Showing 3001 words to 6000 words out of 23161 words

Chapter 2 - Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

21 Oct 2025

423

Minal ya kike?"

"Lafiya qalaw, wani aiki nake so muyi da ke gobe kizou ina neman ki."


"Okay,Sai nazo."Inji Nidal."


"Nagode sai na ganki minal tace tare da kashe wayar."Wallahi na dauki alkawarin illata ko wace mayya ce!Ko wace sakarai!Banza!Kucakar da Yaya salman ke wulakantani akanta!"Ko 'yar gidan uban wace kasheta zanyi!"Sai dai nima akashe ni!"Lami ce ta katse zantukan da minal keyi azahiri kamar mahaukaciya ta ce,"Anty minal na gama wankin toilet din zan iya tafiya?"


"Mari ta watsawa Lami tace,Har kin isa in sakaki aiki kizo kice min kin gama ni zaki nunawa lokacin wucewarki ya yi!? meye amfaninki?"Idan ba bauta ba?"To kisani ke baiwata ce bakida amfanin kanki sai nawa!" Kuma ki koma acan toilet din ki zauna har sai kinyi awa biyu ki fito."Mtwssss banza yar talakawa da basu da cikakken hankali!"Wuce kibani guri!"Ta fada tana huci!"


"Lami da ke dafe da kuncinta kwallah na zuba a idonta tace ayi hakuri Anty!"Allah ya huci zuciyarki nagode!"juyawa tayi zuwa toilet din shiga tayi ta zauna ciki tare da rufo kofa domin bin umurnin minal!"


"Wadda ko ba komai ta rage zafi da radadi takeji aranta!" tafara rage haushi da takaicinta akan lami da kaddara ta fadawa."


(Ni kuma na ce Allah ya shirya minal da masu rayuwa kamar irinta ta Amin)











BAKAR AKIDA


©TASKAR NABEELA DIKKO


®PEN WRITERS ASSOCIATION




Page 16/20



" _An karbou daga Abdullah d'an umar ,Yardar Allah ta tabbata agare su yace,"Manzon_ _Allah(SAW) ya ce,Kunya na daga cikin Imani."Bkhari da Muslim ne su ka ruwaito."_
_Allah ya sanya mu acikin bayinsa masu kunya Amin_ ."










"To kin dai ji dalilin zuwana Yaya mai gado dole sai mun tashi tsaye akan lamarin yaran nan!"In ji Hajia Zainab(Maman minal)."




"Ba komai mummyn Salman yadda kin ka ce haka za'ayi in ji Hajiya mai gado da ya ke hakan ta ke kiran Hajiya Zainab wato(Mummyn salman)"




"Ki duba ki gani Yaya mai gado wallahi salman idan ba minal ta kira shi awaya ba!"Ba zai kirata ba ko kiran nasa ma tayi sai ya ga dama ya ke d'agawa."Ban da zagi!da cin mutunci ba abinda ya ke mata!"Kullum ce mata yakeyi marar tarbiyya! Batada mutunci da adduni!Mahaukaciya ma Ya ke kiranta."Yanzu a karshe ma ya ce kada ta qara kiran sa a waya!"Ta fita harkarsa saboda ya tsaneta.....!"Yanzu kenan harmu iyayenta yana nufin bamu mata tarbiyya ba!Ni kaina ya daina kirana baya son ganina!"Kamar ba salman nawa ba.......Kuka ne Hajiya Zainab ta saki na kissa tana mai juyarda kanta hannayenta aka tana kukah!"




"Da sauri Hajiya mai gado ta taso daga kan kujerar da take zaune zuwa inda qanwarta ta ke zaune tana kuka!"Ta ce kiyi hakuri mumyn salman!"komai zai wuce idan har ni na haifi salman to bayada mata sai Minal!"




"Dole ne inyi kuka!Yaya kibarni inyi kukana!Tunanin duniyar nan nakeyi da yaran zamani!ace ka haifi yaro yafi karfinka Yaya?"Yanzu ko ni kinka ba umurni zanbi!"Bare Salman!"Ni da ke uwa daya uba daya kuma sun bar duniya da dadewa ynzu ke ce uwa agareni!"Banda kowa banda komai sai ke!"Yaya mai gado kece komai nawa ke da iyalanki!"Amma yanzu ace ni da minal ne Salman ya daurawa kiyayya!"Me mukayiwa salman d'ana da nikeso kuma minal ke so da ya tsanemu?"Me zamu yi masa ya so mu!?"Ni dai tunda bai so abar maganar auren nan Yaya domin mu zauna lafiya!"




"Wannan wane irin zance ne mumyn salman ai aure ba fashi!"Domin bazan. Zauna ina kallo salman ya auro wata bayan 'yatah Minal."



"Bari kiji shi fa wacce ma yake son ba kowa bace ba diyar gidan uban kowa bace agari, 'Yar talakawa ce gaba da bayanta!" marar gata!"Idan kinje gidansu kamar juji!"Ita yarinyar sunanta salma da kaina naje har gidan naga yadda suke rayuwa kamar ba mutane ba!"Naci mutuncinsu tare ja musu kunne akan Salman, babu 'yarsu ba d'ana su nemi talaka ajinsu!"kuma na shaida musu cewa ashirye nake domin sauke musu kwando kwado na cin zarafin su matukar mayyar 'Yar su mai masifar shiga ran tsiya ba ta bar yarona ba!"Ke koni sai da nayi da gaske da ta shiga ran nawa Allah ne ya tsare ni!"Dan hakan Ba zan baiwa salman damar auren wannan yarinyar ba!" ki kwantarda hankalinki!"Na saka ranar auren minaal da salman nan da wata daya!."




"Yaya mai gado kar kiyi masa dole mu dai bishi ahankali ranar da kin kasa kamar tayi kusa sosai!"



"Ba komai Kedai kuje Ku fara shiri aure ba fashi!"Ni zanyiwa minal komai Wanda uwa zatayiwa 'yarta kuma nan zata dawo nice uwarta"Ki turota mufara shiri."Shi kuma dama ya kammala ginin da Abbansa ya fara masa alokacin yana Raye!"Yanzu kudin laife kawai zai bamu muje Dubai mu hado!"Ko kuwa ya kika gani?"



"To Yaya hakan yayi Allah yasa shi ne Alheri ni bari nazo na wuce."Daddyn minal yaje sokoto yau zai dawo."



"To Ameen,
Ki gaishe shi Allah ya dawo da shi lafiya ki ce ina neman minal din."



"In sha Allah zan turo ta Yaya nagode Allah yabarmu da zumuncinmu."



"Ameen,Bari na kawo maki kayan turarukan da nasayo maki wurin Hajiya Uwany Yar Dubai."



"To Yaya nagode sosai sannu da kokari."


"Bayan Anty Zainab ta karba turarukan tayi godiya ta bar gidan zuciyarta cike da farin ciki ta isa gidanta."Matsuwa tayi safiya bata waye ba Dan ta gana da minal dinta!"




"Tun lokacin da Jameel da salman suka bar kofar gidan su Salma."Direct gidan su Dr Jameel Jibril suka nufa a nan ne ya dinga ba shi hakuri!"


"Salman ya ce " Jameel Ina so Ka fahimce ni,"Ina son salma so bana wasa ba!Kuma har na mutu bazan daina son Salma ba!"Da sonta da zan rayu kuma da shi zan mutu!"Jameel ina son minal amatsayinta na jini na kuma qanwata"Amma na tsani halayenta da dabi'unta!"Minal macece marar kunya batada tarbiya bare addini bugu da qari gata da shigar banzah!"Halayenta basu kama da na mata masu mutunci ba bata cancanci zama uwa tagari ba!"Ba tada Da kamun kai ko kadan!"Wannan ne dalili na da bazan iya auren minal din ahakan ba!"Hmnnnn


"Allah Sarki rayuwa yau dan babana baya cikin duniya Hajiya ke son azabtarda ni da auren dole,akan kawai *BAK'AR AKIDA* da suka dauka kamar addini ko al'ada!! saboda kawai salma na diyar talakawa za ace bazan aureta ba Jameel!?"Salma Yarinya ce mai ladabi da biyayya ga sanin girman manyanta."Abinda ke burgeni da ita Addininta da tarbiyyarta kuma nasabarta mai kyau ce!"Dan kawai talauci ne yayi musu katutu arayuwa, kuma mai nema baya da fidda ran samu bamu san me zasu zama ba watarana!"Jameel shin meye aibun salma wanda kagani?"


"Tanada aibu tunda Basu da arziki kuma kasan cewa awurin Hajiya shi ne babban aibu da abin kunya ka auri Yar qaramin gida!"Salman ina son kawai kabi umurninta ka auri zabinta kai hakuri da naka zabin kabi umurnin uwa."In ji Jameel cikin tausayin abokin nasa da duk ya rame ya fita hayyacinsa saboda damuwa."




"Jameel na amince da zabin Hajiyata amma kuma na dauki alqawarin auren salma kul ba dade kul bajima na shiryawa fuskantar komai a rayuwata!"Idan dai kan salma ne!"


"To abokina Allah ya baka Nasara ni kaina ina sonka da yarinyar saboda nutsuwarta kawai dai Hajiya da fushinta nike jin tsoro!"Amma Allah ya samuna hannu muci abinci muje hospital daga nan zan bika gidan in gaida Hajiya."


"Ameen Jameel nagode kaci abincin ni komai bai min dadi ka gama mu wuce!"






BAKAR AKIDA


©TASKAR NABEELA DIKKO


®PEN WRITERS ASSOCIATION




Page 26/30



_"An karbou daga Saubanah (R.A)Ya ce,Manzon Allah(SAW) Ya ce,"Hakika Allah ya la'anci mai bayar da Rashawa(Cin hanci)Da Wanda ke cin rashawa."_

_A'hmad ya ruwaito._









________________________________

"Salman Zaune sai faman gumi yake hadawa duk da kasancewar sanyin A.c na dukan jikinsa!"Tun sanda Hajiya mai gado ta fara magana."


"Kana ya ce to Hajiya Allah ya bani ikon kiyayewa!."


"Kallon gefen ido Hajiya mai gado tayi masa sannan ta ce to Amin."


"Dama abin da zan fada maka shi ne"Na saka ranar aurenka da diyata Minal nan zuwa karshen wannan watan."Ina son ka fara duk wani shiri da ango keyi alokacin aurensa!"Domin aure ne na 'yan dangi auren Yar gata minal."Komai da za ayi na al'ada zan sa su kawunka bala sukai gobe."Kai kuma ka turo min kudin da za'a hada lefe,gyaran amarya da sauran sabgogin da zamuyi da na abokanta!"Bana bukatar wasa acikin lamarin nan Salman !"Dan haka ka nutsu ayi komai yanda zai kayatar ."Kasan cewa wannan Hadi na Ku daga Allah ne tun minal na qarama ta ke qaunarka!"Ina laifin masoyinka kuma dan uwanka jininka!"Kaje ka sameta gobe kuyi shirinku daga nan ka daukota saboda zamu fara shiri ba time saura sati biyu!"Kana iya tafiya!"Sai da safe!"





"Salman kam tun lokacin da Hajiya ta ambaci ranar aurensa da minal kansa ke juyawa ga faduwar gabansa ya tsananta!"Numfashinsa sai fita yakeyi sama-sama!"



"Hawaye ne!Ke zuba a fuskarsa!"A Hankali ya kalleta yace Naji zancenki Hajiya na yadda da umurninki Allah yasa hakan ne Alheri!"Tashi yayi da niyyar fita daga falon."


"Duk da jikinta yayi sanyi tausayin danta namiji tilo ya kamata!"Saboda tana son yaranta sosai kuma ta tsani bacin ransu!"Sai dai ce mashi tayi to Ameen Allah yai maka ALBARKA."


"Ameen Hajiya,Salman ya ce,Ya wuce da Sauri!Ya bar wurin!"



"Ajiyar zuciya Hajiya mai gado tayi da tunanin anya tayiwa rayuwar salman adalci!"Amma kuma a wani gefe dole ne ta tashi tsaye akan lamarin shi!"Dan batason ya kwaso mata suruka Yar talakawa wacce ko aurensa akayi ba zaiyi suna acikin garin Argungu ba, bare ya mamaye kebbi da kasar Nigeria baki daya!"Auren gata shi ne aure inda zakayi bajinta a nuna maka bajinta shi ne aure."Da tunanin hakan ta tashi tabar falon zuwa bedrum."Wayar Ilhaam ta kira ta shaida mata 10:00pm tayi bacci zatayi duk lokacin da ta gama fira da Dr.jameel ta shigo ta rufe falon nasu."Iklhaam ce mata tayi toh!"Tare da datse kiran."




"Agogon Hannunsa ya duba ya ga lokaci na tafiya tashi yayi domin sallama da Babynsa ya ce,My Elhaam sai nadawo gobe kinga dare yayi nasan Hajiya ma kiranki ne tayi ko?"


"Haba Doctor tun yanzu!"Ai Umma cewa tayi na rufe Part dinmu idan na shigo!"Ilhaam tace cikin shagwaba."




"Ya ce kiyi hakuri kin San halin yayanmu(salman) yace da ten zan dinga tafiya ba komai gobe nan zamuyi lunch."sowrie muje in yi masa sallama."



"Okay!"My Mutafi Allah ya kaimu,Rakiyarsa tayi har part din salman amma kofar arufe yayi knocking ba a bude ba, kofar Gam!"Wayarsa ya kira a kashe!"Dr.jameel ya dubi ilhaam yace anya lafiya salman yake?Ba dai fita yayi ba ga kuma motarsa na hango a parking place!"







"Ilhaam tace mtwssss ka kyale shi mana!"my man nasan yana cikin part dinnan nasa Hajiya ce tabata masa rai!" fada tayi masa kan Yaya minal shi ne ya harzuqa ya rufe kan shi!"muje shi acciki!"



"Haba My ilhaam meyasa kike taya Hajiya wurin tilistawa abokina auren wacce baya so!"yanzu Idan aka rabamu kina jin dadine!?"Shin kina da labarin ya kamu da ciwon zuciya mai tsanani!"Wanda akan sa zai iya barin duniyar nan!"Meyasa ke bazaki tausaya masa ba!?"Idan nine ke cikin wannan halin na tsaka mai wuya zakiji dadi ilhaam!?"



"Ta Yaya zanji dadi Baby!? Kaga mu bar zancen bana so kuma ai ni da kai mun dace, amma ita wacce Yaya salman din ke so sam basu dace ba!"Kasan ana son dace da juna!"Me ake da yar tsiya!"Ai matsiyaciya bata dace da zuri'armu ba!"Dan ruwa ba sa'an rariya ba ne!"Shi kuma Allah ya bashi lpia yana son asaramu akan so!"Ni muje har kasa naji ba dadi!"Da haka har suka isa wurin motarsa ya Shiga ya wuce mai gadi ya rufe gida,"Ilhaam part dinsu ta rufe ta fada dakinta domin shirin kwanciya bacci cike da tunanin nasihar da Dr jameel yayi mata akan rayuwar yayanta!"Da tausayinsa da kuma niyyar taimakonsa domin taga yasamu abin sonsa bacci ya dauke ta."




"A hanya ma Dr.jameel na driving yana tunanin wane hali abokinsa ke ciki a gaskiya shi kam yayi tir!"Da wannan BAK'AR AK'IDA ta mutanen wannan zamani ace Dan masu kudi sai yar masu kudi hakan talaka sai dan talaka kwarya tabi kwarya!"Da hakan ya isa gidansu sashensa ya nufa texts din ban hakuri ya turawa Salman kana ya kwanta domin samun Hutu arayuwarsa."






"Gefen salman ko yanda ya ga safe hakan yaga dare domin baiyi bacci ba akarshe nafiloli ya dinga yi domin samun sauki arayuwar sa!"




"Salma ta gama shirinta tsaf!Dan tuni baba ya bata izini"Na tafiya qauyen su Inna Baraka domin ita tana son rayuwar dangin Innarta"Domin suna nuna mata so sosai."Da tunanin tafiyar ta zuwan qauyen felende ta kwanta bacci!"






"Anty Zainab kuwa ta kosa safiya bata wayewa ba domin ta sanarwa minal abin farin ciki."Da murna da zancen ta kwanta bacci."











BAKAR AKIDA



©TASKAR NABEELA DIKKO



®PEN WRITERS ASSOCIATION




Page 21/25


_An karbou daga Abdullah d'an Abbas (R.A)ya ce,"Annabi(SAW) ya ce,Yin kyauta ka koma tamkar kare ne da yakeyin amai daga baya ya lashe abinsa."Bukhari da Muslim suka ruwaito."_

*ALLAH ya sanya mu acikin bayin sa masu kyauta saboda shi Ameen.*











"Hajiya mai gado ce,Zaune akan 3siter ta sha kwalliya sai kamshi takeyi kamar wacce zataje gasa,Da yake macece mai son kwalliya da shigar girma,Hankalinta na kan T.v da take kallon AREWA24 Inda ake shirin nan na HASKE MATAN AREWA da qawarta kuma abokiyar business dinta Hajiya Aisha Falke"Haka kawai jinin su ya hadou har suka zama aminan juna saboda tana yin matar sosai."(Ni kaina matar ina yinta over da dukkan matan Hasken saboda sun tsaya da Kansu sun jajirce agida da waje,Ya kamata mu kama Sana'a mata domin mu kasance Haske aduk in da mu ke.")



"A gidan Hajiya mai gado
Ilhaam ce ke ta waya da Dr.jameel abokin yayanta Salman kuma mijin da take burin aure da zarar ta kammala karatunta nan da 'yan watanni."In da yake sanarda ita suna zuwa yanxun nan shi da mutumen wato Salman."



"Ilhaam tashi tayi ta shiga kichen an gama girki ta hada musu a daning."

"Dakinta ta fada domin ta tsantsarawa Habibinta kwalliya."Dr jameel."




"Dr.Salman ko sai faman mita yakema Dr.Jameel wai ya daina nunawa Ilhaam so da yawa hakan,Shi fa baison ilhaam qaramar yarinya ta raina shi akan jameel saboda bai son raini!"


"Dr.Jameel dariya yayi kana yace haba dai nawan kai ka manta har kuka kakeyi akan wacce ko sa'an ilhaam din batayi ba!"Ai ko ba'ayi ba Ilhaam dina tana bawa salma, 2/3years na kwarai wallahi..."


"Murmushi Salman yayi yace to Dan iska saura ka fadawa Ilhaam!"Kaga ita fa salma ta daban ce wani abu ban ma sanin ina yinsa akanta."




"Hahaha ai kuwa zan fadawa Ilhaam yayanta mayen so ne taima dariya.."In ji Jameel cikin sigar zolaya"


"Aiko da na karye mata kafa na buge mata baki!"Ka ga sai kazo jinya bayan ta daku."




"Haba salman ai bazan fara ba!" mai da wukar wasa nikeyi yanzu dai ka daina matsawa abin kaunata Ilhaam nasan ka baka wasa!"



"Kai yaran sai da hakan ayanzu nine matsayin Abbanmu dole in kula da tarbiyar ta shiyasa bana daga mata kafa da yanzu ta wuce saninka wayewar kawayenta tayi yawa sai da sa mata ido sosai jameel amma ina sonta matuka!"Kasan fa Yar gatan Umma da Abba ce Maryama(Sunan umman marigayi babanmu shiyasa muke kiranta da ILHAAM)


"Wannan kuma gaskiya ne salman ana son hakan Allah ya bamu ikon kulawa da su."



"Ameen suka ce dukan su a daidai lokacin da mai gadi ya wangale musu gate domin shiga cikin gidan."




"Mummyn Minal ce zaune da Abbanta da ya dawo daga sokoto bayan ya ci abinci ya huta ne suke tattaunawa dangane da auren minal da salman da suka da d'ai suna marari,da burin gani."




"Abban minal yayi matukar farinciki da ya samu labarin auren kuma ya bada goyon bayansa 100% akan zancen bugu da qari yasha alwashin shirya shagalin da ba'a tab'a yiwa 'Yar kowa ba a jihar Kebbi da kewayenta saboda zai ba naira kashi!."



"Hajiya Zainab ta nuna jin dadin akan kudin da Abban minal zaiyi facaka da su Idan ransu ya gani"Tasha alwashin ko ita ba za a barta baya saboda dole ta fita kunyar qawayenta ta ayi hidima ta yadawa a mujallu,Dan tun kan shigarta da minal ta alfarma Zasuyi yadda ake yiwa sauran diyan manyan mutane masu hannu da shuni kamar minal."





"Tun lokacin da salma ta dawo daga wurin su salman ta shiga daki tana rusa kuka!"




"Babu abinda takewa kuka!Irin rashin masoyinta mai kyau da kyawawan hali,mai mutunci,tausayi da taimakon al'umma."Sannan ga son sa da kaunarsa da ke addabar rayuwarta!"




"Da sallama Inna Baraka ta shigo dakin rike da kwanon pura a hannunta,Karasowatayi awurin da Salma take kwance ta tasheta furar ta miqa mata ta sha,sannan tace share hawayenki Salmana in shaa Allah,Sai kinga musanya ta alheri agurin ubangiji yana tare da mu kiyi hakuri ki kuma jure!"


"Salma duban Inna Baraka tayi da rinanun idaniyanta da suka kumbura saboda kuka!" tace to inna nayi!"Daga yau na debe salman arayuwata!"Bazan kara sonsa ko tuna shi arayuwata ba!"Ki tambaya min Baba idan zai barni zanje qauyen ku(Felande) inda Gwaggo Hassana in kwana biyu ko na samu nutsuwa.!


"Naji Salma babu damuwa kuma zan sanarda shi ki fara shiri dan nasan Malam zai barki ki tafi!"


"To inna zan fara nagode."In ji salma.



"Allah shi miki ALBARKA ya albarkaci rayuwarki ya sa ki huta duniya da lahira salma."


"Amin Innata, Nagode,Allah ya Baku aljanna kuma."


"Ameen ya rabbi suka fada gabaki dayansu cikin jin dadin addu'ar."





"Dr.Salman da Jameel suka shigo falon da sallama da fara'arta ta amsa musu saboda tana son yaranta sosai musamman Salman da take gani kamar marigayi babansa saboda kamarsu da halayensu iri daya ne."


"Cikin ladabi suka gaisheta yayinda suke shirin zaunawa a 2sitr dukansu, ta amsa musu fuskarta asake."



"Hajiya mai gado ta tambayi Dr.jameel ya gidan nasu"


"Ya ce, mata lafiya lau."



"Ihaam......"

"Hajiya ta kira awaya tace tazo ta kawowa yayyenta abinci."


"Cikin material red riga da siket da Dan qaramin gyale red Ikhram ta fito kayan sun amsheta sosai kuma sun kame jikinta da kyar take tafiya sai qamshin Arabian perfumes(Sadat,Taiba,Burhan,Oud) ke tashi ajikinta."A hankali ta qaraso wurin su ta gaishe su."



"Dr.jameel ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login