Showing 12001 words to 15000 words out of 23161 words
auren nasa abisa yarda da amincewar dangin babansa kuma ya samu nasarar saye kawun salma baban karime domin shi ne waliyyin salma ya ce zai tsaya masa ayi auren domun salma 'yarsa ce!" agefen dangin inna ma tuni suka yaba da hankalina kuma sunce sun bani salma ayi komai a felende na bukin, dAga baya a sanarwa iyayen mu su saka albarka tunda su *BAK'AR AK'IDA* irin tasu ta hana su fahimci halalcin auren mu da salma sai dai dinbim haramci da suke gani!"Dan haka kaji yadda muka shirya abin mu ni da salma kuma zanyi mata komai tun kan sutura har kayan daki."
"Ina Neman alfarmar ka taimaka min ka rufe min asirin nan kamar yadda muka saba!"Ka taimaka min domin samun cikar burina Salma!"Ka kuma tayamu da addu ah domin samun Nasara."In ji Salman da ya kare maganar yana kalon Dr jameel."
"Numfashi ya saki mai nauyi sannan yace tabbas wannan shi ake kira da gadar zare sai mai rabo zai fita "Ka ga laifin nan abokina har ni sai ya shafa bazan taba fita ba!"Shiyasa nikejin tsoro bana son rayuwar Hajiya ta baci akan mu!" Ba abinda zance Salman sai dai Allah yasa mudace yasa shi ne alheri saboda ina jin tsoron sabawa umurnin iyaye!"In ji Dr.Jameel."Fuskarsa dauke da damuwa!"
"Ba abinda zai faru Jameel,kawai ka tayani addu'a dan babu fargaba!"A zuciyata hakan na nuna min zanyi Nasara!"kasan dukkan mu daga ni har salma iyayen mu na sonmu bazasu iya fushi damu na tsawon lokaci ba, zasu yafe mana."
"Hmnnnn daga baya kenan."Inji jameel.
"Da hakan dai suka Wuce zuwa parking place na hospital din motocin su suka shiga suka wuce kowa da abin da yake tunani a ran sa!"
BAKAR AKIDA!
👸
©TASKAR NABEELA DIKKO
®PEN WRITERS ASSOCIATION
Page 51/60
*"THE VIRTUE OF REMEMBERING ALLAH*:" _Allah the all mighty has said:"Therefore remember me,I will remember you,Be grateful to me and never show me Ingratitude."Al baqara 2:152."_
_And He said:"O you who believe, remember Allah with much remembrance. Al-ahzab 33:41."_
*Subhanallahi wabi hamdihi*
*Alhamdulillahi Kaseeran*
*Allahu Akbar kabeeran*
________________________________
"Ilham da Hajiya mai gado zaune a cikin katafaren red and black din falon gidan nasu."A lokacin ne Hajiya ke sanarda Ilham duk abinda ke faruwa."
"Ilham ta ce"A gaskiya nima tuni na gane gaskiya na fara goyon bayan Yaya salman yanzu hakan ina zumunci da Yaya salma."Dan kuwa muna waya kuma gaskiya tana da kirki nima na goyi bayan abarshi ya auri zabinsa sai ya hada da naki zabin, kuma ina da tabbacin zai musu adalci!"Idan ma ansamu matsala Yaya minal ce kinsanta sarai ba tasan kimar mutane ba!"Kuma nayi faricikin amincewarki Ummana Allah ya qara maki lafiya."Ilham ta ce fuskarta a sake."
"Hajiya ta numfasa domin duk zancen autar ta gaskiya ne!"Sai yanzu ta gane rayuwar salman da minal ba daya ba!"Sai dai kaddara ta riga fata!"Ta ce "Ba komai Ilhaam Allah yasa hakan ne alheri!"
"Ameen Umma,yanzu kin sanarda Aunty Zainab din da minal?"Sun san da auren?"
"Ban fada musu ba!"Ni ina jin abin ba dadi ne!"Kishiya ba dadi!"amma kuma rayuwar salman nike dubi yana bani tausayi!"Sannan iyayen salma har yanzun ba su sanarda Mu
Ko sun amince sun yarda da auren duk da nasan Su na da fahimta!"
"Umma akwai damuwa a tattare da shi Dan fa tun kwanaki Baby (Dr.jameel)ke sanar min Yaya salman ya kamu da matsanacin ciwon zuciya!" yanzu hakan an daura shi akan magani duk akan ciwon son salma!"Da auren dole da ake son yi masa!"Ya ce kada afada miki ne, ko ni Yaya baisan cewa jameel ya sanarda ni ba!"Dan haka umma hakuri zamuyi dukkan mu, tun da kowa ba wani so yakeyi ba, minal dai jinin mu ce dole mu so ta fiye da salma, kawai a aura masa burin ran sa kowa yasamu kwanciyar hankali shi yafi dacewa!"Inji ilham."
"Hajiya mai gado ta ce ikon Allah yanzu shi baida lafiya ya boye min, abinda bai taba faruwa ba!"Duk kusancina da yarana ashe da kadan na rasa shi batare da nasan dalili ba sai dai inji labari a gari !"
"Wallahi Umma Allah kadai ya tsare akan wata can *BAK'AR AK'IDA* ta banza da ba amfani bare tushe!"Da mun rasa magajin Abbana Yaya salman shi ne garkuwan mu kiyi hakuri Umma ya auri zabinsa ni kaina banaso hakuri kawai zamuyi dan samun farincikinsa.!
"Ai bari kedai auta yanzu kam na gane gaskiya ashe talaka mutum ne,Mai hakuri da juriya,Duba fa duk rashin mutunci da cin zarafin da nayi musu akan salman, ashe minal da Nidal sunje sunyi musu ubansa har citta!"Amma matar nan bata wulaqanta Mu ba!"Sai yanzu na fahimci girman kai!Daukar kai! Da wulaqanci da fariya na ga wad'an su masu kudi kuma masu *BAK'AR AK'IDA* irin ta mu!"Allah ya yafe mana."
"Ameen umma gaskiya bamu kyauta musu ba!"Da masu saurin fushi ne bama zasu saurare ku ba!"Yanzu Ni zanje na karbo dinkin nan namu na dinner idan telan ya qare Umma."
"Kada kiyi yamma Auta!"
"Okay,Umma bazan jima ba!"
"Adawo lafiya Allah ya tsare min ke."Hajiya ta ce tare da shigewa bedrum."
"Malam a duba mana kuma a yafe mana mun san munyi ba daidai ba!" Amma ayi hakuri abar yaran nan su samu kwanciyar hankali."Hajiya Raliya ta ce cikin sanyin murya."
"Inna Baraka ta ce Hajiya da kin hakura domin shi malam idan ya hau yana da wuyar saukowa!"Saboda wallahi tun ranar da kuka zo na yi ta bashi baki amma fuuur!"Ya ce bazata sab'u ba!"Dan ya ce Yar sa bazata auri salman ana mata wulaqanci da cin fuska ba!"Kamar
Yadda kinkaji ya fada miki da bakinsa!"Dan haka maganin kar ayi kada afara!"
"Malam da ke gefen zaune yana jan carbin sa kallon Baraka da haj raliya kawai yakeyi domin shi ya qare magana idan sun gama cin kasuwar su zasu tashi a karshe!"Daga nan tashi yayi yama Haj Raliya sallama da ban hakuri kada taga kamar bai raga mata ba!"Ya wuce abinsa ya bar gidan zuwa majalisinsu na dattiban unguwa.'
"Itama sallama tayi da inna Baraka ta bar gidan tare da shaida mata!"Za dawo jibi kuma zataje felende abisa kwatancen da inna tayi mata domin dauko salma aji ta bakinta idan ta amince dole ne Baba ya barta ta auri shi salman din!"
"Inna Baraka tuni ta yarda da shawarar Hajiya Raliya domin tana da tabbas idan har ya lura salma har yanzun tana son salman zaiyi hakuri!"Duk da ta fahimci kamar salma ta bar salman din har abada ne!"
"Bayan fitar Hajiya Raliya daga gidan inna cigaba tayi da surfenta."
"Kawu Bala da matarsa Inna larai sai facaka sukeyi da kudi su karime har sababbin dinkuna akayi mata sai kuri ake acikin gida!"
"Larai ta ce shin malam har yau kudin da Hajiya melal ta bakane basu kare ba naga namu da ka bamu sun kare da dadewa?"
"Haba larai ana babbakar kura wa zai jiyo kaurin zomo."Ai salman ne ke bani kudi kuma yace min gidan sumunti zai gina min idan har na bashi auren salma."
"Hararar takaici ta watsawa kawu Bala ta ce lalle malam zuciyarka ba ta kishin kanka ba ce ta yaya ga karime nan gida batada mai kudi ko daya a ma nemanta!"Muna nema bamu samu ba!"Zaka bari salma ta auri salman mai kudi!"Kuma kana gani tun bata aure shi babu abinda baya yimasu har mu kan mu!"Meyasa baka watse maganar auren ba!"Ko ka mayarda zancen kan karime ni wallahi na tsani tauraruwar salma domin idan ta hasko na fahimci ta karime disashewa takeyi mtsssssww!Yarinya kamar aljana!"Inna larai ta karashe maganar cikin takaici!"
"Hahaha Larai ta malam Bala ikon Allah!"Ke meyasa tsabar son kanki rufe miki ido yakeyi ki kasa bude su ki gane waye gabanki nine naki bala fa larai kamar kin mantani da halina!"
"Ai tun farko da yazo min da zancen salma ce masa nayi ya hakura da salma tunda yaya Habu bayaso ga karime nan zan bashi amma ya nuna min salma ya ke idan bai samu ba zai hakura da su dukan su!"Kinga ko gwara na amshi kudi na kada nayi asara na aura masa ita!"Nasan bazataji dadin zama da matarsa,uwarsa,da danginsa ba,Wuya da tsangwama zata hanata zama acikin su!"Dole ta baro gidan idan taji babu dadi ko!?"
"Haba malan to ai mijinta na sonta kuma zai bata kudi kaga ko zamu sha kallo wurin su baraka!"
"Meye amfanin kudi babu kwanciyar hankali larai!?Shi salman kullum zaune zaiyi gida yana kulawa da ita ne!?Ai dole ya fita aiki kedai ki yarda bazata ji dadin ba kuma kinsani komai ta ba su baraka da kason mu Dan Yaya habu zai bani nawa!"Ita wannan yarinyar karime nagane kashin tsiya ne da ita tayo mugun gado wallahi!"
"Wurin ku kenan ta gado shi!?"Saboda nidai Allah yayi min arzikin ma nema masu kudi yan kasuwa karyarka tasa na aure ka ashe kaima duk jaar kanwar ce!"Wallahi Bala ka cuceni!"
"Dakata larai rashin kunyarki ya tashi kinka dai cuci kanki da kwadayinki na banza kashin tsiya kuma naki ne karime ta gado!" dan ga salma nan tabiyo kashin arzikina tasamu mai kudi!"Aini da zarar nasamu gidan nan mai kashin arziki zan auro ku ruwa na canja kala!"
"Mtwssss!!!Ai kin banza ai sai ka gina naka da arzikin Kanka ba da na wani ba!*Banzah!"Mai matacciyar zuciya!"Kuma gidanda za a ginawa Yaya Habu sai yafi naka komai saboda shi ada surukin ba kai ba!"Larai ta ce cikin hushi!"
.."Babu komai aure kuma sai na karo matsiyaciya!"Bala ya ce ya wuce yabar gidan!"
"Kai ne matsiyacin ba niba!"Dan bakinciki da hassada!"Da ko dan uwansa bai bari ba!" Ai zaka dawo wallahi!zaka sameni!"Mtwsss banda kaddarar aure me zanyi da kai ma karyaci!"Larai tace tare da zama tsakar gidan tana neman wanda zai tsakanota ta sauke masa Kwadon cin mutunci kamar yadda ta saba ta cika faam sai batsewa takeyi!"
BAKAR AKIDA!?👸🏻
©TASKAR NABEELA DIKKO
®PEN WRITERS ASSOCIATION_
~Page 66/70~
" _Wannan Shafin naki ne Qanwata Qawata Aminiyata 'Yar uwa rabin jiki my twiny *NANA AYSHA AMEEN DIKKO Ina* yinki Over."_ 😍
________________________________
"A zaune ta ke gefen katafaren bed din ta da misalin 9:pm na dare, cikin shigar bacci waya ce a hannunta tana magana cewa tayi..."Kai!Haba?Ki ce dai kin sha fama da Baban na salma!"Wallahi ni kaina sai addu'a nike tayi Allah ya sa ya amince!"Amma yanzu
"Alhamdulillah a gaskiya naji dadin zancen nan Qawata," Nagode sosai da kokarin ki wallahi kin fidda dani daga cikin duhun jahilcin *BAK'AR AK'IDA*." Allah ya saka maki da alheri Hajiya Raliya,Kuma idan Salman ya dawo zan sanarda shi komai!"
"Gaskiya sun fimu gaskiya saboda shi baban salma din da so yayi kada ayi auren domin yana ganin fa abinda akai musu! Akan talauci!"Amma Kada ki damu Hajiya Bilkis yanzu ya zama tarihi,"Sannan ai yiwa kai ne salman D'ana ne Kuma ki tuna aminchi ba wasa ba."Tun fa yarinta har ga shi mun tsufa,..."Sai dai Na zo goben nagode!"Inji Hajiya Raliya a dayan bangaren.cikin raha da jin dadi"
"Allah sarki,Kuskure kam anyi shi," Hakane Wallahi...."kurciya dangin hauka har kin tuno min da baya...Hajiya" nagode nima Kwarai da gaske sai da safe."
"Allah ya kai mu Hajiya Raliya ta ce tare da katse kiran bayan sun gama sallama da qawarta Hajiya mai gado."
"Itama Hajiya mai gado tana gama waya ta kira layin Aunty zee (qanwarta)Ta ce gobe tazo tana son ganinta."
"Cikin murna Aunty zee ta amsawa hajiya mai gado tare da bata tabbacin zatayi sammako gobe goben." saboda duk zaton ta akan sabgogin auren Minal da Salman ne."
"Hajiya mai gado tana kashe wayar ta koma kan layin My son."
"Bayan ya dauka ya gaidata."
"Amsawa tayi,Kana Ta ce kasa me ni a bedrum idan ka dawo."
"Owk Umma gani nan shigowa yanzun nan ma."
"Kwance suke a makeken bed din kayataccen bedrum din."Ta ce Hello! Nidal ke din dai ashe banza ce wallahi!" yau nai ta Dubin ki shiru!"Ba ke ba labarin ki!"Meyasa zaki min hakan!?"
"Mai da wukar qawata gobe zan zo in shaa Allah, Naso in shigo yau,"Ammi nayiwa rakiya unguwa."kuma na kira layinki baya zuwa!"
"Okay ki gaishetah yanzu gobe ki zo da wuri kinga week din nan ya kamata mu kammala duk wani shiri na mu."
"Hakane Minal amarsu sai nazo din Mrs Dr salman."Nidal tace tana dariya."
"Minal tayi wani fari da ido kamar Nidal na gabanta ta ce kina da kyautar 5k gobe na baki qawata.."
"Ooooh!Kai amma nagode Minal sai mun had'e."
"Okay Bye Nidal Nagode Night!"Ta kashe wayarta ta ce
"Allah ka nuna min an daure auren nan nawa next week."
"Ameen Sisi na juilet uwar soyayya Ilham ta ce tana dariyar minal."
"Pillow ta jefawa Ilham din ta ce kema mun kusa kai ki gidan Dr.jameel Majnun."
"Dariya Ilham tayi tare da juyawa baya,a saman bed din tace to Sisinah Allah ya nuna mana dukanmu.
(A zuciarta ko tausayin Minal takeyi saboda son ma so wani takeyi)"
"Ameen my Sis."
"Daga nan sukaci gaba da fira akarshe ilham waya ta dinga yi da jameel ita ma minal wayar habibinta salman ta kira suka gaisa saboda yanzu suna dan dasawa amma sai dai ita ce ke kiransa da wuya ya kirata!"daga nan mummie ta kira da Daddy suka gaisa kana ta koma online domin sada zumunchi."
"Knocking! Knocking!!
"Bismillah."Bude dakin yayi kana ya shigo cikin dakin da sallama"
"Mummy Ina wuni,lafiya qlaw ya ka ci abinci?"
"Eh, na ci."
"To daman magana nike son muyi ni da kai."kuma ina son ka tattaro min hankalinka da tunaninka anan!"Abinda zan fada maka shi ne ranar assabar idan Allah ya kaimu za a daura aurenka da Minal da kuma yarinyar da kake so wato Salma........"
"Cikin razana da tsoro ya ce Salma fa Hajiya..?"Fuskarsa dauke da mamaki."Da alamar tambaya?"
"Eh,Hakane Salman na nemo maka auren salma kuma na yarda da amince ka aureta domin naga ita ce zabinka!"Kuma ita ce silar ciwon zuciyarka da kake boye min salman!"Ita ce kuma silar kafara yi min boye boye a dukkan lamarinka abinda bai taba faruwa ba atsakanin mu dan hakan naga ya dace ka sameta tun kan ni da ita muyi asarar rasa ka!"Amma kuma wani hanzari ba gudu ba!"Ina da sharadi daya!.
"Kada kaga kasamu zabin ranka kace zaka wulaqanta minal!"Kasani 'yatah ce kuma jinina ce!"Bazan lamunce cutarta!cin zarafinta!"Kada ka kuskura in ji wani sabani atsakanin ku kayi kokarin daidaita adalci atsakanin su!"Fatana Allah ya Baku zaman lafiya!"
"Ameen Umma nagode."Kuma in shaa Allah zanyi kokarin yin hakan!"Dan Allah Hajiya ki yafe min na rufe ki!"Kuma ni yanzu ina jin kunyar fada maki shirina.........!"
"Dakata Salman duk abinda kakeyi dangane da aurenka da salma ina sane saboda tun kafin kaje wurin kawunka da maganar ni naje na same shi da zancen kuma duk abinda kakeyi ina sane domin d'ana Jameel yana sanarda ni."Idan kai boye min kakeyi!"Kavani mamaki wato kai Auren Sirri!"Batare da sani na ba!"Hmnnnnn Dan yau kenan."Kayi kuskuren farko karka soma kayi kwatankwacin sa!"Kaje Na yafe maka Allah shi maka albarka."
"Ameen ummana nagode kuma nasan nayi wauta da kuskure kiyi hakuri dan Allah.. " Salman ya ce fuskarsa dauke da dinbim kunya da nadamar kuskuren da yayi."Ga mamakin iron yadda Hajiya mai gado ta canja nan take."Kara godewa mahaifiyarsa yayi."A kan abinda tayi masa na bazAta."Da hakurin da tayi da iyayen salma wanda batada shi saboda yasan ta sarai batason Jan rai!"Da hakan yayi sallama da cikin jin dadi ya wuce."
"A part dinsa ma baiyi bacci ba sai da ya kira jameel yana masa tsiyar dan iskanci da neman wurin Shiga shi ne ya fadawa Hajiya da hakan dai har suka gama wayar tare da alkawarin gobe zasu hadu."Daga nan Salma ya kira ya labarta mata Hajiya ta yarda da zancen auren su."
"Ta ce masa ai ita tuni tanada wannan labarin na dukkan avinda ya faru tun farko har karshe ta zayyano masa."
"Fushi yayi ya kashe wayar bayan ya gama mata bambami akan ta dan ta rufe shi!"A karshe wayarsa ya kashe ya kwanta yana mamakin zurfin ciki irin na salma gimbiyar mata."Salma kwantawa tayi tana tunanin bahagon halin Salman dinta."
*3:00pm*
"To kin dai ji dalilin kiranki da nayi ke da minal domin in sanarda ku rubutaccen al'amarin da zai faru!"Kuma na amince ne saboda ai masa adalchi kuma lafiyarsa nake duba masa!"Ni kaina ba hakan naso ba Zainab!"Kin ga hajiya Raliya nan ita ce shaidata."Minal Kiyi hakuri ki yarda da wannan kaddarar kinji 'yahtah.......!"
"Dakata hakan ya isa! Yaya mai gado!....sannan ta juya wurin minal da Nidal da sukayi mutuwar zaune cikin zuciya tace ku tashi mu tafi gida!"
"Haba zainab meye haka daga magana.....dan Allah can ki min shiru nayi da ke!?ko na saka ki acikin lanari na!?Saboda tsabar munafunci mai shiga a tsakanin jini daya wallahi Raliya Yanzu nagane wannan duk Sharrin ki ne daman can kina bakin cikina ni da minal baki kaunar ganina da yayata mai gado lafiya to burinki ya cika kin rabamu!"
"Zainab kina cikin hankalinki ita hajiya raliyar ce zakiyawa wannan rashin mutunci!"Inji Hajia mai gado cikin bacin rai!"
"Eh na yarda!kuma na amince banda mutuncin meye aciki dan na cinye na tsohuwar banza...!"Munafuk....!"
"TAtass taji saukar marin da hajiya mai gado ta watsawa zainab ta ce na gane ke baki da kirki kuma ba a maganar girma da arziki da ke!"Duk karamcin da nai maki da wannan zaki saka min zainab!"Meye kikeso ban miki ba!? ni zakiyiwa wulaqanci!"Meyasa kinka cikaa son kai!"Ki tuna tilastawa salman nayi sanadin hakan ya kamu da cutar ciwon zuciya!"Amma duk baki damu ba kanki da minal kawai kinka sani!"Baki damu da rayuwar shi ba!"Meyasa zainab!"Duk irin sonki da kaunarki da nikeyi baki gani!"Meye aibu dan ya hadasu duka ya aure su haram ne..."
"Ba haram ba ne amma ni zainab uwar minal mai qaunarta na haram ta 'yata ta auri salman kuma bazan lamunce zaman ta da matsiyaciya yar mayu ba!" kuma ku fadawa salman ya kyauta!"Yaya mai gado mun gode!"Nidal kuzo mu wuce!"
"Ilham cikin kukah!"Ta ce,Dan Allah Aunty zainab kuyi hakuri bamu taba jin tsakaninku ba!"Kada kiyi fushi kibari asamu masalaha!"
"Ke dallah yimin shiru makira azuza duk shirin da kukayi ai kina sane kinka rufewa minal abin bakin ciki tana zaune da ku acikin gidanku amma