Showing 21001 words to 23161 words out of 23161 words

Chapter 8 - Bakar Akida Part 1 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

21 Oct 2025

417

"Barrister minal maina ce zaune tsakar qawayenta ta sha kyau har ta gaji!"Da ganinta kasan cewa dalolin naira ne kwance ajikinta domin "ance ido mudu ne" ko da ba'a fada ba zai auna."Haka ma Nidal da Ilhaam sunyi kyau sosai da sauran abokan su duk sun zo."Sai ciye-ciyen kayan dadi sukeyi kafin time din dinner yayi da abokan Dr.salman suka shirya musu."





"Hajiya Zainab Maina zaune cikin matan abokan mijnta da danginta su Sa'adatu hannatu hafsatu da sauda dai sauran yan uwa da abokan arziki."Sai faman hidima sukeyi cikin jin dadi yayinda Hajiya Zainab ke boye damuwarta kada mutane su fahimta domin akan dole ne ta aminta ba dan ranta ya so ba!"



"Hakan dai ta faru akowane bangare shagalin buki buduri sukeyi."




"Kawu Bala sai kwasar wasa wasar buki akeyi yana d'aga kwalbar fanta sama..."Bakinsa kamar zai tabo kunne kan dadi saboda ya samu kudi sosai wurin su Salman."



"A gefen salman din ma sai san barkah domin abokan sa sai tsiya suke masa suna kiransa da mijin Mace biyu."Shirin sukeyi sosai domin zuwa daukar amaren aje dinner."



*8:33 PM*

"Salma ce gurfa ne agaban Babanta da inna suna yi mata huduba mai ratsa jiki da zuciya!"Ba abinda takeyi sai rera kuka!"Mai tsuma zuciyar mai sauraro!"Inna ce ta katse mata tunani!"Da ta ce kin ji duk abinda mukace da ke salma ina so ki rike su kuma ki Santa su azuciyarki kada ki dauki Munanan halaye da *BAKAR AKIDA* wadanda ba irin naki ba!"Kin ga dai salmanu yayi miki komai a rayuwa ba abinda bai saya miki ba agidanki duk da ba hakan mukaso ba,Amma ya hana muyi maki komai ,dan hakan kiyi biyayya Allah ya Baku zaman lafiya Ameen."


"Baba ya ce yanzu kuje bala da larai suyi mata nasiha da gwagwanninta da iyayenta Kinji Baraka kuma zan tsaya abakin kofar gida no zan kai ki salma gidanki da kaina ba wani wuri na Bidi'a da zakije dan bazan aminta da ayimaki walima dazu da Yamma sannan yanzu ace zakije wurin kidi sam ba zai sabo ba!"



"Inna Baraka ta ce"To Malam za ayi yadda kace tashi muje salma."Tallafota tayi tana share mata hawaye suka wuce!"


"Sashen Kawu bala Gwaggo Hanne ta wuce da salma yayi mata huduba sosai"Daga nan ne tace to larai ga salma ta zo neman gafararki"A dakile tace Amara Allah ya raki taki gona ya yafe mana!"Larai tace tare da shigewa dakinta!"Kawu Bala yace ke hanne Ku tafi abinku Allah ya ba su zaman lafiya kubarni da ja'ira mai baqin hali!"Hanne tace to Yaya Habu mungode Allah ya nuna manager nasu karime."Ya ce,"To Amin Sai kun dawo."Tuni suka dauki haramar barin gidan bayan nasihohin da yan uwa da abokan arziki sukeyi ma salma."



"Babu yadda abokan salman basuyi da babanta ba! amma fir yaqi!"Yace bazataje dinner ba dole suka hakura suka kai salma a Katafaren gidanta."


"Gefen ango Dr.salman ko sai faman bude ido yake domin yaga ta ina zai ga sarauniyar mata salma zata fitou."Sai dai kash!Minal ya hango kamar wata queen da abokanta suna biye da sauran danginsu abayanta haka Hajiya mai gado da abokanta sun sha ado da gwalagwalai da gani ba sai an fada ba kasan cewa wannan Bukin na 'yan gata ne masu arziki ."



"An gyara wurin ya sha kyau wato Dancing Arina Argungu,"Kujeru ne na alfarma aka ajiye,Domin zaman manyan mutane maza da mata kayan makulashe ne ajiye agaban su."A kan higher table ko zance bai faduwa domin wurin ya sha kyau da ado,"Dr.salman ne atsakiya gefen daman kujerar da aka tanada domin salma ne abokinsa Dr.jameel ya zauna gefen hagun shi minal ce zaune sai wani shan qamshi takeyi tana jin dadin labarin da suka samu akan salma bazata zo ba!"


"Anyi dinner mai kyau wadda ta qayatar." makada da mawaqa sun baje kolin su anyi liki da naira dollars har Europe an mannawa ango da amarya, iyayensu sai barin kudi suke sun nuna bajinta sosai masu hoto sai aikinsu sukeyi yan mata ko sai selfie akeyi ana daurawa a whsup istagram fcbuk twnter,da sauran su tun kan kace kwabo auren Dr.salman da Barrister minal ya bazou a duniya kowa sai yaba auren yakeyi da koda irin dukiyar da aka kashe musu."Da hakan aka watse misalin 12am na dare."Hajiya mai gado tayi ma danta nasiha sosai da abokanta had minal duk an musu huduba ba sannan suka wuce a hanya yayi umurnin afara kai shi gidan salma."Sai dai abin yabawa minal mamaki kar dai ananufin salma ce uwargida!"


"Kallon shi tayi sannan tace Yaya me zai hana ni ka saukeni agidana naga kai ka hana kowa ya biyomu domin dare yayi sosai kuma nafi salma shekaru ka ga ai nice babba a kanta!"


"Salman ya kalleta ta gefen ido."Ya ce kiyi hakuri minal,"salma ta riga da ta shiga gabanki domin tayi kusan awa hudu agidana."Kuma amatsayin mata ta,"kinga ta rigaki shigowa gidana ita ce uwar gidana."Saboda haka kiyi biyayya kawai a zauna lafiya."



"Hawayen da take kokarin maqalewa ne ke zuba a idonta kamar an bude famfo tace Yaya salman meyasa bazaka kai ni gidana ba!? sannan ka tafi gidanta!"Kasan cewa haka zakayi min ka hana kowa ya biyo bayan mu."


"Bazan kai ki gidanki ba sai na tafi da ke gidan yayarki!"Inji salman."Cikin fushi tare da Daure fuskarsa!"


"Da hakan suka isa gidan salma,Kowa da abinda yake tunani akai!"Sun sameta zaune afalonta tana share hawaye! Sunna t.v take ta kallon tun bayan tafiyar yan uwanta!"Da sukaji da jiran angwaye suka wuce!"Kamar daga sama tagansu tafe cikin tsoro!Ta miqe tsaye saidai ganinsu yasa taji sanyi gaida su tayi aladabce tare da tarbar su."Kallonta yayi daa tausayi Yace amaryata sannu da zaman kadaici kowa ya watse an barmunke ke daya!"Kiyi hakuri kinji tunaninki kawai nikeyi Bakomai mujina tace cikin sanyin murya!"



"Daga nan nasiha yayi musu sosai tare da alqawarin yin adalci atsakanin su."Sannan ya ce minal ta tashi ya sauketa gidanta ya dawo!"Minal ta cika sosai irin yadda salman ya gyare gidan Salma kamar 'yar wani da wata."A karshe kuma ya bata muqamin zama uwar gidansa."Da hakan har ya sauketa agidanta tare da Jan kunneta sannan yabar gidan."Hakan ta kwanta cikin baqin ciki da bacin rai tare da alqawarin daukar mummunan mataki akan salma!"
________________________________

"Bayan watanni al'amurra sai tafiya sukeyi budi da haske sai qara shigowa yakeyi acikin rayuwar salman."



"Hakan Rayuwar matansa normal sai dai babu zaman lafiya atsakanin su.Sam ko magana basayi bare biya juna dan minal tafi karfin salma acewarta!"Tuni Hajiya mai gado ta shirya da qanwarta da yan uwanta."Yayinda minal tana fita aikinta kudi na shigota ta ko ina tazama babbar mai kudi kuma sawon farko na manyan matan garin na ARGUNGU ana damawa da ita,"Aunty Zainab abin nema ya samu!"Sai baza rashin mutunci sukeyi ita da minal dinta." ita kuma salma tana business sai dai har yanzu babu abinda take fuskanta ga yan uwan mijinta sai zagi,da kyara,da gorin arxiki!" A kullum cikin kuka Take domin *BAKAR* *AKIDAR* su ta hana su yadda da ita kuma su zauna da zuciya daya ita minal kowa ke so!"Daga Maman salman da qanwarsa ilham sai shi kadai ne takejin dadi da sassauci tare da su!"Hakan ta cigaba da hakuri da taimakawa iyayenta."



"Salman ya ginawa iyayen salma katafaren estate mai Babban get daya yayi kyau matuka gini kalar na qasashen waje ba zaka ga abin burgewa sai an shiga daga ciki tamkar aljannar duniya."Inna baraka da Malam an murje kurciya ta fito sunyi kyau sosai ashe daman talauci ne ya mayar da su tsofaffi!" .A cikin estate din duk yan uwan Malam ne suka dawo ciki da zama sai dai part din Iyayen salma yafi na kowa kyada tsaruwa akwai masu gadi masu baiwa flowers ruwa drivers yan aiki da sauran ma'aikata."Part dinKawu Kawu Bala ma ba laifi komai ya wadace su shi da matansa,Dan ya auri wata malamr islamiyya Ayshatou suna zaune lafiya da abokiyar zamanta"Tuni Larai tayi laushi ta gane hanya kuma ta tuba."Domin ta fahimci duk arzikin da suke ciki ayanzu albarkachin salma da iyayenta ne."Yanzu komai tana yiwa inna baraka cikin jin dadi."Karime ko tana gidan dan ummaru suna zaune cikin tufin asirin Allah.


"Anyi shagali Auren Dr.jameel da Engr.Maryam(Ilhaam) da dadewa ta tare gidanta da haduwarsa ma bazai fadu ba da me unguwar lowcost Argungu,"Suna zaune lafiya da mijinta."Nidal qawar minal ma tayi aure a garin sakkwato."Tashin hankalin da minal da mahaifiyarta ke ciki bai wuce salma nata haihuwar yan biyu har sau biyu ta farko maza ne Muhammad,da mahmood,ta. biyu mata Nabeeha da Nabeela."Amma ita har yanzu ba amo ba labari!"Dalilin hakan yasa suka tilastawa Dr.salman da yayi iya kokarinsa domin ganin ya sama mata magani !"Amma basu gani sunce dole sai an fita waje anyiwa minal dashe!"Ta haihu!Saboda duk duniya ba wacce suka tsana irin salma da yaransa!"Dole salman ya amince shi Hajiya ba dan ransu ya so ba!"Aka fita da minal qasar India."Anyi aiki kuma an samu Nasara minal tasamu juna biyu sai wani kaudi da iyayi akeyi duk wani shiri anti."Saboda suna son ayi sunan da ba'a taba irinsa agidan Dr.salman ba."


"Lokacin haihuwar minal yazo daya da salma inda ta haifi d'a namiji minal ko C.S akai mata inda tasamu baby girl."sai dai minal ko 'yartah bagani ba Allah yayi mata rasuwa!Saboda wuya da azaba da wahala!"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!!!Mutuwar minal!"Ta razana kowa duba ga irin shirin da sukayiwa sunan idan ta haihu!"Aunty Zainab da Hajiya mai gado da salman sunyi kukan rashin minal sosai da sauran dangi 'yan aikinta ma sunji ba dadi falmata da lami duk da bawani jin dadinta sukeyi ba amma kudin da suke samu ne abin bakin cikin su"Bayan sadakar arba'in yarinya taci sunan Zainab ana kiranta da (mimah)Shi kuma yaron salma yaci sunan Marigayi Taheer (Mu'allim)Sai dai mima na hannun Aunty Zainab tana bata madara."Ba yadda salman baiyi da ita ba dan abawa salma ta hada mimah da mu'allim ta dinga shayarda su amma tace sam ba za'a gurbata mata jinin jika da gubar talauci da tsiya ba!"Haka ya hakura ya barta hannun Aunty Zainab din, tare da nuna mata so da kauna da kulawa saboda yana jin tausayin marainiyar yarsa Mimah mai kama da mamanta minal!"Fatan shi kada ta biyo halayen mamanta duk da tuni ya yafe mata."Domin Sam minal batasan darajar aure ba!"Bata iya komai sai dai yan aikinta suyi!"





*BAYAN WASU SHEKARU*

"HAjiya salma ce zaune acikin hadadden gidan su da Ambr.Mahmood Salman ya Gina musu."Yanzu ta zama hamshakiya uwar manyan mutane masu ji da kudi."Domin Mahmud shi ne Ambassador na Nigeria, Muhammad ko comisioner of police, Sai Dr.Nabeela da Nabeeha ta zama International business woman."Duk Kansu sunyi aure an fara tara iyalai." "Mima da mu'allim suna saudiya suna karatun Islamic shar'ah low."


A yanzu family *GALADIMA KO MAI WALDA* sune family da yayi sunan kudi ciki da wajen Nigeria saboda yawan kamfanoninsu,Gidajen sayarda man fetur, super market, da sauran ababen kasuwanci makarantu,Asibitoci,gidajen marayu Da sauransu."Malam Abu Sufyan mai walda An zama kakan alhazai da hajiyoyi duk shekara sai sunje Hajj da umrah kawu Bala naira ta zauna sai kasuwanci yakeyi shi da yaransa."


"Hajiya Zainab taga iznah!"Da dadewa tagane gaskiya kuma tayi nadama akan *BAK'AR AKIDA!* Irin tasu ta banzah!Yanzu daga ita har mijinta basuda komai tunda yayi ritaya da jimawa kuma minal ta bar duniya asirin su yaso ya to no sai dai diyan salmar da suka tsana!A yau su ne suka tufa masu asiri suka tallafa masu ta hanyar dauke duk wasu lalurorin su da na sauran danginsu baki daya."Su saudat ancigaba sosai domin tana shiri da salma kwarai."Hakan Yaya Hafsa da sa'adatu an bi hanya angane gaskiya tuni suka nemi gafarar Hajiya mai gado da salma domin anyi laushi biye ake Ana cin arzikin salma da yaranta."Dama can BAKAR AKIDA CE ta rudesu ta bata masu tunani."


"Yanzu kam duk masu tsanar salma akan tana 'Yar matsiyata sun tuba sun gane gaskiya kuma sun tabbatar samu da rashi duk na Allah ne, shi ke bayarwa alokacin da yaso ya kuma aminche!"Da talaka da mai arziki duk daya ne agurinsa!"Shi ke maida mai arziki talaka ya kuma mayar da talaka mai arziki."Dan ayanzu sun ga zahirin gaskiya."Hajiya Salma Dr.salman a yanzu batada matsala tana zaune da kowa lafiya Dama can batada problem da kowa tsakaninta da kowa alheri."


"Ya kamata mutane masu irin wannan *BAKAR AKIDA* Su gane gaskiya akwai aure atsakanin mai kudi da talaka."Wani auren kwarya-tabi-kwarya ko bani-gishiri in baka manja ba alheri ba ne!"Da macen da namijin duk nagari masu nagarta yafi dacewa a aura."Masu nasaba mai kyau ilimi tarbiyya gaskiya da amana masu riko da addini."Kalubale gareku iyaye masu iron wannan Dabi'ar."
"ALLAH YA SA MUGANE AMIN ,ALLAH YA SA MUTANE SU AMFANA DA HALAYE DA D'ABI'U MASU KYAU, ALLAH YA YAFE MIN KURAKUREN DA NAYI ACIKIN WANNAN RUBUTUN DA NA BAYYANE DA NA AIKATA , AMIN."













*TAMAT BII HAMDILLAHI*

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login