Showing 48001 words to 51000 words out of 60085 words

Chapter 17 - Narjeesah Book One Complete Hausa Novel

15 Oct 2025

223

yayi shiru muna jiran muji daga garesa, harda maƙota masu kallon Ikon Allah, duk suna a gurin.

Wayar Yaya Jafar ce tayi ƙara, da sauri ya kalli Baban ya ce, "sun neman izinin shigowa"

Murmushi Baban yayi ya maida idon sa akan Yaya Mudarsir ya ce, "kaje ku shigo da baƙi".

Tashi yayi ya fita, sai gashi sun shigo tare zaro ido waje nayi, na buɗe baki zanyi masifa, da sauri Humaira tayi wa Inno da Yaya raɗa a kunne da sauri suka ce, "A hir ɗinki Narjeesah Allah kikayi wata magana a gurin zamu swaɓa maki ".

Zuɓurar baki nakeyi gaba, ina ɗaure fuska, Shuraim kuwa ƙafata, yazo ya haye Salman a kusa da Yaya Jafar ya zauna, Muhseen kuwa a kusa da inda muke zaune ya zauna ya ce, "Anty Narjeesh bakiyi maraba da zuwan mu ba ne? ".

Gir giza masa kai nayi nace, "kai nayi maraba da zuwan ka amman banda wan can mutumen ka duba yanda yake harara ta"

Ɗaga ido sukayi shida Amrah ai kuwa harar ta, suka kamasa yana yi dariya sukeyi ƙasa_ƙasa.

Gyaran murya Baban yayi yace, "To Alhamdulillah Allah shine mai tsara yanda yaso a duk lokacin da yaso, to gashi Allah yayi dawo wata a cikin iyalai na, kuma gashi nasami sauye_sauye da dama kuma abubuwa duk sun birkice, motar da muke ciki ce, tayi hatsari ba tare da mun san miye musabba bin ba, amman kuma ni a cikin jeji aka jefa ni, motar ta kama da wuta, kaina ya bugu da icce nikam ban sake sanin inda kaina yake ba, na dai falka ne na sami kaina a asibiti kuma na manta kaina da Sunana kawai dai na rasa Yaya zanyi na tuna inda na fito, koda aka sallame ni daga asibiti wannan yaron ne na gani a kaina, kuma shine ya ɗauke ni ya kaini gidan sa, naci gaba da jinya ta har nasami sauƙi amman kuma, hal zuwa lokacin bana iya tuna waye ni, ganin haka ne ya mai dani asibiti aka ce, idan naga abunda nafi ƙauna zan iya tunawa, gidan su muka dawo ya bani aiki wanda na nema duk da kuwa cewar gidan sa cike yake da ma'aikatan kaki da marasa kaki ya bani gadin get ɗin ƙuryar gidan sa, kasan cewar get huɗu a gidan nasa".

Kallon Salman sukeyi wanda idon sa yake a watar sa kamar baya gurin.

Baban ya ce, "sai shekaran jiya ne Allah ya kawo mani Narjeesah da Amrah, muka haɗa ido dasu ne, a lokacin ne, nafaɗi ƙasa, kaina na juya mani, a take na some a gurin, ina farkawa na fahimci cewar nawo cikin hayyaci na".

to kunji abunda ya faru.

Zufa su kawu suke gogewa, kallon Baban Inno tayi tace, "Alhamdulillah barka da dawowa Malam, sai kuma abunda ya faru bayan baka nan" a take Inno ta labarta masa komai.

Ai kuwa kallon kowa yakeyi a gurin yana gir giza kai, ya ce, "wato koda mutuwar ce, haka zakuyi wa iyali na, wula'kanci, Narjeesah! Narjeesah!! Narjeesah!!! Kuna nufin ita ƙaddara bata isa ta faɗa a kan ta bane ko miye kuke nufi? Ai ada na ɗauka, koda a ce da gaske cikin jikin Narjeesah da gan ganci ta same sa irin yanda kukafi kowa sanin ina son ta, to kuma zaku sota kuma zaku janyo ta a jikin ku, a hankali kuna nuna mata, laifin ta,

To yan dai bari kuji waye wannan Shuraim ɗin yaron Narjeesah wanda kuka tsana kuka kureta ida da 'yan uwan ta, harda mahaifiyar ta, suka rasa matsu gunni, kuka basu wasu 'yan kuɗi, wai gadon da suka samu ke nan, to kun ga wannan yaron Shuraim? "

Ya janyo hannun Shuraim ya zaunar dashi a jikin sa ya ce, masu "yaron nan ɗan halak ne kuma wannan yaron da kuke gani Narjeesah ta hanyar sunna suka sami cikin sa, kuma, shi jika ne, a gurin sarakai kafin nan Aliyu ku sanar dasu waye mahaifin Shuraim"

Gyara zaman Yaya Aliyu yayi yace, "Shuraim" labarin komai ya basu har sace sa zuwa yan zun, san nan ya sake kallon su, ya ce, "kun ga wannan"

Ya nuna Shuraim yace, "ga Salman nan shine uban Shuraim halak malak".

Dukan su mamaki sukeyi wai a ce Shuraim ɗan gata gaba da baya, sukayi muna wannan walaƙancin haka?.

Salman kuwa haushin su yakeji, Inno ce da YAya da su Yaya Auwal Hanan da wasu daga cikin yan uwa na kawai yaji baya jin haushin su, tashi kawai yayi ya bar gurin yayi waje kamar wani kubu buwa.

Da sauri su Yaya Aliyu da Jafar suka mara masa, baya.

Inno ce ta ce, "Malam Shamsiyya da Atika ciki biyu sunayin kuma suna haifewa, ita Shamsiyya wannan cikin na jikin ta shine na ukku, duk da anso zubar dashi amman abun ya faskara".

Cike da mamaki Baban ya ce, cikin fushi, wato........

*Comment And share*



*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

💐💐 *NARJEESAH* 💐💐

*Rubutawa*

*NANA KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

5⃣1⃣⏭5⃣5⃣



➿➿➿➿➿➿➿➿➿ "wato sune "ya'yanso ko? Basa laifi, ai ni a ganina duk yara na ɗaya suke a gurin ku kamar yanda nake ji a zuciya ta, Bala kai da ƙanwata da ke Larai kun cutar dani kun raba mani kan "ya"yana manya basa tausayin naƙasa dasu, ni kuma ba haka nabar ku ba, amman babu komai kunyi son ranku, duniya ce, gashi nan tun yanzun kun fara gani!".

Kawu Bala yace, "kayi hakuri ɗan uwana sharrin sheɗan ne hakan ba zata sake faruwa ba "

Goggo ta ce, "haba ɗan uwana ai wallahi mu bamu da niyar watsaye maka zaman lafiyar da ka ɗora iyalan ka, shi yasa ma bamu siyar da gidan ba".

Tsaki Muhseen Humaira da Hindu sukayi, ni kuma na ce, "andai ji kunya wallahi, a ce ya'yan ɗan uwan ka, kayi mugun tsana to taya ma zan yarda in saki jiki daku, kudai kawai a daiyi zumunci".

Baban murmushi yayi, ya ce, "ba kuda bakin kariyar kan ku amman ina mai jin takaicin abunda kuka aikata mani, domin ni kuka to zarta ba wani ba, ke kuma Larai kin girbi abunda kika shuka ko? Nafi kowa sanin irin yanda kike ƙin Narjeesah amman na ɗauka ko da bayan rai nane zaki iya renin duk nin abunda na bari a baya na, amman ba bu komai a ga su Shamsiyya nan sun bar maki darasi, Narjeesah ƙarama ce, akan su Shamsiyya amman babu tausayi babu tausayawa keda yan uwa na da sauran yara na aka kora mani iyali, saboda idon ku ya rufe akan dukiya, to gani nadawo kowa ya dawo mani da abunda yake hannun sa indai nawa ne! "

Shiru duk sukayi sai zarar ido sukeyi da soshe_soshe.

Muhseen ne ya ce, Anty Narjeesh nifa haushin mutanen nan nake ji wallahi, musam man yan zun dana ƙa jin haushin su"

Dariya mukayi na ce, "duk alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare su, sai wani kame_kame sukeyi"

Fira akeyi tsakanin Inno da Yaya da Umma na yaushe gamo har suke sanar da ita cewar ai su yayan mu sunyi Aure, wannan sabon ɗakin da muke gani na sune, da matan su, Yaya Auwal ne da Yaya Anas ne basu yi Auren ba, saboda sun ce, sai Mun dawo ko suna dawowa cikin natsuwar su, haushin kansu sukeji, saboda kasa iya tsare muna wannan fitinar data faru da rashin adalci, sun je neman mu gidan da muka zauna ko suna da labarin garin da muka nufa? Maƙota sukace basu da labari, shine bayan kwana biyu suna neman mu basu same mu bane shine suka tuna da ƙawar Umma baba Luba, to sunyi nasarar zuwa gurin ta, sun gano gidan ta, amman kuma itama ta ce, dasu neman ku takeyi ta nemi yafiyar ku, domin saboda ita kuka zo garin amman hassada ta saka ta koreku, gashi ita bata da labarin, wasu 'yan uwan ku, bayan kawu, haka suka dawo jiki babu lakka, to shima dai kawun Umma yana cikin tashin hankalin rasa, rike ammar da aka bashi saboda tsabar son zuciya , kun fa ji abunda ya faru ".

Amrah ta ce, yauwa Inno ina mutumen da ya tashi sace muna Shuraim ya turo muna yan daba, wanda shine silar barin mu garin nan? "

Ai kuwa da sauri Mariya ta ce, "number shi tana nan na amsa, mayar sa ta kusan bakwai neman ku, shi da yan daban sa, ala dole sai anfito masa da ɗan sa, bari na ɗauko maku number "

Tashi tayi ta shiga cikin ɗakin Inno mu kuwa murmushi muke sakar wa juna, Muhseen ya ce, "kamar ya ke nan?"

Nusaiba ta ce, "bari na baka labarin abunda ya faru" ai kuwa harda zufar sa cike da masifa ya anshi number wayar ya tashi ya fita waje Yaya Auwal ya mara masa baya.

A can ƙofar gida suka sami su Daddyn Shuraim tare da Shuraim ɗin yana maƙale da hannun sa, sai rigima ya keyi, duƙawa Salman yayi ya ɗauke sa, ya ce, "my friend miye ne mi kake so ne wai, wannan rigimar ta miye? ".

Dariya Shuraim ya yi ya ce, "Daddy ka bani sharabar da nace, maka ance na kawo idan kazo, kuma na ce shan bata".

Dariya suka saka masa, "a'a Shuraim yau kuma maganar ma irin ta shagwaba ce akeyi, to Allah ya taimaka man bashi tsarabar sa da sukayi rigima shida Inno ya kai mata"

Salman ya ce, "Aliyu yaron nan harda su cika baki yayi wa matan nasa ke nan? Eh lallai nabaka goyon baya, ka kai masu kada matan su kira ka miji marar cefane ".

Dariya aka saka Jafar ne ya buɗe motar yana dariya ya fara ɗauko masa ledodin masu zane kuma cike suke baya iya ɗaukar su, gashi leda ukku ce, riƙo masa sukayi har cikin Zauren gidan namu, suka rage yawan kayan suka bashi da ket yake tafiya su kuwa dariya sukeyi masa, da sallama ya shigo cikin gidan sai uban nishi yakeyi, duk muka amsa muka bishi da ido.

Dariya mukeyi ganin yanda yake ta uwar zufa, ya raɓa ta gefen mu yayi gurin Inno yana cewar, " wai...! Wai..! Na gaji Inno ga sharabar ki na kawo maki, kuma bari na kawo maki sauran, Anty Nusy muje ki tayani ɗauko mata shauyan".

Kowa sakin baki yayi yana kallon sa musam man yan da ya riƙe kun kumin sa, yana sauke numfashi, tashi Nusaiba tayi tana yi masa dariya ta ce, "wallahi Shuraim ka cika ran ganci yaro daga ɗaukar wannan yan kayan sai uwar zufa kakeyi da sauke numfashi a cikin wahala? ".

Baki ya turo mata yayi gaba abin sa ya ce, "ban ma so kada kizo nama fata dake".

Auta ta ce, "Ai kuwa yaro sai nabika dan kaji daɗin kai ƙarata a gurin Daddyn ka ko? "

bin bayan sa tayi a cikin Zauren ne ta gan su ta anshi kayan tare da neman ta kira masu ni, a tare suka dawo ɗauke da kayan a gaban Inno suka ajiye, Inno ta ce, "Shuraim wannan aikin ai yayi yawa ko? Nifa da wasa nake yi "

Humaira ta ce, "Inno ko yan zun idan kina buƙatar wani abun kiyi bayani dan yaron namu akwai lafiyar kyauta".

Dariya akeyi a gurin Yaya tace, "a a iyayen sa dai suke wannan aikin "

Hindu da Humaira da Amrah harda Auta shiga chapta da su Inno, zuwa can Auta tace, "Anty Narjeesh Daddyn Shuraim yana neman ki a waje".

Ɗaure fuska nayi, kawai na share ta, kowa ya maida hankalin sa a kaina, Inno da Yaya cikin hasala su kace, "anya Narjeesah ba kiji mijin ki na kiran ki bane ko ya ya? "

Umma tac, "humm...!

Hindu da Humaira suka ce, "Inno sai kunyi da gaske fa, dan har yan zun haushin sa, takeji bayan kuma ta riga da tasan ƙaddarar suce a hakan bayan ma ta gode Allah da Mai martaba da yasa da Auren su wannan abun ya faru "

Ɗaure fuska Inno tayi, tace, kina tashi ko sai nasamu wani abun na jefeki dashi, ja'irar yarinya kawai "

Cin no baki nayi gaba, na tashi na ɗaure fuska na fita, waje. Baban mu ne yayi dariya ya ce, "Narjeesah manya in banda harkar ƙuruciya ina ke ina Salman keda Allah yayi maki babbar kyauta, ai kuwa kada kiyi wa kanki mugun abu, koda ace Salman a iya taimako na ya tsaya ai zaki so ki faran tawa wanda ya ceci rayuwar mahaifin ki a lokacin da kika kusa rasa shi, koda kuwa wannan farin cikin naki shine ya rage maki"

Amrah tace, Baba tanafa son shi, haushin da take ji idan Haulart tana yabon shi da mugun abunda takeyi masa, har jikin ta ke rawa sai nayi da gaske gudun kada ta bari kishi ya saka ta, ɓata muna aiki, kai Baba a ranar da muka shiga cikin gidan kasa bacci tayi, sai yawo takeyi a tsakiyar ɗakin da aka ware muna, sai faɗar take, wallahi ita sai ta ramawa Daddyn Shuraim wannan cin kashin kajin da akeyi masa"

Kun san Allah ce mata nayi, "Anty Narjeesh miye naki a ciki kedai mu ɗauki Shuraim shida yake namu kawai ".

Anty Humaira kin san yan da ta taso mani kamar ta dakeni ta ce, "ke mahaukaciyar ina ce halan, uban ya'yan nawa zaki ce na barshi a cikin wannan halin tare da wannan mummunar mata? To wallahi ni bazan iya barin shi tare da wata ba, sai dai ke ki ɗauki Shuraim ɗin ku tafi ni kubar ni na kwaci "yan cina ehe! ".

A da ido kawai nake bin ta, na zama wata wawuya dani, amman idan suka haɗu sai haushin wannan lokacin ya taso mata, sai ta murje idon ta kamar ba ita ba".

Dariya suka saka, "Yaya ta ce, ai kuwa zamu riƙa takura mata da lurad da ita kada taje tayi saki na dafe "

Amrah tace, "shima fa halin su ɗaya wallahi idan suna a kusa da juna faɗa kawai ke shiga tsakanin su, amman idan bata a kusa himm..! "

Nusaiba ta ce, nice zan baki wannan labarin domin yayi maya ta kai goma neman ta, har sai da ya riƙa zuwa shida Salma da Muhseen, sune suka tambayi inda taje, mukace, bamu sani, ba cike da masifa ya ce, "da Auren nawa zata tafi wani gurin ba tare da izini ba? "

Nan dai sukayi ta bada labarin irin halin, su Inno da Yaya sukayi wani shiri akan mu.

Ni kuwa ina kaiwa zaure na haɗu da shi, shima cikin fushi ya janyo ni, jikin sa, ya riƙe ina ta son na kwace jiki na na kasa, yace, "uban waye ne uban sa a garin nan da zai ce zai rabani da ɗana! ? "

Na ce, to malam sake ni mana, nama ɗauka gamo ne nayi, ashe akan wan can shegen mutanen ne"

Ƙin sakin nawa ya yi, "na ce nifa ban ma taɓa ganin saba sai yaran sa, Amrah da Nusaiba ne suka taɓa ganin sa, sai Mariya, ko farmakin da suka kawo muna a cikin dare bamu gan su ba, dan maƙota sune suka ce ce mu".

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "to kuwa zai gamu da gamon sa, tun da ya firgita mani rayuwar iyalina, sai na ɗauki fansa, muje cikin mota muyi magana saura kiyi mani musu, ni kuwa na baki mamaki dan wallahi har cikin gidan zan shiga na ɗauko ki a jikina ".

Kallon sa nayi nace, "ai dama nasan zaka iya aikata hakan muje ni kada ka kunya tani dan ni nasan darajar mutane ".

Sakina yayi ya riƙe hannu na, muka jera muka fita, kallon mu mutane kawai suke, abokan Baban mu ne suka aika kiran sa, ya fito yayi ta gaisawa da mutane, tafiya mukayi, har jikin motar daya zo da ita muka shiga nida shi su Jafar kuwa a can cikin majalisar samari muka hango su.

Shiru mukayi nida shi babu wanda ya ce, uffan har tsayin wani lokacin motocin su na can gefe sun faka.

Wata mota ce gob3 ta iso ƙofar gidan mu a tsiyace, duk taci uban ta, ta bubbuge ta tsofe, sai mashin kusan bakwai, duk mutanen dake bisa moshin ɗin da na cikin motar ɗauke suke da makamai, sauka sukayi, suka fara ihu, na cikin motar ne suka fito suna busa taba, sigari.

Zaro ido waje nayi ina kallon ikon Allah, shi kuwa murmushi yakeyi wayar sa kawai yake shafawa, cike da tsoro na ce, "Daddyn Shuraim wannan mutanen fa irin sune suka tashi kashe mu, harda su Umma ".

Kallo na ya yi yace "to ke kuma keda kika je kikayo rigima kika ɗauko Shuraim yau kece da tsoro? Ki fita kawai ki zama jaruma dan sun sami labarin zuwan ki, kin ga yan zun ma sun zo ɗaukar Shuraim ne".

Dariya nayi nace, "to su ɗauke sa mana, ai yanzun bani ce kawai abun zai shafa ba, dan gasu Yaya Jafar da Yaya Aliyu da Muhseen can idon su saboda harara kamar su fito waje, kai ni kallo ne kawai nawa".

Shima kallon su Yaya Aliyu yakeyi, ai kuwa bai san lokacin da ya kama dariyar su, ba.

Ƙofar gidan mu suka suka yada zango, Yaya Auwal ne dasu Humaira Hindu da Amrah da Nusaiba su Mariya suka fito suna ƙare masu kallo, wani mummunan mutum ne ya tsaya a gaban su,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login