Showing 6001 words to 9000 words out of 23161 words
amsa mata sai faman kallonta yakeyi saboda ba karya ta hadu."
"Dr.Salman ko harara ya watsa mata saboda shidai ya tsani irin saka banzan kayan nan da takeyi."yace,ke lafiya kika zo kika wani tsaya mana hakan wuce zuwa saka Hijab!"
"Cikin tsoro da fargaba!"Ta ce tou! daman Yaya salman abincinku ne!"Yana dining....!"
"Okay,Jameel Bismillah muje muci abinci."Tashi sukayi dukan su zuwa dining place."
"Baki Ikhram ta tunzura cike da takaicin yayanta salman!"Ta nufi wurin Hajiyar tace Umma kina jin wancan bagidajen wai nasa hijab kamar wata malamar allo!"
"Tsaki Hajiya mai gado tayi tace,barni da shi bakisan takaicin da ya bani ba!"Ga shi daman shi nike jira yafi son ya ganki kamar bagidajiyar yarinyar da yake so!"Meye acikin hijab banda zafi!"Mtwsssa ki kyale shi!"
"A'ah Umma kinsan da zarar yazo yaga ban sa ba zai min fada agaban abin so na!"Umma kinga yadda naje da hankalin da Dr.jameel na burge shi amma shi wancan yana son kwafsa mana!"In ji Ilhaam.
"Bakomai Auta na(Ilhaam) zan hana shi takura miki in dai kan wannan shigar taki ne saboda nima kin burgeni gaskiya telan nan ya fidda ke sosai kamar wata balaraba zan Baki 5k kikaai masa goron dunkin nan."
"Kai Ummana zaiji dadi jibi yayi min Wanda yafi wannan duk da na biyasa kudin aikinsa amma yaba kyauta tukuici nagode Umma."
"Suna cikin firar ne su salman suka dawo bayan sun kammala Dinner dinsu."
"Bayan sun zauna Hajiya tace ke Ihaaam ku kuma dayan falon keda Jameel zanyi magana da Yayanki."
"Okay Umma,Ikharam tace cikin jin dadi suka bar wurin ita da Dr.jameel."
"Salman yace Hajiya kina fa gani hijab nace tasaka kafin ta tafi, hakan zataje
Kamar wata bamaguza!"
"Kai dataka!"Kasan batada tarbiya da kamun kai shiyasa zataje hakan!"ka fita idona in rufe!"Nasha fada maka kadaina takurawa Auta!"Amma bakaji to bamaguzar ce!"Kuma hijab bazata sa ba!"Ni na hanata Dan ba ta'aziyya ko Islamiyya zataje ba!"Dan ba ku maza ke sawa ba!"kasan yadda yake da takura!"Naga dai ba bare agidan nan, daga Ni sai kai da kuma abokinka ne,Kuma kai da shi tun kuna yara kuke tare yasan kurciyar Ikhram duka, kuma aurenta zaiyi ka ko ga ai anzama daya!"To waye acikin mu Autanah zata sawa hijab!"Ka fita harkar 'yahtah na gaya maka!"
"To Hajiya Ayi hakuri."Salman yace cikin ladabi."
"Naji!Kasan dalilin tsayarda kai nan!"
"A'ah Hajiya.........."
"Magana zamuyi kuma umurninah ne ba shawara nike nema va bana bukatar comment dinka ko guda!!!!!........."
BAKAR AKIDA
©TASKAR NABEELA DIKKO
® PEN WRITERS ASSOCIATION
Page 31/35
_Wannan page na Ku ne, Masoyan Nabeela Dikko Novels, ina ganin sak'on Ku abin da yawa shiyasa ba kowa nakewa reply ba, amma nagode sosai da kulawa, na samu tsaikon typing sanadin zazzabi da nayi na kwana biyu amma_ _Alhamdullilah na samu sauqi sosai na kuma gode da addu'oinku da fatan alherin Ku agareni, kusani ina tare da Ku,A duk inda Ku ke kuma kwarin gwuiwar da kuke bani shi ke kara sa ni ina sanbadou muku novels masu ma'ana,Ba na mai da hankali kan soyayya a novels dina manufar rubutuna nikeso ku gane Ku dauki darasi mai kyau acikinsa Nagode Nagode Allah ya bar zumunci Ameen._
________________________________
"Misalin karfe sha biyu da rabi na rana "Minal ce zaune a katafaren falon ta ita da mummynta su na tattaunawa bayan mummy ta bata labarin yadda sukayi da Hajiya mai gado sarai."
"Minal taji dadi ba kadan ba kuma ta nuna farin cikin ta tare da jinjinawa mummynta bisa ga kokarinta domin ganin ta samu farin cikin ranta wato Yaya salman."
"Mummy kara kwantar mata da hankali tayi tare da alqawarta mata irin shagalin da za ayi alokacin auren na su."
"Murnar minal ta qaro ta ce agaskiya mummy ina alfahari da samunku da nayi amatsayin iyayenah kuna so na matuka."
"Babu komai Minal idan bamu so ki ba wa zamu so?Ke kadaice Allah yabamu amatsayin 'ya kinga dole muyi kaffa kaffa da rayuwarki bamuson abinda zai dameki bare ya bata rayuwarki ko menene Minal dina,"
"Okay mummy yanzu zamu fita ni da Nidal Nasir zan bi ta gidansu mu wuce."
"Ina za ku tafi Minal naga baki cika fita da wuri ba idan ba office zakije ba?"
"No mummy karki da mu idan muka dawo zakiji."
"To Allah ya tsare ki gaida Umman minal din."
"To mummy zan fada mata bye!"Minal tace tare da daukar keys din motarta da glass dinta ta wuce."
"Hajiya Zainab ko tashi tayi tabar part din minal da tuni 'yan aikinta suka fara gyarawa ta wuce nata sashen cikin jin dadin ganin minal ta sake sosai."
"Salma ta shirya tsaf acikin wata yar kodaddiyar atamafar ta super java orange da hijab dinta har qasa tayi kyau matuka"Kayanta ta ke cusawa acikin wata jikka(Gari yayi zafi)Babanta kawai ta ke jira suyi sallama ta wuce Filende."Inna Baraka ko sai faman sakon gaisuwa ta ke ba salma zuwa ga yan uwanta da dan tarkacen kayan yaji da tsintsiyar sharar daki tace akaiwa qannanta."
"Da kwantancen da Akayiwa Nidal har suka karaso kofar gidan bayan tayi parking ne ta kalli Nidal fuskarta dauke da mamaki tace Anya Nidal bakiyi batan kai ba!"Kin ko gane gidan sosai nifa tunda muka shigo unguwar nan nake kwankwanton da gaske ne Danbasaja yayi miki aikin kwarai kar dai address din sa na karya ne dan kawai yaci kudin Mu ne."Minal ta fada cikin mamaki!"
"Hmnnnn....kawata kenan wallahi Danbasaja bai min hakan duk iskancinsa yana tsoron nawa dan yasan banda mutunci zanyi masa wankin babban bargo nan ne dai gidan da mukasa shi aiki akai Minal !"
"Mtwsssss nan ne gida ai ko mahaukata ba zasu iya rayuwa anan ba!"Ni kinga ki fara shiga daga ciki idan nan ne kiyi flash dina!"Bazan iya shiga wannan banzan gidan ba Kada ma mu dauki wata cuta aciki!"In ji minal cikin jin haushi!Da takaicin abnda take tunani!"Azuciyarta!"
"Okay bara ni na Shiga din nagani ko nan ne ." Nidal tace ta fita motar ta zarce zuwa hanyar shiga cikin dan akulkin gidan."
"Inna Baraka na cikin daka taji motsin mutum batare da ta dago kanta ba, tace haba salma ba dai har kin gaji da jiran Malam din ba kiyi hakuri tunda yace ki jirasa mana kila Ma wani dan abu ne zai saya yabaki ki qara ga tsaraba!"
"Mtwssssss duk da gidan naku kamar na mahaukata hakan ashe har abubuwan da ke ciki suna da cutar hauka!Ba zanyi mamaki ba dan naji kina magana ke kadai dan na karanta tun akofar gidan naku "Nidal ta ce cikin gadara."
"Inna Baraka tabarya ta fitar cikin turmin tace baiwar Allah daga ina cikin mamaki da tsoro?"
"Ke malama kiyi min shiru ba wurin ki Nazo ba nan gidan su Salma sufyanu mai walda!?"
"Eh!"Nan ne ni ce Innarta kar dai laifi tai miki?"Inna tace cikin sanyin murya saboda daga ganin shigar Nidal tasan batada mutunci dan kamar ba yar hausawa ba."
"Fine good tsohowa ki kirata batayi min laifi ba magana kawai zanyi da ita in ji Nidal sannan ne ta dannawa qawarta minal kira ta ce ki shigo nan ne gidan nasu ta maida wayarta ajaka!"
" Inna Baraka tace bari in kira maki salma, jikinta na tsuma ta fara kiran sunan Salma ."
"Hankali salma ta amsa tare da kinkimo jakarta saboda taji magana awaje ta dauka Ko Baba ne ya dawo tafiyarta ta tashi."Sai dai me wata mai kama da kabila ta gani tsakar gidan tsaye!"A jiye Jakarta tayi a gefe."
"A hankali ta qarasa wurin da Innarta ta ke tsaye ta ce Inna lafiya!?"
"Lafiyar ce zata kawo mu wannan makararran gida a bahagon tunaninki na dabbobi ko ban tambaya nasan ke ce Salma!"Sannu 'Yar matsiyaci da matsiyaciya!"A Jere ta zubo wadannan magangannu kafin ta karaso!"Minal Kenan."
"Haba malama ya zaki shigo mana gida ko sallama babu kuma cike da magana maras dadin ji bare sauraro!"In ji Salma cikin bacin rai tana kallon su!"
"Dariya Minal tayi tare da karewa gidan kallo tace wannan ne gidan!?Aini wallahi na dauka ma gidan ajiye gawar mahaukata ne!"To bazamuyi sallamar ba bamu iyaba sai ki koya mana!"
"Inna ta ce kuyi hakuri bayin Allah kunga bai kamata ku shigo har gidanmu ba sallama ba maganarki sannan kuce zaku ci zarafin mu shin daga ina kuke?Me ke tafe da Ku?"
"Minal cire glass din idonta tayi ta kalli inna da salma da ke tsaye ta watsar sannan ta maida glass din mazauninsa tace Ashe dai tsohowar nan kina da sauran hankali da kinka iya tambaya wadda ta dace!"
Sunana Minal ni ce Matar da Dr.Salman zai aura nan da sati biyu nazo in muku kashedi ke da yarki ance min Ku mayu ne idan kun kama Baku saki!"To kusani kurwar yayanah Salma tafi madacci daci!"Daga yau babu ke ba mijina idan ba haka wallahi zansa a batarda ke a duniya!"Kisani salma nafi karfinki haka ma Yaya salman yafi karfin 'Yar tsiya Ahlil kwakwaf irinki!"Kije ki nemi dan talakawa kamar ke ki Aura!"Ni minal nice zabin salman kuma ajinsa ba ke ba banza ballagaza!"Narasa me ya gani yake so in banda kaddara an magancesa daga talla watakil!"
"Tabbas haka yake qawata inji Nidal sannan ta karasa wurin Salma ta dafata ta ce"Malama Salma wannan umurni muke baki ba shawara ba!"Wane karambani ya kaiki ga mannewa dan masu Arziki saboda kwadayin abin duniya!"Ki duba acikin fadin qasar nan tamu ta Nigeria gaba daya atarihin auren 'ya'yan mayan mutane duk auren bani gishiri in baka manja akeyi haka gefen talaka sai talaka to akanki kike son afara auren kunya da takaici!"Auren da ba za'a iya wani abun azo agani ba!"Gwara tun wuri ki kama gabanki kije can ki nemo mudi ko tanko ki aura dan Dr.Salman na Brr.Minal ne ita kadai idan ba haka ba daga ke har iyayenki zaku hadu da Bala'i da cin mutuncin da zai iya zama ajalinku.....!"
"Hannu Salma tasa ta kabe hannun Nidal da ta aza a kafadarta cikin fushi ta ce Wallahi kunyi kadan kuma ta Allah ba taku ba!"Kusani kunyi kadan Ku shigo gidanmu kuyimana abinda kukaga dama!"Ni ban damu Salman ba ku ya dama da har zaku zo fada da rashin mutunci akan shi kuma shi ke bibiyata !"Shi ke so na!"Kuje Ku masa fada ya daina sona!"Sannan kisani ke Minal dukan da nayi maki yafi wanda zakiyi min har abada!"Ni zuciyata kika daka saboda ki gayamin magana mai zafi!"Amma ni rayuwarki na daka inda baki ganin ciwo bare ki magani!"Na lura son maso wani kikeyi to kisani sona da kaunata sun riga da sun zama jinin jikin Salman."Duk da kasan cewar ina diyar talakawa amma a hakan nayi tagomashi da farinjini awurin shi duk dukiyarsa yace yana sona!"kuma Ina da masoya ban taba maular masoyi ba bare tada harshe na akan shi, nagode Allah!"Kuma har gobe ina qara gode masa da baiyi min kwakwalwa irin ta jahilan dabbobi ba, da bazan iya bambance tsakanin Kaddara mai kyau da marar kyau ba, Alhamdulillah mu talakawa ne kuma muna alfahari da jarabawar ubangiji kuje diyan masu arziki da za'a saku kabari da arzikin Ku....!"
"Taaataasss!!taas!Salma taji saukar marin da minal ta yi mata cikin fushi!"Har ta daga hannu ta rama tayi daidai shigowar Babnta sai ta fasa!" da sauri ya qaraso yace subhanallahi!"Baraka lafiya?Me salma tayi musu!?"Salma ban yadda ki daki kowa ba acikin su kiyi hakuri!"
"Salma da ke dafe da kuncinta tana zubda hawaye ta ce toh Baba!"
"Dariya sukayi suka tafa minal tace haba tsoho ai idan yarka ta tabani to da baki dayanku sai kun mutu agidan kaso dan ba wanda ya isa ya fito da Ku!"
"Ke kuma kashedi zan miki na karshe kisani idan ina magana ba'a mayar min da martani ko martani masu zafi ki kiyaye ni, kuma ba ke ba mijina, banza! mai bin maza! 'Yar iska! matsiyaciyar banza!"Minal tacewa Salma." ta kalli Baba da Inna da ke zugum suna sauraren su tace nadawo kan ku"Tsoho da tsohuwa nasan......."
"Da sAuri ya karaso wurin....Yaya Habu shin lafiya mukaji hayaniya na tashi inji kawu tare da su karime ko wanne lungu na gidan kowa ya fito yayi tsaye suna kallon minal da Nidal cikin shigar su ta rashin mutunci!"
"Minal cigaba tayi da maganarta ina son kujawa yarku kunne tafita da harkar mijina Dr. Salman nasan kuna sane yafi karfinta amma saboda kwadayi da son abin duniya kunka kyaleta!"
"Kawu Bala ya amshe maganar minal yace"Hakane wallahi sai da na fadawa yarinyar nan da Yaya habu ku fita harkar yaron nan mai kudi kun kace shi ke bin salma Ai ga irinta nan dama ance kwadayi mabudin wahala!Azo har gida aci mutuncin mu!""Dan Allah kuyi hakurii...!!!Dakata Bala suwa zaka ba hakuri wadan nan yara marasa tarbiyya da mutunci!"Kufita Ku bamu wuri marasa kirki yara!"Baba yace ranshi abace."
" Jakarta ta bude bandir din kudi yan dari biyar ta dauko da batasan yawansu ba ta jefawa Kawu Bala cikin gadara da sauri ya capke kada sukai kasa," Tace goronka ne na fadin gaskiya kai kuma tsoho meye acikin gidan ko dai kango ma," ai wannan baikai darajar akira shi da gida ba!"Zamu tafi amma kasani yarka ce marar mutunci ba mu ba!"Mu tafi Nidal tsaki Sukayi suka wuce su ka bar gidan."
Kawu Bala har yaso yabisu yacewa minal ya gode da wadannan dambun kudi da tabashi amma yana tsoron Yayansa saboda ya ga ranshi ya baci matuka!"saurin Barin wurin yayi kowa ya bishi saboda kudin da yasamu suma araba da su!"
"Salma barin wurin tayi tana kuka!"Dan anci mutuncinta da na iyayenta amma ta dauki alkawarin sai ta ramaabinda Minal tayi mata tunda har Salman na sonta to aikinta da kudurinta zaizo da sauqi!"
"Inna baraka ko kayan salma ta duka ta kwashe ta shiga cikin dakin tana share hawayenta!"
"Baba ko Alwala yayi yabar gidan zuwa masallaci saboda aduk sanda ranshi ya baci can ne wurin zuwansa sai ya huce ya dawo gida!"
BAKAR AKIDA
©TASKAR NABEELA DIKKO
® PEN WRITERS ASSOCIATION
Page 36/40
*"An karbou daga Abih sA'idul khuduriy (R.A)Ya ce,"Annabi Muh'd (SAW) ya ce"Hakika Mafi sharrin mutane,Masu mummunar masauki agurin Allah ranar Alkiyama sune wadanda mutane suka guje musu saboda yawan ayyukan su na Alfasha(Marasa kyau)."Bukhari ya ruwaito."*
________________________________
"A hanyar su ta komawa gida sai murna sukeyi suna shewa saboda sunyi abinda ransu ke so."
"Nidal ta ce,"Kin san Allah minal magangannun da kika yiwa baban salma sun min zafi saboda haka kawai naji ya bani tausayi!"
"Mtwsssss amma ke Nidal anyi sakarya shi talaka maras gata kuma uban makiyiyar ta wa!wadda na tsana aduniya zakice kin tausaya masa!"Kenan har salmar kina so kuma kina tausayi ko!? saboda naga so yana tare da tausayi!"Minal tace tana duban Nidal cikin tuhuma! tare da sauraren amsar da zata bata."
"Haba!Qawata ta yaya zan so salma?Kawai a lokacin da kike musu madifa ne sai naga kamar bamu kyautawa iyayenta ba!Domin ba laifin su ba ne,Laifin na Salma ne!"Amma ya wuce ai mun musu horo mai shiga zuciya bazasu manta da mu ba kuma bazasu qara Shiga gonar mu ba!"Ko ba komai Barazanar mu zata hori kwadayin su."
"Atou Ni har kinsa nafara jin haushin ki saboda na tsani salma da duk wani da zai so ta wallahi!"
"Ni kinga ma abin haushi da takaici da yafi tsaya min arai bai wuce wancan bagidajen ba wato Yaya salman shi kuwa wace bacewar basirace zata sa shi ya so wannan kucakar dabbar yarinya da bata wuce ko sa'ar Suhaima ba (Qanwar Nidal) ni duk na raina ajin shi da miskilancinsa!"Abin ban takaici!"Da ban haushi wai akanta ma ne yake wulaqanta yake cin zarafina!"Na dauki alkawarin illatah banzan nan matukar bai fidda ita a rayuwar sa ba!"Sai naga bayanta, Nidal!"Qarashe maganar minal tayi muryarta na rawa yayinda ta qara gudun motarta saboda bacin rai!"
"Kiyi hakuri qawata komai ya zo karshe ke da Salman mutu ka raba!"Ba wani banza dan banzah da zai raba ku!"Ai yar gata sai dan gata Tawan."
"Murmushin jin dadi Minal tayi,Domin maganar Nidal tasa taji sanyi aranta da hakan suka cigaba da firar su a hanya suka tsaya *Marhabah Super market* suka sayi ice cream da sauran kayan makwalashe suka wuce abin su zuwa gida cikin jin dadi."
"Salman ne zaune a office dinsa duk wunin ranar bai ayyana aikin komai ba, fa ce tunanin sahibar sa Salma, babu abinda yake kona masa zuciya, irin yadda Salma tai masa gatanga da gidan su."A hakan yayi zaune da dakon tunaninsa inda agefe ga patients na ta jiran sa amma ya ce anema musu wani doctor shi baya jin dadi da hakan yayi sallama da amininsa Dr.Jameel,"Shi kuma yayi haramar komawa gida har ya kama hanyar gidansu amma kasa jurewa yayi karya kwanar da zata sada shi da unguwar su Salma yayi domin bazai iya jure rashin ganin ta ba na tsawon mako biyu!."
"Tsaye yake a kofar gidan,"Bayan ya aika yaro a sallamo masa ita a zuciyarsa yana fargaba kar dai tace bazata fito ba!"Yana cikin zancen zucin ne sai ga yaro ya dawo"Wai tace bazata zo ba kuma kayi hakuri ka koma inda ka fito"Yaron ya ce yabar wurin!"Subhanallah!"ya fadi afili me na miki salma da zaki yi min wannan danyen hukunci... !"
"Ba salma kayiwa laifin ba Salman mahaifiyarka da matarka da dukkan danginka kayiwa laifi da kake neman dauko cuta ka kai acikin zuri'ar Ku!"Baba ne da tun fitar su minal da yaje masallaci bai dawo ba sai yanzu ya ba Salman amsa.!"
"Kamar daga sama Salman yaji zancen Baba abin yazou masa wani iri!"A ladabce ya durkusa ya gaida Baba cikin nutsuwa da sanyin jiki ya koma irin kalar tausayi nan!"
"Amsa masa Baba yayi kana ya ce"Ina fatan lafiya Salman saboda ina so ka fita hanyar 'yatah Salma kaje ka rike matar da zaka aura!"Ka bi umurnin mamanka ka cikawa danginka burin su domin *BAK'AR AK'IDAR* su bazata barsu ka auri wacce zuciyar ka ke so!"Domin haka bakai ba salma!" Kasan kafi karfin salma Mu talakawa ne ba masu arziki ba!"Kuma Salmata bazata iya zama acikin daula ba, saboda bata taso acikinta ba!"Abin da nikeso kaja motarka kabar mana kangon gidanmu yanzu matarka da qawarta