da Mai martaba da kan sa yaje yana dukan ƙofar tasu akan su fito zaiyi magana dasu amman kamar bada su yake ba.
Fruit, ɗin dake cikin ɗakin shi sukeci, da swan saboda sam basu iya cin abincin yan nageria ba, dan haka su basu jin komai sai kewar iyayen su da mahaifar su, sai da Mai martaba ya saka aka ɓalle masa ƙofar ya shiga cikin ɗakin shida matan sa, da ƙannen mahaifin su, Salman, a zaune suka samesu kowa ne su ya yi uban tagumi, kowa da ƙana nan kaya harda Salma ita da take mace a cikin su, kuma a lokacin tana da shekara goma sha bakwai ne, shiyasa hankalin su yaƙara tashi, su Mai martaba a tsaye suke akan su, amman sunyi kamar basu san da zuwan su ba.
Mai martaba ganin yayi idan ya cika matsa masu tofa abin caɓe masa zaiyi, kawai sai ya zauna a kusa da Salman ya dafasa, a lokacin shi kuma Salman ya yi niyar tashi yabar gurin amman kuma ƙwar jinin Mai martaba sai ya hana shi aikata hakan amman bai kallesa ba, kallon su Salma da Muhseen yayi yaga duk sun juya masu baya kawai, ya yi dariya ya ce, "haba ku kuwa miye nayin fushi dan naso ganin ku a tare dani? Ashe laifine, dan na ce ina son na sabu da jikoki na? To kuyi hakuri dama sati ukku kawai nake son kuyi a nan sai ku koma ƙasar ku inda kuka saba, amman yan zun na janye wannan maganar idan naga duk kun saki jikin ku damu duka zan baku damar tafi, can ku futa inda ba'a takura