Showing 9001 words to 12000 words out of 23161 words
suka zo har gidanmu sukaci mana zarafi bamuji bamu gani ba!"Tun farkon haduwarka da Salma na sanarda kai kafi karfin ta mu talakawa ne, ba mutane muke ba acikin duniyar masu arziki!"Dan haka ina maka fatan alheri kuma ina code maka abisa son diyata da kakeyi da zuciya daya batare da tsangwama da dubin *BAK'AR* *AK'IDA* irin ta ku masu hali ba!"Nasan kana da mutunci kuma ina ganin mutuncika da kimarka salman to ka rikesu dan Allah daga yau kar ka qara neman Salma!"Nagode ka iya tafiya."Baba yace wa salman da tuni duniyar sama ke masa yawo maganar Baba ta yamutsa masa kwakwalwa!"
"Ganin Baba da gaske gida zai wuce abinsa ne yasa yayi saurin dawo hankalinsa ya durgusa kasa ya ce"Dan Allah Baba kayi hakuri kada ka hukunta ni akan abinda bani na aikata wallahi ni kaina na tsani *BAK'AR AK'IDA* nan tasu da batada asali da amfani na yarda samu da rashi duk na Allah ne kuma da talaka da mai kudi duk daya ne babu banbamci domin duk bayi ne na Allah!"Baba karku rabani da salma ina sonta tana sona kawai akan *BAK'AR AK'IDA*"Baba nasan Minal ce tazo tayi muku rashin mutunci kuma zan dauki mataki Dan Allah kuyi hakuri!"Salman ya ce yana zubda hawaye!."
"Tausayinsa ya kama Baba tallafosa yayi ya tashi tsaye yace babu komai Salman mun yafe maka bakai mana laifi ba!"Kuma munyi hakuri zan fadawa Baraka da Salma nasan zasu hakura Allah shi maka Albarkah!"
"Amin Baba nagode."
"Babu komai ni zan shiga daga ciki."
"Baba dan Allah kaimin alfarmar inga salma in bata hakuri!"
"Ba yanzu ba!Salman nasan salma bazata Saurareka ba!dan nasan cewa ta tsani ganin Bacin ranmu!"Ga shi yau agabanta anci mutuncin mu kuma na hanata daukar duk wani mataki da taso dauka saboda gudun hayaniya!"Amma ka tafi zan fada mata!"
"To Baba ina gaida su zan dawo idan an kwana biyu ta huce nafiso nabata hakuri da kaina!"
"To Salman Baba yace,tare da murmushi saboda yagano lagon shi, Da kallon tausayi ya bi Salman da yayi wani zuruzuru kamar wanda ya kwanta ciwo"
"Sallama sukayi Baba ya Shiga gida Salman ko ya wuce Direct gidansu Aunty Zainab ya wuce saboda ya hasala da minal amma yasan ta ina zaiyi maganin iskancinta da rashin mutunci!"Shi zata rainawa hankali!"
"Hajiya Maigado ce zaune a bedrum dinta gefenta qawarta ce Hajiya Raliya zaune agefen gadon da aka cika da laces,super,materials da sauran kayan da zasu bukata na bukin saboda shiri ake yiwa Auren na musamman."
"Hajiya Raliya cikin kulawa ta dubi qawarta tace,Yanzu Hajiya Bilki kina nufin duk tulin kayan nan masu tsadar gaske kin saye su kenan?"
"Dariya tayi tace,sosai qawata wannan ma soman tabi ne sai munje Dubai."Karfa kin manta aure ne yan dangi yn gata wadanda suka gaji arziki kinga dole ne mu nunawa duniya naira ta zaunu."Har tana kuka da hawayenta!"
"Lalle kice min zamu sha mamaki, kuma mu kan mu muje mukara shiri kan wanda mukeyi, saboda na lura auren nan na fito na fito ne,"To kenan dole ne mu kure adaka,ka da ayake mu afimu wanka mai cizo zan sauya wani sabon shiri"Hajiya Raliya tace cikin dariya da raha."
"Murmushi wanda yafi kuka!Ciwo Hajiya mai gado tayi tace Bari Hajiya Raliya abu daya ne ke ci min tuwo a kwarya wanda idan na tuna sai naji farincikinah ya gushe!"Shi ne yaron nan da har yanzu yaqi yarda ya so minal!"A kan tilas ne zaiyi auren dan kawai na tashi tsaye ne akansa!"
"B'ata fuska Hajiya Raliya tayi cikin mamaki ta ce wai shin kina nufin Har yanzu Salman bai ce yana son minal ba!?Kuma a hakan zaki xuba ido ya aureta!?To meye ribarki dan kinyiwa danki Auren dole!?Ina iliminki da tunaninki ina wayewarki Hajiya mai gado!?"Salman danki ne mai miki biyayya idan har kin kayi masa hakan baki masa adalci ba d'a ne abin alfahari ga kowa!"
"Kiyi hakuri qawata nasan cewa Zainab qanwarki ce kuma jininki bazan iya bata alakar Ku ba kuma bada wata manufa zan fadi maganar nan ba sai domin ita ce gaskiya!"
"Shakka banayi Zainab bazata yiwa yarta minal auren dole ba!"matukar salman ke son yartah, batason sa." To Da tuni an wuce warin,"Kisani yanzu farinciki ne take nemawa minal." kuma tana sane da cewa shi fa bayaso!"Aini aganina dukkansu 'ya'yanta ne, da babu son kai aciki da ta hanaki tilastawa Salman dan ganin an masa adalci a rayuwa!"
"Shawarata ki so abinda danki ke so, ki kuma taya shi neman farin cikinsa!"Meye aibun ita wadda kinka taba fada min yana so kwanakin baya?"
"Hajiya mai gado da jikinta yayi likis tace Batada aibu face talauci da yayi musu katutu a rayuwa!"Gaba da bayansu talakawa ne kinga idan nabari ya aurota sai aitayi damu a dangi ya zama na farko da ya fara auro bare (Talaka)Acikin zuri'armu kuma kinsan irin su ance abin biyarsu yakeyi har gidan aure!"Shi nike gujewa Salman kada ya auro mai farar kafa asamu abin yayatamu a dangi."👸🏻👸🏻
BAKAR AKIDA
©TASKAR NABEELA DIKKO
® PEN WRITERS ASSOCIATION
Page 41/45
" *Wannan page na ku ne Dangi na Dikkon Kebbi and Madawakin Kebbi Family's Allah ya sanyawa zuriya ALBARKA Ameen.* "
_"3rd February 2019,Wannan ranar ta kasance daya daga cikin ranakun alfahari da bazan manta da ita ba a rayuwata Alhmdllh acikin matakai rayuwa na samu nasarar d'ane mataki na biyu Fatana Allah ya tabbatar mana da alheransa Amin Nagode 'yan uwa da Abokan arziki Allah ya sanyawa zuriya Albarka yabar mu tare Amin summa Ameen."_ 🤝🏻
________________________________
"Amma a gaskiya Hajiya Mai gado kin bani mamaki yanzu akan wannan *BAK'AR AK'IDA* ne da batada asali bare tushe maras kan gado kike son takurawa rayuwar Salman."A wane hadisi ko aya aka hana mai arziki auren talaka!Tabbas talauci bai da dadi domin Annabi(SAW) ya ce mu nemi tsari daga talauci!" Amma kuma ba'a hana auren talaka ba!"Domin mutum ne kamar kowa!"Samu da rashi duk na Allah ne!"Ki gyara imanin ki Hajiya Bilkisu ki gane cewa Ko ke baki wuce komawa talakar ba jarrabawa ce ta ubangiji!"Ki bar salman ya auri wacce yake so."Saboda shi talauci ba'a gadonsa kuma arziki na Allah ne!"Inji Hajiya Raliya cikin yanayin damuwa."
"To Hajiya naji zancen ki amma yanzu ta ina ma zan fara!"Yanzu ya zanyi da dangina da Minal!."Hajiya mai gado tace fuskarta dauke da danasani!"
"Babu abinda za kiyi sai dai kiyi kokarin toshe kunnuwan ki daga sauraren zantukan mutane!"Sannan auren minal da salman yana nan daram matukar ba ita tace bazata iya zama da kishiya ba!"Domin kokari za'ayi a hade auren har na salma kinga sai ayi mai gaba daya ko ya kika gani?"
"Nikam ina tsoron lamarin nan yadda zai zo!"Ina jin kunyar yarinyar nan salma da iyayenta saboda har gidansu naje ba kalar masifar da banyi musu ba!"Akan su fita harkar d'ana yanzu kuma inje amatsayin mai nema masa aure kinsan na tsani awulaqanta musamman a inda nafi karfi!"
"Kada ki damu zamuje mu basu hakuri kuma nasan cewa suna da ilimi bazasu wulakanta mu ba!Kawai ki sa muna rana mutafi kuma kar ki sanarda kowa har salman din sai munga yadda lamarin zai kasance"Hajiya Raliya ta ce tare da haramar komawa gidanta."
"Sallama sukayi da Hajiya Mai gado inda ta qara godewa qawarta ta bisa ga ankarar da ita da tayi!"A kan lamarin Salman."
"Da sallama Dr.Salman ya shiga falon Aunty Zainab zaune ya sameta ya gaidata cikin ladabi tare da tambayar minal."
"Amsawa Aunty zainab tayi cikin kulawa sannan tace to sun fita ita da qawarta minal tun dazu basu dawo ba."
"Dr.Salman ya ce,okay Aunty zainab ba damuwa daman nazo ne dan ta bani list din abinda kawayenta ke bukata na dangane bukin nan ne kuma in dauketa saboda daman hajiya ta ce"In daukota."
"To Salman idan tazo ni zan kawo maku minal da kai na Aunty zainab tace fuskarta dauke da murmushin jin dadi."
"Yayi Aunty zainab ni zan wuce dan Allah ayi hakuri da duk abinda ya faru a baya Aunty!"Dr salman ya fada a yanayin damuwa!"
"Bakomai yarona duk komai ya wuce Allah ya yafe mana ka gaishe min da yaya mai gado."
"Zan gaya mata in shaa Allah Aunty sai na dawo."Salman ya ce"Ya wuce a zuciyar sa ko tausayin Aunty da Minal ma yakeyi!"Allah dai yasa ya samu nasarar abinda ya shirya da hakan yabar gidan yana tunanin mafita."
"Assakamu Alaikum."
"Amin malam sannu da dawowa."In ji Inna Baraka tare da shinfida masa tabarma kusa ga kofar dakin nasa."Suka zauna dukkan su."
"Yawwa Baraka ya gida.?"
"Lafiya lau malam ka dawo ka sameni ina ta masifa da yaron nan salmanu yanzu nan ya aiko yaro aimasa sallama da salma nace bazata ba!"Da yasan rashin kunyar da akai mana yau akanshi da bai zo ba wallahi!"
"Baraka kenan!"Ai yanzun nan muka rabu da shi........"
"Salma da ke kwance a uwar daki ta kashe kunnenta ne ta zabura ta tashi saboda taji me Baba zai ce cikin faduwar da fargaba ta tashi." kwanon fura da abinci ta Baba ta dauka ta fito waje ta ajeye masa tare da gaida shi."Tana kokarin komawa daki Baba yace "Salma dakata!"Magana zamuyi!"
"To Baba salma tace tare da zaunawa akasa tana fuskantar su idanuwata sunyi jajur saboda kuka!"Ta dukar da kanta a kasa tana sauraren jawabin Baba."
"Yanzun nan muka rabu da salman Wanda zuwa yayi kawai domin ya gaishe ya ganki kamar yadda ya saba!"Sai kuma ya sameni awaje nayi masa bayanin duk abinda ya faru dazu amma fa mai faduwa da sauraruwa dan barna batada dadi!"Kuma naga rayuwarsa ta baci da jin labarin nan ba yadda baiso ya shigo ya Baku hakuri ba!"Dai dai ni na hana shi!"Saboda nasan baku huce ba!"Ina son kuyi hakurri Ku yafe masa da zuciya daya!"Saboda yaron yana kirki kuma baida labarin sun zo dan haka abin ya wuce Allah ya sauwaqa ki shirya gobe ki wuce Felende Allah yayi miki wani zabin nagari kinji koh."
"Kanta ta daga ahankali alamar"Eh"
"Tace Inna,Baba dan Allah kuyi hakuri.....Dakata salma munyi hakuri babu komai bakida laifi agurin mu har shi salman din " *BAK'AR AK'IDA* ce irin tasu ta masu arziki!"Tashi je ki abinki Allah yayi maki ALBARKA."
"Amin Baba Nagode."Salma ta ce tare da shigewa dakin tana jin dadi saboda ba shakka haqar ta tayi kusa cimma ruwa.!"Minal zata dandana kodar ta!"Da yardar Allah."
"Inna Baraka ta dubi Malam cikin jin takaici "ta ce Malam gaskiya naso ace ka nunawa yaron nan bakaji dadin hakan ba!"Ai cin mutunci da zarafi ne!"
"Ai shi ba mahaukaci bane Baraka zai fahimta mana kuma bacin ran sa da ya nuna yasa nagane baiji dadi ba shi kan shi!"Abar maganar ta wuce Allah ya yafe mana!"
"Ameen."Malam,Inna Baraka tace tare da sauke ajiyar zuciya."Malam ko abincinsa ya fara ci."Suka cigaba da firar su ta duniya kamar komai bai faru ba."
"Minal da Nidal ne suka kara so part din mummy cikin dariya da shewa."
"Mummy ta ce kai amma kunyi sabani da yayanku yanzu ya fita."
"Haba Mummy bagan shi ba me yazo yi ne?"
"Wurin ki yazo mana."Na ce kun fita run dazu Baku dawo ba!"
"Ayyah mummy ai mun dawo da dadewa abinci muka tsaya ci apart dina kuma ina dawowa nabawa garbati motana ya kai agyara min problem take bani kwana biyu!"
"Ai bansan kuna ciki ba!"Da nace masa kuna nan saboda ba motar ki."Abinda yafi ma a canjawa miki mota yafi gaskiya!"
"Nidal ta ce mummy yau munyi abinda ranmu ke so gidan su matsiyaciyar can Salma mukaje muka keta musu rigar mutunci munja musu kunnuwa kuma barazanar mu ta shige su sosai."
"Aunty Zainab ta ce haba dai yan albarka wallahi kun kyauta min da bakuje ba da ni zanje in musu kashedi na karshe!"
"Minal ta ce haba Momy aini zanyi maganin maitar su!"Mutane kamar almajirai!"Matsiyata da su!"
"Nidal da minal cigaba sukayi da ba mummy labari irin rashin mutuncin da sukayi agidan su Salma."
."Mummy ko sai dadi takeji tare da yaba musu dan sun burgeta kuma hakan ne daidai da talaka mai karambani acewarta."
( _Ya kamata iyaye mu lura mu kula da tarbiyyar yaran mu idan sunyi ba daidai ba atsawatar musu kadamu zuba mana su ido sunayin abinda rayuwar su ke so Hattara iyaye!"👂🏼)
BAKAR AKIDA
©TASKAR NABEELA DIKKO
®PEN WRITERS ASSOCIATION
Page 46/50
*Meyetti Kwirei Allah Suddo'on Asiiri Duniyaro i lahira Ameen* 😍😍😍
"Yau ta kama Assabar saura mako daya auren Dr salman da Minal tuni aka fara shiri haiqan na budurin auren a dayan bangaren kuwa Salma makon ta daya a qauyen su Innarta Felende."
"Tuni soyayyarta da Dr.salman ta dawo sabuwa dan suna waya sosai kuma ya bata hakuri dangane da abinda su minal suka aikata musu!"Da hakan ta hakura kuma dangin innarta kowa ya yaba da salman irin yadda rayuwar shi ta ke kmr ba mai arziki ba saboda yana zuwa wurin salma din amma asace batare da sanin Hajiyarsa ba hakan ita ma salma inna da baba sam basu sani ba."
"A hanyar su ta zuwan gidan ne qawarta ke mata jawabi da jan hankalinta tare da ba ta muhimman shawarwari masu amfani har su ka isa gidan basuyi mamaki ba saboda sun san yadda gidan ya ke."Fita sukayi a mota su shiga cikin gidan."
"Assalamu Alaikum Salamu Alaikum matar ta fada akaro na biyu yayin da dayan ta fara daure fuska alamar rashin jin dadi!"An ki karba sallamar su!"Matar qara sallama tayi...."
"Da sauri wata mata ta fito daga bayan gida ta ce"Amin wa alaikumus salam maraba da Ku!"Tabarma ta shinfida musu ku zauna ku hakuri ina kewayawa kuna shigowa!"Kamar ance ta dago kanta sukayi ido hudu da matar da in ba mantawa tayi ba ita ce wacce taci mutuncin su akan danta!"To me yakawo su gidanta?ko sun zo su kara cin zarafinta ne?A gaskiya yau kam bazata sabo ba!?Ta fada azuciyarta a fili ko ta ce Hajiya ina fatan lafiya. Saboda idan ba gizo idanuwa keyi ba naga kamar ke ce mahaifiyar salman nace dai lafiya ba wani abin magana diyatah ta koma jawo min ba!"Inna Baraka ta ce ma Hajiya Mai gado da tuni kunya ta fara rufeta ganin yadda inna har wurin zama ta ba su."
"Murmushi Hajiya Raliya tayi kana tace ba abinda ya faru Maman salma mun zo ne mu baku hakuri Dan Allah ayi hakuri komai ya wuce shi ne Maman salman din tazo da kanta ta ba Ku hakuri."
Inna Baraka ta ce babu komai amma Hajiya da ciwo kam kananan yara suzou har gida su ci mutuncin mu abin takaici har mahaifin yarinyar nan yaran nan basu ragawa ba!"Ni shi ne abinda ya bani haushi..."
"Daga Hajiya mai gado har Raliya duban Inna sukayi da mamaki dan basu fahimce ta ba!"
"Hajiya mai gado ta ce kuyi hakuri amma suwa ne suka zo nan gidan bayan ni!?"
''Inna ta ce"Ko minal sunanta da kawarta marar kunya ba abinda basu ce mana ba! A gidan nan duk kowa na gidan nan na tsaye agabansu kuma a kan salman ne wai ita ce wadda zai aura salma ta fita harkar shi ba dai barazanar da basuyi mana ba mu kuma ba ruwanmu mun barwa Allah lamurran mu ba dai mutum ba!"
"Subhannallah! Hajiya Raliya ta ce tare da kallon Hajiya mai gado ta ma rasa ta ina ne zata fara!"
"Ta ce Dan Allah Maman Salma ayi hakuri abawa Malam hakuri!" kin san dan yau!"Wallahi mu bamu ma san sun zo ba kuma za ai musu fada ai an zama daya mu da ku komai ya wuce duk sharrin shaidan ne.....!"
"A'ah Hajiya mu da ku ba guda ba!"Ina talaka bawan Allah, ina mai kudi!"Kinga akwai bambanci kuma hanyar jirgi daban da ta mota !" Sannan *BAK'AR AK'IDA* irin ta ku ta manyan mutane ita kesa kuna ganin sam talaka bai dace da Ku ba! Ku nemi wulakanta shi!"Dan haka komai ya wuce Allah yabamu hakuri da juna ya hada kowa da rabon sa!"Salma zatayi aure amma talaka dan uwanta shi ma salman din ya zauna da Yar uwarsa jininsa yafi sauki kunga kwarya tabi kwarya kamar yadda *BAK'AR AK'IDAR* ku ta tanada!"Allah yayi mana mafita ta alheri."
"Amin Hajiya Raliya ta ce yayinda Hajiya mai gado jiki yayi sanyi, ko ba komai Inna ta saka musu magana!"
"Daman abinda muka zo yi shi ne ban hakuri da kuma Neman alfarma agurin Ku Maman Salma, Ga dai qawata nan Hajiya Bilkisu tayi nadama ta gane zabin danta shi ne farin cikinsa har ita kanta,To shi ne muka zo nemawa salman auren yarku salma kuma ashirye muke idan kun yarda a hade da na yar uwarsa minal ayi mai gabadaya."Hajiya Raliya tace cikin tausasa murya."
"Inna ta ce Dan Allah Ku rufa mana asiri ina d'an ku mai arziki ina salma yar matsiyata!"Ai ko gari ya watse ba'a kwashe daidai ba!" kuma ni agaskiya bazan iya hada 'yahtah da minal ba saboda ba rayuwar su daya ba,"bata da fitina da son fada kuma bana son a wulaqanta min yarinya akan wata *BAK'AR AK'IDA!."*
"Ai kowacce acikinsu da gidan ta daban kuma hakuri dai za ayi adaina tuna baya,Salman da Salma hadin Allah ne ,"kar mu cutar da yaran mu tunda suna son junan su! Dama can rashin sanin illar wannan *BAK'AR AK'IDAR* ne ayanzu mun gane gaskiya *BAK'AR AK'IDA* nan ta auren bani gishiri in baka manja Bakomai bace kuma batada wani amfani bare nasaba!"Kuma Akida ce ta wadanda suka jahilci meye gishirin zaman duniya!"Da Allah a qara hakuri Maman salma yanzu an zama daya komai ya wuce adaina tuna baya"In ji Hajiya Raliya."
"To ni ba zance komai ba sai dai idan Malam yazo zamuyi magana Inna ta ce atakaice."
"To mun gode ina Yar tamu salma bamu ganta ba har zamu koma."
"Dan Allah Ku tsaya ko ruwa baku sha ba fa,salma tayi tafiya taje garin mu sada zumunci."
"A'ah ba komai mun gode in Shaa Allah gobe zan dawo in ji kome kun ka yanke shawara akai."In ji Hajiya Raliya.
"Mun gode Hajiya mai gado tace,suka wuce yayinda inna tayi musu rakiya har zaure ta sannan ta koma daga ciki."
"Dr Salman da abokinsa
Dr.Jameel tsaye a bakin office dinsu tattaunawa sukeyi akan zancen auren sa anan yake fadawa Dr.jameel kudurinsa na auren salma a boye batare da Hajiya tasani ba saboda shi ita ya ke so ba minal ba."Kuma tuni ya gama shirin