Showing 51001 words to 54000 words out of 60085 words

Chapter 18 - Narjeesah Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

227

ya ce, "ina take ina yaro na da aka gudu dashi? Dan yau ba babu wani tausayi ko ɗauke ƙafa, sai naje da yaro na, kuma sai nayi gun duwa_gun duwa da naman duk wanda ya hana mu ɗaukar ɗana! "

Cikin irin maganar yan tasha, da shaye_shaye yake maganar, dariya Yaya Auwal yayi ya dube shi ya ce, "daga cikin wannan wace, ce, uwar yaron naka duba da kyau dan duk suna da yaro a wannan lokacin? "

Kallon kun raina mani hankali yakeyi masu, sai kuma ya tsare Humaira da ido ya ce, "ke kin ɗauka zan manta kine, to kin gama guje_gujen naki kin dawo ina yaro na yake ne? dan yau ko ki bani na tafi dashi ko nayi filla_filla da naman ki"

Mutane cike da mamaki suke kallon wannan mahaukacin mutumen kace, yaro naka ne amman kuma baka san uwar yaron ba, wata dariya ce, naji Salman nayi, harda dafe ciki da sauri nake bin sa da ido, cike da mamaki nake kallon sa dan yau shine farkon ganin sa yana yin irin wannan dariyar.

Buɗe motar yayi ya fito nima fitowa nayi su Yaya Jafar dasu Muhseen dasu Baban da yan gidan cikin gidan mu da maƙota duka gurin muka dosa, Humaira kuwa cike da haushi ta ce, "amman dai kai kam anyi jahilin mutum, a ce kai saboda tsabar jahilci da ƙarya da rashin hankalin wato kama rasa sanin wace haukar zakayi sai ta satar yara ai kuwa da kasan ko suwaye a gaban ka da kasan irin masifar da kajefa kanka, da kayi kuka da dana sani na shekara ukku zuwa huɗu dan ba ƙaramin bala'i ka jefa kan kaba, amman na lura da kai da wanda ka kwaso suka biyo ka daƙiƙaine wawaye, kida humai kun zo ku saci, yaro, yaron ma wanda baku san ɗan waye ba, to ina taya ku farin cikin zaman gidan yari tare da horo mai tsanani, dan naga ku mahaukata ne, baku ma gane ko miye nake nufi ba, Muhseen bashi yaron shi! "

Mutumen ya ce, "amman wallahi kin sa'a kina da kyau kuma har yanzun ina son ki, kuma naji kin ce a bani yaro na, amman da kin gane waye kikeyi wa maga haka, kai bani ɗana" yana mai kallon Muhseen kamar yanda Humaira tayi.

Dariya Muhseen ya yi ya ce, "Salman kazo yana neman ka".

Aikuwa shima mutumen ya bushe da ƙatuwar dariya ya ce, "kunji sunan yaro na, wai Salman amman kin kyauta kin saka mashi suna mai daɗi".

Wasu mutane ne wanda ban san lokacin da suka zoba, suka biyo bayan Salman yana ɗauke da Shuraim a kafaɗar sa, suna zuwa Salman yayi murmushi ya ce, "Shuraim duba ka gani su waye wannan mutanen? "

Ai kuwa Shuraim yana haɗa ido da wannan mutanen ya kwasa wani uban ihu wanda sai kowa ya rufe kunnen sa, da sauri Hindu ta janyo hannu na na ƙaraso a kusa da Salman na anshi Shuraim ɗin ina jijjiga shi dan yayi shuru, yana yayi shirun na sauke shi na riƙo hannun sa na ƙasa gurin na ce, "lallai yan zun nasan kowa ya fahim ci waye kai a wan can lokacin da naso su fahimci halin da nake ciki akan cewar ban san kaba, bani da wata alaƙa dakai duka basu yarda dani ba, sai gashi sabo da satar yara ta zama sana ar ka, ka saka aje har gida a kashe mu A ɗauko maka yaron, Allah ne ya kare mu, ya nuna maka shine ya haliccemu, mu dakai ya kuɓutar damu, a hannun ka, muka bar garin mu mahaifar mu saboda kai, shine yan zun dan ɓatan basira kazo ƙarasa nufin ka, kuma baka ma san uwar da ta haifi yaron ba, mutane yan zun kowa ya shaida him lallai duniya! "

Zan ƙara magana Mariya ta ce, "to andai ji kunya duk wanda ya baka shawarar nan kwanyar kifi ne dashi, kaga wannan ba ita ce kake nema ba wannan ce kake nema, ga kuma yaron nan "

Ta nuna Humaira dani da Shuraim, sannan tace dashi, "kazo kana wani zaƙewa da hura hanci kai ala dole aji tsoron ka, to ga uban yaron nan a gaban ka shine Salman ɗin da kaji a na faɗa, wawa kawai ".

Salman kallon wannan mutanen yayi wanda suke bayan sa, "da sauri suka kewaye su, suka fito da bindigogin su, suka ɗora a kan yaran sa, dashi kansa aka nuna masu aid card, tare da faɗar kidnappers, your under arrest "

Dur ƙusawa ƙasa sukayi suka ɗora Hannuwan a ƙeyar su, sai kuka wasu sukeyi, dariya aka sanya masu, Salman ya ce, "mu haɗu daku a kotu, nine mijin Narjeesah kuma nine mahaifin Shuraim Salman Muhammad Yunus ke nan, jika a gurin Mai martaba Sarki Yunus, kuma ni loya ne mai zaman kan sa, wanda ƙasa take alfahiri dani, mahaifina kuma Muhammad Yunus ambassador ne, ina fatan ka fahimci ɗan waye kake son yin kidnapped ɗin sa, ku tafi dashi ".

Magana mutumen yaso yi gurin bada hakuri amman babu wanda ya kula sa, hannu na Salman ya kama muka nufi cikin gidan haka su Humaira su Yaya Jafar suka tasa su a gaba sai cikin gida.

Kowa dole ya watse mutane cike suke da mamakin a ina na haɗu da Salman gashi, koda ganin Shuraim an san ɗan sane, a cikin gidan kuwa muna shiga na nufi cikin ɗakin Inno nayi kwanciya ta, tsakiyar gidan sai firar haukar wannan mutanen sukeyi su Salman kuwa suka bar garin suka bar mu, tunda na samu labarin basa nan na fito akaci gaba da fira dani.

Kwanan mu biyar muka shirya muka nufi gidan Kawun Umma, zo kuga yanda ake yin ina nakan a za daku, jin sukeyi kamar su goye Umma sai hakuri suke bata, har dare muka kai, sannan muka dawo gida.

Yau tun da safe aka fara kawo mani tantabu masu romuwar magani, ai kuwa nace, Inno a gaskiya daga ganin wannan abun zaiyi ɗaci, nikam ba zan ci ba, haka kawai naje na ɓata baki na".

Inno ta ce, "ci kuwa kamar anyi an gama ne, da alama kin soma man tawa da halina, ko? "

Jan kwanon nayi a gaba na, na soma ci ina zubda hawaye, su kuwa dariya sukayi Hindu ta ce, "kada ki ci ƙashi malama kuma kisha romuwar da yawa kinji matar Salman " ta kashe mani ido ɗaya.

Harara na zabga mata, sai da na ƙoshi na fara yun ƙurin amai sannan aka ajiye sai zuwa anjima, tsimi Yaya ta kawo ta tsare ni babu musu nasha dan nasan halin Yaya.

Haka sukeyi mani kullum wata rana harda su Humaira a gurin ci, ko sha.

Kwanan mu goma sha biyu a gidan mu, Mariya tayi muna zanen lalle ja, da baƙi, Hanan tayi muna kitso, gyaran jiki kam kullum sai anyi maganin mata sun ishe ni, da kayan fruit da su Yaya Auwal suke kawo wa ni abun harma tsoro nake ji gashi a jiki na tabbas naji chanji sosai.

Turare humra kayan ƙamshi kuwa kawo wa akeyi yan uwa da abokan arziki, yau muna zaune a ɗakin Inno harda su Baba da su Yaya Auwal ana fira nake cewa, "Yaya Auwal dan Allah su Inno su tashi garin nan su koma gidan mu da yake a garin Yola inda muka fito wallahi babban gida ne kuma akwai ɗakuna da yawa, ko Amrah? "

Cike da farin ciki Amrah tace, "wallahi Yaya gidan zai ishi kowa dan kowa zai samu nasa ɗakin ".

Hindu da Humaira da Auta suka ce "Allah da yafi kam dan zamu fi jin ɗadin ganin ku a tare da mu, dan kada abari zumunci mu ya lalace ".

Shiru duk sukayi Umma ta ce, "Inno to ku yarda mana tunda gashi wannan gidan yan zun yayi kaɗan saboda yara sun fara zama a cikin gidan su".

Yaya tace, "a gaskiya hakan ba zaiyuyu ba saboda gidan Shuraim ne da Nargeesah taya zamu yarda muje gidan yara mu zauna haba dai ku duba ku gani ".

Da sauri nace, "Allah Baba ku yarda na mallaka maka gidan Yaya Auwal kuma na mallaka maka mota ɗaya a cikin motocin nawa, dan Allah kuyi hakuri ku yarda".

Cike da mamaki suke kallo na, Amrah kuwa da Humaira da Mariya da Hanan rungume ni sukayi, suna dariya Anty Asma tace, dan Allah Baba ku anshi wannan kyautar da tayi maku Allah nikam naji daɗi sosai ".

Yaya Auwal kuwa cike da mamaki yake kallon kowa a gurin wai kyautar mota kodai mafalki ne yakeyi?.

Baban mu ya ce, zamu ansa mana Narjeesah amman sai kin anshi tayin mu bada tursa sawa ba, tukun".

Da sauri nace, "Allah zan yarda da duk abunda kuka umarce ni, tunda har kune iyaye na kuma Inno da Yaya basu gujeni ba, har bayan rashin gatan da nayi da ƙaddarar da ta afka mani, lallai ni kam mai biyayya ce a gare ku".

Jikin kowa sai da yayi sanyi amman Inno ta daure tace, "Narjeesah kiyi wa kiyiwa Shuraim gatan komawa gidan Salman ku riƙe yaron ku da kyau yanda zaiyi farin ciki mai ɗaurewa".

Da sauri na ɗago ido ina kallon Inno da duk wanda yake cikin ɗakin naga duk idon su yana a kaina, duƙar da kaina nayi ƙasa da ket na buɗe baki na ce, "indai wannan shine burin ku na amin ta, wallahi Allah yasa hakan shine mafi alkhari! "

Amin duk suka amsa cike da farin ciki Yaya tace, "to yau she ne kike son mu koma gidan Narjeesah? "

Da sauri na ce "Yaya duk ranar da kuka shirya, zamu iya tafiya ".

Cikin sanyin murya Mama tace, "nikam nasan bani da masauki a gidan saboda abun da na aikata maku, sai nace Allah ya kaiku lafiya Allah ya sanya alkhari ".

Nidai ban ce komai ba Umma ta ce, "Larai ai duk abunda ya faru yari ga da ya wuce, miye amfanin dawo da abunda ya wuce baya, kin fi kowa sanin yanda muke da yanda malam ya koyar damu yafiya da maida komai ba komai ba, dan haka abar komai dan Allah a fuskanci gaba, kawai, anriga da an zama ɗaya, babu yanda za'ayi ".

Kuka Mama ta fashe da shi ita da yaran ta, Anty Basira ce ta ce, "Umma mun gode da haƙurin ku haƙiƙa ke mace, ce, abun koyi a cikin duniyar nan muna godiya da halaccin ki a gare mu ".

Inno ce tayi murna da wannan sabuwar rayuwar ta ce, "to Narjeesah muna godiya sosai zamu tashi wannan gidan mu barwa sauran yaran mu da sukayi Aure, ke kuma da mun koma zaki bi mijin ki, ku ɗauki ɗanku ku tafi dashi Allah yayi maki albarka ya huci zuciyar ki, ya ƙara maku haƙuri ya baku zuri'a ta gari mai albarka, mun gode sosai Narjeesah yar Albarka keda sauran yan uwan ki da abokan ku duk Allah ya albarkace ku da iyalin ku baki ɗaya ".

Duk muka amsa da, "Amin " Baban mu kuwa farin ciki kawai yakeyi, su kawu da goggo kuwa, hawaye suke sharewa.

Haka akaci gaba da fira, kullum cikin farin ciki muke shirye_shiryen tafiya akeyi mutane sai zuwa taya murna sukeyi Shuraim kuwa tun da safe idan yaci abinci akayi masa wanka bana sake saka shi a idona sai dare idan yayi bacci.

Yau tun da safe Humaira take sanar damu su Salman suna a hanya, tun a lokacin nake jin wani irin, ganin idan fa yazo zan bar su Umma dasu Amrah da gani sai Shuraim, kawai naji kuka ya zo mani.

Sun fahimci abunda nakeyi wa kuka dan haka suka shiga bani baki.

Ƙarfe goma na safiya suka iso nasan kuwa a garin mu suka kwana, tare da motocin ɗaukar kaya suka zo, ai kuwa aka shiga fitar da kayan mota ake saka su, gidan gaba ki ɗaya muka fito motoci muka shiga, aka rufe gidan muka ɗauki hanya........

*Comment and share*

*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

💐💐 *NARJEESAH* 💐💐

*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

🔚

5⃣6⃣⏭️6️⃣0️⃣



➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Alhamdulillah mun iso lafiya cikin amin in Allah, tun lokacin da muka ɗauki hanyar unguwar mu, su Mariya aka fara buɗe ido, suna kallon yanayin unguwar, bamu tsaya ko ina ba, sai bakin kofar gidan mu, su Yaya Aliyu basu ma shiga cikin gidan ba, sukayi tafiyar su, mu kuwa fitowa mukayi, muka dum fari bakin get ɗin mu, na fara ƙoƙarin buɗe get ɗin, duk da ido suke bin mu cike da mamakin ganin irin wannan haɗaɗɗen gidan.

Kasa hakuri Yaya tayi tace, "anya kuwa Narjeesah gidan ne kuwa? "

Murmushi na sakar mata, ban bata amsa ba, har na buɗe gidan Shuraim da gudu ya riga kowa shiga, su Yaya Auwal suka ɗauki kayan suka mara masa baya, Umma kuwa ita ta yiwa su Inno jagora suka shiga cikin gidan kwasar kaya muka tsaya yi, na baiwa Auta makullin ƙofar falon, ai kuwa da sauri ta shiga ciki dan ta buɗe masu ƙofar, muka ɗauki kayan muka mara masu baya, a bakin kofar falon na ajiye masu na dawo na rufe get ɗin, na juya na shiga cikin falon.

Koda na shiga duk sun baje a tsakiyar falon wasu a kujeru wasu a ƙasa, nida Amrah Nusaiba da Humaira da Hindu muka haye sama, ɗakin Umma muka shiga muka kwashe mata kayan ta, muka dawo dasu cikin ɗakina, muka shirya mata komai nawa kayan kuwa a akwati suka zuba su, da kayan Shuraim.

Bayan mun ƙarasa ne, muka fito muka shirya wa Inno nata, ɗakin inda muka kwashe kayan Umma, a ɗakin kusa da Inno muka shirya wa Yaya nata, haka Mama ma mukayi mata, muka sauko Amrah ce ta sanar dasu, suje ta nunawa kowa nasa ɗakin, haka kuwa akayi Mariya a ɗakin su Amrah aka kai nata kayan, su Zuwaira Shamsiyya nasu ɗakin daban.

Su Yaya Auwal kuwa a ɗakin ƙasa suka zaɓa sai farin ciki suke yi Baban mu ma ɗakin sa yana sama yana daga gefen nasu Inno.

Kai Alhamdulillah gidan kam sai sam barka kowa ka gani a cikin farin ciki yake, kamar wanda akayi wa albishir da kujerar makka.

Bayan komai ya dai_dai tane, su Humaira suka tafi, gidan iyayen su, mu kuwa duk yam matan a kicin muka haɗu domin shirya abinci, saboda basu san takan komai ba hakan ya saka muka dage gurin koyar dasu, bayan mun kam mala ne, Zuwaira Basira da Shamsiyya suka ni a gaba suna ƙara neman yafiya a gare ni, nikam na ce dasu, "na riga da na yafewa kowa dan Allah abar tuna baya".

Godiya sukayi mani, haka muka yini cikin farin ciki muka tashi cikin farin ciki, su Mommyn su Humaira da Hindu da Haleema, duk sun zo tare da yaran su, sosai suka nuna farin cikin su da jin daɗin su, akan dawowar familyn mu guri ɗaya.

Bayan kwana biyu, muna zaune anata fira, nace, Yaya Auwal gafa motoci nan guda biyu a harabar gidan nan muje ka zaɓi wadda kake so, ɗayar kuma su Yaya sai ku san yanda zakuyi da ita, dan nikam na mallaka maku ita halak malak amman Yaya Auwal shi ɗaya yake da wadda ya zaɓa"

Cike da farin ciki muka doshi harabar gidan ai kuwa Anty Asma da Anty Basira suka zaɓar masa, shi kuwa kukan farin ciki yakeyi musam man lokacin da na bashi makullin motar su kuma na basu makullin ɗayar.

Yau ne a tarihin rayuwa ta naji Mama ta kama hannu na, ta rungume ni, tana zubar da hawaye tana faɗar, "haƙiƙa ɗan hakin da ka raina shine yake tsone maka ido, haƙiƙa ko wane ɗan adam Allah ya rubuta masa arzikin sa, a haƙiƙa zafin nema baya kawo samu, tabbas hassada gamai rabo taki ce, na yarda da wannan Narjeesah tun daga lokacin da Allah ya nuna mani, cewar bani da dubara kuma babu wanda yake tserewa ƙaddarar sa, kuma yan zun na ƙara yadda da cewar, mutum yana tare da arzikin sa, Narjeesah gashi Allah ya nuna mani da ido na, cewar ke ɗin dai da nake fatan naga kin dauwa ma a cikin baƙin ciki, sai gashi Allah ya nuna mani, ke baiwar sace, shine mai tsara komai akan bayin sa, gashi dai a ƙarƙashin ki yau muka dawo, ina riƙon Allah da ya yafe mani,

kuma kema ki yafe ni, kada kiga laifin yan uwan ki na rashin sonki nace na ɓata ki a gurin su, ada ina dariyar kinyo cikin shege duk da na fahimci kin ɓiye wa kowa gaskiya ne, kuma ni kaina na fahimci cewar cikin jikin ki, ba shege bane, tun lokacin da na fara shegan ta cikin na fahimci hakan amman a lokacin bana sonki da farin ciki shiyasa nayi ta, zagin ki ina saka kowa ya kyace, ki, Narjeesah tabbas duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba, to shi tashi tukunyar ko zafi ba zatayi ba, kuma tabbas na yarda da cewar mai ɗa goye baya cewa ɗan wani shege dan bai sani ba ko ya haifa, sai gashi ina zagin ki ashe nima a cikin ɗaki na, akwai shegu har huɗu, dan Allah kiya feni wallahi haƙin kine yake bibiyar rayuwar mu...

Kuka mai cin rai Mama ta fashe dashi tana mai dur ƙusawa a ƙasa saman kafafuwan ta, da sauri na ɗago ta, nace, "Mama na daɗe da yafe maki Allah ya yafe muna baki ɗaya ".

Riƙa ta nayi muka dawo cikin gidan a gurin Umma taje neman yafiya kuma Umma tun kafin tayi maga ta ce, ta yafe, haka su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login